Jamilah Tangaza
Gaskiyar Magana
Siyasa Raayi Alumma
Où écouter ?
Les podcasts dans l'appli Replaio Radio Bientôt disponibleLes podcasts arrivent très bientôt dans l'appli. Installe-la dès maintenant et découvre en avant-première une toute nouvelle façon de vivre les podcasts
Épisodes
Me Matasan 'Yan Siyasa Ke Cewa? 28.09.2026 2:57
A shirin yau mun tattauna da Hon. Bello Babajo, daya daga cikin matasan 'yan Najeriya da a yanzu haka ma shi ne shugaban jam'iyya a jiharsa. Ko yaya su ke kallon kamun ludayin magabatansu 'yan siyasa?
Hukuncin Kotun Koli Da Zaben Fidda Gwani 28.09.2026 12:35
Wani hukuncin Kotun Koli na makon da ya gabata ya ja hankali. A shirin yau, mun tattauna da masanin shari’a a Najeriya Barrister Umar Isa Sulaiman dan jin takamaimai abin da wannan hukunci na Kotun Kolin ke nufi ga zaben 2027.
Yaya Jam'iyyu Su Ke Yakin Neman Zaben 2027? 21.09.2026 11:47
A wannan shirin, Profesa Bello Bada, fitaccen masanin harkokin siyasa, kuma malami a jami’ar Usman Dan Fodio dake Sokoto, ya maida hankali kan dalilin da ya sa har yanzu ake batun kabila a zaben Najeriya.
INEC TA BUDE KOFAR YAKIN NEMAN ZABE 16.09.2026 12:37
A yau, mun tattauna kan shirin jam’iyyun siyasar Najeria dangane da zaben 2027 da Profesa Bello Bada, fitaccen masanin harkokin siyasa, tarihi da al’adu, kuma malami a jami’ar Usman Dan Fodio dake Sokoto.
Me Ya Faru Bayan Fafutukar Kafa Dimokradiyya? 14.09.2026 10:05
A wannan shirin mun tattauna da daya daga cikin wadanda suka yi fafutukar wanzar da dimokradiyya, Alhaji Abdulkarim Dayyabu, dan ji ko ya gamsu da yadda ake gudanar da tsarin dimokradiyya a Najeriya a yanzu?
Nasara Bayan Kalubale A Ilimi 09.09.2026 11:15
A wannan kashi na hirata da Profesa Rahinatu, za mu ji yadda ta tunkari kalubale a matsayinta na mace, matashiya, bayan da ta yanke shawarar barin kasarta Najeriya dan neman ilimi.
Nasarar Ilimin Mata A Yau 07.09.2026 9:40
A wannan shirin mun tattauna da Profesa Rahinatu Muazu, malama a Jamiar Kansas dake Amurka dan jin yadda tafiyarta ta kasance bayan an yi mata aure tana mai shekaru 15 a duniya.
ILIMIN MATA: NASARORI DA KALUBALE 02.09.2026 12:40
A wannan shiri, mun duba sauyin da aka samu na bai wa ‘ya’ya mata karatu a kasar Hausa kamar Kano. Na tattauna da Profesa Zubaida Farouk Ladan, likitan yara, kuma malama a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano dan jin yadda tafiyarta a ilimin boko, ta kasance.
HASARA: KAURAR KWARARRU DAGA NAJERIYA 02.09.2026 12:39
Najeriya na tafka hasara inda kwararrunta ke ficewa daga kasar. A wannan shirin na Gaskiyar Magana, mun tattauna da Profesa Zubaida Farou-Ladan, malamar koyar da aikin likita a Jami’ar Bayero dake Kano, dan jin yadda su ke ji a game da guduwa daga Najeriya da likitocinsu ke yi zuwa kasashen waje.
MULKIN SOJE DA FAFUTUKAR WANZAR DA DIMOKRADIYYA A NAJERIYA 02.09.2026 12:38
Tun daga mulkin turawan mulkin mallaka har zuwa mulkin soje. A shirin mu na yau mun tattaunawa da Alhaji Abdulkarin Dayyabu, shugabqn Kungiyar Rundunar Adalci, dan jin abin da ya sa suka dage dan ganin sun kori sojoji daga mulkin Najeriya.
FASAHAR SADARWA: SAUYE-SAUYE A AL'ADAR HAUSAWA 02.09.2026 12:34
Shin Fasahar Sadarwa ta Zamani ta na tasirri kan a al'adun Hausawa a yau, ko kuwa dama wadannan halayyar mu ce? A wannan shirin mun tattauna da Profesa Maryam Mansur Yola, malama a fannin al'adu ta Jami'ar Bayero dake Kano.
Al'adun Hausa A Zamanin Yanzu 17.08.2026 12:01
Ko kutsowar bakin al’adu na barazana ga al’adun Hausawa a wannan zamani da muke ciki? Yau na tattauna da Profesa Maryam Mansur Yola, kwararriya a fannin al’adu a Jami’ar Bayero dake Kano.
Tarbiyya: Bangaren Addini Da Zamani 17.08.2026 12:14
Shin akwai dangantaka tsanin addinin Musulunci da al’adun Hausawa? A yau na tattaunawa da Dr Usman Ahmad Mustapha, malamin Shari’ar Musulunci a Kwalejin Koyar da Shari’ar Musulunci da Ilimin Addini ta Kano.
Tasirin Sauyin Yanayi Ga Samar Da Abinci 12.08.2026 10:30
Ko me masana ke cewa a game da barazanar sauyin yanayi wajen samar da wadataccen abinci? A yau mun tattaunawa da Profesa Amina Mustapha ta fannin tsimi da tanadi na aikin goma na Jami’ar Bayero dake Kano.
Bangaren Shari'a Da Yancin Tsayawa da Kafafunsu 10.08.2026 11:54
A yayinda ake shirin zaben 2027, babbar tambaya ita ce: Anya ‘yan bangaren shari’a zasu iya tsayawa da kafafunsu? Mun tattauna da fitaccen lauya a Kano Barista Umar Isa Suleiman.
Tiriliyan Nawa? Bashin Da Ke Kan Najeriya 05.08.2026 12:15
Fitaccen masanin tattalin arziki, Dr. Abdussalam Kani, ya ce cin bashi ga Najeriya ba laifi ba ne. Amma akwai wata babbar damuwa ta daban. Shin mecece wannan matsalar?
Tarbiyya a Yau: Zamani Ko Damuwa? 05.08.2026 12:10
Hira da Dr Aminu Ismai’il Sagagi, malami a jami’ar Bayero dak Kano kuma mai sharhi kan harkokin yau da kullum kan tarbarewar tarbiyya a yankin Arewa a yanzu.
Tattalin Arzikin Najeriya A Yau 30.07.2026 12:38
Dr Abdussalam Kani, fitaccen masanin tattalin arziki a kasar ya bayyana ainihin abubuwan da suka sa Najeriya ke fama da matsalolin tattalin arziki.
Tarihin Noma A Arewa 30.07.2026 12:23
Tattaunawa da Profesa Amina Mustapha, kwararriya a fannin tsimi da tanadi na aikin noma, dan jin tarihi da matsayin noma a Arewan Nigeria, inda mafi yawan al’ummunta manoma ne.
Matsayin Bangaren Shari'a A Dimokradiyya 18.07.2026 12:24
A shirin mu na yau, Barista Umar Isa Suleiman fitaccen lawya a Najeriya, ya bayyana matsayin bangaren shari’a a tsarin dimokradiyyar Najeriya da irin kalubalen da ya ke fuskanta.
Yanayin Noma Yanzu A Nigeria 18.07.2026 11:44
A shirin yau na Gaskiyar Magana, Alhaji Hamisu Ahmed Uba, Sarkin Kasuwar abinci ta Dawanau dake Kano, ya ce har yanzu, akwai fata a harkar noma duk da matsalar rashin tsaro a wasu sassan Najeriya.
Hukumar Bogi: Gaskiya Ko Al'mara? 18.07.2026 12:32
Hukumar bogi da ake zargin wani mutum mai suna Adeniyi Adeyemi ya kafa a Najeriya na ci gaba da janyo cece-kuce. A wannan shirin, mun tattauna da Dr. Aminu Isma'il Sagagi, malamin jami'a kuma fitaccen mai sharhi kan wannan batun.
Sai An Ceto Kasuwancin Arewa 13.07.2026 11:06
A wannan shirin, Alhaji Sa'idu Adhama ya bayyana cewa dole sai an tallafawa masana'antu a Arewa da Kano, muddin ana san bukasa tattalin arzikin yankin.
Rudani: Hukunce-Hukuncen Kotuna a Nigeria 08.07.2026 12:32
Tattaunawa da Barista Umar Isa Suleiman, fitaccen lauya a Nigeria, wanda ke sharhi kan yadda ake gudanar da harkokin shari'a a wannan zamani na siyasa a kasar.
Tun Da Farko Aka Saki Hanya 06.07.2026 11:06
Yaya tsarin dimokradiyya da gudanar da mulki ke tafiya yanzu a Nigeria? Hira da Dr Hakeem Baba Ahmed, fitaccen mai fafutukar wanzar da mulki na-gari.
Podcasts similaires
Replaio n'est pas éditeur de podcasts ; les noms des émissions, les visuels et l'audio appartiennent à leurs auteurs et sont diffusés via des flux RSS publics