Daga Laraba

News HA ↓ 254 episodes

Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan jin ta-bakin wadanda abin ya shafa.

Category

News

Podcast website

www.buzzsprout.com

Latest episode

Jul 8, 2026

Where to listen?

Podcasts in the app Replaio Radio Coming soon

Podcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts

Get it on Google Play Install for free Android 5M+ downloads · 4.8 rating iOS soon

Episodes

Yadda Iyaye Ke Lalata Da ’Ya’yan Cikinsu 16.11.2022

Shirin Daga Laraba na wannan lokaci ya dubi yadda matsalar lalata tsakanin iyaye da ’ya’yansu ko tsakanin yayyu da kanne ta zama ruwan dare ne. Mun tattaro bayanai masu nuna yadda kwamacalar take kara kamari a wannan zamani.

Yadda Yi Wa Kananan Yara Fyade Ya Yadu A Arewacin Najeriya 09.11.2022

Me ya sa ake yawan samun mutane masu manyan shekaru da ke afka wa kananan yara mata ko mazayarinya ko karamin yaro? Shin wane dalili ke sa kawo yawaitar wannan kazamar dabi’a ta lalata da kananan yara? Shirin Daga Laraba ya dubi yadda wannan matsala ta zama ruwan dare, musamman a Arewacin Najeriya. A yi sauraro lafiya.

Abin da kishi ke sa maza aikatawa 02.11.2022

Duk lokacin da aka ambaci zafin kishi, to da dama mata ke zuwa zukatan jama’a. Shin yaya maza ke kishi, kuma me suke iya aikatawa saboda tsananin kishi? Shirin Daga Laraba na wannan mako ya tattauna da masu ruwa da tsaki game da tsananin kishin maza, abin da yake iya sa su da kuma yadda ya kamata a yi kishin.

Yadda Masu Aure Suka Zama Mazinata A Najeriya 26.10.2022

Ana samun korafe-korafe game da yaduwar zinace-zinace tsakanin ma’aurata a Najeriya?  Shin me ya faru ma’aurata suka tsunduma ka’in-da-na’in a harkar alfashar da a baya an fi dangantawa da marasa aure marasa kamun kai? Shirin Daga Laraba na wannan mako ya tsananta bincike da  tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan wannan batu domin gano inda gizo ke saka, domin fid-da jaki daga duma.

Yadda Aka Zalunce Mu A Bainar Jama’a, Amma Kowa Ya Kau Da Kai 19.10.2022

Taimakon juna na daya daga cikin hallayyar da ake kwatanta mutane masu nagarta da shi, amma a yanzu abin yana neman zama tarihi. Shin me ya sa taimakon juna ya yi karanci a wannan zamanin? Saurari labarin wadansu da aka zalunta a gaban jama’a amma ba a kawo musu dauki ba. Mun kuma tattauna da masana kan yadda aka tsinci kai a halin rayuwar ba ruwan kowa da kowa.

"Mun Ci Karfin Aikin Zaben 2023" - Shugaban INEC 12.10.2022

Shirin Daga Laraba na wannan mako ya tattauna da Farfesa Mahmood Yakubu, Shugaban Hukumar INEC, kan zaben 2023 da ke tafe. Shin kana bukatar sanin inda INEC ta kwana kan shirye-shiryen zaben 2023? Saurari shiirn Daga Laraba na wannan lokaci.

Yadda Yawan Harsuna Da Kabilun Najeriya Zai Amfane Ta 05.10.2022

Wata kididdiga da jaridar Vanguard ta fitar a 2017 ta bayyana cewa akwai kabilu da ke amfani da harsuna 371 a fadin Najeriya. Ta yaya wadannan kabilu za su fahimci junansu su zauna lafiya har su amfani kansu da kasarsu? Saurari cikakken shirin Daga Laraba domin jin yadda masana da ’yan Najeriya suka bayyana hanyoyin da za a bi wurin cudar guna da man jikinta.

Yadda ‘Sakacin Ma’aikata’ Ke Lakume Rayuka A Asibitin Murtala 28.09.2022

Zargin sakaci da rayukan marasa lafiya, musamman mata masu ciki a Asibitin Kwararru na Murtala da ke Kano ya karade kafafen sadarwa a ’yan kwanakin nan. Ana zargin yadda ma’aikatan asibitin ke nuna halin ko-in-kula da rayukan jama’a na sanadiyyar mutuwar mata da jarirari kusan kowace rana. Shin me ya sa asibitin Murtala ya yi kaurin suna haka a wurin jama’a? Shirin Daga Laraba ya tattauna masu kor...

Tashin Hankalin Da Samari Ke Ciki Amma Suke Boyewa 21.09.2022

Samari na daga cikin mutanen da ba a cika damuwa a san abin da ke ci musu tuwo a kwarya ba. Amma shin kun san irin mawuyacin halin da matasa maza ke ciki kuwa? Akan dauka cewa halin da suke ciki ba abin damuwa ba ne, kuma bai dace su nuna gazawarsu ba, ballantana har su saki jiki su nema ko a ba su shawara kan matsalolin da ke addabar rayuwarsu. Shirin Daga Laraba na wannan mako ya yi nazari mai z...

Yadda Shawarwarin Zamantakewar Aure Ke Gudana A Kafafen Sada Zumunta 14.09.2022

Cigaban da aka samu a bagaren sadarwar zamani ta sa abubbuwan da ake yi a zahiri yanzu an koma yin da yawa daga cikinsu ta kafafen sadarwa, ciki harda cinikayya da kuma shawarwari kan zamantakewar rayuwa da na auratayya.  Shin wadanda ke da irin wadannan  shafukan kwararru ne kuwa, wace irin nasara a ke samu in an dauki shawarar, ko kuma dai barna a ke yi mai-makon gyara? Shirin Daga Laraba na wan...

Yadda Abincin Da Ake Yawan Ci Ke Iya Zama Guba 07.09.2022

Dan Adam na rayuwa da cin abinci da shan abin sha daidai bukatar jikin.  Shin wane abinci ne jikin dan Adam ya fi bukata, kuma a wane lokaci?   Lura da yadda cututtuka sanadiyyar abinci ke kara yawaita, shirin Daga Laraba na wannan mako ya dubi batun abinci da ababe shan da ake mu'amala da su yau da kullum, domin neman mafita kan yadda za a gujewa kamuwa da cutuka sanadiyyar abinci 

'Yan Ta'adda Na Fada A Ji A Najeriya. 31.08.2022

Yawaitar ta'addancin 'yan bindiga a Najeriya ya sa 'yan kasar sauya tunaninsu da yadda suke rayuwa.  Shin sauya tunani da yadda ake rayuwa a Najeriya domin tsoron ta'adancin 'yan bindiga mafita ce kuwa? Shirin Daga Laraba na wannan makon ya dubi yadda kasashen da suka ci gaba ke yakar ta'addanci da yadda 'yan kasar ke magance matsalolin ta hanyar kin sauya yadda...

Yadda Rabon Gado Ke Neman Zama Tarihi 24.08.2022

Rabon gado a wurin musulmi tarbiyyace da ta samo asali a cikin addinin, amma a yanzu magada da dama na kukan yadda 'yan uwansu ke cinye musu gado da aka bari kafin a raba ko kuma in an raba. Ko kun san dalilan da ke sa a cinye gado a wannan zamanin kuwa?  Shirin Daga Laraba na wannan mako ya dubi irin mawiyacin halin da rabon gado ya stinci kansa a ciki, wanda ke jefa magada da dama cikin tas...

Kayan Mata: Gyaran Jiki Ko Janyo Ciwo? 17.08.2022

Maganin mata da aka fi sani da kayan mata ya samu karbuwa a tsakanin mata musamman na Arewacin Najeriya.  Amma wai da gaske ne waɗannan hade-haden da mata ke sha wani lokacin kuma su yi kunzugu dashi na amfanin da ake saya domin sa? Shirin Daga Laraba ya bigi jaki ya bigi taiki, domin kuwa ya tattauna da masu hada irin wadannan magunguna da masu saya, da ma wadanda ake saya domin su da kuma likito...

Kamen ’Yan Arewa: Shin Lokacin Daina Ci-Rani Ya Yi? 10.08.2022

’Yan Arewacin Najeriya akalla 200 ne ke tsare a hannun jami’an tsaron yankin Kudu maso Yammcin Najeriya (Amotekun), cikinsu har da fasinjoji 19 da suka shafe wata 10 a tsare. Shin Amotekun halastacciyar kungiya ce a Najeriya kuma tana da harumin tsare ’yan kasar haka kawai? A shirin namu na yau, za ku ji halin da ’yan Arewa da Aamotekun ta tsare suke ciki da matsayin doka a kan kungiyar da kamen d...

‘Ina Sayar Da Kwalaba 1,000 Na ‘Kurkura’ A Mako A Zariya’ 03.08.2022

Shin da gaske ne ‘Kurkura’ na maganin basir, ko dai shigo-shigo ba zurfi ake yi wa jama’a su fara shaye-shaye? Kurkura wani magani mai guba da kuma sa maye nan take idan an zuba shi a baki. Sai dai kuma duk da haka, yana ci gaba da samun kasuwa a tsakanin jama’a musamman a Arewacin Najeriya da sunan maganin basir da karin kuzari. Shirin Daga Laraba na wannan makon ya yi wa wannan batu duba na musa...

Daga Lahadin Nan INEC Za Ta Rufe Rajistar Katin Zaɓe 27.07.2022

Hukumar Zabe ta kasa, INEC; za ta rufe Yin rajistar katin Zabe ranar Lahadin nan Mai zuwa, wato 31 ga watan nan na Yuli. Idan za a iya tunawa hukumar Zaben ta kara wa'adin yin rajistar katin Zabe na wajen wata daya. Amma duk da haka, jama'a da dama na korafe -korafen cewa lokacin bai ishe su ba, tunda har yanzu akwai mutane adadun da ba su yi rajistar ba. Mun tattauna da 'yan Najeri...

Dalilan Da Daliban Kano Ke Yawan Faduwa Jarabawa 20.07.2022

Ko me ya sa harkar ilimi, musammam a Arewacin Najeriya sai kara tabarbarewa yake yi, har yana neman mutuwa? A makonnin baya, mun kawo muku yadda harkokin ilimi ke tafiya a jihohin Bauchi, Kebbi, Sakkwato da Zamfara. Yau ga mu a Jihar Kano, inda muka yi tankade da rairaya kan yadda dalibai ke yawan faduwa jarabawar kammala sakandare ta WAEC da NECO da kuma JAMB, wadda ake zanawa domin sharar fagen...

Matsalar Tsaro Da Rashin Tsari Ne Suka Kara Ruguza Ilimi a Zamfara 13.07.2022

Idan ana biye da mu, a cikin shirin Daga Laraba na makon jiya, mun tattauna ne a kan harkar ilimin jihar Sakkwato, a wannan makon kuma, mun tabo harkar ilimin jihar Zamfara ne. Ilimi aka ce shi ne gishirin zaman duniya, amma idan ba ilimi, sai jahilci ya yi katutu. Masana da masu ruwa da tsaki a harkar ilimin jihar Zamfara, sun alankanta rashin tsaro a matsayin matsala ta farko kuma babba da ke ci...

Halin Da Harkar Ilimi Ke Ciki A Jihar Sakkwato 06.07.2022

Idan ba ku manta ba, makonni biyu da suka gabata, mun tattauna ne a kan tsarin ilimin Jihar Bauchi da na Jihar Kebbi. A wannan makon kuma mun karkata ne zuwa kan tsarin ilimin Jihar Sawkwato. A yayin da ilimin daliban firamare da sakandare ke tabarbarewa, iyaye da malamai na kokawa kan irin kalubalen da baganren ilimin jihar ke fuskanta. Laifin waye kuma ina mafita? Shirin Daga Laraba ya tattauna...

Ainihin Halin Da Harkar Ilimi Ke Ciki A Jihar Kebbi 29.06.2022

Batun lalacewar harkar ilimi a Jihar Kebbi ba sabon labari bane a kunnuwan 'yan Najeriya, musamman batun daliban da ke jarrabawar sharar fagen shiga jami'a. An jima ana kwarmata batun lalacewar gine-gine da rashin kwararrun malamai da kayan koyarwa a jihar, domin samar da ilimi mai inganci. A wannan karon, shirin Daga laraba ya yada zango a bangaren ilimin Jihar Kebbi domin bankado irin...

Halin Da Karatun Boko Ke Ciki A Jihar Bauchi 22.06.2022

Rahotanni kan halinda makarantu da karatun boko ke ciki a Jihar Bauchi na cigaba da janyo takaddama a tsakanin jama'a. Biyo bayan sabbin tsare-tasren da gwamnatin jihar ta kawo. Wadanne tsare-tsare ne wadannan da jama'a ke tattaunawa akansu, kuma ta wadanne hanyoyi suka shafi rayuwar jama'a. Shirin Daga Laraba na wanna mako ya yada zango a Jihar Bauchi domin binciko gaskiyar abinda...

Yadda Cin Zarafi Da Bidiyon Tsiraici Ke Zama Ruwan Dare 15.06.2022

A yan shekarunnan amfani da bidiyon tsiraici domin cinma burika ke neman zama ruwan dare a cikin jama'a. Mene ne akayi ba dai-dai ba har wannan dabi'a ta samu karbuwa  a tsakanin matasa da wadansu manyan? Mun tattauna da masu ruwa da tsaki domin gano bakin zaren. 

Alakar Matar Gida Da Dangin Miji 08.06.2022

Sau da dama ana samun rashin jituwa tsakanin dangin miji da matar dan uwansu, a wadansu lokutan ma har ya kai ga ya shafi 'ya'yansu.  Daga ina matsalar take, sannan me ake yi ba daidai ba?  Mun tattauna da masu ruwa da tsaki domin neman mafarin wannan fitina da kuma hanyoyin da za a bi domin warware ta. 

Jikoki A Hannun Kakanni Tausayi Ko Cutarwa? 01.06.2022

Mutane da dama na tura 'ya'yansu wurin kakanninsu da sunan ziyara ko su zauna su rayu dasu da sunan taimakon kakannin.  Anya taimako ne kuwa? lura da yadda rainon mutum yake da wahala, kaiwa mutum mai shekaru raino ba janyo sabuwar wahala  bane?  Shirin namu na yau ya mayar da hankali akan wannan dabi'a. mun tattauna da wadansu kakanni da kuma malaman addini domin sanin gaskiyar abi...

Listen to the Daga Laraba podcast in Replaio

Radio and podcasts in one app - free, with no sign-up. Install today and do not miss the launch

Get it on Google Play

Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.