Daga Laraba
Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan jin ta-bakin wadanda abin ya shafa.
Where to listen?
Podcasts in the app Replaio Radio Coming soonPodcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts
Episodes
“Sai Na Tara Kudin Cin Abinci Na Nake Iya Siyan Audugar Al’ada” 28.05.2025 24:22
Rashin iya siyan audugar Alada ga mata na kara jefa su cikin matsaloli da dama, a wasu lokuta ma har da cututtuka da ka iya jawo musu matsaloli. A cewar wani rahoto da Asusun yara na majalisar dinkin duniya UNICEF da WaterAid na shekarar 2021 suka fitar, yace daya daga cikin kowace ‘yan mata goma a ƙasashen Afrika ta Kudu da Sahara na rasa zuwa makaranta lokacin da take jinin al’ada, saboda rashin...
"Abba Al'mustafa Bashi Da Hurumin Dakatar Da Fina Finan Mu" 21.05.2025 27:06
Dangantaka na kara runcabewa tsakanin Hukumar Tace Fina-finai ta jihar Kano, wato Kano State Censorship Board, hukumar da aka kafa a shekarar 2001 domin kula da tsaftar fina-finai da nishaɗi a jihar, musamman a fannin kiyaye al’ada da koyarwar addini wacce daya daga cikin jaruman fina finan Abba El-Mustapha, ke jagoranta. A baya-bayan nan, hukumar ta fitar da sanarwa inda ta dakatar da fina-finai...
Tasirin Mulkin Karba-Karba A Najeriya 14.05.2025 26:48
Karba-karba wani tsari ne da ya tanadi kewayarwar ludayi a tsakanin kudanci da arewacin Najeriya wajen rike shugabancin kasa. Manufar tsarin, wanda babu shi a Kundin Dokokin Najeriya, ita ce tabbatar da daidaito da haɗin kai da zaman lafiya a ƙasa. Sai dai yunkurin samar wa tsarin mazauni a ta yadda shugabanci zai rika kewaya a tsakanin shiyyoyi shida na kasar nan bai samu shiga ba a Majalisar W...
Boyayyun Dalilan Da Suke Sa Faduwa Jarabawa A Najeriya 07.05.2025 23:18
Duk shekara, dalibai kan rubuta jarabawa a matakai daban-daban na makarantu daban-daban. Daya daga cikin nau’ukan jarabawa da daliban Najeriya suke yi ita ce Jarabawar Sharen Fagen Shiga Manyan Makarantu, wato UTME. Kamar kowace shekara, a bana ma dalibai sun rubuta wannan jarabawa kuma a cewar Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB), kashi 78.5 cikin 100 na wadanda suka rubuta jara...
Dalilan Rashin Wutar Lantarki A Wasu Jihohin Arewa 23.04.2025 26:11
Wutar lantarki ta zama tamkar gwal a wasu sassan Arewacin Najeriya, inda a wasu yankuna aka ba da rahoton samun sa’o’i biyu kawai a rana, wasu kuma ba sa samun ko daidai da dakika daya. Masu kananan sana’o’i suna kallon rayuwarsu da kasuwancinsu suna durkushewa yayin da kayan sana’arsu suke lalacewa saboda rashin wuta. Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne a kan wannan matsala da yad...
Dalilan Ɓaraka A Tsakanin Iyayen Riƙo Da Ƴaƴan Riƙo 16.04.2025 23:01
Duk wanda aka haifa ya tashi a kasar Hausa ya san al’adar nan ta bayar da ko karɓo ɗa ko ‘ya riƙo. A wasu lokutan mutum ne ke nema a ba shi rikon, a wasu lokuta kuma iyayen ne suke bayarwa don ƙashin kansu. Wannan alada ana yin ta ne da zimmar yauƙaƙa danƙon zumunci, amma a wasu lokuta kwalliya ba ta biyan kuɗin sabulu. Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi nazari ne kan matsalar ’ya’ya da iy...
Abin Da Ya Sa ‘Matar Bahaushe Ba Ta Iya Kiran Sunan Mijinta’ 09.04.2025 23:51
Tun kaka da kakanni an san Hausawa da kawaici da kunya da kuma girmama na gaba da su. Mai yiwuwa wadannan dabi’u ne suka sa matar Bahaushe ba ta iya hada ido da mijinta, balle ta kira shi da sunansa na yanka. To amma a zamanin yau ba abin mamaki ba ne a samu matar aure ta kalli kwayar idon mijinta, ta kuma kira shi da sunansa na yanka. A kan wannan al’ada – asalinta da alfanunta da dalilan sauyaw...
Dalilan Zuwan Mafarautan Arewa Kudancin Kasar Nan 02.04.2025 30:11
Tun bayan kisan mafarauta 16 dake hanyar su ta dawowa gida a garin Uromi dake karamar hukumar Esan dake jihar Edo ne dai al’umma da dama ke ta aikewa da sakon alhini ga ‘yan uwa da abokan arziki yayin da wasu kuma ke ta neman amsoshin tambayoyi game da lamarin da ya shige musu duhu. A yayin da wasu ke ganin a matsayin su na ‘yan kasa masu cikakken ‘yanci, suna da damar kutsawa lungu da saƙo na ko...
Yadda Farashin Kayan Masarufi Suke Gabanin Sallah 26.03.2025 26:36
A duk lokacin da aka ce lokutan bukukuwa sun karato, akan samu sauyi a dukkan alamura. Daya daga cikin irin wadannan sauyi da ake samu shine na farashin kayayyakin masarufi. A wasu lokuta, akan samu tashin farashin irin wadannan kayayyaki, a wasu lokutan kuma akasin haka. Shirin Daga Laraba na wannan makon zai tattauna ne kan farashin kayayyakin masarufi gabanin bikin sallah.
Abin Da Kundin Tsarin Mulki Ya Ce A Kan Ayyana Dokar Ta Ɓaci 19.03.2025 27:18
A karshe dai hasashen da wasu ke yi a Ribas ya tabbata, inda Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-baci, ya dakatar da zababben gwamnan da mataimakiyarsa, da ma ''yan majalisar dokokin jihar. Sai dai bayan ayyana wannan doka da shugaban kasar ya yi 'yan Najeriya da dama suna ta bayyana ra’ayoyinsu kan wannan lamari. Yayin da wasu suke cewa tuni ya kamata Shugaban Kasar...
Ko Kun San Asalin Tashe Da Tarihinsa A Kasar Hausa? 12.03.2025 27:42
Bayan dunbum falala, da yawan samuwar ibadun dake kara kusanta bayi ga ubangijin su, da azumin watan ramadana ke zuwa dashi kamar yadda malamai suka saba fada mana, Hakazalika Kuma a watan na Ramadan dai na zuwa da wata alada mai dimbin tarihi dake debe wa alumma musamman na arewacin Najeriya kewa. Wannan aladar itace ta tashe da ake fara yinta da Zarar watan azumi ya kai kwanaki goma. Maza da mat...
Yadda Zawarawa Suke Dandana Kuda A Watan Ramadana 05.03.2025 31:09
Kowane Musulmi da yadda yakan shiga watan Ramadana – wani kan shiga da shiri, wani kuma da shiririta. Sai dai wasu watan kan zo musu da kalubale – ba don sun shirya mishi b aba kuma don sun gaza shiryawa. Wani rukunin wadannan mutane shi ne na zawarawa, wadanda galibi ba su da masu agaza musu. Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne a kan rayuwar mata zawarawa musamman a watan Ramadana...
Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa 26.02.2025 23:12
A duk lokacin da aka ɗaura aure, wata addu’a da ’yan uwa da abokan arziki kan yi ita ce “Allah Ya kawo ƙazantar ɗaki”. A al’adance, ɗaya daga cikin manyan dalilan yin aure shi ne samun haihuwa. Sai dai a wasu lokuta, wasu mazan kan nuna a fili ba su da muradin hakan. Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne kan waɗannan mazan da ba sa son haihuwa da kuma dalilan su.
Me Ya Sa ’Yan Najeriya Suke Buga-Buga Ko Da Suna Aikin Albashi? 19.02.2025 22:33
Yanayin tattalin arziki da ma wasu dalilai kan tilasta wa mutane da dama, ciki har da masu karbar albashi a karshen wata, neman wata hanya ta daban dake kawo Karin kudade. Shin mene ne yake kawo hakan, kuma mene ne tasirinsa a kan rayuwar masu buga-bugar da ma al’umma? Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne a kan irin buga-bugar da ’yan Najeriya suke yi don sama wa kansu mafita.
Dalilan Da Al’adar Zanen Fuska Ke Neman Gushewa A Kasar Hausa 12.02.2025 29:44
Zanen fuska na da dadadden tarihi a Arewacin Najeriya musamman a kasar Hausa. Sai dai wannan dadaddiyar al’ada tana kan hanyar gushewa domin kuwa ba kasafai ake samun wadanda suke yin ta a wannan zamani ba. Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi nazari ne a kan wannan al’ada da kuma dalilin gushewar ta.
Yadda Al’adun Aure A Ƙasar Hausa Suka Koma 'Event Centre' 05.02.2025 29:48
A da akan kwashe kwanaki ana bukuwan aure a kasar Hausa, kama daga kamu, zuwa sa lalle, yinin bik da zaman ajo zuwa budar kai da sayen baki. Sai dai wadannan al’adu sannu a hankali suna ta gushewa. Ko mene ne dalilin wannan sauyin? Wannan ne batun da shirin Daga Laraba zai duba a wannan makon.
Dalilan Da Suka Sa Mutane Suke Son Haihuwar Maza Fiye Da Mata 29.01.2025 29:49
Son haihuwar ‘ya’ya maza fiye da ‘ya’ya mata abu ne da ake samu tun tale-tale a tsakanin alummomi daban-daban. A tsakanin wasu al’ummomin, samun da namiji abin alfahari ne wanda kuma yake nuni da cigaba da dorewar ahali; sai dai ba a cika bai wa haihuwar ‘ya mace irin wannan muhimmancin ba. Ko wadanne dalilai ne suka sa wasu mutane suka fi son samun ‘ya’ya maza a kan ‘ya’ya mata? Shirin Daga Larab...
Me Ya Sa Matasa Ba Sa Ɗaukar Koyarwa A Matsayin Sana'a? 22.01.2025 26:56
Samun ingattattun malamai a makarantun firamare da sakandare na taka muhimmiyar rawa wajen samar da tubalin ingantaccen kuma nagartaccen ilimi a cikin al’umma. Ɗorewar wannan fafutuka ta samar da ingantaccen ilimi kuma ta dogara ne a kan samun haziƙan matasa da za su maye gurbin malaman da ake da su yanzu. Sai dai a Najeriya, alamu suna nuni da yadda matasa da dama suke gudun aikin koyarwa, musa...
Dalilan Ɓaraka A Tsakanin Iyayen Riƙo Da Ƴaƴan Riƙo 15.01.2025 23:01
Duk wanda aka haifa ya tashi a kasar Hausa ya san al’adar nan ta bayar da ko karɓo ɗa ko 'ya riƙo. A wasu lokutan mutum ne ke nema a ba shi rikon, a wasu lokuta kuma iyayen ne suke bayarwa don ƙashin kansu. Wannan alada ana yin ta ne da zimmar yauƙaƙa danƙon zumunci, amma a wasu lokuta kwalliya ba ta biyan kuɗin sabulu. Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi nazari ne kan matsalar ’ya’ya...
Yadda Sunayen Zamani Suke Neman Kawar Da Na Hausawa 08.01.2025 28:27
A tsakanin Hausawa, sunaye masu alaka da harshen Larabci sun kusan maye gurbin na gargajiya irin su Tanko da Talle da Audi da dai sauran su. Sai dai yayin da a da sunayen da Hausawa kan sanya wa ’ya’yansu na Annabawa ko Sahabbai ko mashahuran malaman Muslunci ne, a baya-bayan nan wasu iyaye kan aro wasu kalmomi su rika kiran ’ya’yansu da su. Mene ne dalilin hakan, yaushe kuma daga ina ya samo as...
Dalilan Da Suka Sa Matan Wannan Zamanin Ba Sa Son Talaka 01.01.2025 27:46
A da soyayya na kafuwa ne sakamakon gaskiyar mutum, ko nasabarsa, ko tarbiyyarsa ko kuma riko da addininsa. Mace kan so saurayinta ko da kuwa ba shi da ko anini, a wasu lokutan ma ko da wani mai hannu da shuni ya fito takan tubure ta ki shi. Sai dai a wannan zamani mata da dama kan fito fili suna bayyana irin saurayin da suke so, a galibin lokuta mai abin hannu. Shirin Daga Laraba na wannan makon...
Dalilan Da Suka Sa Wasu Darikun Kirista Basa Bikin Kirsimeti 25.12.2024 27:33
A dukkan kwanakin karshen watan Disambar kowace shekara, lokacin ne da farin ciki ke cika a fuskokin Mabiya Yesu Almasihu don gudanar da bukuwaN ranar tunawa da haihuwar sa wato kirsimeti. Sai dai, wasu darikun addinin kirista da suka hada seventh day Adventist, Jehovah Witness da ma kuma darikar Deeper Life basu yadda da gudanar da wannan biki na kirsimeti ba. Shirin Daga Laraba na wannan makon z...
Me Nasarar Da John Mahama Ya Samu Ke Nufi Ga kasar Ghana 11.12.2024 29:52
A karshe dai an ayyana John Mahama a matsayin zababben shugaban kasar Ghana bayan da al’ummar kasar sun yanke shawarar zabensa lokacin da suka kada kuri’a ranar Asabar din da ta gabata. Duk da sauran ‘yan Takara da John Mahama ya kara da su, ciki harda mataimakin shugaban kasar mai ci a yanzu wato Mahamudu Bawumia Musulmi na farko da ya tsaya takarar shugabancin kasar. Shirin Daga Laraba na wannan...
Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Suke Kishin Kabila Fiye Da Kasa 04.12.2024 31:41
Kishin kasa na cikin abubuwan da shugabanni, da sauran masu ruwa da tsaki suke kira ga ’yan Najeriya a kullum a kansu. Muhimmancin kishin kasa ga cigaban al’umma, musamman a kasa mai kabilu da addinai daban-daban irin Najeriya, abu ne da ba zai misaltu ba. Sai dai alamu na nuna cewa yan Najeriya sun fi nuna kishin kabilun da suka fito idan aka kwatanta da kishin kasar da suke da shi. Shirin Daga L...
Gudunmawar Da ‘Yan Sa Kai Suke Badawa Wajen Yaki Da Matsalar Tsaro 27.11.2024 30:16
Matsalar tsaro na daga cikin batutuwan da suka hana kasar nan cikas a ‘yan shekarun nan. Kuma kamar yadda alumma ke bayyanawa akwai karancin jami’an tsaro da ya kamata ace suna lura, tare da kiyaye rayuka da dukiyoyin alumma a koda yaushe. Karancin jami’an tsaron ne ya sa wasu daga cikin jihohin da rashin tsaron yafi kamari suka samar da wasu jami’an tsaro dake taimaka wa jami’an tsaron gwamnati w...
Similar podcasts
Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.