RFI Hausa
Bakonmu a Yau
A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban kasa.
Where to listen?
Podcasts in the app Replaio Radio Coming soonPodcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts
Episodes
Kasuwar hada-hadar hannayen jarin Najeriya ta zama mafi ƙarfi a duniya 10.07.2026 3:35
Cikin makon nan, kasuwar hada-hadar hannayen jarin Najeriya, ta kafa tarihin zama mafi ƙarfi gami da bunƙasa a faɗin Duniya, bayan zarta mai riƙe da kambun a baya bayan nan, wato takwararta ta Korea ta Kudu. Rahoton kamfanin Bloomberg ya nuna cewa, zuwa yanzu Kasuwar ta Najeriya ta samu tagomashi ne da kaso 67 cikin 100, yayin da ta Korea ta Kudu ke da kaso 66. Domin jin ƙarin bayanin kan dalila...
Najeriya na neman goyon bayan China wajen yaƙi da ta'addaci - Bello Dambazau 09.07.2026 3:38
Najeriya na tattaunawa da China wajen ganin ta samu goyon bayan da ya dace a fasahar zamani da kuma makamai domin shawo kan matsalolin tsaro da suka addibi ƙasar. Sabon jakadan Najeriya a ƙasar China Janar Abdurrahman Bello Dambazau mai ritaya ya bayyana haka a tattaunawar da suka kayi da Bashir Ibrahim Idris. Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar hirar.
Dakta Sani Gambo kan taron ƙasashen ƙungiyar AES da Rasha 08.07.2026 3:30
A wannan Laraba ake fara taron tuntuɓa tsakanin ƙasashen ƙungiyar AES wato Mali, Nijar da Burkina Faso da kuma ƙasar Rasha a gefe guda a Yamai fadar gwamnatin Nijar, inda ake sa ran za su tattauna batutuwan da suka shafi tsaro, tattalin arziki da kuma makamashi. Wannan ne karo na biyu da ake gudanar taron bayan makamancinsa da aka yi a birnin Moscow na Rasha a watan Afrilun 2025, kuma ya na zuwa...
Ɗambarwar Naira Triliyan 8 ta girgiza gwamnatin Bola Tinubu 06.07.2026 3:34
A Najeriya, daidai lokacin da ake neman sanin matsayin shugaba Bola Tinubu dangane da zargin kafawa da kuma tafiyar da wata ma’aikatar jabu a ƙarƙshin gwamnatin tarayya, sai kuma ga wasu bayanai daga Asusun Lamuni na Duniya IMF da ke cewa gwamnatin ta kashe sama da Naira triliyan 8 waɗanda sam kasafin kuɗin ƙasar bai san da su ba. Shiga alamar sauti don sauraron cikakkiyar hira da Abdoulklarim Ib...
Isa Sanusi kan rahoton Amnesty da ke zargin gwamnatin Najeriya gaza kare al'umma 03.07.2026 3:37
Ƙungiyar Amnesty International a Najeriya ta zargi gwamnatin shugaba Bola Ahmad Tinubu da gaza kare ƴan Najeriya daga matsaloli na ta’addanci da na tattalin arziki da ake fama da shi. Ruƙayya Abba Kabara ta tattauna da daraktan Amnesty a Najeriya, Malam Isa Sanusi kan rahoton nasu. Latsa alamar sauti don sauraren sa....
Dakta Isa Abdullahi akan soke lasisin wasu ƙananan bankuna da aka yi a Najeriya 02.07.2026 3:34
Babban Bankin Najeriya na CBN ya sanar da soke lasisin wasu ƙananan bankuna 46 saboda saɓawa ƙa'idar aiki. Waɗannan bankuna sun haɗa da guda 12 a Kano da wasu takwas a Lagos, baya ga wasu ɗaiɗaikun jihohi. Domin sanin tasirin wannan mataki, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Isa Abdullahi, masanin tattalin arziki, kuma ga yadda zantawar su ta gudana a kai.
Muhammad Sani Sufyan kan watsin Kotu da buƙatar Trump game da ƴancin zama ɗan ƙasa 01.07.2026 3:14
Kotun Ƙolin Amurka ta yi watsi da buƙatar shugaba Donald Trump ta soke dokar da ke bai wa waɗanda aka haifa a ƙasar ƴancin zama ƴan ƙasa kai-tsaye. Kotun ta tananata cewa, duk wanda aka haifa a Amurka na da ƴancin mallakar shaidar zama ɗan ƙasa. Trump ya ruga kotun kolin ne bayan rashin nasara a ƙananan kotunan ƙasar. Kan haka, Abdurrahman Gambo Ahmad ya tattauna da Muhammad Sani Sufyan, mazaunin...
Rakiya Sa'idu akan cika wa'adin korar baƙi a Afirka ta Kudu 30.06.2026 3:29
An shiga wani yanayi na fargaba da tsananin tashin hankali a Afirka ta Kudu, yayin da yau wa’adin ranar 30 ga watan nan na Yuni ke cika, game da zanga-zangar da wasu ƙungiyoyin ƙyamar baki suka shirya don tilasta wa baƙin da ba su da takardu barin ƙasar. Ko da yake hukumar ’yansandan ƙasar ta ce ta tura ɗimbin jami'an tsaro zuwa yankunan da ake sa ran za su fuskanci tashin hankali, kamar su Pret...
Soumaila Amadou akan rikicin diflomasiyyar Faransa da Burkina Faso 29.06.2026 3:42
Mahukunta a Faransa, sun ce yanzu haka suna kan yin nazari domin ɗaukar matakin da ya dace bayan da Burkina Faso ta sanar da katse duk wata hulɗar diflomasiyya da ƙasar, inda ta zargi Faransa da taimaka wa masu tayar da ƙayar baya da ke neman wargaza sha’anin tsaro da na zamantakewar al’ummarta. A game da wannan batu ne Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Malam Soumaila Amadou, wanda ke bin di...
CP Muhammed Indabawa kan samar da ƴan sandan jihohi a Najeriya 26.06.2026 3:44
A Najeriya ra’ayoyi sun sha bambam a tsakanin al’umma dangane da shirin bai wa jihohi damar kafa rundunar ƴansanda don inganta sha’anin tsaro a ƙasar. Tuni dai Majalisun Tarayyar Ƙasar biyu suka amince da daftarin dokar da ke bayar da damar ɗaukar wannan mataki, kamar dai yadda gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta buƙata. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da tsohon Kwamishinan Ƴansanda CP Muhammed Ind...
Baba Usman Ngelzerma,kan tsangwamar da Fulani ke fuskanta a kudancin Najeriya 24.06.2026 3:26
Fulani makiyaya a Najeriya sun koka dangane da irin tsangwama da kuma barazanar da suke fuskanta a kudancin ƙasar, sakamakon matsalar tsaro da kuma garkuwa da mutane da ake fama da shi. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da shugaban ƙungiyar Miyetti Allah, Baba Usman Ngelzerma. Ku danna alamar sauraro domin jin cikakkiyar tattaunawar.
Dakta Abdulhakeem Garba kan cikar Birtaniya shekaru 10 da ficewa daga EU 23.06.2026 3:29
Yau ake cika shekaru 10 da ficewar Birtaniya daga cikin kungiyar ƙasashen Turai domin cin gashin kan ta wajen gudanar da harkokin mulki da kuma kasuwancin ta ba tare da sanya hannun ƙungiyar EU ba. Bayan share shekaru ana tattaunawa, Birtaniya ta fita a hukumance a ranar 31 ga Janairun 2020. Wannan mataki na Birtaniya ya canza taswirar siyasa, tattalin arziki, da dangantakar kasuwanci ta duniya ba...
Alhassane Intchinicar kan sharuɗɗan da Nijar ta kafa kafin buɗe iyaka da Benin 22.06.2026 3:32
An fara tattaunawa tsakanin Benin da kuma Jamhuriyar Nijar da nufin sake buɗe iyakar ƙasashen biyu, sai dai mahukuntan birnin Yamai sun gindaya sharuɗɗa biyu kafin sake buɗe iyakar. Ministan cikin gida kuma jagoran tawagar Nijar a tattaunawar, ya ce na farko dole ne a ƙulla yarjejeniyar tsaro wadda a ƙarƙashinta ba ɗaya daga cikin ƙasashen biyu da za ta bari a yi amfani da ita domin kai wa ɗaya ha...
Gobe za a gudanar da zaɓen gwamna a jihar Ekiti ta kudancin Najeriya 19.06.2026 3:33
Gobe ne hukumar zaɓe a Najeriya ke gudanar da zaɓen gwamnan Ekiti da ke yankin kudanci, inda ƴan takara 13 za su fafata. Ana kallon wannan zaɓen a matsayin zakaran gwajin dafi ga sabon shugaban hukumar zaɓen Farfesa Joash Amiputan. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da mai magana da yawun hukumar Hajiya Zainab Abubakar. Latsa alamar sauti don sauraren yadda zantawarsu ta gudana...
Amnesty ta ci gaba da matsa wa gwamnatin Najeriya lamba kan ceto ɗalibai 18.06.2026 3:37
Ƙungiyar Kare Hakkin Bil'adama ta Amnesty International ta bukaci gwamnatin Najeriya da ta dauki matakai na gaggawa don kare dalibai da kuma ceto wadanda har yanzu suke hannun masu garkuwa da mutane. Ƙungiyar ta jaddada cewa gazawar hukumomi wajen kawo ƙarshen hare-hare da sace-sacen dalibai na nuna cewa rayuwar yara na cikin matsananciyar barazana. Ƙungiyar ta bukaci Shugaba Tinubu da ya dauki ma...
Akwai takaici yadda wasu ke son haddasa gaba tsakanin ƙabilu a Plateau-Joyce Ramnap 17.06.2026 3:38
Gwamnatin Jihar Filato da ke Najeriya ta bayyana matuƙar damuwar ta dangane da yadda ta ce wasu na amfani da hukuncin wata kotu dangane da baiwa wasu Hausawa takardar zama ƴan ƙasa domin haifar da tashin hankali a tsakanin al'ummar da suka kwashe shekaru da dama su na zaman lafiya da juna. Gwamnatin ta ja kunnen al'umma inda ta ce waɗanda ba su gamsu da hukuncin ba na da hurumin ɗaukaka ƙara kamar...
Dakta Abubakar Sadiq kan matakin rushe wasu jam'iyyu siyasa a Najeriya 16.06.2026 3:34
Wata babbar kotu a Najeriya, ta bai wa hukumar zaɓe ta INEC umarnin soke wasu jam'iyyun adawa har guda biyar, saboda saɓawa dokokin zaɓen shekarar 2023 na ƙasa samun kashi 25 na ƙuri'un da aka kaɗa. Jam'iyyun sun haɗa da ADC da AA da APP da ZLP da Acoord Party. Tuni wannan hukunci ya haifar da mahawara da kuma zargin yunƙrin haa 'yan adawa shiga zaɓe mai zuwa. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da D...
Yadda mutuwar Janar Rabe ta ɗaga hankulan jama'a a Najeriya 15.06.2026 3:39
A Najeriya, mutuwar tsohon kakakin rundunar sojin ƙasar Janar Abubakar Rabe mai ritaya a hannun ƴan bindiga, lamari ne da ya yi matuƙar ɗaga hankulan jama’a, tare da ƙara haifar da shakkun game da yiyuwar cewa anya kuwa za a iya magance matsalar tsaro a ƙasar? An dai gaza ceto janar Rabe daga hannun ƴanbindigar, duk da cewa ya share kusan makonni biyu a hannunsu. Shiga alamar sauti don sauraron hi...
Tattaunawa da Hussaini Abdu na ƙungiyar Action Aid kan matsalolin Najeriya 12.06.2026 3:37
Wasu fitattun mutane a Najeriya, da suka haɗa da tsohon shugaban hukumar zaɓe Farfesa Attahiru Jega, da tsohon jakadan ƙasar a Majalisar Dinkin Duniya Farfesa Ibrahim Gambari, sun yi gargaɗi a game da irin barazanar da ƙasar ke fuskanta sakamakon rashin tsaro, da yadda ake yi wa tsarin gudanar da zaɓuka na ƙasar karen-tsaye. Kan wannan na gana da guda daga cikin masu ruwa da tsakin da suka yi wann...
Abubuwan da ya kamata ku sani a gameda gasar cin kofin duniya ta 2026 11.06.2026 3:34
Yau ake fara gasar cin kofin duniya ta bana, inda ƙasashe 48 za su fafata domin samun zakarar bana. A karon farko ƙasashe uku ne ke daukar nauyin gasar, wato Amurka da Cnada da kuma Mexico kuma kalla yan wasa 1,248 da alkalan wasa 52 za su jagoranci wasanni 104 da za'a kwashe kwanaki 39 ana yi. Shiga alamar sauti don sauraron cikakkiyar da Bashir Ibrahim Idris ya yi da tsohon Sakataren hukumar kwa...
Samaila Abdullahi Muhammad kan rahoton IMF game da ƙaruwar talauci a Najeriya 10.06.2026 3:33
Asusun bada lamuni na duniya IMF ya ce sauye-sauyen da gwamnatin Najeriya ke yi na ƙarfafa tattalin arzikin ƙasar, sai dai kuma sun haifar da ƙarin ƴan Najeriya sama da miliyan 60 da suka faɗa cikin talauci. Ku danna alamar saurare domin jin tattaunawar Bashir Ibrahim Idris, da masanin tattalin arziki a Najeriya Samaila Abdullahi Muhammad kan wannan batu.
Farfesa Bello Bada game da ta'azzarar matsalar tsaro a yankin Arewacin Najeriya 09.06.2026 3:27
Yankin arewacin Najeriya na ci gaba da ɗanɗana kuɗar sa a hannun ƴan bindiga, waɗanda ke kai hari suna sace mutane da kuma hallaka su ba tare da ƙauƙautawa ba. ko a jiya sai da ƴan bindigar suka yi garkuwa da wata tawagar masu neman sulhu da su a jihar Zamfara, baya ga wasu ɗaruruwa da ke hannun su a jihohi da dama, a daidai lokacin da gwamnoni da ƴan majalisun yankin suka mayar da hankali a kan s...
Alhaji Sa’adu Yusuf Ɗandare game da kamen marabarata a birnin Lagos 08.06.2026 3:32
Gwamnatin jihar Lagos a Najeriya ta ƙaddamar da wani gagarumin samame kan mabarata da suka cika titunan birnin, inda aka cafke ɗimbin mabarata ciki har da masu fama da naƙasa da kuma waɗanda ke yi musu jagora, kazalika da ma waɗanda ke cikin ƙoshin lafiya. Kwamishin Ma’aikatar matasa da jin ɗadin jama’a na jihar Mobolaji Ogunlende, ya ce daga ƙarshen watan Mayun da ya gabata zuwa yau, sun cafke sa...
Dr Umar Yakubu kan fitar bayanan sirri daga rumbun ajiyar bayanan INEC 05.06.2026 3:35
A Najeriya, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙaddamar da bincike akan zargin fitar bayan sirri daga rumbun ajiyar bayananta na masu zaɓe, wanda ya jamnyo cece-kuce a ƴan kwanakin nan. Wannan ya biyo bayan wallafa bayan wani ɗan takara ne da ake zargin wani ma’aikacin INEC ya yi a dandalin sada zumunta a yayin zaɓwen fidda gwani na wata jam’iyyar siyasa a babban birnin tarayyar Najeriya Abuja. Ak...
Similar podcasts
Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.