Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Where to listen?
Podcasts in the app Replaio Radio Coming soonPodcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts
Episodes
Abubuwan Da Za Su Kwadaita Muku Azumtar Sitta Shawwal 23.03.2026 24:06
Send us Fan Mail Alqurani mai girma a cikin suratul Baqarah Allah ya wajabta wa musulmi da suka cika wasu sharudda azumtar watan Ramadana. Kamar yadda malamai suka sha fadi, wannan wata na dauke da wasu falala maras misaltuwa da bawa kan samu idan ya maida kai wajen ibada don samun rabauta daga ubangiji. Kazalika hadisai sun ruwaito kan falalar azumtar kwanaki shidda na watan shawwal, watan dake b...
Azumin Ramadana: Ko Kun San Dabinon Da Kuke Shan Ruwa Da Shi? 13.03.2026 30:13
Send us Fan Mail Ko kun san sunan dabinon da kuka fi so ku ci a lokacin shan ruwa? Dan Agadas ne, ko Ruwa-Ruwa, ko Annakhiyl? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai ya yi nazari ne kan nau’ukan dabino da alfanunsa ga dan’Adam, musamman mai azumi.
Kalubalen Dake Tattare Da Samar Da ‘Yansandan Jihohi A Najeriya 06.03.2026 25:43
Send us Fan Mail Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sha nanata muhimmancin samar da ’yan sandan jihohi a Nigeria, yana mai cewa hakan na daga cikin hanyoyin da za su taimaka wajen magance matsalolin tsaro da ke addabar sassa daban-daban na kasar. Shugaban ya bayyana cewa tsarin ’yan sanda da ke karkashin gwamnatin tarayya kadai ba zai iya biyan bukatun tsaro na kasa mai yawan jama’a da fadi kamar...
Yadda Cutar Zazzabin Lassa Ke Kisa Da Hanyoyin dakile Ta 05.03.2026 19:44
Send us Fan Mail A yayin da Najeriya ke fuskantar kalubale daban-daban a fannin lafiya, cutar zazzabin Lassa ta sake ɗaga kai a wasu jihohin ƙasar. Cutar wadda ake dangantawa da berayen da ke ɗauke da ƙwayar cutar, tana yawaita ne musamman a lokutan sanyi zuwa farkon damina, lamarin da ke jefa al’umma cikin fargaba a kowace shekara. Rahotanni daga hukumar dake hana yaduwar cututtuka ta Najeriya su...
Yadda Ake Kamuwa Da Basir Da Hanyoyin Magance Ta 04.03.2026 26:06
Send us Fan Mail Cutar basir na daga cikin cututtukan da mutane da dama ke da mabanbantan ra’ayoyi akan ta. A lokuta da dama za ka ji yadda mutane ke fadin dalilai daban daban da ke janyo cutar basir, yayin da wasu ke ganin yawan zama ne ke kawo ta, wasu kuwa gani suke yi zaki da maiko ne ke kawo ta. Wannan shine abun da da yawa daga cikin mutane suka sani kan wannan cuta, sai dai masana kiwon laf...
Yadda Azumi Ke Inganta Lafiyar Jiki 03.03.2026 29:58
Send us Fan Mail Alumma na yin azumi ne bisa dalilan addini don samun lada kamar yadda Allah ya umurta a cikin Qurani mai girma. Sai dai daga baya binciken masana kimiyya ya gano cewa bayan lada da ake samu daga yin azumi, akwai wasu alfanu da mai azumi ke samu ga lafiyar jikin shi da suka hada da inganta karfi da zurfin tunani zuwa fitar da gurbatattun abubuwa da jiki baya bukata. A takaice dai...
Falalar Bude Baki Cikin Iyali A Lokacin Azumi 27.02.2026 26:29
Send us Fan Mail Hadisi ya tabbatar da yadda cin abinci tare yake kara dankon zumunci da kaunar juna da albarka a tsakanin al’umma. Mai yiwuwa wannan ne ya sa akan samu Karin kusanci da shakuwa a tsakanin duk iyalan da kan zauna su ci abinci. Ko kafin watan azumi dai, wasu magidantan kan mayar da cin abinci tare da tare da iyalin su al’ada. Shin ko mene ne matsayin bude-baki tare da iyali a wat...
Me Nadin Sabon Sufeton 'Yansanda Ke Nufi Ga Tsaron Cikin Gida Najeriya? 26.02.2026 18:51
Send us Fan Mail Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa sabon Sufeto Janar na ‘Yan Sanda (IGP), matakin da ya sake jawo hankalin al’umma kan makomar tsaro da gyaran harkokin rundunar ‘yan sandan ƙasar nan. Naɗin sabon jagoran rundunar ya zo ne a daidai lokacin da ake fuskantar ƙalubale daban-daban na tsaro, ciki har da satar mutane, ta’addanci, da rikice-rikicen cikin gida a wasu sassan ƙasa. S...
Shin Da Gaske An Fara Samun Ɓaraka Tsakanin Atiku Abubakar Da Peter Obi A Tafiyar ADC? 24.02.2026 20:11
Send us Fan Mail Rahotanni daga sassa daban-daban na siyasar Najeriya na nuna cewa ana fara samun ɓaraka a tsakanin manyan jiga-jigan haɗakar tafiyar ADC, musamman tsakanin tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi. Ko da yake har yanzu babu wata sanarwa ta hukuma da ke tabbatar da wannan saɓani, majiyoyi na nuni d...
Falalar Sallan Tarawih Ga Alummar Musulmi A Watan Ramadan 20.02.2026 17:10
Send us Fan Mail A duk lokacin da watan azumin Ramadan ya kama, al’ummar Musulmi kan cika masallatai domin gudanar da sallar Tarawihi cikin karsashi da himma. A kwanakin farko, ana ganin sahu sun cika, zuciya cike da nishadi da kwadayin lada. Sai dai abin takaici, bayan wasu kwanaki, wasu kan fara ja da baya — wani saboda gajiya, wani saboda shagaltuwa da harkokin yau da kullum, ko kuma rashin jur...
Dalilan Kamuwa Da Cutar Hawan Jini Da Hanyoyin Magance Ta 19.02.2026 24:51
Send us Fan Mail Cututtuka da dama suna Kamari a Najeriya wanda a mafi yawancin lokuta ma wadanda ke dauke da irin wadannan cututtukan basu da masaniyar suna dauke da su. Kamar yadda majalisar dinkin duniya ta bayyana, zaman lafiya, rashin matsalar kwakwalwa, da samun wadata na daga cikin abubuwan dake tabbatar da lafiyar bil’adama. Wata cuta da ta addabi da yawa daga cikin al’umma itace cutar H...
Yadda Masu Larurar Ulcer Za Su Gudanar Da Azumin Ramadan Ba Tare Da Matsala Ba 17.02.2026 18:14
Send us Fan Mail A duk lokacin da watan azumi ya zo, Musulmai da dama sukan karɓe shi da murna da shauƙi, suna shirya ibada da ƙara kusanci da Allah. Sai dai ga wasu, musamman masu fama da larurar gyambon ciki wato ulcer, watan azumi kan zo da wani yanayi na damuwa da fargaba. Yayin da wasu ke jin daɗin azumi, su kuma suna cikin ƙalubalen yadda za su iya jure yunwa da ƙishirwa ba tare da cutar ta...
Yadda Muka Yi Asarar Miliyoyin Naira A Kasuwar Singa Muna Ji Muna Gani 16.02.2026 17:21
Send us Fan Mail ‘Yan kasuwa da dama a jihar Kano sun kwana sun tashi da juyayi da alhinin gobara da ta faru ta kuma lashe musu dimbin dukiyarsu suna ji suna gani ba tare da sun iya tabuka komai ba. Gobarar da ta tashi a kasuwar singa dake jihar Kano, ta fara ne da misalin karfe 4:30 na ranar asabar ta kuma cigaba da ci har zuwa wayewar garin ranar lahadi. Wannan gobara ta yi sanadiyyar raba ‘yan...
Ya Kamata Najeriya Ta Samar da Dokoki Kan Amfani da AI? 13.02.2026 25:30
Send us Fan Mail Tun bayan bayyanar kirkirarrriyar basira wato AI ne dai wasu mutane suke amfani da ita ta hanyar da da bai kamata ba. Wasu sukan yi amfani da ita wajen saka hoto ko kirkirar faifan bidiyo wanda zai nuna wani yana yin abun da bai kamata ba. Hakan dai ya sa wasu suna ganin ya kamata a samar da dokokin da za su rinka lura da yadda ake amfani da kirkirarriyar basirar. Shirin Najeri...
Hanyoyin Magance Laifukan Da Matasa Ke Aikatawa A Cikin Al'umma 12.02.2026 24:44
Send us Fan Mail Masu iya magana kan ce banza ba ta kai zomo kasuwa. In ba haka ba, me ya kai matasan da ake zargi da aikata manyan laifuffuka ofishin ’yan sanda, suka kuma fit oba tare da wani ya harae su ko ya yi mutsu tsawa ba, balle ya saka su a cell? ’Yan sandan dai sun ce wannan wata dabara ce ta yakar aikata manyan laifuka irin su sata da fashi da makami da kwacen waya da fyade kai har ma...
Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Sa Samun Wadataccen Abinci 10.02.2026 25:59
Send us Fan Mail A wannan zamani, ’yan Najeriya da dama ba sa samun wadataccen abinci a yini. Magidanta da dama, musamman, sun tsallake sun bar iyalansu sun shiga bariki don neman na sanyawa a bakin salati. Mene ne dalilin hakan, kuma yaya za a yi a kauce wa fadawa cikin irin wannan yanayi? Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan halin da galibin ’yan Najeriya suka tsin...
Dabarun Bunkasa Kasuwanci A Intanet 09.02.2026 27:23
Send us Fan Mail Masu iya magana kan ce “zamani riga”. Sauyin zamani ya kawo sauye-sauye da dama a yadda ake gudanar da harkoki, ciki har da kasuwanci. A yanzu haka, zamani, intanet na taka muhimmiyar rawa wajen tallata haja ko saye da sayarwa. Shrin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan dabarun da za ku iya amfani da su don bunkasa kasuwancinku ta hanyar amfani da intanet.
Tasirin Yankan Al’aura A Rayuwar 'Ya'ya Mata 06.02.2026 25:44
Send us Fan Mail A tsakanin al’ummomi daban-daban akan samu wasu al’adu na yanke wani bangare na al’aurar ’ya’ya mata saboda wasu dalilai. A kasar Hausa akan yi abin da ake kira yankan angurya da nufin rage wa mace sha’awa, musamman kafin ta yi aure. Ko menene tasirin wannan al’ada a rayuwar ’ya’ya mata? Albarkacin Ranar Yaki da Yankan Al’aurar Mata ta Duniya, shirin Najeriya A Yau zai yi nazari...
Hanyoyin Mallakar Gida Ga Mai Karamin Karfi 05.02.2026 24:47
Send us Fan Mail Mallakar muhalli na cikin burace-buracen kusan kowanne dan Najeriya. Sai dai wadannan burace-burace, a galibin lokuta, ba sa cika – musamman ga masu matsakaitan samu. Amma wasu masana suna ganin akwai dabarun da marasa karfi ma za su iya amfani da su don su mallaki nasu muhallin, daidai ruwa daidai tsaki. A kan wadannan dabaru shirin Najeriya A Yau zai yi nazari..
Abin Da Ya Kamata Ku Yi Yayin Takaddama Da ’Yan Sanda 03.02.2026 20:08
Send us Fan Mail Babban alhakin da Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya dora wa Rundunar ’Yan Sanda shi ne kare rayuka da dukiyoyin ’yan kasa. Sai dai a lokuta da dama, akan samu fito-na-fito sakamakon zargin ’yan sanda da wuce gona da iri wajen gudanar da aiyyukan nasu. Shirin Najeriya a Yau ya tattauna a kan yadda abubuwan da ya kamata ’yan kasa su yi idan ’yan sanda suka nemi cin zalinsu.
Rayuwar Mazan Da Ba Sa Haihuwa 02.02.2026 21:40
Send us Fan Mail Rashin haihuwa matsala ce da ka iya wargaza gidajen aure musamman a wannan zamani. Da an samu shekara biyu zuwa uku bayan an daura aure ba tare da an samu karuwa ba za a fara yamadidi da matar a kan ba ta haihuwa. Sai dai likitoci sun ce maza ma ka iya fama da wannan larura saboda wasu dalilai. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan wadannan matsalolin da su...
Radadin da masu amosanin jini suke sha 28.01.2026 23:35
Send us Fan Mail
Inda Aka Mike Da Inda Aka Kauce Tun Bayan Dawowa Mulkin Dimokuraɗiyya A Jamhuriya Ta Hudu 23.01.2026 15:09
Send us Fan Mail Kamfanin yaɗa labarai na Media Trust ya daɗe yana taka muhimmiyar rawa wajen buɗe tattaunawa masu ma’ana kan manyan al’amuran da suka shafi tafiyar da ƙasa da dimokuraɗiyya a Najeriya. Daga cikin fitattun shirye-shiryensa akwai muhawarar shekara-shekara da kamfanin ke shirya wa, wadda ta zama wani dandali na musamman da ke haɗa masana, ‘yan siyasa, masana doka, da masu ruwa da tsa...
Tasirin Siyasar Matasa A Najeriya Tun Bayan Dawowar Jamhuriya Ta Hudu 20.01.2026 19:57
Send us Fan Mail Shekaru kafin a sanya hannu kan dokar Not Too Young To Run , siyasar matasa a Najeriya na fuskantar ƙalubale masu tarin yawa. Duk da cewa matasa su ne mafi rinjaye a yawan al’umma da kuma masu katin zaɓe, an dade ana kallonsu ne a matsayin masu ɗaukar tutoci, da yaɗa saƙonni ko kuma masu tayar da tarzoma a lokacin zaɓe, ba tare da ba su cikakkiyar dama ta tsayawa takara ko shiga m...
Yadda Siyasar Ubangida Ta Yi Tasiri Ga Siyasar Najeriya A Jamhuriya Ta Hudu 19.01.2026 25:06
Send us Fan Mail Tun bayan dawowar mulkin farar hula a shekarar 1999, siyasar Najeriya ta kasance karkashin inuwar wasu ’yan tsiraru da ake kira iyayen gidan siyasa. Wannan tsari ya ginu ne a kan karfin mutum guda ko rukuni, inda su ke rike da makullin jam’iyya, su tsara wa’adi, su zabi ’yan takara, su kuma yanke hukunci ba tare da la’akari da ra’ayin mafi yawan mambobi ko jama’a ba. A Jamhuriya t...
Similar podcasts
Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.