Daga Laraba
Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan jin ta-bakin wadanda abin ya shafa.
Where to listen?
Podcasts in the app Replaio Radio Coming soonPodcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts
Episodes
Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya A Najeriya 08.07.2026 24:57
An daɗe ana muhawara, musamman a Arewacin Najeriya, a kan buƙatar yin garambawul ga tsarin makarantun tsangaya. A baya dai waɗannan makarantu kan samar da mahaddata alqur’ani waɗanda kuma sukan dogara da kai Sai dai a wannan zamani, yaran da suke karatu a ƙarƙashin tsarin sun zama mabarata. Gwamnatoci da dama dai sun yi kokarin yin garambawul ga yadda ake gudanar da tsarin, amma ga alama haƙa ta...
Yadda Almajiri Ya Rikide Ya Zama Mabaraci 01.07.2026 29:35
A zamanin nan, ana alakanta almajirai da bara – hasali ma a lokuta da dama akan yi amfani da kalmar “almajiri” idan ana nufin mabaraci. Amma a da ba haka lamarin yake ba – almajiri bay a bukatar yin bara ko roko kafin ya sami na sakawa a bakin salati. Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi nazari ne a kan yadda almajirci ya sauya salo a wannan zamani da ma irin halin da almajirai suka tsinci kan...
Tarihin Almajirci A Kasar Hausa Da Yadda Yake A Da 24.06.2026 24:13
Kalmar almajiri ta samo asali ne daga yaren larabci wato almuhajir, dake nufin wanda ya bar garin sa don zuwa wani gari neman ilimi. Mafi yawan alummar arewa inda akafi sanin Kalmar sun taso ne sun ga ana gudanar da karatun allo ko almajirci, wanda hakan ke nufin almajirci ya samo asali ne tun lokacin da musulunci ya fara shigowa Najeriya daga garin Maidugurin Jihar Borno zuwa kasar Hausa. Shirin...
Yadda Shara Ke Neman Binne Manyan Biranen Najeriya 10.06.2026 27:44
Tururuwar da mutane suke yi zuwa manyan biranen Najeriya na barazana ga wadannan alƙaryu ta fuskar tsaftar muhalli. Misali, wani rahoto da Bankin Duniya ya fitar ya nuna cewa a duk sa'a daya birnin Legas kan yi baƙi 77 – hakan kuma kan haddasa karuwar sharar da ake zubarwa. Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan yadda shara ke addabar wasu manyan biranen Najeriya da tasiri...
Asarar Da Hausawa Ke Tafkawa Sakamakon Bacewar Tatsuniya 03.06.2026 30:53
Tatsuniya wata hanya ce ta ilmantarwa da bayar da tarbiyya da kuma koyar da al’adu da halaye na gari a tsakanin Hausawa. Tatsuniyoyi na ɗauke da darussa na rayuwa, suna kuma koya wa yara da manya jarumta da tausayi da sauran dabi’u kyawawa. Sai dai a yayin da duniya take sauyawa, ba kasafai matasa suke sha’awar sauraron tatsuniya ba. Wannan ne batun da shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi naz...
Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Suke Kishin Kabila Fiye Da Kasa 20.05.2026 31:41
Kishin kasa na cikin abubuwan da shugabanni, da sauran masu ruwa da tsaki suke kira ga ’yan Najeriya a kullum a kansu. Muhimmancin kishin kasa ga cigaban al’umma, musamman a kasa mai kabilu da addinai daban-daban irin Najeriya, abu ne da ba zai misaltu ba. Sai dai alamu na nuna cewa yan Najeriya sun fi nuna kishin kabilun da suka fito idan aka kwatanta da kishin kasar da suke da shi. Shirin...
Dalilan Da Suka Sa Mutane Suke Son Haihuwar Maza Fiye Da Mata 29.04.2026 29:49
Son haihuwar ‘ya’ya maza fiye da ‘ya’ya mata abu ne da ake samu tun tale-tale a tsakanin alummomi daban-daban. A tsakanin wasu al’ummomin, samun da namiji abin alfahari ne wanda kuma yake nuni da cigaba da dorewar ahali; sai dai ba a cika bai wa haihuwar ‘ya mace irin wannan muhimmancin ba. Ko wadanne dalilai ne suka sa wasu mutane suka fi son samun ‘ya’ya maza a kan ‘ya’ya mata? Shirin Dag...
Shin Ko Kare Kai Daga Harin ‘Yan Ta’adda Zai Kawo Karshen Matsalar Tsaro? 22.04.2026 28:33
Hare haren ‘yan ta’adda na kara ta’azzara a yankuna daban daban na fadin kasar nan wanda hakan ke nuni da Karin rashin tsaro da ya dade yana ciwa alumma da ma gwamnati tuwo a kwarya. Ko a kwana kwanan nan an ga yadda jihar filato tayi ta fama da irin wadannan hare hare da kuma hare haren ramuwar gayya. Wani kididdiga kungiyar dake tattara bayanan hare haren ta’addanci ta fitar ya nuna cewa Najer...
Yadda Talauci Ke Hana Wasu Mata Sayen Audugar Al'ada 15.04.2026 24:22
Rashin iya siyan audugar Alada ga mata na kara jefa su cikin matsaloli da dama, a wasu lokuta ma har da cututtuka da ka iya jawo musu matsaloli. A cewar wani rahoto da Asusun yara na majalisar dinkin duniya UNICEF da WaterAid na shekarar 2021 suka fitar, yace daya daga cikin kowace ‘yan mata goma a ƙasashen Afrika ta Kudu da Sahara na rasa zuwa makaranta lokacin da take jinin al’ada, saboda rash...
Yadda Sunayen Zamani Suke Neman Kawar Da Na Hausawa 08.04.2026 28:27
A tsakanin Hausawa, sunaye masu alaka da harshen Larabci sun kusan maye gurbin na gargajiya irin su Tanko da Talle da Audi da dai sauran su. Sai dai yayin da a da sunayen da Hausawa kan sanya wa ’ya’yansu na Annabawa ko Sahabbai ko mashahuran malaman Muslunci ne, a baya-bayan nan wasu iyaye kan aro wasu kalmomi su rika kiran ’ya’yansu da su. Mene ne dalilin hakan, yaushe kuma daga ina ya sam...
Shin Ya Kamata A Biya Kudin Fansa Ga Masu Garkuwa Da Mutane? 01.04.2026 22:12
A cikin ‘yan shekarun nan, batun garkuwa da mutane ya zama babban kalubale ga tsaro a Najeriya da wasu ƙasashen duniya. Lokacin da mutane suka fada hannun masu garkuwa, iyaye da ‘yan uwa sau da yawa suna fuskantar babban zabi mai wahala: biyan kudin fansa don sakin wanda aka sace ko tsayawa da kafafun tsaro har zuwa samun taimakon hukumomi. Shin ko ya kamata alumma su cigaba da biyan kudin fansa...
Yadda 'Yanbindiga Ke Amfani Da Hakar Zinare Wajen Mallakar Makamai 25.03.2026 28:03
Kiyasi ya nuna cewa Najeriya tana asarar sama da dala biliyan 9 a duk shekara sakamakon ayyukan masu hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba, kuma kaso mafi tsoka shi ne fannin zinare. Rahotanni sun ce hakan na karawa ‘yan ta’adda karfi, inda suke amfani da wannan dama wajen tara muggan makamai a yankin Arewa maso Yamma da ke fama da matsalar tsaro. 'Yan bindigar sun yi ikirarin suna sa...
Dalilan Tashin Farashin Kayan Miya Gabanin Bikin Sallah 18.03.2026 25:44
Yayin da sallah ya gabato, mutane da dama kan yi fadi tashi don biyan wasu bukatun su na bukukuwan sallah, kuma kamar yadda aka saba, a irin wannan lokaci ne iyalai da dama kan maida hankulan su don ganin sun biya wasu daga cikin bukatun su musamman wadanda suka jibanci bikin sallah. Siyayyan kayan kayan abinci na daya daga cikin wadannan hidindimu, sai dai kayan miya da suka zama dole ayi amfan...
Yadda Sinadaran Dandanon Abinci Ke Yin Illa Ga Lafiya 11.03.2026 26:09
A yau, yawancin mutane suna amfani da sinadaran dandano wajen girki domin ƙara wa abinci ɗanɗano da ƙamshi. Amma, binciken masana ya nuna cewa ana yawan amfani da su fiye da yadda ake bukata, musamman irin waɗanda aka sarrafa a masana’antu. Wannan rashin kiyaye ƙa’ida yana iya jawo matsalolin lafiya. Sau da yawa mutane kan manta cewa a cikin waɗannan sinadarai akwai gishiri mai yawa da wasu ƙar...
Takaddamar Da Ta Dabaibaye Zargin Sacewa Tare Mayar Da Walida Abdullahi Kirista 25.02.2026 31:24
Takaddama ta dabaibaye batun wata matashiya mai suna Walida Abdullahi, bayan iyalanta sun zargi wani jami’in Department of State Services mai suna Ifeanyi Onyewuenyi da sace ta daga gidansu tare da tsare ta na tsawon lokaci ba tare da sanin inda take ba. Rahotanni sun ce ana zargin jami’in ya sauya mata addini daga Musulunci zuwa Kiristanci tare da canza mata suna zuwa Chinaza, lamarin da iyalanta...
Halin Da Zawarawa Ke Tsintar Kansu A Ciki A Watan Ramadan 18.02.2026 31:09
Kowane Musulmi da yadda yakan shiga watan Ramadana – wani kan shiga da shiri, wani kuma da shiririta. Sai dai wasu watan kan zo musu da kalubale – ba don sun shirya mishi b aba kuma don sun gaza shiryawa. Wani rukunin wadannan mutane shi ne na zawarawa, wadanda galibi ba su da masu agaza musu. Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne a kan rayuwar mata zawarawa musamman a watan Ramad...
Yadda Bude Kan Iyakokin Najeriya Da Jamhuriyar Benin Da Niger Zai Amfani Alummar Kasashen 11.02.2026 20:59
A watan Agustan shekarar 2019, gwamnatin Najeriya ta rufe kan iyakokinta da wasu ƙasashe makwabta ciki har da Jamhuriyar Nijar da Jamhuriyar Benin. Wannan mataki a wancan lokaci an ɗauke shi ne domin yaƙi da fasa-kwauri, hana shigo da kaya ba bisa ƙa’ida ba, da kuma kare tattalin arziƙin cikin gida. Bayan wannan tsawon lokaci da aka dauka na takaita zirga-zirga tsakanin wadannan kasashe, lamarin y...
Mene Ne Ya Fi Kawo Samu Tsakanin Sana’a Da Digiri? 04.02.2026 27:11
An dade ana muhawara a tsakanin masu sana’a da masu digiri, musamman wadanda suka yi gam-da-katar suka samu ayyuka masu tasiri, kan abin da ya fi kawu samu. Ko wanne bangare yana da kwararan hujjoji; amma masu raba gardama sun ce akwai zabi na uku. Shin wanne zabi ne wannan? Abin da shirin Daga Laraba zai yi nazari a kai ke nan.
Shin Ko Dawowar Dimokradiyya Ta Samar Da Kyakkyawan Fata Ga ‘Yan Najeriya? 21.01.2026 18:35
A farkon Jamhuriya ta Hudu a shekarar 1999, dawowar Najeriya mulkin dimokuraɗiyya ya haifar da babban fata a zukatan ‘yan ƙasa, inda mutane suka yi tsammanin ƙarshen mulkin soja zai kawo adalci, ci gaban tattalin arziƙi, tsaro, da shugabanci nagari da ke sauraron muradin jama’a. Jama’a sun yi imanin cewa za su sami ‘yancin faɗar albarkacin baki, ingantaccen zaɓe, aikin yi, da rage talauci ta hany...
Yadda Tattalin Arziki Da Ababen More Rayuwa Suke A Farkon Jamhuriya Ta Hudu Da Kuma Yanzu 14.01.2026 26:13
A shekarar 1999, lokacin da Najeriya ta sake komawa mulkin farar hula, tattalin arzikin ƙasa da kayayyakin more rayuwa na cikin wani yanayi na dogon mulkin soja. A wancan lokaci, masana da manazarta harkokin tattalin arziki sun bayyana cewa dogaro da man fetur ya yi wa ƙasar katutu, masana’antu da dama sun tsaya cik, kuɗin ƙasa ya raunana, yayin da rashin aikin yi da talauci suka yi ƙamari. Haka...
Dalilan Da Suka Sa Matan Wannan Zamanin Ba Sa Son Talaka 31.12.2025 26:47
A da soyayya na kafuwa ne sakamakon gaskiyar mutum, ko nasabarsa, ko tarbiyyarsa ko kuma riko da addininsa. Mace kan so saurayinta ko da kuwa ba shi da ko anini, a wasu lokutan ma ko da wani mai hannu da shuni ya fito takan tubure ta ki shi. Sai dai a wannan zamani mata da dama kan fito fili suna bayyana irin saurayin da suke so, a galibin lokuta mai abin hannu. Shirin Daga Laraba na wanna...
Yadda Ragin Farashin Man Fetur Zai Shafi Rayuwar ‘Yan Najeriya 17.12.2025 15:50
Rage farashin man fetur a Najeriya na daya daga cikin batutuwan da ke daukar hankalin al’umma, musamman ganin yadda tsadar rayuwa ta yi wa ’yan kasa katutu a ‘yan watannin nan. Man fetur ba wai kawai makamashi ba ne da ake amfani da shi wajen tafiyar da ababen hawa; ginshiki ne da kusan dukkan harkokin tattalin arziki ke jingina da shi – daga sufuri, da samar da kayayyaki, har zuwa rabon su zuwa k...
Ko Ziyarar Tawagar Amurka Za Ta Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Najeriya? 10.12.2025 13:57
A kwanakin nan, tawagar ’yan majalisar dokokin Amurka ta kawo ziyara Najeriya domin tattaunawa kan tsaro da tashin hankalin da ake ta fama da shi a yankunan Arewa da tsakiyar ƙasar, musamman rikice-rikicen da suka yi sanadiyyar kashe-kashe da duniya ke fargabar suna iya daukar salo na kisan kare dangi ga Najeriya. Ko wannan ziyarar da tawagar Amurka ta kawo zai kawo karshen matsalar tsaron da Naje...
Kalubalen Dake Gaban Janar Christopher Musa A Matsayin Ministan Tsaro 03.12.2025 28:22
Ana sa ran Majalisar Dattawa za ta tantance tare da tabbatar da Janar Christopher Musa mai ritaya a matsayin Ministan Tsaro, bayan da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya aike da sunansa zuwa majalisar. Wannan naɗin ya zo ne a wani lokaci da Najeriya ke fuskantar ƙalubalen tsaro a sassa daban-daban na ƙasar, musamman hare-haren ’yan bindiga, da ‘yan ta’adda, da masu garkuwa da mutane da rikice-rikic...
Shin Ya Kamata A Biya Kudin Fansa Ga Masu Garkuwa Da Mutane? 26.11.2025 22:12
A cikin 'yan shekarun nan, batun garkuwa da mutane ya zama babban kalubale ga tsaro a Najeriya da wasu ƙasashen duniya. Lokacin da mutane suka fada hannun masu garkuwa, iyaye da 'yan uwa sau da yawa suna fuskantar babban zabi mai wahala: biyan kudin fansa don sakin wanda aka sace ko tsayawa da kafafun tsaro har zuwa samun taimakon hukumomi. Shin ko ya kamata alumma su cigaba da biyan ku...
Similar podcasts
Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.