Daga Laraba
Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan jin ta-bakin wadanda abin ya shafa.
Where to listen?
Podcasts in the app Replaio Radio Coming soonPodcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts
Episodes
Yadda Amare Suka Mai Da Ankon Bikinsu Hanyar Tara Kuɗaɗe 01.11.2023 23:05
Ƙawayen amarya na yawan korafi a duk lokacin da suka ji labarin kawar su za ta yi aure kuma lokaci ya matso kusa, ba wai dan ba su son ta yi ba, aa sai dan tunani da zura ido domin ganin samfurin ankon da za a fitar. Wasu amaren kan tsuga kudi a kan ankon bikinsu kuma su tilasta kawaye a lalai tilas sai sun siya a hannun su, baki isa kije kasuwa ki siya ba, idan ma kin samu din toh lallai wannan k...
Dalilin Da Aka Kasa Magance Rikicin Manoma da Makiyaya 25.10.2023 28:00
Gwamnati ta sha bullo da tsare-tsare da nufin magance tashe-tashen hankulan tsakanin makiyaya da manoma a sassan kasar nan. Sai dai lamarin ya ki ci, ya ki cinyewa, inda wasu ke ɗora laifin hakan a kan yadda bangarorin suka kasa gane cewa kowannensu na bukatar dan uwansa. Shirin Daga Laraba na wannan makon ya duba abin da ya sa rikicin makiyaya da manona a Najeriya ya ƙi ci, ya ƙi cinyewa.
Abin Da Ke Sa Maza Shan Maganin Karin Kuzarin Auratayya 18.10.2023 28:17
S han maganin karfin maza ya zama ruwan dare a wannan zamani, ta yadda masu sayar da shi ke yi a bainar jama'a, ba tare jin ko dar ba, sakamakon yadda suke cinikinsa. Shin mene ne dalilin da maza ke shan maganin karfin maza? Shirin Daga Laraba na wannan mako ya ji ta bakin maza da ke shan Wadan nan magunguna, ya tuntubi mata da aka ce ana sha saboda su, ya kuma ji ta bakin likitoci.
Gaskiyar Abin Da Ke Kawo Cutar Basir 11.10.2023 28:03
Cutar basir daya ce daga cikin cututtukan da jama'a ke sha wa magani ba tare da sun nemi sahhalewar likita ba. Shin da gaske zaki da maiko na haddasa cutar basir? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci na tafe bayani dangane da abin da ke haddasa cutar basir, da kuma hanyoyin kauce masa a likita ce.
Me Ya Sa Waɗanda Suka Kammala Jami'a Ke Komawa Sana'ar Girke-Girke 04.10.2023 28:35
A yadda wasu masu sana’o'in suka ginu, ko da za a ajiye musu aikin albashi sun gwammace si cigaba da sana’o’in su. A shirin daga Laraba na yau mun duba yadda matasan da suka kammala jami'a ke komawa sana'ar girike-girke da kayan maƙulashi. To me ya sa matasan suka fara yiwa kansu ƙiyamul-laili, ko cigaba hakan ke haifarwa. Ku biyo mu cikin shirin.
Dalilin Da Ba Za Mu Bari Likita Na Miji Ya Duba Matanmu Ba 27.09.2023 28:54
A yanayi na rashin lafiya a kan ga wasu maza na tuburewa likita namiji ba zai duba musu iyali ba, musamman wajen haihuwa a asibitoci. Amma akwai matan da su ma a ganin su, kunya kan hana su sakin jiki likitoci maza su duba su. Shirin Daga Laraba na wannan makon ya yi nazari a kan meyasa wasu basu yarda likita namiji ya duba matansu a asibiti.
Matakan Nasara Wajen Neman Aure A Soshiyal Midiya 20.09.2023 27:00
Samari da 'yan mata da dama sun samu abokan rayuwar su a shafukan sada zumunta, wasu kuma sun gamu da ƙaluabale. Shin da gaske ana aure a soshiyal midiya ko nishaɗi kawai ake yi? Masu haɗa aure a shafukan sada zumunta sun bayar da matakan da za a ɗauka idan ana so a yi nasara. Shirin Daga Laraba na wannan mako ya duba wasu mahimman abubuwa da ya kamata ku sani gameda neman aure a shafukan sad...
Da Wuya Talakan Najeriya Ya Iya Zuwa Aikin Hajjin Bana 13.09.2023 28:42
Tun bayan da hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce maniyatta aikin Hajjin 2024 su fara neman kafin alkalamin Naira miliyan 4 da rabi, yan ƙasa ke ta cece-kuce kan wannan labari. Wasu na ganin anya wannan lamari ba zai gagari talaka ba, yayinHda kuma masana da hukumomin ke kare kansu a kan wannan mataki. A cikin shirin daga laraba na wannan mako mun duba dalilan karin kudin aikin Hajji, da kuma abin da...
Me Ya Sa Juyin Mulki A Wasu Kasashe Ya Dami Tinubu? 06.09.2023 29:35
Juyin mulkin da ake yi a ƙasashen Afrika a 'yan kwanakin nan yana tayar da hankalin shugabannin yankin, inda suke ta ƙoƙarin ganin an dawo mulkin dimokraɗiyya. Sai dai wasu na ganin yawan tsoma baki da shugaban Najeriya Bola Tinubu ke yi, bai kamata ba musamman ƙasashen da ba su cikin yankin ECOWAS da yake jagoranta. Duk da yake akwai masu ganin girman Najeriya a Afrika ya sa dole ya yi magan...
‘Yadda Rashin Gaisuwa Ya Kashe Aure’ 30.08.2023 29:56
A al’adan bahaushe, gaisuwa wata abu ce mai matuqar muhimmaci a cikin zamatakewar sa ta yau da kullum kuma Gaishe da mutum na daya daga cikin alamomin girmama shi. A ‘yan kwanakin dai nan ana ta taƙaddama akan wane ne ya kamata ya fara gaida wani tsakanin ma’aurata, shin miji ne ko mata. A shirin Daga Laraba na wannan mako, mun duba yadda batun gaisuwa tsakanin ma'aurata yake neman lalata wa...
Mun Fi Son Mulkin Sojoji —Al’ummar Nijar 23.08.2023 27:07
A yanzu ana sati na 4 da juyin mulkin jamhuriyar Nijar da aka yi a ranar 26 ga watan Yulin 2023. Ana ta kai ruwa rana domin ganin an dawo kan tsarin dimokradiyya, inda ECOWAS ta ke son ganin an samu daidaito da ƙarfin soji. Amma 'yan Nijar na bukatar sojoji su ci gaba da mulki a ƙasa, sakamakon yadda suke zanga-zangar nuna goyon baya Shirin Daga Laraba na wannan mako, ya duba dalilin da ya s...
Mece Ce Ribar Kai Gwamnati Ƙara 16.08.2023 25:15
A duk lokacin da gwamnati ta yunƙuro domin yin wani abun da ya saɓa da ra’ayin talakawa a kan samu ƙungiyoyi masu ƙalubalantar wannan matakin a kotu. Amma irin waɗannan kararraki da kungiyoyin ke shigarwa a kotu da kalubalantar gwamnati suna tasiri kuwa? Meyasa ba kasafai ake jin sun yi nasara ba? Abin da shirin mu na Daga Laraba ya duba a wannan makon kenan.
Matsalolin Zama Nesa Da Iyali 09.08.2023 29:49
Rayuwar ma'aurata na buƙatar kasancewa kusa da juna domin taimakekeniya da kuma shaƙuwa. Saidai ma'aurata kan shiga damuwa da zarar aka yi nesa da juna, musamman wajen da ya kasance ba makawa sai an je kamar irin su sauyin wajen aiki ko kuma kasuwanci. A cikin shirin Daga Laraba na wannan mako mun duba yadda rayuwar ma'aurata ke kasancewa a lokacin da suka yi nesa da juna.
Abin Da Ya Sa Muke Yin Ciko —’Yan Mata 02.08.2023 28:45
Shin me ke sa mata sarrafa surar jikinsu ta yadda suke zama son kowa, son wanda ya samu. A shirin Daga Laraba na wannan karo, ’yan mata sun fede biri har wutsiya kan dalilan da ke sa su yi wa surarsu ciko, da kuma tasirin da hakan ke musu. Domin jin taƙaddamar da ke tsakaninsu da maza game da mata masu ciko a jikinsu, sai ku saurari shirin Daga Laraba na wannan makon
"Wahalar Da Mu Ka Sha A Wurin Iyayen Riko" 26.07.2023 29:16
Sau da yawa ana samun labaran cuzgunawa tsakanin iyayen riko da 'ya'yan riko, sai dai kowa na zargin kowa ne a cikinsu. Mene ne gaskiyar abin da ke faruwa tsakanin 'ya'yan riko da iyayen gidan nasu? Shirin Daga Laraba na wannan mako ya yi nitso cikin wannan tsohuwar matsala, ya bankado gaskiyar abin da ya ke faruwa.
"Dole Ne Mace Ta Yiwa Mijinta Wanki" 19.07.2023 29:07
Muhawarar ya kamata ko bai kamata mace ta riƙa yiwa mijin ta wanki ba, ya sa ana ta tada jijiyoyin wuya tsakanin maza da mata. Wasu na ganin daya daga cikin ayyukan mace shine wanke kayan mijinta da dai sauran aikace-aikacen gida domin ƙara danƙon soyayya da zamantakewa. To amma nauyin hakan ya rataya a wuyan namiji ne ko mace? Shirin Daga Laraba na Yau, ya yi nazari akan ko ya kamata mata su r...
Da Gaske Ana Iya Canza Injin Janareta Ya Koma Amfani Da Gas? 12.07.2023 29:21
Tsadar man fetur a Najeriya ya tilastawa jama’a masu injin Janareta a gida da wuraren kasuwanci sauya masa tsari ya koma amfani da Gas na girki. Wannan dai wata fasaha ce da wasu mutane suka ƙirƙira bayan sun yi nazari a kai. A cikin shirin Daga Laraba na wannan mako, mun duba alfanu ko akasin hakan da za a iya samu gameda wannan sabon salo da aka ƙirƙira.
Yadda 'Yan Najeriya Suke Shiga Tasku a Kasashen Waje 05.07.2023 27:49
Daga cikin ‘yan Najeriya musamman matasa akwai da dama da ke da burin guduwa daga Najeriya zuwa kasashen Turai ko na Larabawa, ido rufe. Ko masu irin wadannan burika sun san abubbuwan da ke tattare da zama a kasar da ba taka ba? A wannan karon, mun dubi yadda matasa ke hankoron tafiya wadansu kasashe neman arziki ido rufe. Mun ji dalilansu, mun kuma ji ta bakin wadanda suka samu tsallakawa, sann...
Dalilan Lalacewar Al'adun Sallah 28.06.2023 29:58
A yayin da ake bikin babbar Sallah a Najeriya da sauran ƙasashen Musulmin duniya, shirin Daga Laraba na wannan mako ya dubi yadda al'adun bikin sallah suka canza zuwa wani abu na daban. Mene ne dalilan da al'adun bikin sallah suka lalace a kasar Hausa? Saurari bayanai daga bakin dattawa, masana, da kuma matasa kan wannan maudu'i na lalacewar al'adun bikin sallah.
Martanin 'Yan Najeriya Kan Bashin Kudin Karatu 21.06.2023 30:08
Batun bada rancen kudin karatu ga daliban jami'o'i na matakin digiri a Najeriya na ci gaba da daukar hankalin 'yan ƙasar. Wace fahimta 'yan Najeriya su ka yi wa wannan batu na bashin kudin karatu ga dalibai masu neman digiri? Saurari shirin Daga Laraba na wannan lokaci domin jin martanin 'yan Najeriya kan wannan batu da kuma matsayin kungiyar ASUU.
Yadda Kungiyoyi Ke Neman Hana Zaman Aure 14.06.2023 30:01
Kungiyoyin bada agaji masu zaman kansu na kasashen yammacin duniya da aka fi sani da NGO na neman hana mata zaman aure a Jihar Borno, Arewa maso Gabashin Najeriya. Ko ta wadanne hanyoyi wadannan kungiyoyi na NGO ke shiga sha'anin zamantakewar aure? Saurari shirin Daga Laraba domin jin inda gizo ke saka.
Yadda Cire Tallafin Mai Ya Shafi Rayuwar 'Yan Najeriya 07.06.2023 29:59
Tun ranar 29 ga watan Mayun 2023 da aka rantsar da Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban Najeriya ya bayyana cewa babu tallafin mai a cikin kasafin kudin da ya gada da zai kama aiki daga 1 ga Yunin da muke ciki, saboda haka batun tallafin mai ya tafi ke nan. Ko ta wadanne bangarori cire tallafin mai ya shafi rayuwar 'yan kasar? Shirin Daga Laraba na wannan lokaci na tafe da gamsassun bayana...
Abin Da 'Yan Arewa Ke Son Tinubu Ya Yi Musu 31.05.2023 29:53
Litinin 29 ga watan Mayun 2023 aka rantsar da sabuwar gwamnati a Najeriya bayan sabon shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya lashe zaben da aka yi ranar 25 ga Fabrairun wannan shekara. Shin wadanne abubuwa al'ummar Arewacin Najeriya ke fata sabon shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi musu? Shirin Daga Laraba na wannan mako ya tattauna da wadansu 'yan Arewacin Najeriya daga Jihohi 7. Ga...
Yadda Rashin Sanin kimar Waliyyai Ke Shafar Zamantakewar Aure 24.05.2023 29:37
Matsalar rashin zaman lafiya da tausayin juna a tsakanin ma'aurata a wannan zamani daya ne daga cikin matsalolin da ke ciwa mutane da dama tuwo a kwarya, lura da cewa, wadannan matsaloli na zama sanadiyyar mace-macen aure. Shin ko kun san baya ga matsalolin da ke samo asali daga ma'aurata da abokan huldar su akwai sako-sako da walittaka a cikin musabbaban tabarbarewar zamantakewar ma’au...
Yadda Hausawa Ke Shiga Kungiyoyin Asiri A Kudu 17.05.2023 30:06
A da, ba a san ‘ya’yan Hausawa da shiga kungiyar asiri ba, sai dai wasanni irin su dambe da farauta da kokawa da sauransu. Mene ne ya canza yanzu aka fara samun ‘ya’yan Hausawa a kungiyoyin asiri? Shirin Daga Laraba na wannan Mako ya dubi yadda ‘ya’yan Hausawa suka fadawa kungiyoyin asiri a kudancin Najeriya.
Similar podcasts
Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.