Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Where to listen?
Podcasts in the app Replaio Radio Coming soonPodcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts
Episodes
Untitled Episode 17.01.2026 23:38
Send us Fan Mail
Abun Koyin ‘Yan Siyasa Da Matasa Kan Jarumtar Goodluck Jonathan A 2015 16.01.2026 19:09
Send us Fan Mail Kiran wayan da tsohon Shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan ya yi wa marigayi Muhammadu Buhari ta bar tarihi mai muhimmanci a Najeriya. Waya da ta kwantar da hankalin kasa, ta kuma dakatar da fargabar tashin hankali. A ranar da sakamakon zaben shekarar 2015 ya fara bayyana, tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Ebele Jonathan, ya zabi zaman lafiya a kan mulki, ya kuma zabi Najeriya a ka...
Bayan Shekaru Sittin, Me Ya Sa Har Yanzu Ake Tunawa Da Su Sardauna? 15.01.2026 21:37
Send us Fan Mail A tarihin kowace ƙasa, akwai wasu mutane da ba lokaci ko sauyin zamani ke iya gogewa daga ƙwaƙwalwar al’umma ba. A Najeriya, waɗannan su ne founding fathers — jagororin da suka tsaya tsayin daka wajen jagorantar gwagwarmayar neman ’yancin kai, kafa tubalan dimokuraɗiyya, da shimfiɗa tsarin ƙasa tun kafin a haifi Jamhuriyar Tarayya ta Najeriya. Gudunmawarsu ba ta tsaya kawai ga siy...
Zabukan Da Aka Gudanar Lokacin Dawowar Mulkin Farar Hula A Jamhuriya Ta Hudu 13.01.2026 21:52
Send us Fan Mail Bayan kusan shekaru goma sha shida na mulkin soja, Najeriya ta dawo kan tafarkin mulkin farar hula a shekarar 1999, abin da ya buɗe sabon babi a tarihin siyasar ƙasar. Zaɓen da aka gudanar a wannan lokaci shi ne zaɓen farko na Jamhuriya ta Huɗu, inda aka gudanar da zaɓukan kananan hukumomi, majalisun dokoki, gwamnoni da kuma shugaban ƙasa a ƙarƙashin kulawar Hukumar Zaɓe ta Ƙasa,...
Waiwaye Kan Yadda Jam’iyyun Siyasa Suka Kafu A Jamhuriya Ta Hudu 12.01.2026 29:28
Send us Fan Mail Jamhuriya ta Huɗu a Najeriya ta fara ne a ranar 29 ga Mayu, 1999, bayan kawo ƙarshen mulkin soja, inda ƙasar ta koma tafarkin dimokuraɗiyya bisa Kundin Tsarin Mulki na 1999. A wannan lokaci ne aka kafa manyan jam’iyyun siyasa kamar PDP, wadda Alex Ekwueme, Solomon Lar da wasu tsofaffin ‘yan siyasa suka jagoranci kafuwarta; APP (daga baya ANPP) ƙarƙashin jagorancin Mahmud Waziri da...
Lokacin Da Ya Kamata A Fara Yakin Neman Zaben 2027 08.01.2026 10:05
Send us Fan Mail A siyasar Najeriya, akwai ka’idoji da dokoki da ke tsara yadda ake gudanar da zaɓe, ciki har da lokacin da doka ta amince a fara yaƙin neman zaɓe. Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, wato INEC, ita ce ke da alhakin bayyana jadawalin zaɓe da kuma ranar da ‘yan takara za su fara neman goyon bayan al’umma a hukumance. Sai dai duk da waɗannan tanade-tanade, ana ci gaba da ganin alamu da ayyuka da...
Yaya Matsayar Katsalandar Din Da APC Tace Nyesom Wike Na Yi A Jam’iyyar? 07.01.2026 14:57
Send us Fan Mail A cikin ‘yan kwanakin nan, siyasar Najeriya ta sake daukar sabon salo, bayan barkewar takaddama tsakanin Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, da manyan shugabannin jam’iyyar (APC). Jam’iyyar APC na kallon yadda Wike — wanda ba cikakken ɗan jam’iyyar ba ne amma ke rike da mukami a karkashin gwamnatinta — ke yin katsalandan a harkokin jam’iyyar, musamman a matakin jiho...
Yadda ‘Yan Bindiga Suka Yanka ‘Yan Kasuwa A Jihar Neja 06.01.2026 15:14
Send us Fan Mail Harin da wasu ‘yan ta’adda suka kai kasuwar Daji da ke karamar hukumar Borgu a Jihar Neja ya sake jawo hankalin al’umma kan matsalar rashin tsaro da ke kara ta’azzara a yankunan karkara na Arewa ta Tsakiya. Kasuwar Daji, wadda ke zama cibiyar hada-hadar kasuwanci ga manoma, ‘yan kasuwa da mazauna kauyuka makwabta, ta kasance wuri na zaman lafiya kafin wannan mummunan lamari da ya...
Sharuddan Da Jam'iyya Za Ta Cika Kafin A Kira Ta Babbar Jam'iyyar Adawa 02.01.2026 23:04
Send us Fan Mail A fagen siyasar Najeriya a halin yanzu, ana ta ce-ce-ku-ce kan wacce ce babbar jam’iyyar adawa da za ta iya tsayawa ƙafada da ƙafada da jam’iyyar APC mai mulki. Wannan takaddama ta fi karkata ne tsakanin jam’iyyar PDP, wacce ta dade tana taka rawa a matsayin babbar jam’iyyar adawa bayan ficewarta daga mulki a 2015, da kuma jam’iyyar ADC, wacce a ‘yan shekarun nan ta fara samun kar...
Yadda Ya Kamata Ku Gudanar Da Rayuwa A Shekarar 2026 01.01.2026 17:00
Send us Fan Mail Shekarar 2026 ta zo a wani lokaci da ’yan Najeriya da dama ke fuskantar matsin tattalin arziki, da sauye-sauyen siyasa, da kuma ƙalubalen rayuwa da ke bukatar sabon tunani. Wannan ba lokaci ba ne na fatan samun sa’a kawai, lokaci ne na tsara hanya, da ɗaukar matakai, da yin gyara a rayuwar yau da kullum. A wannan shiri, za mu duba yadda ya kamata ’yan Najeriya su fara sabuwar shek...
Siyasa Da Tsare-tsaren Gwamnati Da Suka Dabaibaye 2025 30.12.2025 21:38
Send us Fan Mail Yayin da muke bankwana da shekarar 2025, siyasar Najeriya ta kasance cike da sauye-sauye, rikice-rikice, da kuma manyan al’amura da suka shafi iko, jam’iyyu da shugabanci. Shekarar ta shaida sauyin sheƙa na ‘yan siyasa, rikicin cikin gida a wasu jam’iyyu, da kuma fafutukar karɓar ragamar mulki a jihohi da matakin tarayya, lamarin da ya ƙara zafafa siyasar ƙasa. A bangaren tsare-ts...
Waiwaye Kan Manyan Kalubalen Tsaro Da Suka Faru A 2025 29.12.2025 18:49
Send us Fan Mail A shekarar 2025, Najeriya ta fuskanci manyan ƙalubalen tsaro da suka fi daukar hankali, musamman hare-haren ‘yan bindiga, garkuwa da mutane, da ta’addanci a jihohin Arewa kamar Zamfara, da Katsina da Sokoto da Kaduna da kuma Borno. Hare-haren sun yi sanadin rasa rayuka, da rufe makarantu, da kaura daga gidaje, da kuma durkushewar harkokin tattalin arziki a wasu yankuna. Wadannan m...
Yadda Kiristoci Ke Gudanar Da Bikin Kirsimeti A Cikin Musulmi 26.12.2025 16:33
Send us Fan Mail A duk faɗin Arewacin Najeriya, ana gudanar da bukukuwan Kirsimeti cikin kwanciyar hankali da fahimtar juna, duk da kasancewar Musulmai ne suka fi rinjaye a yawancin yankuna. Kiristoci kan yi bukukuwansu cikin mutunta al’adar Musulmai, yayin da Musulmai kuma ke nuna goyon baya ta hanyar gaisuwa, da tsaro, da mu’amala ta zamantakewa. A wurare da dama kamar Kaduna, Jos, Zaria, Minna...
'Halin Kunci Da Muke Ciki A Sansanin Gudun Hijira Yayin Bikin Kirsimeti' 25.12.2025 14:01
Send us Fan Mail A yayin da al’ummar Kirista a sassa daban-daban na ƙasar nan ke gudanar da bukukuwan Kirsimeti cikin walwala, da annashuwa da haɗuwa da iyalai, akwai kuma waɗanda wannan lokaci ya zo musu cikin ƙunci da jimami. Waɗannan su ne mutanen da matsalolin tsaro—kamar hare-hare da rikice-rikice—suka tilasta musu barin gidajensu da muhallansu. A maimakon shagulgula a cikin gidajensu, suna...
Yadda Farashin Kayayyaki Suke Gabanin Bukukuwan Kirsimeti 24.12.2025 14:23
Send us Fan Mail Gabannin bukukuwan Kirsimeti, kasuwanni a sassan ƙasar nan sun cika sun bunkasa. Jama’a na ci gaba da zirga-zirga domin sayen kayan bukukuwa, yayin da ‘yan kasuwa ke kokarin jawo hankalin masu saye ta hanyar daidaita farashi. A wannan shekarar, alamu sun nuna ba a samu hauhawar farashin kayayyaki a yawancin kasuwanni ba, sai dai wasu na kokawa da rashin kudaden saye. Ko yaya hak...
Cushe-cushen Da Ake Zargin An Yi A Sabbin Dokokin Haraji 23.12.2025 19:37
Send us Fan Mail Takaddama mai zafi ta dabaibaye sabbin dokokin haraji da Majalisar Tarayya ta amince da su, bayan zarge-zargen cewa an samu sauye-sauye a cikin dokokin bayan an kammala dukkan matakan amincewa da su a majalisa. Batun da ya taso ya jawo cece-kuce daga ‘yan majalisa, jam’iyyun adawa da kungiyoyin fararen hula, inda suke tambayar sahihancin abin da aka mika wa Fadar Shugaban Kasa dom...
Irin Asarar Da Aka Tafka A Kasuwar Kafintoci Dake Kano 22.12.2025 18:46
Send us Fan Mail Gobara a irin wannan yanayi na iska musamman a kasuwanni da gidaje ba sabon abu bane kuma ba abun mamaki ba. Wasu kafintoci dake aiki a kasuwar lale dake unguwar Tal’udu a karamar hukumar Gwale dake jihar Kano sun wayi gari da alhinin gobarar da ta yi sanadiyyar raba su da hanyar abincinsu. Wannan gobara da ba’a san musabbabinta ba ta janyo asarar miliyoyin Naira tare da jefa wad...
Darasin Da Za a Yi Koyi Dashi Cikin Takaddamar Dangote Da Farukh Ahmed 19.12.2025 18:45
Send us Fan Mail Murabus din da Shugaban Hukumar Kula da Harkokin Mai ta kasa Ahmed Farukh ya yi daga mukaminsa ya sa ‘yan Najeriya da dama na ta tofa albarkacin bakinsu musamman a bangaren harkokin mai. Murabus din na zuwa ne bayan doguwar takaddama tsakaninsa da Shugaban Rukunin Kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote kan batutuwa da dama. Shin ko wanne darasi za a koya daga wannan takaddama da t...
Yadda Takunkumin Amurka Zai Shafi Tattalin Arzikin ‘Yan Najeriya 18.12.2025 16:25
Send us Fan Mail Takunkumin da Shugaban Ƙasar Amurka, Donald Trump, ya sanya wa wasu ‘yan Najeriya ya sake jawo hankali kan irin tasirin manufofin ƙasashen waje ga rayuwar mutane da tattalin arzikin ƙasa baki ɗaya. Wannan takunkumi, wanda ya haɗa da hana shiga Amurka, da toshe kadarori ko hana mu’amala da wasu hukumomi da kamfanonin Amurka, ba wai hukunci ne ga mutum ɗaya kaɗai ba, kazalika yana...
Ce-ce Ku-ce Da Ya Dabaibaye Dauke Shalkwatar Bankin Masana’antu Zuwa Legas 16.12.2025 14:58
Send us Fan Mail Batun matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na mayar da shalkwatar Bankin Masana’antu zuwa jihar Legas ya haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin ’yan Najeriya. Wannan mataki ya tayar da mabanbantan ra’ayoyi daga bangarori daban-daban na al’umma, inda wasu ke kallonsa a matsayin shawara mai ma’ana da za ta karfafa harkokin masana’antu da jawo jarin cikin gida da na kasashen waje. Sai dai...
Yadda Matsalar Tsaro Ke Hana Mu Tafiye-tafiyen Kirsimeti 15.12.2025 15:19
Send us Fan Mail A ’yan shekarun nan, lokaci na bukukuwan ƙarshen shekara—wanda a da ake ɗauka a matsayin lokacin farin ciki, da haɗuwa da iyalai, da tafiye-tafiye—ya fara sauya salo ga mutane da dama. Maimakon shirye-shiryen ziyartar ’yan uwa ko halartar bukukuwa a garuruwa daban-daban, mutane da yawa yanzu suna cike da fargaba da damuwa. Babban dalilin hakan shi ne ƙalubalen tsaro da ke ƙara tsa...
Alfanu Da Kalubalen Sabon Jadawalin Karatun Makarantu Da Gwamnati Ta Bijiro Dashi 11.12.2025 15:19
Send us Fan Mail A kwanakin baya, Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da sabon tsarin jadawalin karatu ga makarantun firamare da sakandare. Sabon tsarin, wanda Ma’aikatar Ilimi ta ƙasa ta tsara, yana da nufin inganta koyarwa da koyo, da rage nauyin lodi ga dalibai, da kuma tabbatar da cewa malamai suna da isasshen lokaci don isar da darussa tare da kwarewa. Tsarin ya mayar da hankali kan daidaita ranaku...
Yadda Abincin Da Mutane Ke Ci Ke Zamewa Guba 09.12.2025 17:01
Send us Fan Mail A yau al’ummar mu na fuskantar barazana ta wata siga da ba kasafai ake gane ta ba, wato guba da ke shiga jikin ɗan Adam ta hanyar abinci irin su nama, kifi, madara da sauran kayayyakin da muke ci a kullum. Sau da yawa dabbobi ko kifaye suna cin wasu tsirrai, ganye, ko ababen da ke dauke da sinadarai masu haɗari, waɗanda daga baya suke taruwa a jikinsu har su zama guba ga mutum ida...
Kudaden Da Samar Da ‘Yansandan Jihohi Zai Lashe 08.12.2025 22:20
Send us Fan Mail Batun samar da ‘yansandan jihohi na ƙara ɗaukar hankalin ‘yan Najeriya, musamman a dai-dai lokacin da matsalar tsaro ke ƙara ta’azzara a sassa daban-daban na ƙasar nan. Sai dai, samar da ‘yansandan jihohi ba abu ne mai sauƙi Kamar yadda wasu ke tunani ba. Gwamnatocin jihohi na buƙatar abubuwa masu yawa kafin su iya ɗaukar wannan nauyi, banda batun samar da dokar samar da wadannan...
Abun Da Masu Ruwa Da Tsaki Ke Yi Na Dakile Laifuka A Wurin Matasa 04.12.2025 24:44
Send us Fan Mail Masu iya magana kan ce banza ba ta kai zomo kasuwa. In ba haka ba, me ya kai matasan da ake zargi da aikata manyan laifuffuka ofishin ’yan sanda, suka kuma fit oba tare da wani ya harae su ko ya yi mutsu tsawa ba, balle ya saka su a cell? ’Yan sandan dai sun ce wannan wata dabara ce ta yakar aikata manyan laifuka irin su sata da fashi da makami da kwacen waya da fyade kai har ma...
Similar podcasts
Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.