Daga Laraba
Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan jin ta-bakin wadanda abin ya shafa.
Where to listen?
Podcasts in the app Replaio Radio Coming soonPodcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts
Episodes
Yadda ’Yan IPOB Suka Kashe Mai Tsohon Cikin Da ’Ya’yanta 25.05.2022 30:29
A cigaba da ayyukan 'yan ta'addan IPOB a Kudu maso Kudancin Najeriya, yan kungiyar sun kai farmaki yankunan da Hausawa ke zaune inda suka hallaka wata mata mai dauke da cikin wata tara da 'ya'yan ta hudu a Isolo dake Jihar Anambra. Bayan nan rahotanni da muka samu sun nuna cewa a kasa da awa 24 bayan kashe matar nan da 'ya'yanta, yan haramtacciyar kungiyar sun sake ka...
Yadda Za A Magance Matsalolin Matasan Arewa 18.05.2022 29:45
A makon da ya gabata mun binciko matsalolin matasan Arewa da kuma dalilan da aka bar su a baya. A shirinmu na wannan karon mun tattauna da wadansu matasan yankin, wadanda da suka san matsalolinsu da kuma maganin matsalolin. Matasan sun bayyana ainihin abin da ke hana su ci gaba, sun kuma bayar da shawarwari kan hanyoyin da za a shawo kan matsalolin nasu.
Dalilin Da Muka Bar Matasan Arewa A Baya 11.05.2022 30:01
Yara manyan gobe, inji Hausawa; amma anya matasan Arewacin Najeriya sun samu damar zama manyan goben yadda ya kamata? In aka yi la'akari da halin da matasan Arewan ke ciki, wani abin tambaya shi ne, ko dai su a yarintar za su kare? Me ke kawo musu wannan tarnaki? Shirin Daga Laraba ya tattaro fahimtar masana da matasa kan ababen da ke mayar da matasan Arewa koma baya.
Anya Akwai Ranar Da Za A Wayi Gari Ta'addancin 'Yan Bindiga Ya Zama Tarihi A Najeriya? 04.05.2022 29:53
Ta'addancin 'yan bindiga ya zamo ruwan dare a Najeriya. Domin babu nau'in da ba a gwada irinsa a kasar nan ba. Anya akwai ranar da wannan ta'addanci zai zamo tarihi kuwa? Mene ne ya kamata ayi domin a gaggauta kawo karshen ta'addanci, wane ne ya kamata a sa a gaba domin neman mafita, mene ne ake yi daidai kuma mene ne ake bukatar a gyara? Mazauna yankunan da 'yan ta...
Yadda Za A Magance Matsalar Tsaro A Arewacin Najeriya —Masana 27.04.2022 29:57
Rashin tsaron da ya addabi yankin Arewa maso Yammacin Najeriya na nema ya gagari kundila. Mene ne ake yi ba daidai ba, wa ya kamata ya amsa tambayoyin da jama'a ke yi kan yadda za a warware matsalolin tsaron? Masana sun yi wa Shirin Daga Laraba na wannan makon bayani kan hanyoyin da suka dace a bi domin warware matsalar da ta ki ci, ta ki cinyewa .
Kokarin Da Gwamnati Ke Yi A Yakar ’Yan Ta'adda 20.04.2022 29:56
Yawan hare-haren da ’yan ta’adda ke kaiwa kan jama'ar da ba su ji ba, ba su gani ba a jihohin Katsina, Zamfara, Sakkwato, Kebbi, Neja da Kaduna, ya sa shakku a zukatan ’yan Najeriya bisa kokarin da Gwamnati ke cewa tana yi. Shirin Daga Laraba na wannan mako ya binciko irin kokarin da gwamnatin ke yi a matakin kasa da jihohin da abin ya fi shafa.
Abin Da Muka Gani A Dabar ’Yan Ta’adda 13.04.2022 30:09
Satar mutane domin karbar kudin fansa ya zama ruwan dare a Najeriya. A wane hali mutanen da ake sacewa ke tsintar kansu a hannun masu garkuda da mutane da kuma bayan an sako su? Shin yaya wadanda ke satar mutane ke tunani?
Barnar Da 'Yan Bindiga Suka Yi A Arewa Maso Yammacin Najeriya 06.04.2022 30:24
A makon da ya gabata, cikin shirin Daga Laraba mun kawo muku bayanin asalin ta'addanci a Arewa maso Yammacin Najeriya, inda kuka ji yadda abubuwa suka faro daga Jihar Zamfara A wannan karon, shirin ya bankado irin asarar rayuka da dukiyoyin da aka yi da kuma yadda zamantakewa ta lalace tsakanin jama'ar wannan yanki a sanadiyyar ta’addancin ‘yan bindiga.
Asalin ta’addanci a Zamfara 30.03.2022 31:10
Jihar Zamfara ta yi suna a duniya a shekarar 2000, sanadiyyar kaddamar da shari’ar Musulunci. Jama’a sunyi ta zancen Jihar da sa albarka, suna kuma kallon ta a matsayin wani wuri da za a samu wanzuwar adalci saboda abinda ake sa ran wannan sabon tsarin mulkin zai tabbatar. Sai dai a baya-bayanan, Jihar ta tsinci kanta a bakin jama’a a wannan karon ana tir da abinda ke fitowa na ta’addanci da duk...
Ina Makomar Masu Yada Labaran Karya A Lahira? 23.03.2022 24:51
Makonni biyar ke nan da shirin Daga Laraba ya fara fede biri har wutsiya kan batun labaran karya domin gano asalinsa da masu amfana da shi da masu yadawa da kuma amfanin da su ke samu. Yadda Ake Gane Labaran Karya ne batun da shirin Daga Laraba na makon da ya gabata ya mayar da hankali a kai. A wannan makon kuma shirin ya karkata ne kan Irin Kallon Da Addini Ke Yi Wa Labarin Karya. Mun tattauna d...
Yadda Ake Gane Labaran Karya 16.03.2022 30:06
Ta wace hanya mutum zai gane labarin karya a kafar intanet ko kuma a kafofin sada zumunta? Wani lokaci bambance labaran karya abu ne mai sarkakiya ta yadda hatta amintattun kafafen yada labarai kan fada a tarko, su dauke su a matsayin sahihan labarai. Tambayar da ke yawan ci wa jama’a da dama tuwo a kwarya ita ce, ta yaya mutum zai gane labarin karya? Shirin Daga Laraba na tafe da bayanan hanyoyi...
Hanyoyin Da Illar Labaran Karya Ke Shafar Jama'a 09.03.2022 28:50
Makwanni biyu da su ka gabata mun karkata akalar shirin Daga Laraba zuwa batun labaran Karya. Mun dubi wadanda ke yadashi da masu kir kirarshi. A wannan karon, mun tura shirin gaba ta yadda mu ka dubi tasirin da illar labaran Karya ke haifarwa jama'a. Mun tattauna da masu yada labarai ta intanet, da 'yan siyasa da kuma masana a wannan fage domin fede biri har wutsiya.
Yadda ’Yan Siyasa Ke Yada Labaran Karya Don Su Ci Zabe 02.03.2022 27:27
Labaran karya sun samu wurin zama a fagen siyasa, kusan ko’ina aka leka za a iske ’yan saiya na gudanar da harkokinsu ta hanyar amfani da labaran kanzon kurege a matsayin hanyar neman magoya baya da kashe farin jinin abokan hamayya. Shirin Daga Laraba na wannan karon ya yi nazari kan yadda ’yan siyasa ke amfani da kafafen sada zumunta wurin yada labaran bogi domin sace zukatan jama’a da kuma kayar...
Ungulu Da Kan Zabo: Yadda Labaran Karya Ke Buya A Tsakanin Al’umma 23.02.2022 31:40
Galibi idan aka ambaci labaran karya abin da ke fara zuwa zuciyar mutane shi ne soshiyal midiya, wato kafofin sadarwa na zamani. Amma ko masu sauraro sun taba tunanin cewa yayin hira a majalisa ko teburin shayi, wani ka iya ba da labaran da basu da tushe balle makama? Shirin Daga Laraba na wannan makon na tafe da karin bayani
‘Yadda Masu Kwacen Waya Suka Kashe Dan Uwana Bayan Sun Illata Ni’ 16.02.2022 30:13
A shirin Daga Laraba da ya gabata kun ji ta bakin wani karamin yaro mai kwacen waya da ya kashe mutum uku, ya raunata wasu akalla 25 sannan ya karbe wayoyi da dama. A yau kuma za ku ji yadda wata baiwar Allah ta safe wata 10 tana fama da irin lalurar da ta samu a sakamakon harin da masu kwacen waya suka sumar da ita sannan suka kashe dan uwanta.
Yadda Masu Kwacen Waya Ke cin Karensu Babu Babbaka A Kano 09.02.2022 28:54
Waya na daya daga cikin abubbuwan da ake saurin sacewa amma a fakaice, saboda in a ka kama barawon waya, to yana dan dana kudarshi. Sai dai wani babban abun mamaki shine yadda birni kamar Kano, mai yawan al’umma da tarin jami’an tsaro, ya tsinci kanshi a cikin mawucyacin hali saboda aika-aikar masu kwacen waya a bainar jama’a dare da rana Shirin Daga Laraba na wannan mako, ya zaga birnin Kano domi...
Yadda labaran karya ke hana ruwa gudu a rayuwar al'umma 02.02.2022 30:43
Samuwar fasahar sadarwa ta zamani ta fadada damar da mutane suke da ita ta samarwa da kuma yada labarai ta hanyoyin zamani musamman kafofin sada zumunta. A hannu guda kuma hakan ya haifar da fantsamar labaran kanzon kurege da a wasu lokuta suke yin illa ga mutuncin jama'a har ma da tayar da zaune tsaye. Shirin Daga Laraba na wannan karon ya bankado yadda aka fara samun labaran bogi, wadanda...
Waiwaye: Yadda Rufe Hanyoyin Sadarwa Ya Shafi Harkokin Kasuwanci 26.01.2022 28:37
Wayar tarho da intanet sun kama hanyar zama jinin jikin al’umma a wannan karni na 21. Alakar mutane da harkokin sadarwa ta zamani ta sa kusan harkokin kasuwanci sun tasamma komawa intanet, a wasu lokutan kuma ana amfani da wayar tarho ne wurin assasa harkokin kasuwanci da kuma tabbatar da su. Shirin Daga Laraba na wannan mako ya yi waiwaye kan irin halin ni-’yasun da harkokin kasuwancin suka shig...
Hanyoyin Warware Matsalolin Bayan Jefa Kuri’a 19.01.2022 23:59
So da dama bayan an kammala jefa kuri’u, masu zabe kan dakata su ga abin da zai ture wa buzu nadi – suna kasawa su tsare, a kirga, a kuma sanar da sakamako. Hakan na faruwa ne saboda wasu matsaloli da kan kunno kai bayan an gama kada kuri’u, wani lokaci har a yi ta kai ruwa rana. Don haka masu zabe ke son su san ko ’yan takarar da suka zaba sun kai bantensu. Shirin Daga Laraba na yau za ku ji irin...
Yadda Za A Magance Matsalolin Ranar Zabe 12.01.2022 30:31
’Yan Najeriya na fuskantar matsaloli da dama a lokacin zabe, musamman ranar zabe, duk kuwa da cewa za a iya magance matsalolin idan aka bi hanyoyin da suka dace. Shirin Daga Laraba na wannan makon, ya zakulo irin matsalolin da ake fuskanta a lokacin zabe da kuma hanyoyin da za a bi domin warware su.
Matakan Yin Katin Zabe Domin Kawo Sauyi 05.01.2022 29:48
Zabe na yi wu wa ne idan a kwai masu zabe, nan da watanni 13 za’a gudanar da babban zabe a Najeriya. Shin kun san yadda zaku yanki katin zabe? Idan kun sauya unguwa ko gari wadanne hanyoyi zaku bi wurin karbar sabon katin da zai baku damar zabe a duk inda kuke? Shirin Daga Laraba na wannan makon ya tattaro bayanan matsalolin da a ke fuskanta wurin yankar katin zabe, da hanyoyin da za’abi wurin war...
Yadd kuri'arku za ta iya sauya rayuwarku 29.12.2021 29:12
Tun da aka dawo mulkin Dimokuradiyya a Najeriya a 1999, yawan masu kada kuri’a sai raguwa yake ta yi, ko mene ne dalili? Anya masu zabe sun san irin karfin da kuri’arsu take da shi kuwa? Shirin Daga Laraba na wannan lokaci na tafe da amsar wannan tambaya har ma da bayanin amfanin zabe da muhimmancinsa wurin kawo sauyin rayuwa mai ma’ana. A yi sauraro lafiya.
Karfin Ikon Talakawa A Dimokuradiyyar Gaskiya 22.12.2021 34:45
An fara mulkin dimokuradiyya ne a Karni na 17 bayan kafa kasar Amurka, jim kadan bayan juyin juya hali. Shi ne tsarin mulkin da ya bai wa ′yan kasa damar fadin yadda suke so a mulke su. Hakan ta sa suke da damar tofa albarkacin bakinsu a harkokin gwamnati ta hanyar wakilansu da suka zaba zuwa majalisu a matakai daban-daban. Shirin Daga Laraba na wannan karon na kunshe da bayani kan nau’ikan tsari...
Illolin da rashin kaunar juna ke yi wa mata 15.12.2021 31:08
A shirin Daga Larabar da ya gabata, mun yi duba ne a kan Dalilan Da Mata Ba Sa Kaunar Junansu. A kashi na biyu da za ku saurara a wannan karon kuma, shirin ya mayar da hankali ne kan yadda rashin kaunar juna a tsakanin mata ke hana musu ci gaba a fannoni da dama na rayuwa. A yi sauraro lafiya.
Dalilan Da Mata Ba Sa Kaunar Junansu 08.12.2021 30:29
Mata na yawan ambaton kansu da zumunci a tsakaninsu har sukan bugun kirji da cewa ‘ciwon ’ya mace na ’ya mace ne.’ Amma a zahiri ko takarar siyasa mace ta tsaya, ’yan uwanta mata ke fara yaƙarta kafin maza? Me ya sa kishi ya yi yawa a zukatan mata har ba sa iya bari mijinsu ya auro kawarsu su zama abokiyan zama? Ina ciwon ’yan macen? Shin ko’ina haka abin yake, ko a Najeriya ne kadai? Shirin Daga...
Similar podcasts
Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.