Daga Laraba
Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan jin ta-bakin wadanda abin ya shafa.
Where to listen?
Podcasts in the app Replaio Radio Coming soonPodcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts
Episodes
Matsayin Gwamnonin Arewa Kan Kudurin Haraji – Kishin Kasa Ko Son Zuciya? 30.10.2024 27:49
Taron da Kungiyar Gwamnonin Arewa (NGF) ta yi a Kaduna ya bar baya da kuria’a. Daya daga cikin shawarwarin da gwamnonin suka yanke ita ce ta kin amincewa da wani Kuduri da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya kai Majalisar Dokoki ta Kasa. Shin kishin Arewa ne ya sa gwamnonin suka yi Allah-wadai da Kudurin ko kuma son zuciya? Wannan ce muhawarar da ta biyo bayan sanarwar bayan taron na NGF, kuma shir...
Shin Duka Ne Hanyar Ladabtar Da Yara Mafi Inganci? 23.10.2024 26:18
Tarbiyya kamar yadda aka san ta a al’adance tana inganta ne idan al’umma gaba daya ta hada hannu wajen ladabtar da yara. Duk wanda ya kai shekaru talatin zuwa sama ya san cewa a da can iyaye da sauran jama’ar gari suna iya daukar tsumagiya don ladabtar da shi idan ya kauce hanya. Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi duba ne kan alfanun ko illar hakan wajen ladabtar da yara.
Me Ya Sa Kimar Dattawa Ta Ragu A Cikin Al’umma? 16.10.2024 30:29
Afrika na da dadadden tarihin girmama na gaba, musamman dattawan da ke cikin al’umma. Sai dai a wannan zamani akan samu matashi ya shafa wa idonsa toka ya fito bainar jama’a yana musayar zafafan kalamai da sa’o’in mahaifinsa. Shin me ya sa ake samun irin wannan? Don jin amsar wannan tambaya da ma wasu sai ku biyo mu a cikin shirin Daga Laraba na wannan makon.
Da Gaske Ciwon ’Ya Mace Na ’Ya Mace Ne? 09.10.2024 30:07
Sau da yawa akan samu rashin fahimtar juna a duk lokacin da wata mu’amala ta haɗa mata. Misali, a asibiti wajen haihuwa mata sun sha kokawa da yadda suke ce ’yan uwansu suna nuna musu rashin tausayi. Shirin Daga Laraba zai tattauna a kan wannan lamari, ya kuma auna shi a kan mizanin magamar da matan kan yi cewa “Ciwon ’ya mace na ’ya mace ne”.
Da Gaske ’Yan Arewa Ba Sa Fita Kasashen Waje? 02.10.2024 28:19
Wata muhawara da ta karade shafukan sada zumunta a kwanakin nan ita ce ko ’yan Arewa, musamman Hausawa, suna fita kasashen waje. Duk da wannan ba wani sabon abu ba ne, batun ya dauki sabon salo ne a shafukan sada zumunta, musamman Facebook da TikTok, inda ’yan kudancin Najeriya suke wallafa fayafayen bidiyo suna tambayar: shin Hausawa suna zuwa kasashen waje? Shirin Daga Laraba na wannan makon zai...
Me Ya Sa ’Yan Najeriya Suke Buga-Buga Ko Da Suna Aikin Albashi? 25.09.2024 22:33
Yanayin tattalin arziki da ma wasu dalilai kan tilasta wa mutane da dama, ciki har da masu karbar albashi a karshen wata, neman wata hanya ta daban dake kawo Karin kudade. Shin mene ne yake kawo hakan, kuma mene ne tasirinsa a kan rayuwar masu buga-bugar da ma al’umma? Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne a kan irin buga-bugar da ’yan Najeriya suke yi don sama wa kansu mafita.
Abin Da Ya Hana Dalibai Da Dama Komawa Makaranta 18.09.2024 24:42
Sama da mako guda ke nan bayan komawa makarantu domin fara sabon zangon karatu a kusan dukkanin sassan Najeriya. Sai dai rahotanni sun yi nuni da cewa, ana samun karancin komawar dalibai makaranta a wasu sassan kasar. Shirin Daga Laraba na wananan makon zai yi duba ne a kan dalilan faruwar hakan.
Ribar Da ’Yan Najeriya Za Su Samu Daga Hulda Da China 11.09.2024 29:25
Dangantaka ko alaka a tsakanin Najeriya da China tana ƙara yaukaka, musamman a baya-bayan nan. Ko a kwanan nan, Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya jagoranci wata tawaga zuwa kasar ta China domin halartar taron kyautata alakar kasuwanci tsakaninta da kasashen Afirka. Shirin Daga Laraba na wananan mako zai tattauna a kan ko mecece ribar ’yan Najeriya a irin wannan dangantakar?
Me Ya Kamata A Yi Lokacin Komawar Yara Makaranta? 04.09.2024 21:51
A duk lokacin da dogon hutun zangon karatu na karshe ya kare, iyaye su kan kasance cikin taraddadin yadda zasu fuskanci komawar Yara makaranta, saboda dumbin bukatu da yanayin ke zuwa dasu. Shin, me ya kamata, iyaye da masu makantu su fi mayar da hankali a kai, musamman la'akari da irin yanayin tsadar kayayyaki da kuncin rayuwa da ake fama dasu a Najeriya? Shirin Daga Laraba na wananan mako,...
Muhimmancin Al'adar Ciyayya. 28.08.2024 26:22
Duk da cewa, a wuni daya ne ake bikin ta, amma muhimman al'adun Hausawa da ake tattaunawa game dasu a ranar Hausa Ta Duniya, suna da tasiri a rayuwar al'umma ta yau da Kullum. Wata dadaddiyar al'ada da aka san al'ummar Hausawa da ita, ita ce al'adar nan ta fito da Abinci daga gidajen makota, inda ake haduwa aci tare musamman ma a Kullum da daddare. Shirin Daga Laraba na wa...
Me Ya Kamata A Yi Wa Mutanen Da Rikicin Ta’addanci Ya Rutsa Da Su? 21.08.2024 26:09
Majalisar dinkin duniya ta ware ranar 21 ga watan Agusta domin tunawa da wadanda ayyukan ta’addanci ya rutsa da su. A duk lokacin da mutum ya fada hannun ‘yan ta’adda ko rikicin ta’addanci ya rutsa da su, sukan dade cikin damuwa a ransu. Shirin Daga Laraba na wannan mako zai tattauna kan wannan rana da abin da ya kamata a yiwa irin wadannan mutane.
Abin Da Ke Faruwa Da Bankunan Da Suka Haɗe Waje Guda 14.08.2024 23:09
A Najeriya babban bankin kasa CBN ya bayar da wa’adi ga bankunan domin tara adadin wasu kudade a matsayin jarinsu ko kuma su hade guri daya da masu karamin karfi a bankuna. A halin yanzu wasu har sun fara hadewa da wasu bankunan, duk da yake ba sabon abu ba ne hadewar bankuna waje guda a Najeriya. To amma me ke faruwa indan bankunan suka hade? shin lamarin na shafar kwastomomi? Shirin Daga Laraba...
Yadda Za Ku Gane Shafukan Tallafin Gwamnati Na Bogi 07.08.2024 23:53
Gwamnati na fidda shafukan da ‘yan kasa za su iya neman bashi ko tallafi, a lokaci guda kuma masu zamba ta intanet na bullo da shafukan bogi domin yaudarar al’umma. Yana da kyau mutum ya iya tantance shafin da za a iya yi masa kuste musamman abin da ya shafi kudi. Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi bayani kan yadda za ku tantance shafukan intanet na tallafin gwamnati na bogi da na gaske.
Abin Da Gwamnati Za Ta Yi Idan Tana Son Hana Zanga-Zanga 31.07.2024 27:41
Lokaci na tafiya kuma matasa na turjiya kan shirinsu na zanga-zanga, duk da matakan da gwamnati ke ta dauka. Ana ta kokarin ganin zanga-zangar ta yiwu cikin lumana, domin kauce wa rikidewa zuwa ta tarzoma. Shirin Daga Laraba zai tattauna kan hanyoyin da suka kamata gwamnati ta bi domin samun mafita kan zanga-zanga.
Dabarun Kauce Wa Dagulewar Lissafi Sakamakon Ruwan Sama 24.07.2024 23:21
A wannan yanayi na damina kusan kullum wuni ake yi ana tafka ruwan sama a wasu sassan Najeriya. Akwai masu sana’o’in da sai sun fita za a samu taro da sisi amma kuma babu hali. Shirin Daga Laraba zai tattauna lan dabarun da ya kamata masu sana’o’i su yi amfani da su domin ganin ruwan sama bai dagula musu lissafi ba.
Ko Tallafin Shinkafar Gwamnati Zai Magance Damuwar Talakan Najeriya? 17.07.2024 24:56
Tun bayan janye tallafin man fetur, gwamnati ke ta rarraba kayan abinci ga talakawa domin rage musu radadi. A wannan makon Shugaban Kasa Bola Tinubu ya bayar da umarin raba tirela 20 ga kowace jiha a Najeriya da Birnin Tarayya duk da wasu na wannan salo ba ya tasiri. Shirin Daga Laraba ya duba yadda tallafin abincin daga gwamnatin zai magance damuwar talakan Najeriya.
Matakan Kauce Wa Hadarin Ambaliyar Ruwa 10.07.2024 29:48
Kusan ko wace damina sai hukumomi sun gargadi mazauna wasu yankuna game da yiwuwar samun ambaliyar ruwa. A bana ma Hukumar Hasashen Yanayi ta Najeriya (NiMET) ta yi gargadin cewa jihohi kusan 31 za su fuskanci ambaliyar da rushewar gine-gine. Shirin Daga Laraba ya tattauna kan abin da ya kamata a yi domin kauce wa asara sakamakon ambaliya.
Digiri Ko Sana’a - Wanne Ya Fi Muhimmanci? 03.07.2024 29:50
Ana ci gaba da tafka muhawara a kan abin da ya kamata mutum ya fi bai wa muhimmanci a tsakanin digiri da sana’a. Shin wanne ne daga ciki mafi a'ala a rayuwar mutum? Shirin Daga Laraba zai yi muhawara a kan wannan batu.
Shirin Gwamnonin Arewa Maso Yamma Na Magance Matsalar Tsaro 26.06.2024 23:01
Yayin da ake kammala taron yini biyu a kan matsalar tsaro a shiyyar Arewa maso yammacin Najeriya, hankali ya karkata zuwa ga mataki na gaba. Shirin Daga Laraba na wannan makon zai duba yadda gwamnonin yankin suka shirya aiwatar da abin da aka cimma.
Yadda Kanawa Suka Je Kallon Hawan Daushe A Zazzau 19.06.2024 28:40
Hawan Daushe al’ada ce ta sarakunan Kasar Hausa a lokacin bikin Sallah. A masarautar Zazzau a kan yi wannan hawa a ranar ukun Sallah da yamma, kuma yakan tara ‘yan Kallo daga wurare daban-daban ciki har da Kano. Shirin Daga Laraba na wannan makon zai duba yadda aka yi hawan na bana da yadda ya samo asali musamman a masarautar Zazzau.
‘Na Yi Nadamar Ajiye Aiki Saboda Tsohon Mijina’ 12.06.2024 25:09
Yayin da wasu mazan suke kyale matansu su yi aiki, wasu kan yi kememe su ki bari nasu matan su yi. Shin barin matar aure ta yi aiki ne ya fi alheri ko hana ta? Wadanne dalilai kowanensu ke da su? Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba a cikin wannan lamari.
Dalilin Da Maza Ba Su Son Likita Namiji Ya Duba Matansu 05.06.2024 28:54
A yanayi na rashin lafiya a kan ga wasu maza na tuburewa likita namiji ba zai duba musu iyali ba, musamman wajen haihuwa a asibitoci. Amma akwai matan da su ma a ganin su, kunya kan hana su sakin jiki likitoci maza su duba su. Shirin Daga Laraba na wannan makon ya yi nazari a kan meyasa wasu basu yarda likita namiji ya duba matansu a asibiti.
Ƙalubale Da Ci Gaban Dimokraɗiyar Najeriya Cikin Shekara 25 29.05.2024 28:52
Najeriya ta cika shekara 25 cikin tsarin dimokradiyya ba tare da katsewa ba. Ana kan tsari ne na shugaban kasa mai cikakken iko tun daga 1999 a ranar 29 ga watan mayu, duk da yake an sauya bikin wannann rana zuwa 12 ga watan Yuni. Toh shin wane irin ci gaba ko akasin haka aka samu cikin wadannan shekaru 25? Shirin Daga Laraba na wannan mako ya tattauna kan wannan cikar Najeriya shekara 25 cikin mu...
Abin Da Ke Sa Fararen Hula Su Raina Sojoji 22.05.2024 23:12
Mu’amalar farar hula da sojoji a Najeriya ta mutuntuwa ce wadda zarar aka hangi soja a cikin gari jiki har karkarwa yake. Sai dai a ‘yan kwanakin nan a iya cewa yadda labarai ke yawan fita game da yadda fararen hula ke yin tsaurin ido wajen takalar sojoji da fada yana karuwa. Shirin Daga Laraba na wannan mako ya duba abin da ya sa fararen hula ke kokarin daga hannunsu kan jami’an tsaro musamman na...
Abubuwan Da Aka Haramta Wa Mai Aikin Hajji 15.05.2024 29:49
Yau Laraba rukunin farko na maniyyata Hajjin bana daga Najeriya za su tashi zuwa kasa mai tsarki Duk da matsin tattalin arziki da ake ciki a kasar nan, akalla mutum sama da 50,000 ne ake sa ran za su sauke faralin daga Najeriya. Shin wane abu maniyyatan ya kamata su maida hankali a kai? NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Sa Masu Gidajen Haya Suke Tsuga Kudi DAGA LARABA: Dalilan Da Za A Hana ’yan kasa da s...
Similar podcasts
Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.