Daga Laraba

News HA ↓ 254 episodes

Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan jin ta-bakin wadanda abin ya shafa.

Category

News

Podcast website

www.buzzsprout.com

Latest episode

Jul 8, 2026

Where to listen?

Podcasts in the app Replaio Radio Coming soon

Podcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts

Get it on Google Play Install for free Android 5M+ downloads · 4.8 rating iOS soon

Episodes

Dalilin Da Za A Hana ’Yan Ƙasa Da Shekara 18 Shiga Jami’a 08.05.2024

Idan aka zagaya jami’o’i ana samun dalibai da dama wadanda ba su wuce shekara 15 ba a aji. A yanzu zamani ya sauya, abin ya zama Ruwan dare. Mai yiwuwa a lokacin da kuke makarantar firamare ko sakandare kun hadu da wadanda aka yiwa tsallaken aji, wato a bai wa dan aji 4 damar rubuta jarabawar kammala firamare ko kuma dan SS2 damar rubuta WAEC ya wuce jami’a Wannan ne ya sa gwamnatin tarayya ta ce...

Muna Rayuwa A Cikin Ƙunci - Ma’aikatan Najeriya 01.05.2024

Yau ce ranar 1 ga watan Mayu da aka ware a Najeriya da wasu sassan duniya domin jinjina ga rawar da ma’aikata ke takawa wajen ci gaban kasa.  Sai dai yayin da 'yan Najeriya da dama ke kuka da halin da aka shiga na ƙuncin rayuwa, ma'aikata na kan gaba wajen bayyana yadda suka ce suna tagayyara kuma aikin ba riba ta wani ɓangaren.   Shirin Daga Laraba na wannan makon ya duba yadda rayuwar...

Me Ya Sa Kamfanonin Lantarki Suke Fifita ‘Yan ‘Band A’? 17.04.2024

Bayan komawa tsarin rukuni daban-daban na bayar da wutar lantarki Idan kamfanoni na neman afuwa to yawancin ga ‘yan rukunin farko ne. Wasu na ji a ransu kamar su ba kwastomomi bane ga kamfanonin domin kulawar da ake ba su ta nuna ba a tare da su. Shirin Daga Laraba na wannan mako ya duba abin da ya sa hankalin kamfanonin wutar lantarki ya karkata wani fanni.

Yadda Sabbin Ma'aurata Ke Morewa A Ramadan 03.04.2024

A watan Ramadan sabbin ma'aurata na alfahari da azuminsu na farko a gidan aure. Shin mene ne abin da yake kayatar da gidan aure musamman a wannan lokaci na Ramadan? Ya ya kamata ma'aurata su kasance? Shirin Daga Laraba na wannan mako ya tattauna yadda ma'aurata ke samun tabarruki da falala a yanayinsu na farko.

Abubuwan Da Ba A So Mai I'itikafi Ya Aikata 27.03.2024

I’itikafi  sunna ce mai karfi a wannan lokaci, kuma jama’a masu sukunin shiga na kwashe kwanaki kusan goma a masallaci wajen ibada. To amma me ya kamata ku sani gameda shiga itikafi kuma wadanne abubuwa ake son mutum ya kiyaye a lokacin? Shirin Daga Laraba na wannan mako ya duba matakan yin i'itikafi da abubuwan da ya kamata ku sani gameda hakan.

Abin Da Ake Yi A Goman Tsakiyar Ramadan A Addini Da Al'ada 20.03.2024

A yayin da ake shiga goman tsakiya na watan Ramadan, malamai na kira ga al’umma da su dage wajen ibadu domin samun dacewa. A al’adance a wannan goma ta tsakiya akwai wasu al’adu musamman na tashe da kuma kirarin goma ta wuya bayan ta marmari. Shirin Daga Laraba ya yi tsokaci ne a kan wasu abubuwa da da ake yi a goman tsakiyar Ramadan a addinance da al'adance.

Abin Da Addini Yace Game Da Azumin Ƙananan Yara 13.03.2024

Watan ramadana na jefa shauki a zukatun yara masu tasowa ta yadda har rige-rige ake tsakanin juna na ganin an kai wannan munzali. Shin ta wace hanya ya kamata iyaye su bi domin koya wa yarasu azumin ramadana? Shirin Najeriya a Yau ya duba matakan koyawa yara azumin ramadana cikin sauki.

'Amfani Da Tsaffin Takardun Naira Zai Iya Jefa Mutum A Matsala' 06.03.2024

Mutane da dama sun shaida cewa takardar Nairar Najeriya na saurin lalacewa. Wasu na ganin masu liki a wajen bukukuwa da yadda ake kasuwancin sabbin kudi na taka rawa. Toh amma me ya kamata a yi, me kuma doka tace kan kudin da suka tsufa suka lalace. Shirin Daga Laraba na wannan mako ya duba halin da mutum zai iya jefa kansa idan har aka same shi da wulakanta takardun Naira da yadda za a bada gudum...

"Ruwan 'Fiyowata' Na Neman Ya Gagari Talaka" 28.02.2024

Tsadar rayuwa ta sa ruwan leda wato 'fiyowata' ya fara zama abin tattaunawa gameda yadda yake tsada. Wasu na ganin shine ruwan da ake samu mai dama-dama wajen tsafta idan mutum na so ya sha ruwa, sai dai yadda yake kara tsada a sassa daban-daban na Najeriya ya sa ana komawa shan  ruwa mara tsafta a wasu wuraren. Sai dai masu sarrafa ruwan na cewa ba daga su ba ne, inda har ta kai ga wasu...

Harshen Uwa: Dalilin Da Mutane Ke Mance Yarensu Na Asali 21.02.2024

Wannan rana ce majalisar dinkin duniya ta ware a matsayin ranar harshen uwa ta duniya.  Majalisar Dinkin Duniya ta ce kashi 40 cikin 100 na al’ummar duniya ba sa samun ingantaccen ilimi ne saboda rashin amfani da yarukansu na asali. Wasu harsuna na fuskantar barazanar shafewa a duniya saboda iyaye sun daina koyar da ’ya’yansu yadda za su yi magana da harshen. Shirin Daga Laraba na dauke da karin b...

Ranar Masoya: 'Da Wuya A Samu Soyayyar Gaskiya A Yanzu' 14.02.2024

Ranar masoya kan dauki hankali a ranar 14 ga watan Fabreru, inda yawancin masoya ke kure malejin soyayyarsu. Amma akwai masu ganin ba lallai a samu soyayyar gasakiyaa yanzu ba. Sai dai ko kun san yadda aka yi wannan ta samo asali? Albarkacin ranar masoya Shirin Daga Laraba na wannan mako ya duba tasirin wannan rana da salsalar ta.

Yadda ‘Yan Arewa Za Su Samu Kuɗi A Soshiyal Midiya 07.02.2024

Kafafen sada zumunta sun zama farfajiyar baje kolin basira, yayin da ta kan zame musu hanyar bayyana damuwa da share kokensu.  Ana yawan buga misali da cewa an yiwa yankin Arewacin Najeriya  nisa wajen samun tagomashin a soshiyal midiya. Shirin Daga Laraba na wannan mako ya duba dabarun da masu amfani da shafukan za su bi wajen  ganin sun amfana yadda ya kamata.

Yadda Takura A Wajen Aiki Ke Ta'azzara Rayuwar Ma'aikaci 31.01.2024

A duk lokacin da ma’aikaci ya tsinci kanshi a ofishi mai matsin lamba da takura, masu sharhi na ganin aiki bai cika tafiya daidai ba. Wasu wuraren aiki na fuskantar matsin lamba daga oganni ko kuma tsarin aiki da zai sa a yi ta korafi. Shirin Daga Laraba na wannan mako ya duba yadda wuraren aiki masu matsin lamba ke takura rayuwar ma’aikata da yadda za a warware damuwa a irin wannan yanayi.

Matakan Kariya Daga Kwantawa Rashin Lafiya 24.01.2024

Lafiya dai ita ce uwar jiki, babu mai fushi da ita. A yanayin da aka ciki babu mai son ya ga ya kwanta rashin lafiya, domin ana lallaba halin da ake ciki. Jama’a na kokawa a fannoni da dama yayinda wasu kyale batun ziyartar asibiti ko shan magani ko da sun ji alamar canji a jikinsu. Ku kasance da shirin Daga Laraba na wannan mako domin wasu dabarun da za su taimaka wajen ganin ba ku kwanta rashin...

Yadda Wasan Kanawa Da Zagezagi Ya Samo Asali 17.01.2024

Abu ne da za a iya cewa sananne ga al’ummar Kano da Zazzau na tsokanar juna a tsakaninsu. Ana yawan taƙaddama kan shin wane ne mai gida tsakanin Kanawa da Zazzagawa. A cikin shirin Daga Laraba na wannan mako mun duba tasirin wannan wasa tsakaninsu da kuma yadda ta samo asali.

Matsalolin Da Suka Kewaye Kannywood 10.01.2024

Rade-radin matsaloli basa karewa dangane da masanaantar shirya finafinai ta Arewacin Najeriya mai cibiya a Kano Kannywood.  Shin mene ne abin da ke hana Kannywood cigaba kamar sauran takwarorinta na duniya?  Shirin Daga Laraba na wannan mako ya dubi boyayyun matsalolin da suka dabaibaye Kannywood. 

Ina Aka Kwana A Binciken Harin Tudun Biri? 03.01.2024

Yanzu wata guda kenan tun bayan da sojoji suka yi kuskuren kai hari kan masu Maulidi a garin Tudun Biri dake jihar Kaduna. Harin ya yi sanadin mutuwar mutane kusan 100, inda hukumomi da gwamnati ba su yi wata-wata ba wajen daukar alhakin hakan da kuma bayyana cewa za a yi abin da ya dace wajen bin hakkin waɗanda lamarin ya shafa. Toh shin zuwa yanzu wane hali ake ciki? Ko an fara bincike kuwa? Ina...

Abin Da Zai Faru Idan Mutum Ya Cika Cin Goro 27.12.2023

Tasirin goro ga masu cinsa yana zama abu mai wahala mutum iya dainawa. Goro na da mahimmanci a Kudancin Najeriya musamman ga Kabilar Igbo. Haka ma yawanci dattawa a Arewacin Najeriya har ma matasa da mata a wasu lokutan suna cin goro, inda abin ya kan zame musu jiki, yayinda ake amfani da shi a wajen taruka na aure ko suna duk da ba a nomanshi a yankin. Shirin Daga Laraba na wannan makon ya duba a...

Mahimmancin Barin Wasiyya Tun Kana Da Rai 20.12.2023

Da zarar an ambaci wasiyya sai mutum ya fara tunanin mutuwa, ko wani abun na daban a rai. Wasu kan bar wasiyya ko da za su yi tafiya zuwa anguwa saboda gudun riskar wa'adi a lokacin da ba shiri. Shin ya mahimmancin wasiyya take da kuma tasirin hakan? Ku biyo mu shirin Daga Laraba na wannan makon domin jin mahimmancin barin wasiyya tun mutum na raye.

Dalilin Da Maza Ke Haura Shekar 40 Babu Auren Fari 13.12.2023

Maza da dama na son aure amma kuma su kan ce fargabar ɗawainiya ta hana su.  Wasu kuma na cin karo da ƙalubale tun a wajen nema, lamarin da ya sa suke zarta shekarun samartakansu  ba aure. Toh shin da gaske ne abinda suke fada na cin karo da kalubale bayan aure Ku biyo mu cikin shirin Daga Laraba na wannan makon inda muka duba yadda wasu mazan kan shafe sama da shekara 40 ba aure.

Da Gaske Shan Garin Kwaki Na Kashe Ido? 06.12.2023

Shin kun yarda cewa garin kwaki na kashe ido ko zuƙe ruwan jiki? Wasu na shan gari a matsayin abinci su koshi, yayinda wasu ke sha dan marmari. A cikin shirin Daga Laraba na wannan makon mun duba gaskiyar zancen cewa garin kwaki yana kashe lafiyar ido ko akasin haka.

Yadda Za Ku Gane Kuna Da Ƙarancin Suga A Jikinku 29.11.2023

Mutune kan  ziyarci asibiti domin gwaji inda a wasu lokutan ake bayyana musu cewa suna da karancin suga a jikinsu. Akwai alamomin da masana ke cewa su ke nuna mutum na da karancin suga a jiki, amma kuma akwain abubuwan da ke haddasa hakan. Shirin Daga Laraba na wannan makon ya duba yadda za ku gane kuna da karancin suga a jikinku da kuma matakan kariya.

Abin Da Ya Sa Kotu Ta Tsige Gwamnonin Arewa Huɗu 22.11.2023

Bayan watanni tara da kammala zaben 2023 da zubar da wasu jiga-jigan yan siyasa, bangaren shari’a ma na cigaba da zartar da hukunci, inda zuwa yanzu aka tsige akalla gwamnoni hudu daga jam’iyyu daban-daban. Wasu na ɗiga ayar tambaya kan saƙaƙiyar da alƙalai ke amfani da su wajen yanke hukunci a kotunan. Shirin Daga Laraba na wannan mako ya duba ainihin dalilan da suka sa kotunan tsige gwamnonin hu...

Ƙalubalen Da Matan Aure Ma'aikata Ke Fuskanta 15.11.2023

Mutane na tunanin matan aure dake aiki ba sa iya sauke haƙƙoƙin da suka rataya a wuyansu saboda tarin uzuri a wuyansu da kuma kula da iyali  Ko da yike akwai matan da suke da jajircewa a wajen aikinsu matuka. A shirin Daga Laraba na wannan mako mun yi nazarin rayuwar matan aure masu aiki da irin yadda suke magance kalubalen da suke fuskanta.

Abin Da Ya Sa Ba a Ɗaukar Hoton Alƙali a Kotu 08.11.2023

Duk wanda ya taɓa halartar zaman kotu zai iya bayar da shaidar cewa ba wurin wargi bane, ya zama wajibi mutum ya kama kansa tare da girmama alƙalai. Mutane na yawan tambayar ko me ya sa ba a barin jama’a su ɗauki hoto ko bidiyon alƙalai a lokacin shari’a a Kotu? Shirin Daga Laraba na wannan mako ya duba abin da doka tace gameda hana ɗaukar hoton alƙalai a kotu

Listen to the Daga Laraba podcast in Replaio

Radio and podcasts in one app - free, with no sign-up. Install today and do not miss the launch

Get it on Google Play

Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.