Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Where to listen?
Podcasts in the app Replaio Radio Coming soonPodcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts
Episodes
Me Ya Sa Mutane Suka Dawo Daga Rakiyar Kirifto? 23.06.2026 26:05
Send us Fan Mail A ’yan watanni da suka gabata, matasa da yawa a Najeriya sun dukufa don ganin hakar su ta cimma ruwa wajen samun kudaden kirifto. Amma alamu na cewa a baya-bayan nan wasu daga cikinsu sun sare sun kuma saduda sun dawo daga rakiyar harkar. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan dalilan wasu matasan na yin watsi da harkar kirifto.
Dalilan Da Daliban Makarantar Kudi Suka Fi Na Gwamnati Kokari 18.06.2026 24:33
Send us Fan Mail Duk da cewa gwamnati na da dubban kwararrun malamai a makarantunta, har yanzu ana ganin ɗaliban makarantun gwamnati na kasa da na makarantun masu zaman kansu wajen ƙoƙari da kuma sakamakon jarabawa. Wannan matsala ta daɗe tana jawo muhawara tsakanin iyaye, malamai da hukumomin ilimi. Wasu na ganin matsaloli ne da ba za su rasa nasaba da rashin kulawa da watsi da harkar ilimi da g...
Masu Nau'in Jinin AS Sun Fi Masu Nau'in AA Lafiya 16.06.2026 20:54
Send us Fan Mail Sau da dama wadanda ke dauke da nau’in jini na AA na bayyana cewa sun fi kowa lafiya. Suna bayyana cewa basa rashin lafiya kamar yadda masu sauran na’ukan jini ke yi. Shirin Najeriya A Yau na wanna lokaci zai yi nazari ne kan ko da gaske ne masu nau’in jini na AA sun fi sauran masu nau’ukan jini lafiya.
Yadda Masu Yi Wa Kasa Hidima Za Su Ci Arzikin Yankunan Da Suke AIki 11.06.2026 22:09
Send us Fan Mail Bayan hadin kai da karfafa fahimtar juna wadanda hidimar kasa take kawowa, akan samu wasu masu hidimar da sukan yi amfani da duk wata dama da suka samu don neman na sakawa a bakin salati. Yayin da wasu masu hidimar kasa sukan kama sana’a ko su saka hannun jari a inda aka tura su, wasu kuwa komawa garuruwansu suke yi bayan sun kammala. Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi...
Nasarori Da Kalubalen Da Bankin Musulunci ke Fuskanta A Najeriya 09.06.2026 24:59
Send us Fan Mail A Jamhuriya ta Hudu a Najeriya, wadda ta fara a shekarar 1999, an samu sauye-sauye masu yawa a bangaren tattalin arziki da harkokin kuɗi, ciki har da tasowar bankunan Musulunci. Wannan tsari na banki ya samo asali ne daga buƙatar samar da hanyoyin mu’amala da kuɗi da suka dace da koyarwar addinin Musulunci, wato hanyoyin da ba su ƙunshi riba, da zamba, ko rashin tabbas ba. A fark...
Shin Da Gaske Irin GMO Na Da Matsala Ga Amfanin Noma A Najeriya? 04.06.2026 25:25
Send us Fan Mail Alamu na nuna cewa galibin manoma a Najeriya suna da shakku a kan amfani da irin da aka sauya ƙwayoyin halittarsa. Hakan dai na faruwa ne duk da bayanan da wasu masana suka yi game da alfanun wannan iri wanda ake kira GMO ko Genetically Modified Organism a turance. Tuni dai wasu masanan, waɗanda suka shirya wani taron bita ga manema labarai, suka yi gargaɗi game da illolin irin. K...
Dalilan Yaduwar Cutuka A Irin Wannan Lokaci 02.06.2026 27:36
Send us Fan Mail Da zarar damuna ta fara bankawana, yanayi na sanyi da zafi kan fara sallama, wanda hakan kan zo da rashin lafiya dake yaduwa a cikin alumma. Ko wadanne dalilai ne suka sa ake samun yaduwar rashin lafiya a wannan lokaci? Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.
Abin Da Dokar Kasa Ta Ce Kan Takarar Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan 22.05.2026 27:28
Send us Fan Mail Batun siyasar Najeriya ya sake ɗaukar hankali yayin da jam’iyyar PDP ta bayyana cewa tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan, zai tsaya mata takarar shugaban ƙasa a 2027. Wannan batu ya tayar da muhawara mai zafi a tsakanin masana, da ‘yan siyasa da ma al’umma. Idan za a iya tunawa dai, an rantsar da tsohon shugaban ƙasan, har sau biyu: a karo na farko a shekarar 2010 bayan...
Halin Kunci Da Matan Da Aka Yi Garkuwa Da Su Ke Tsintar Kansu A Ciki 15.05.2026 23:03
Send us Fan Mail So da yawa matan da aka yi garkuwa dasu kan shiga halin kunci ko da bayan sun kubuta. Yayin da kadan daga cikinsu ke komawa gudanar da rayuwarsu yadda ta kamata, wasu da dama kan tsinci kansu cikin halin damuwa da tagayyara. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokacin ya yi duba ne kan wannan batu da irin shawarwarin da za a basu don fita daga irin wannan kangi.
Yadda Wasu Al'ummomi Suke Kare Kansu Daga Ambaliyar Ruwa 14.05.2026 28:31
Send us Fan Mail Ambaliyar ruwa na cigaba da salwantar da dukiyoyi da rayukan al’ummomi da dama a sassa daban-daban na Najeriya. Ko a farkon makon nan, hukumomi sun yi gargadin cewa akwai yiwuwar samun ambaliyar a jihohi akalla 11. Sai dai wasu alummomin tuni suka dauki matakai don rage barnar da ambaliyar ka iya yi musu. A kan wadannan matakai shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi naza...
Yadda Talauci Ke Hana Shayar Da Yara Nonon Uwa Zalla A Najeriya 08.05.2026 28:44
Send us Fan Mail Ga alama kwalliya ba ta biyan kudin sabulu a fafautukar da ake yi ta ganin iyaye mata sun shayar da jariransu nono Zalla a wata shida na farko. Rahotanni sun ce duk da dadewar da aka yi ana wayar da kai har yanzu matan da suke shayar da yara nono uwa Zalla ba su haura kashi 29 cikin dari ba. Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan dalilan da suke hana mata...
''Yadda Cutar Amosanin Jini Ta Hana Ni Cimma Buri Na'' 07.05.2026 23:57
Send us Fan Mail Cutar amosanin jini wacce aka fi sani da cutar sikila na cigaba da barazana ga rayukan masu dauke da ita. Wannan cuta na saka masu ita da ‘yan uwan su cikin halin ha’ula’i, a wasu lokutan ma tana haifar da rasa rayukan wasu dake dauke da ita. Rahotannin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) sun nuna cewa, kusan yara 300,000 ne ake haifa da cutar Sikila a duk shekara a fadin duniya, ind...
Yadda Raguwar Maniyyatan Najeriya Ke Tasiri Ga Aikin Hajji 28.04.2026 23:47
Send us Fan Mail A kwanakin nan ana samun raguwar kujerun maniyyata aikin Hajji daga Najeriya, abin da ya jawo fargaba ga masu shirin zuwa kasa mai tsarki da kuma masu hidimar su. A da, Najeriya na samun kujeru sama da dubu casa’in daga gwamnatin Saudiyya, amma cikin shekaru kadan da suka gabata adadin ya ragu zuwa kusan dubu sittin da biyar. Ko yaya kara raguwar kujerun maniyyatan Najeriya ke...
Matsalolin Da Suke Tarnaki Ga Kananan Yara A Najeriya Da Hanyoyin Magance Su 27.04.2026 29:05
Send us Fan Mail Najeriya tana cikin ƙasashen da suka fi yawan yara a duniya, a cewar Hukumar Kula da Kananan Yara ta Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF). Sai dai a cewar Hukumar ta UNICEF, kusan rabin wadannan yara suna fuskantar kalubale, kama daga cin zarafi zuwa rashin samun kulawa da dai sauran su. Wadannan matsaloli da yara suke fuskanta dai sun dade suna ci wa masu ruwa da tsaki tuwo a kwary...
Yawan Kudaden Da Ake Bukata Wajen Samar Da 'Yan Sandan Jihohi 21.04.2026 22:20
Send us Fan Mail Batun samar da ‘yansandan jihohi na ƙara ɗaukar hankalin ‘yan Najeriya, musamman a dai-dai lokacin da matsalar tsaro ke ƙara ta’azzara a sassa daban-daban na ƙasar nan. Sai dai, samar da ‘yansandan jihohi ba abu ne mai sauƙi Kamar yadda wasu ke tunani ba. Gwamnatocin jihohi na buƙatar abubuwa masu yawa kafin su iya ɗaukar wannan nauyi, banda batun samar da dokar samar da wadanna...
‘Halin Kunci Ya Sa Muke Zama A Baca A Abuja’ 17.04.2026 30:22
Send us Fan Mail Halin matsin tattalin arziki ya tilasta da yawa daga cikin mutane zama a bacoci a garin Abuja da wasu biranen Najeriya. Mutane a birane kamar Abuja da Legas Da Fatakwal na cikin halin matsi sakamakon rashin ingattaccen muhalli. Ko wannen irin rayuwa irin wadannan mutanen ke yi? Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai a yau da ake bikin...
Yadda Ake Juya Ababen Hawa Zuwa Masu Amfani Da CNG 16.04.2026 23:52
Send us Fan Mail Galibin ’yan Najeriya ba su san amfanin da sauya ababen hawansu daga masu amfani da man fetur zuwa masu amfani da iskar gas ta CNG ke da shi ba, musamman a wannan lokaci da ake fama da tsadar man fetur. ’Yan Najeriya da dama dai suna amfani da man fetur ne saboda karancin wuraren sauya ababen hawan da sauran dalilai. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a k...
Abun Da Ya Sa Matan Arewa Ke Gujewa Karantar Ilimin Kimiyya 14.04.2026 30:00
Send us Fan Mail Mata a Arewacin Najeriya na fuskantar kalubale da dama a fannin karantar kimiyya. Akwai darussan da a mafi yawan lokuta ba mata kadai ba, har da mazan na kaurace musu. Shirin Najeriya a Yau ya yi nazari ne kan dalilan da suka sa matan Arewacin Najeriya ke tsoron karantar ilimin kimiyya.
Ko Wa'adi Daya Ya Isa Wanda Aka Zaba Cika Alkawuran Da Ya Dauka? 10.04.2026 30:11
Send us Fan Mail Duk bayan shekaru hudu, Najeriya na kara yin zabe kuma ko wanne lokaci 'yan takara kan dauki alkawurika. Ko shekaru nawa wadanda ake zabe ke bukata don cika alkawuran da suka dauka? wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.
Gaskiyar Tasirin Amfani Da Irin Noma Da Aka Canzawa Halitta GMO 09.04.2026 25:26
Send us Fan Mail Alamu na nuna cewa galibin manoma a Najeriya suna da shakku a kan amfani da irin da aka sauya ƙwayoyin halittarsa. Hakan dai na faruwa ne duk da bayanan da wasu masana suka yi game da alfanun wannan iri wanda ake kira GMO ko Genetically Modified Organism a turance. Tuni dai wasu masanan, waɗanda suka shirya wani taron bita ga manema labarai, suka yi gargaɗi game da illolin irin. K...
Shin Ya Kamata A Samar Da Dokokin Da Za Su Sa Ido Kan Amfani Da AI? 07.04.2026 22:58
Send us Fan Mail Tun bayan bayyanar kirkirarrriyar basira wato AI ne dai wasu mutane suke amfani da ita ta hanyar da da bai kamata ba. Wasu sukan yi amfani da ita wajen saka hoto ko kirkirar faifan bidiyo wanda zai nuna wani yana yin abun da bai kamata ba. Hakan dai ya sa wasu suna ganin ya kamata a samar da dokokin da za su rinka lura da yadda ake amfani da kirkirarriyar basirar. Shirin Najeri...
Yadda Masu Yi Wa Kasa Hidima Za Su Ci Arzikin Yankunan Da Suke AIki 02.04.2026 22:09
Send us Fan Mail Bayan hadin kai da karfafa fahimtar juna wadanda hidimar kasa take kawowa, akan samu wasu masu hidimar da sukan yi amfani da duk wata dama da suka samu don neman na sakawa a bakin salati. Yayin da wasu masu hidimar kasa sukan kama sana’a ko su saka hannun jari a inda aka tura su, wasu kuwa komawa garuruwansu suke yi bayan sun kammala. Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai...
Yadda Matasa Ke Bada Gudunmawar Cigaban Al’ummarsu 27.03.2026 28:24
Send us Fan Mail Samun matasan dake bada gudunmawa a alummomin da suke rayuwa a cikin ta yana da matukar wuya a wannan zamani. Amma duk da haka, wasu matasa sun sadaukar da rayuwarsu wajen bada gudunmawarsu wajen cigaban alummarsu. Shirin Najeirya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan irin gudunmawar da matasa ke badawa wajen cigaban alummarsu
Yadda Na Rasa 'Ya'ya Na Ga Guban Abinci 26.03.2026 25:47
Send us Fan Mail Cin guba ta hanyar abinci (food poisoning) wata cuta ce da ke faruwa idan mutum ya ci abinci ko ya sha abin sha da ya gurɓace. Gurɓacewar abincin na iya fitowa daga ƙwayoyin cuta kamar Salmonella, E. coli, ko Listeria, ko kuma daga ƙwayoyin cutar virus, ƙwari (parasites), ko sinadarai masu guba. Alamomin cutar sun haɗa da ciwon ciki, amai, zazzabi, gudawa, da rashin jin daɗin ji...
Daga Alkawari Zuwa Mulki, Yadda Siyasa Ke Sauya Manufa 24.03.2026 27:00
Send us Fan Mail Duk bayan shekaru hudu, Najeriya na kara yin zabe kuma ko wanne lokaci 'yan takara kan dauki alkawurika. Ko shekaru nawa wadanda ake zabe ke bukata don cika alkawuran da suka dauka? wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.
Similar podcasts
Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.