Jamilah Tangaza

Gaskiyar Magana

News HA ↓ 24 episodes

Siyasa Raayi Alumma

Author

Jamilah Tangaza

Category

News

Latest episode

Jul 8, 2026

Where to listen?

Podcasts in the app Replaio Radio Coming soon

Podcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts

Get it on Google Play Install for free Android 5M+ downloads · 4.8 rating iOS soon

Episodes

Rudani: Hukunce-Hukuncen Kotuna a Nigeria 08.07.2026

Tattaunawa da Barista Umar Isa Suleiman, fitaccen lauya a Nigeria, wanda ke sharhi kan yadda ake gudanar da harkokin shari'a a wannan zamani na siyasa a kasar.

Tun Da Farko Aka Saki Hanya 06.07.2026

Yaya tsarin dimokradiyya da gudanar da mulki ke tafiya yanzu a Nigeria? Hira da Dr Hakeem Baba Ahmed, fitaccen mai fafutukar wanzar da mulki na-gari. 

Dimokradiyyar Nigeria A Yau 30.06.2026

Hira da Dr Sadiu Ahmad Dukawa ya kan dangantakar siyasa da tsaro. Ya fara da yin tsakaci a game da halin tsaro yanzu a Nigeria. 

Mutanen Kasa Ne Zasu Kawo Sauyi A Najeriya 30.06.2026

Dr Saidu Ahmad Dukawa masanin Tarihi da Siyasa na jami'ar Bayero dake Kano ya ce 'yan Najeriya dole su jajirce wajen kawo gyara a harkokin mulkin kasar. 

Sauya Dokar Zabe Ita Ce Mafita 24.06.2026

A wannan hirar da Dr. Aliyu Tilde, masanin siyasa a Nigeria, ya ce dole fa, sai an yiwa dokar zabe gyara muddin ana san saita tsarin dimokradiyya a kasar.

Neman Mafita Ga Dimokradiyyar Nigeria 22.06.2026

Dr Aliyu Tilde masanin tarihi da siyasa daga jihar Bauchi ya fadi yadda za'a samu mafita a tsarin dimokradiyyar Nigeria dake tangal-tangal. 

Rashin Tsaro: Dole Sai An Tashi Tsaye 17.06.2026

Tattaunawa da Profesa Kamilu Sani Fagge, masanin mikiyyar siyasa na jami'ar Bayero dake Kano, kan yaya za'a kawo karshen rashin tsaro a Nigeria. 

Rashin Tsaro A Nigeria: Tushe Da Magani 15.06.2026

Sharhi kan tushen matsalar rashin tsaro a Nigeria, da kuma sakamakon da rashin tsaron ya haifar a kasar, musamman a yankin Arewa. 

Dogaro Da Kai A Matasa 13.06.2026

Hira da matashi Abubakar Haruna, mai aikin wutar lantarki, kan mahimmancin dogaro da kai a tsakanin matasan Nigeria. 

Jagaliya: Matasa Ko Matsala? 02.06.2026

A ci gaba da hira da wani dan dabar siyasa, a wannan shiri ya bayyana irin rawar da 'yan jagaliya suke takawa a ranakun zabe. 

Kowa Na Da Hakki: 'Yan Dabar Unguwanni 01.06.2026

Tattaunawa da Ambasada Yunusa Yusuf Hamza mai gwagwarmayar yaki da shaye-shaye da fadace-fadace tsakanin matasa a Kano.

Jagaliya: Matasa A Siyasar Nigeria 01.06.2026

Hira da wani dan daba dake bayyana yadda 'yan siyasa ke daukar su aiki a matsayin 'yan banga ko jagaliyar siyasa a manyan birane.  

Mata a Siyasar Nigeria 20.05.2026

Me yasa har yanzu mata ke fuskantar kalubale wajen shiga siyasa? Hira da Dr Asabe Vilita Bashir, tsohuwar 'yar siyasa daga jihar Borno. 

Siyasar Ubangida: Amfani ko Illa? 18.05.2026

A wannan shiri mun yi hira da dan Siyasa Hon. Abdullahi D. Dankano, dangane da batun siyasar Ubangida a Nigeria. Ya duba amfani da illolin ta. 

Rikicin Jam'iyyu: Tsohuwar Magane Ce? 13.05.2026

Hira da Profesa Shua'ibu Shehu Aliyu, masanin tarihi da siyasa, kuma tsohon malami a jami'ar Ahmadu Bello ta Zaria. Ya ba da karin haske kan matsalar da ta zama ruwan dare. 

Rikicin Jam'iyyun Siyasa: Da & Yanzu 11.05.2026

Menene dalilan da suke sanya jam'iyyun siyasa a Nigeria a kullum suke cikin rikici? Yaushe aka fara samun wannan matsala a tarihin tsahon shekaru sama da 100 da kasar ke siyasa karkashin jam'iyyu? 

Siyasar Kudi Za Ta Hanu? 06.05.2026

Tattauna da dan siyasa Hon. Abdullahi Dalhatu Dankano, tsohon sakataren  tsohuwar jam'iyyar CPC na jihar Kano. Ya bayyana kalubalen da ke tattare da wannan batu da ya ce kowa na da laifi a ciki.

Siyasar Kudi a Nigeria 04.05.2026

Mun yi nazari kan yadda ake amfani da kudi a siyasar Nigeria. Mun duba tasirin da siyasar kudi take yi bisa tsarin dimokradiyya. 

Lalacewar Zabe: 'Yan Kasa na da Hannu? 29.04.2026

A shirin yau mun tattauna da fitaccen masani kan harkokin siyasa da zamantakewa Profesa Bello Bada, inda yayi tsokaci kan magudin zabe, da wadanda ke da hannu a lalacewar harkar zabe da dimokradiyyar Nigeria. 

Hukumar Zabe Na da 'Yancin Kanta? 27.04.2026

A wannan shiri mun tattauna da Profesa Bello Bada, masanin tarihi da siyasa, kuma malami a jami'ar Usman Danfodio, dake Sokoto, kan jin ko hukumar zaben Nigeria (INEC) na da 'yancin kanta. Idan ba ta da shi, yaya za'a yi a gyara?

Zabe a Nigeria - Tsari da Kalubale 22.04.2026

A cikin wanamn shiri, mun tsunduma cikin wani muhimmin batu: wato - tsarin zaɓe a Najeriya. Ta yaya ake gudanar da zaɓe? Wa ke da alhakin shirya shi? Kuma menene manyan ƙalubalen da ke fuskantar sahihancin zaɓe a Nigeriar?

Tirelar Gaskiyar Magana 20.04.2026
Mishimfidar Dimokradiyyar NIgeria 20.04.2026

Shinfida dangane da takaitaccen tarihin tsarin democradiyya a Nigeria, kafin mu fahimci ainihin abunda ke faruwa a fagen siyasar kasar a yanzu. 

Taken Shiri 13.04.2026

Taken sabon shirin da zamu dinga gabatarwa.

Listen to the Gaskiyar Magana podcast in Replaio

Radio and podcasts in one app - free, with no sign-up. Install today and do not miss the launch

Get it on Google Play

Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.