Daga Laraba

News HA ↓ 254 episodes

Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan jin ta-bakin wadanda abin ya shafa.

Category

News

Podcast website

www.buzzsprout.com

Latest episode

Jul 8, 2026

Where to listen?

Podcasts in the app Replaio Radio Coming soon

Podcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts

Get it on Google Play Install for free Android 5M+ downloads · 4.8 rating iOS soon

Episodes

Hanyoyin Da Suka Kamata A Bi Wajen Ceto Daliban Kebbi Da Aka Sace 19.11.2025

Batun kubutar da ɗalibai mata da masu garkuwa da mutane suka sace na makarantar GGCSS Maga dake karamar hukumar Danko Wasagu a jihar Kebbi na daya daga cikin abubuwan da alumma suka maida hankali a kai. Iyayen wadannan yara, da sauran masu ruwa da tsaki na ganin ya kamata a yi dukkan mai yiwuwa don ganin an ceto wadannan yara ba tare da sun samu rauni ba. Wannan shine batun da shirin Daga Laraba n...

Tasirin Da Tura Jami’an ‘Yan Sanda Kare Manyan Mutane Zai Haifar Ga Tsaron Al’umma 12.11.2025

A Najeriya, an saba ganin jami’an ‘yan sanda suna gadin manyan mutane ‘yan siyasa, ‘yan kasuwa, ko shugabanni maimakon su kasance a cikin al’umma suna tabbatar da tsaro ga kowa. Wannan tsarin ya haifar da tambayoyi masu zurfi game da adalci da yadda ake rarraba jami’an tsaro a ƙasar. A halin da ake ciki, yawancin unguwanni da kauyuka na fama da ƙarancin jami’an ‘yan sanda, yayin da mutum guda ko w...

Yadda 'Yanbindiga Ke Amfani Da Hakar Zinare Wajen Mallakar Makamai 05.11.2025

Kiyasi ya nuna cewa Najeriya tana asarar sama da dala biliyan 9 a duk shekara sakamakon ayyukan masu hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba, kuma kaso mafi tsoka shi ne fannin zinare.  Rahotanni sun ce hakan na karawa ‘yan ta’adda karfi, inda suke amfani da wannan dama wajen tara muggan makamai a yankin Arewa maso Yamma da ke fama da matsalar tsaro. 'Yan bindigar sun yi ikirarin suna sam...

Dalilan Da Suka Sa PDP Ta Ki Sayarwa Sule Lamido Fom Din Takarar Shugaban Jam’iyya 29.10.2025

Sabuwar dambarwa ta kunno kai tsakanin wasu manyan ‘ya’yan jam’iyyar adawa ta PDP, inda ake zargin cewa rikicin ya kai ga hana tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, sayen fom ɗin takarar shugabancin jam’iyyar. Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin manyan jam’iyyar a matakin kasa sun nuna adawa da niyyar Lamido na neman kujerar shugabancin PDP, suna ganin cewa ba shi ne ya dace da wann...

Shin Ko Jam’iyyar PDP Ta Fara Gushewa Ne? 15.10.2025

Yadda ‘ya’yan jamiyyar PDP ke ficewa suna komawa jam’iyya mai mulki na cigaba da nuna yadda take kara samun koma baya a siyasar Najeriya. Banda haka, rikicin cikin gida da yaki ci yaki cinyewa na cigaba da yi mata dabaibayi. Shin ko hakan na nufin jam’iyyar ta fara gushewa ne a siyasar Najeriya? Wannan shine batun da shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari a kai.

Yadda Aka Yi Almajiri Ya Zama Mabaraci 08.10.2025

A zamanin nan, ana alakanta almajirai da bara – hasali ma a lokuta da dama akan yi amfani da kalmar “almajiri” idan ana nufin mabaraci.    Amma a da ba haka lamarin yake ba – almajiri baya bukatar yin bara ko roko kafin ya sami na sakawa a bakin salati.    Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi nazari ne a kan yadda almajirci ya sauya salo a wannan zamani da ma irin halin da almajirai suka tsinc...

Tasirin Bambance-bambance Tsakanin ‘Yan Najeriya Shekara 65 Da Samun ‘Yancin Kai 01.10.2025

Tun daga ranar 1 ga Oktoba, 1960, Najeriya ta samu ’yancin kai daga Turawan mulkin mallaka. Amma tun daga wannan lokaci, al’ummar Najeriya sun kasance cike da bambance-bambancen addini da kabila da harshe da al’adu da kuma ra’ayin siyasa. Wadannan bambance-bambancen sun kasance ginshiki guda biyu: a wani lokaci suna zama jigo wajen gina ƙasa mai cike da nishaɗi da ɗimbin albarkatu, wani lokaci kum...

Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Sa Cin Kifi Yadda Ya Kamata 24.09.2025

Duk da amfanin kifi ga lafiyar jikin mutum da kuma samar da kudin shiga masana sun ce ba a amfani da shi yadda ya kamata a Najeriya.   Baya ga bai wa jiki lafiya, kifi  ka iya samar da kudaden shiga ga daidaikun ’yan Najeriya da ma kasar gaba daya.   Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan dalilan da suka sa ’yan Najeriya basa samun cin kifi kamar yadda ya kamata.

Dalilan Tashin Farashin Doya A Wasu Kasuwannin Najeriya 17.09.2025

A daidaikun kasuwannin Abuja da wasu manyan birane na ƙasar nan, an bayyana yadda farashin doya ke ƙara hawa fiye da yadda ake tsammani.  Wannan na faruwa ne duk da cewa yanzu sabuwar doya ta fara shigowa kasuwa, bisa al’ada, a duk shekara fitowar sabuwar doya kan karya farashin wanda yake kasuwa. Sai dai a bana, wasu daililai na sa farashin doya kara hawa. wannan shine batun da shirin Daga Laraba...

Dalilan Da Suka Sa Nayi Yunkurin Kashe Kaina Har Sau Uku 10.09.2025

Sau da dama mukan ji labarai na mutane da suka ɗauki rayukansu saboda damuwa, talauci ko kuma rashin samun mafita a cikin rayuwa.  A cikin wannan shirin, za mu kalli batun kisan kai daga wani ɓangare na daban, ba wai kawai daga alkaluma ba, amma ta hanyar jin labarin wani da ya taɓa  yunkurin kashe kansa har sau uku.  ko wadanne irin matsaloli ne suka tunzura wannan bawan Allahn yunkurin daukar ra...

Hare-hare Kan Tarurrukan Siyasa Da Alakarsu da 2027 04.09.2025

Karuwar hare-hare kan ’yan siyasa a kwanan nan ta sa wasu ’yan Najeriya sun fara fargabar abin da ka iya faruwa idan aka fara yakin neman zaben 2027. A kwanan nan ne dai wasu wadanda ake zargin ’yan bangar siyasa ne suka kai hare-hare a kan tarurruka ko kadarorin jam’iyyu ko ma daidaikun ’yan siyasa. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan yadda siyasar 2027 za ta kasance dub...

Yadda Mata Dake Auren Gwaji Suke Yamutsa Hazo 03.09.2025

Wani sabon salo da wannan zamani ya zo da shi shi ne auren gwaji, inda mata kan yi shiga gidan miji da niyyar fita bayan wani lokaci. Sai dai manazarta suna cewa hakan ka iya haddasa matsalolin musamman idan mazajen auren ba su san da wannan shirin ba. Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan dalilan da suka sa wasu mata suke yin auren gwaji.

Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa 27.08.2025

A duk lokacin da aka ɗaura aure, wata addu’a da ’yan uwa da abokan arziki kan yi ita ce “Allah Ya kawo ƙazantar ɗaki”.  A al’adance, ɗaya daga cikin manyan dalilan yin aure shi ne samun haihuwa.   Sai dai a wasu lokuta, wasu mazan kan nuna a fili ba su da muradin hakan.  Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne kan waɗannan mazan da ba sa son haihuwa da kuma dalilan su.

Yadda wasu tsare-tsaren ba da tazarar haihuwa ke yin illa ga mata 20.08.2025

A kokarin iyaye mata na kula da lafiyarsu da kuma tsare lafiyar iyalansu, hanyoyin bada tazarar haihuwa na asibiti sun zama zabin da dama ke komawa gare su.  Sai dai duk da shaharar wadannan hanyoyi, akwai mata da dama da ke fuskantar matsaloli daban-daban yayin amfani da su.  Wasu na fama da illa ta jiki kamar zubar jini fiye da kima, ciwon mara ko canjin yanayin jini, yayin da wasu kuma ke fama...

Yadda Sinadaran Dandanon Abinci Ke Yin Illa Ga Lafiya 13.08.2025

A yau, yawancin mutane suna amfani da sinadaran dandano wajen girki domin ƙara wa abinci ɗanɗano da ƙamshi. Amma, binciken masana ya nuna cewa ana yawan amfani da su fiye da yadda ake bukata, musamman irin waɗanda aka sarrafa a masana’antu. Wannan rashin kiyaye ƙa’ida yana iya jawo matsalolin lafiya.  Sau da yawa mutane kan manta cewa a cikin waɗannan sinadarai akwai gishiri mai yawa da wasu ƙarin...

Me Ke Sa Matasa Zama Karnukan Farautar ‘Yan Siyasa A Kafafen Sadarwa Na Zamani? 06.08.2025

Wasu matasa sun zabi tallata ‘yan siyasa a kafafen sada zumunta na zamani ta yadda bai kamata ba a wasu lokutan. Tallata ‘yan siyasa da matasan suke yi kan haifar da hatsaniya, ko kiyayya, a intanet ko ma a zahiri a tsakanin su. Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan dalilan da suka sa wasu matasa suka zabi zama “sojojin baka” ko “karnukan farautar” ‘yan siyasa a kafafen sada zumu...

Dalilan Alummomi Na Rungumar Gwaji Kafin Aure 30.07.2025

Wasu alummomi sun bayyana dalilan da suka sa suka karbi gwajin ma’aurata kafin a daura musu aure. A wasu lokutan akan samu matsaloli sakamakon rashin gwajin jini kafin a hada mace da na miji aure da suka hada da yaduwar cutuka, samun ‘ya’ya marasa lafiya da sauran wasu matsalolin. Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan dalilan da suka sa wasu alummomin suka rungumi gwajin jini kaf...

Abubuwan Da Ya Kamata Yara Su Yi Yayin Hutun Makaranta 23.07.2025

A duk lokacin da akace an kammala zangon karatu, dalibai kan samu hutu don hutawa da yin wadansu abu na dabam da kuma basu damar shakuwa da ‘yan uwa da abokan arziki. Kamar yadda masana harkar masana harkar ilimi suka saba fadi, yawan karatu kan taho da nashi irin matsalolin, ya kuma kamata ace ana warewa dalibai wasu lokuta na musamman don samun hutu daga karatun da suka koya. Shirin Daga Laraba...

Makomar Siyasar Najeriya Bayan Rasuwar Shugaba Buhari 16.07.2025

Masana da masu sharhi suna ganin cewa rasuwar shugaba Muhammadu Buhari ta haifar da babban gibi a siyasar Najeriya, musamman a Arewa. Wasu ma suna ganin rasuwar Buhari ka iya kawo tasgaro ga jamiyya mai Mulki, wadda take ganin shi danta ne, da ma sabuwar hadakar ’yan adawa, wadanda suke ganin yana tare da su. Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne a kan yadda siyasar Najeriya za ta ka...

Shin Ko Zafin Nema Na Kawo Samu? 09.07.2025

Mai yiwuwa masu sauraro sun san wani bawan Allah wanda kusan a kullum, kuksan a ko yaushe a cikin nema yake, amma Allah bai kawo ba.. Wasu dai na ganin yawan fadi-tashin da mutum yakan yi ba shi ne zai ba shi kudaden da yake bukata ba, yayin da wasu suke ganin jajircewar mutum tana da nasaba da yawan abin da zai samu. Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan kujiba-kujibar da mutane...

Cutukan Da Sinadaran Yin Burodi Ke Haifarwa 02.07.2025

Burodi ya zama daya daga cikin abincin da ‘yan Najeriya basa iya yi babu shi. Yayin da wasu ke cin shi a matsayin abin Karin kumallo da safe, wasu kuwa na cin shi a matsayin abincin rana a wasu lokutan ma har da na dare. A duk lokacin da aka ce masu sarrafa burodi sun shiga yajin aiki, ko fulawa tayi karanci hakan kan haifar da raguwar burodi a kasuwa wadda kan jefa masu cin shi a cikin mawuyacin...

Shin Ko Kare Kai Daga Harin ‘Yan Ta’adda Zai Kawo Karshen Matsalar Tsaro? 18.06.2025

Hare haren ‘yan ta’adda na kara ta’azzara a yankuna daban daban na fadin kasar nan wanda hakan ke nuni da Karin rashin tsaro da ya dade yana ciwa alumma da ma gwamnati tuwo a kwarya. Ko a kwana kwanan nan an ga yadda jihar filato tayi ta fama da irin wadannan hare hare da kuma hare haren ramuwar gayya. Wani kididdiga kungiyar dake tattara bayanan hare haren ta’addanci ta fitar ya nuna cewa Najeriy...

June 12: Me Ranar Demokradiyya Ke Nufi Ga Talakan Najeriya? 12.06.2025

An ayyana 12 ga watan Yunin kowace shekara a matsayin Ranar Dimokuradiyya a Najeriya don tunawa da ranar da aka gudanar da zaben da aka yi amanna cewa shi ne mafi sahihanci da inganci a tarihi. Sai dai bayan fiye da shekara 30 da wannan zabe da fafutukar da ta biyo baya, wasu masana suna ganin har yanzu kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba. Ko mece ce hujjarsu? Wannan ne batun da shirin Najeriya a...

Dalilan Rashin Jituwa Tsakanin Marasa Lafiya Da Jami'an Kiwon Lafiya 11.06.2025

Asibiti ko dakin shan magani ko wani bigire mai kama da wadannan wuri ne da marasa lafiya kan je ko ake kai su don neman waraka a duk lokacin da bukatar haka ta taso. Wuri ne da akan ware domin ceto rayukan wadanda suka jikkata suke kuma bukatar agajin gaggawa. A bisa al’ada kuma, ana sa ran samun tausayi da jinkai da sadaukarwa wajen yin dukkan mai yiwuwa kuma a ko wane lokaci don ceton rayuka da...

Dalilan Tashin Farashin Kayan Miya Gabanin Bikin Sallah 04.06.2025

Yayin da sallah ya gabato, mutane da dama kan yi fadi tashi don biyan wasu bukatun su na bukukuwan sallah, kuma kamar yadda aka saba, a irin wannan lokaci ne iyalai da dama kan maida hankulan su don ganin sun biya wasu daga cikin bukatun su musamman wadanda suka jibanci bikin sallah. Siyayyan kayan kayan abinci na daya daga cikin wadannan hidindimu, sai dai kayan miya da suka zama dole ayi amfani...

Listen to the Daga Laraba podcast in Replaio

Radio and podcasts in one app - free, with no sign-up. Install today and do not miss the launch

Get it on Google Play

Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.