Daga Laraba
Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan jin ta-bakin wadanda abin ya shafa.
Where to listen?
Podcasts in the app Replaio Radio Coming soonPodcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts
Episodes
Zama Da Uwar Miji A Gida Daya: Inda Gizo Ke Saka 10.05.2023 30:26
Rigingimu tsakanin ma'aurata dake samo asali daga zama wuri daya da iyayen miji musamman uwa na daya daga cikin matsalolin da ake fama da su a Arewacin Najeriya da ma duniya baki daya. Tarihi ya nuna, an yi zamanin da iyaye da 'ya'ya ke zama wuri guda lafiya, mene ne ya canza da a wannan zamanin ba a iya zama wuri guda da iyaye kuma a zauna lafiya? Shirin Daga Laraba ya tattauna d...
Yadda Iyaye Ke Kashe Wa 'Ya'yansu Aure A Arewa 03.05.2023 29:59
Mutuwar aure daya ce daga cikin matsalolin da ke ci wa mutanen Najeriya musamman 'yan Arewacin kasar tuwo a kwarya. Ko kun san wadansu iyayen ne da kansu suke janyo mutuwar auren 'ya'yansu? Shirin Daga laraba na tafe da karin bayani, ciki harda wanda aka kashewa aure. A yi sauraro lafiya.
Amfanin Kishiya A Zamantakewar Aure 26.04.2023 29:58
Musulunci ya halatta auren mace fiye da daya ga mazan da ke da hali kuma wadanda za su iya yin adalci, amma kuma a rayuwarmu ta yau babu abin da ke ganin adawa da shan kushe kamar karin aure, Shin mene ne amfani kishiya? Wannan karo shirin Daga Laraba ya yi kokarin gano muhimmancin kishiya da kuma amfaninta.
Yadda Mutane Ke Zubar Da Ladan Azuminsu Kafin Sallah 19.04.2023 30:11
Malamai na karfafa wa mabiya addinin Islama guiwa a watan Azumin Ramadana wurin tsayuwar daka wurin Ibada, amma wani abin mamaki shine yadda a karshen watan azumin mutane ke shagalta har su kai ga haramun wurin bikin Sallah. Shin kun san labarin masu tara kudi domin shirya bikin tarbar shaidan? Shirin Daga Laraba na wannan karon ya dubi hanyoyin da maza da mata ke bi wurin zubar da ladan ayyu...
Yadda Rashin Ruwan Sha Ke Lakume Rayuka A Kano 12.04.2023 26:12
Jihar Kano na daya daga cikin jihohin da suka ci gaba a fannoni da yawa na rayuwa. Sai dai wani bincike da muka gudanar ya bankado yadda ake shan wahalar ruwa a wasu yankunan wannan jiha. Mene ne ya sa har yanzu ake tsananin wahalar ruwa a Jihar Kano? A saurari shirin DAGA LARABA na wannan mako a ji yadda ya bankado bakar wahalar da mutane ke sha sakamakon rashin ruwa a wasu yankunan Jihar Kano...
Hukuncin Saka Hotunan Sadaka A Soshiyal Midiya 05.04.2023 29:43
A watan azumin Ramadan an kwadaitar da Musulmai falalar yawaita sadaka da kyauta domin neman yardar Allah. Shin mene ne hukuncin masu daukar hotunan sadaka da kyautar da suka bayar su saka a kafafen sada zumunta na zamani wato oshiyal midiya? Shirin Daga Laraba na wannan lokaci na tafe da bayanan hujjojin masu saka wadannan hotuna da kuma matsayin Malaman addinin Musulunci a kan wannan dabi’a.
Dalilin Da 'Yan Siyasa Ke Kin Karbar Kaye A Najeriya 29.03.2023 29:53
A tsarin zabe dole a samu wanda ya ci, a kuma samu wanda ya fadi. Amma wannan ka'ida har yanzu ba ta samu wurin zama a fagen siyasar Najeriya ba, don kuwa duk wanda ya fadi baya yarda ya fadi sai ka ji suna kiran "Magudi aka yi, amma ni na ci zabe". Mene ne dalilin da 'yan siyasar Najeriya ke kin karbar kaddarar faduwa? Saurari shirin Daga Laraba domin jin dalilin 'yan si...
Matakan Samun Nasara A Watan Ramadan 22.03.2023 30:05
Ana sa ran a tashi da Azumin watan Ramadan mai albarka ranar Alhamis idan Allah ya yarda. Shin kun san matakan samun nasara a cikin ibadar wannan wata? Shirin Daga Laraba na wannan karo ya tattaro bayanai da shawarwari na alheri game da yadda za a rabauta da alheran da ke cikin watan azumin Ramadan.
Hakikanin Abin Da Ya Sa Aka Ki Sakin Naira 15.03.2023 29:48
Shirin Daga Laraba na wannan mako ya leka banki da kasuwa kuma ya gano yadda jama’a ke fama da rashin kudi, ga shi kuma wasu ’yan kasuwa sam ba sa karbar tsohuwar Naira, sai sabuwa ko taransfa. Ko yaushe za’a sakar wa ’yan Najeriya Naira? Saurari Daga Laraba domin jin amsar wannan tambaya, dama wadansu masu alaka. Za ku so karanta wadannan
Wane Ne Bola Ahmed Tinubu? Bayani Daga Dattawan Legas 08.03.2023 29:01
Shirin Daga Laraba na wannan karo ya yi wasu tambayoyi masu kalubale ga shugaban kasar Najeriya mai jiran gado game da lafiyarsa, da kuma kaifin basirarsa. Shin Bola Ahmed Tinubu zai iya tafiyar da harkokin mulkin Najeriya fiye da Muhamadu Buhari? Ku surari shirin Daga Laraba na wannan mako ku ji amsoshin duka tambayoyin namu.
Ba-zatan da Zaben 2023 Ya Zo Da shi 01.03.2023 31:02
Ku biyo shirin Daga Laraba na wannan karo ku ji yadda sakamakon zaben shugaban kasa da ’yan majalisun tarayya na shekarar 2023 ya zo da sabon salon da watakila ba a taba ganin irinsa a wannan zamanin ba. A cikin shirin, za ku ji yadda gwamnoni masu ci suka sha kasa a yunkurinsu na zuwa Majalisar Dattawa.
Anya INEC Ta Shirya Wa Zaben 2023? 22.02.2023 29:54
Ranar Asabar 25 ga Watan Fabrairun da muke ciki ne ake sa ran gudanar da zaben shugaban kasa da ’yan majalisun tarayyar Najeriya. Shin Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta shirya gudanar da wannan gagarumin aiki? Shirin Daga Laraba ya leka lungu da sako a Najeriya domin sanin matakin shirin hukumar zaben da kai.
Wa Zai Lashe Zaben Shugaban Najeriya? 15.02.2023 30:46
Nan da kwana tara ’yan Najeriya za su zabi sabon shugaban da zai mulke su na tsawon shekaru hudu idan Allah ya yarda. Bisa la’akari da yadda yakin neman zabe ke gudana, wane ne cikin ’yan takarar ke da alamun nasara a zaben na mako mai zuwa? Shirin Daga Laraba ya tattauna da kwamitin yakin neman zaben manyan ’yan takarar da ake sa ran daya daga cikinsu zai zamaz zababben shugaban kasar Najeriya,...
Abin Da Ya Sa 'Yan Mata Ke Tallata Kansu a ‘Soshiyal Midiya' 08.02.2023 30:08
Sabuwar dabi’ar neman miji ta kafofin sada zumunta da ’yan mata ke yi na neman zama ruwan dare. Bisa al’adar bahaushe dai, namiji ne ke ganin mace ya ce yana so; To amma sai ga shi ’yan mata sun dukufa tallata kansu ga mai so a kafofin sada zumunta. Shin me ke faruw ne? Shirin Daga Laraba ya tattauna da wasu ’yan mata kan abin da ke sa su dora hotunansu a kafofin sada zumunta don neman miji; mun...
Dalilin Da Mutane Ke Karya 01.02.2023 30:04
A farko babu wanda ke yarda yana dan taba karya lokaci bayan lokaci. Amma idan aka dan matsa da bincike sai a samu jama’a da dama na dan tabawa. Ko mene ne ya sa mutane ke yin karya? Shirin Daga Laraba ya tattauna da wadansu da suka yarda suna yin karya, sun fadi dalilansu, mun kuma ji ta bakin masana kan dalilin yin karya da kuma hukuncinta.
Yadda Matsin Tattalin Arziki Ya Sa Wasu ’Yan Najeriya Suka Rage Cin Abinci 25.01.2023 29:59
Matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa ta tilasta wa 'yan Najeriya sauya yadda suke rayuwa. Shin kun san irin halin da jama'a ke ciki, kawo yanzu? Shirin Daga Laraba ya binciko hakikanin halin da ake ciki, ya kuma tuntubi dalilai.
Alakar ’yan aiki da iyayen gidansu: A ina gizo ke saka? 18.01.2023 27:17
Batun alaka tsakanin ’yan aiki da iyayen gidansu ya jima yana daukar hankali a fagen musayar ra'ayi. Shin tsakanin ’yan aikin da masu daukarsu, wa ke da alhakin abin da ke faruwa? Shirin Daga Laraba ya kutsa lungu da sako, ya zakulo ’yan aiki ya kuma ji ta bakin masu daukar aikin.
Dalilin Da Maza Ke Shakkar Auren Mata 'Yan Boko 10.01.2023 29:55
Muhawara kan abin da ke sa maza tsoron matan da suka yi karatun boko mai zurfi ko masu dukiya, batu ne da ya jima yana daukar hankalin jama’a da dama. Shin ko matan da suka yi karatun boko mai zurfi sun san dalilan da maza ke tsoronsu? Shirin Daga Laraba ya binciko wadan nan dalilai, ya kuma baje su a gadon fida, inda masana suka fede biri har wutsiya.
Yadda Yaudara Ta Zamo Ruwan Dare A Fagen Soyayya 04.01.2023 29:55
A kwankin baya mun kawo muku shiri na musamman akan yadda ake aure da ciki a wannan zamani. Wannan karon, shirin ya dubi yadda yaudara ta zamo ruwan dare a tsakanin masu shirin aure. Shin kunsan yadda yaudara ta zamo rigar ado a wannan zamani? Shirin Daga Laraba na tafe da bayanai masu ratsa zuciya, da kuma mafita kan yaudara a fagen soyayya.
Yadda Son Mata Da Dukiya Ke Raba Zumunci 28.12.2022 30:14
Zumunci wani jigo ne a tsarin rayuwar malam Bahaushe a shekarun baya, amma yanzu yana neman zama tarihi. Shin yaya aka yi yanzu zumunci ke neman zama labari a tsakanin al’umma? Shirin Daga Laraba na kunshe da bayanai. A yi sauraro lafiya.
Yadda Ake Aure Da Ciki A Kasar Hausa 21.12.2022 29:19
Shin idan ka gano cewa da cikin wani amaryarka ta shigo gidanka wane mataki za ka dauka? Shirin Daga Laraba na wannan mako ya bankado al’ada yin aure da juna biyu a Arewacin Najeriya. Shin da sanin angwaye ake daura musu aure da mata masu ciki? Gyara zama domin jin yadda ta kaya tsakanin wadansu angwaye da amarensu suka zo musu da cikin wasu.
Yadda Talla Ke Bata Rayuwar Yaran Arewa 14.12.2022 30:46
Matsalar yawon talla ta dade tana ci wa al’ummar Arewacin Najeriya tuwo a kwarya. Me ya sa aka fi dora wa ’yan mata talla ta kasar Hausa kuma tsakanin amfani da illolin talla wanne ne a gaba? Shirin Daga Laraba ya dubi maganar talla da idon basira, don neman mafita ta hanyar tattaunawa da hukumomi da masana a fannin ilimin addini da na duniya .
Jabun Kayayyaki: Ina Hukumar SON Ta Shiga Ne? 07.12.2022 30:39
Shin me ya sa kayayyaki marasa inganci suka zama ruwan dare a Najeriya? Wani lokacin kayayyaki na jabu ko lalatattu da ake sarrafawa ko sayar wa ’yan Najeriya na hallaka da dama a cikinsu. Me hukumar da ke kula da ingancin kayayyaki ke yi don hana kawo wa ’yan Najeriya kayayyaki marasa inganci? Saurari shirin Daga Laraba na wannan lokaci domin jin wainar da ake toyawa.
Yadda Zubar Da Ciki Ya Zama Ruwan Dare A Najeriya 30.11.2022 29:56
Zubar da ciki al'amari ne mai ba da tsoro saboda hadarinsa da kuma alhakin da ake iya dauka idan an yi ba bisa ka’ida ba. Shin ko mene ne dalilin da zubar da ciki ya zama ruwan dare a tsakani ’yan mata da matan aure a Najeriya? Saurari cikakken shirin Daga Laraba na wannan lokaci domin jin yadda matan aure da ’yan mata suka maida zubar da ciki abin wasa.
Maganin Karfin Maza: Gyara Ko Janyo Ciwo? 23.11.2022 29:58
Shirin Daga Laraba na wannan mako ya mayar da hankali ne a kan maganin karfin maza, amfaninsa, illolinsa da kuma shawarwarin masana a kai. Wannan kari ne a kan shiri na musamman da muka kawo muku a baya kan maganin mata, wanad aka fi sani da kayan mata da yadda ya samu karbuwa a tsakanin mata musamman a Arewacin Najeriya.
Similar podcasts
Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.