Daga Laraba
Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan jin ta-bakin wadanda abin ya shafa.
Where to listen?
Podcasts in the app Replaio Radio Coming soonPodcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts
Episodes
Yadda 'Yan Siyasar Kano Ke Hana Jihar Ci Gaba 01.12.2021 30:31
Masana sun bayyana yadda ’yan siyasar Kano ke hana Jihar ci gaba, lura da yadda siyasar gaba ta maye gurbin siyasar hamayya da kishin jihar. Shirin Daga Laraba na wannan karon ya yi waiwaye kan yadda aka faro siyasar Kano, wuraren da aka wuto, da kuma halin da ake ciki a yau.
Kunci da wulakancin da zawarawa ke fuskanta 24.11.2021 30:00
sanin gaskiyar halin da zawarawa ke ciki sai in ka sauraresu, wai me ya sa ba'a son auren bazawara, wa ya kamata ya dauki nauyin ta, shin zawarci zabin kai ne, ko kuma kaddara ce, ya ya mutane ke kallon bazawara? Saurari irin halin kuncin da mata ke samun kansu da zarar sun rasa auren su.
Auren Wuf: Soyayya ko kwadayi? 17.11.2021 29:57
Mutane na yiwa auren wuf ko auren caraf fassara daban-daban lura da yadda auren yake. wasu na ganin auren wuf a matsayin auren cin kasuwar bukata, amma a zahiri me yasa akeyin auren wuf, meye alfanun yin shi, yanada illa ko kuwa?
Illolin da bilicin ke haifar wa lafiyar masu yi 10.11.2021 1:00:04
A shirin Daga Laraba da ya gabata, mun tattauna dabi’ar bilicin, wato jeme launin fatar jiki daga baka ta koma fara. A yau za ku ji illolin da bilicin ke haifar wa lafiyar masu yi, kuma za ku ji yadda wannan dabi’a ta bilicin ta mamaye, daga maza har mata.
Me ya sa ake bilichin? 03.11.2021 32:31
A wannan karon, shirin Daga Laraba ya mayar da hankali ne a kan masu canza wa kan su kama. Masu canza launin fatar jikinsu daga baka ta koma fara. Wato masu Bilichin. A kashin farkon shirin, mun duba dalilan da ke sa mutane su na canza kamanninsu da Allah Ya halicce su da shi.
Abin Da Ke Sa Mace Ta Fara Neman Namiji Da Aure 27.10.2021 36:04
Shirin Daga Laraba ya yi duba na musamman a kan dalilan da ke sa mace ko hana ta fara neman na da miji aure idan har yana da nagartar da ta dace da zabinsu na abokin rayuwa. Me ya sa ita mace jira take yi sai an zo? Ba a taba yi ba ne a tarihin magabata? Saurari cikakken shirin domin jin amsoshin wadannan tambayoyin.
Mafita Daga Matsalar Yin Watsi Da Tarbiyyar ’Ya’ya 20.10.2021 40:01
Yin watsi da tarbiyar ’ya’ya na daga cikin abubuwan da suka haifar da rigingimun da ke addabar al'umma. A karo na biyu, shirin Daga Laraba ya duba wannan al’amari.
Daga Laraba: Har Da Rashin Tarbiya A Halin Da Kasar Nan Ke Ciki 13.10.2021 39:25
Yin watsi da tarbiyar 'ya'ya na daga cikin abubuwan da su ka haifar da rigingimun da ke addabar 'yan Najeriya. Shirin Daga Laraba ya duba wannan al'amari
Dalilan Mutuwar Kishin Kasa A Zukatan 'Yan Najeriya 06.10.2021 47:32
Jama'a da dama na mamakin yadda 'yan Najeriya basa kishin kasarsu. Shirin Daga Laraba na wannan karon ya bankado dalilan da suka harzuka da yawa daga cikin 'yan Najeriyan har aka wayi gari kasar ta fita daga ransu. Wasudai na ganin soyayya tana wanzuwa idan kowane bangare na amfana, amma 'yan Najeriya sunce manyan kasar ba ta su sukeyi ba. Ayi Sauraro lafiya.
Wane Ne Ke Yada Labaran Karya? 29.09.2021 44:59
Yaya za ki ji idan, ana saura kwana kadan a daura aurenki, angon ya ce ya fasa saboda an turo mishi wani sako da ke nuna wani aibi da bai sani ba game da ke? Kuma me ya sa? Mai yiwuwa tunani na farko da zai zo zuciyarki shi ne, wane ne ya yada wannan karyar a kanki? A zamanin nan, labaran karya na yaduwa kamar wutar daji, yana kuma haddasa rudani a rayuwar mutane da dama.
Anya Camfi Zai Fita Daga Zukatan Mutane Kuwa? 22.09.2021 40:47
Camfi wani abu ne da mutane a ko wanne bangare na duniya kan yi amanna da shi kuma ya zama bangare na al'ada. Mene ne asalin camfi? Zai iya fita daga zukatan mutane kuwa? A wannan karon, shirin Daga Laraba ya yi nazari a kan camfi da tasirinsa a rayuwar al'umma.
Yadda Aka Ceto Mutum 638 Da Ake 'Bautarwa' A Arewacin Najeriya 15.09.2021 39:51
Yaran da ake kaiwa birni da sunan aiki na cikin halin ni-'yasu - abin dai ya yi kama da bauta. Hukumar Yaki da Safarar Mutane ta Najeriya (NAPTIP) shiyyar Arewa Maso Yamma ta ce ta ceto mutum 638 da ake bautatarwa a cikin wannan shekarar.
Fina-Finan Hausa: Gina Al'umma Ko Ruguza Tarbiya? 08.09.2021 41:00
An jima ana takun saka tsakanin masu ruwa da tsaki a harkar shirya fina-finan Hausa, Kannywood, da wani bangare na al'umma bisa zarge-zarge ko korafe-korafe daban-daban. Daya daga cikin zarge-zargen shi ne na bata tarbiya. Ko me ya sa har yanzu masu harkar suka kasa sauya ra’ayoyin jama’a game da wannan zargi? Ku biyo mu ku ji yadda Dokta Abdallah Usman Gadon Kaya ya yi ragargaza, da kuma ya...
Yadda 'Yan Siyasa "Ke Mayar Da Matasa 'Yan Kwaya" 01.09.2021 29:53
Idan kuna biye da mu a shirye-shiryenmu biyu da suka gabata, mun tattauna a kan matsalar shaye-shaye, sannan muka duba wadanda ke amfana da harkar shaye-shayen a Najeriya. A wannan karon kuma mun mayar da hankali ne a kan rawar da ake zargin ’yan siyasa na takawa wajen gurbata wa matasa tarbiyya, da lalata musu makoma ta hanyar saka su shaye-shaye don su cimma wata manufarsu ta siyasa.
Wane Ne Ke Amfana Da Kayan Shaye-Shaye A Najeriya? 25.08.2021 28:45
A shirin Daga Laraba da ya gabata, mun tattauna a kan matsalar shaye-shaye da yadda ta addabi al'umma a Najeriya. A wannan karo za mu duba mu ga shin su wane ne suke amfani da kayan maye?
Yadda Matsalar Shaye-Shaye Ta Zama Ruwan Dare A Najeriya 18.08.2021 36:36
Bala'in shaye-shaye ya kai kololuwa tun da har matan aure bai bari ba. Ko ta yaya za a magance matsalar? Ku saurari shirin Daga Laraba domin jin muhawara da tattaunawa a kokarin gano bakin zarem.
Halin Ni-'Ya-Su: Wa Ya Kamata Ya Jikan 'Yan Gudun Hijira? 11.08.2021 30:50
Mummunan halin da 'yan gudun hijira ke ciki a sansanoni daban-daban a wasu sassan Najeriya ba bakon abu ba ne. Abin da kan zama bako shi ne samun wani mawadaci ko kungiyar mawadata su tallafa wa wadannan mutane. A wannan shiri na Daga Laraba mun duba abin da ya sa masu hannu da shuni ba su cika taimaka wa wadannan bayin Allah ba.
Abin da ke kawo yawan sakin aure a kasar Hausa 04.08.2021 30:57
Mutuwar aure kullum karuwa take yi a Arewacin Najeriya. Mene ne dalili, kuma laifin wane ne? Daga ina matsalar ta samo asali? Mece ce mafita? A wannan karon, shirin Daga Laraba ya yi kokarin nemo amsoshin wadannan tambayoyi da ma fahimtar masana a kan wannan matsala.
Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Ke Rashin Lafiyar Kwakwalwa 28.07.2021 31:28
Matsalar rashin lafiyar kwakwalwa da jirkicewar tunani larura ce da kwararrun likitoci ne kadai ke iya maganinta An dai kiyasta cewa 'yan Najeriya miliyan 20 ne ke fama da wannan larura. A wannan karon, mun tattauna a kan me ke kawo matsalar, da kuma hanyoyin da za a bi domin kauce mata, da magance ta.
Tsadar kayan abinci: 'Yan Najeriya na dandana kudarsu 21.07.2021 30:48
A wannan karon, shirin "Daga Laraba" ya baje tsananin tsadar kayan abinci a faifai don gano abin da ya haddasa ta, wane ne ya haddasa ta, dalilin haddasa ta, da hanyoyin magance ta. 'Yan kasuwa da masana da sauran masu ruwa da tsaki sun bayyana dalilan tsadar, sun kuma bayar da shawarwari a kan yadda za a rage radadin da talaka ke fama da shi.
Yadda Hadurra ke lakume Rayukan Dubban 'yan Najeriya 14.07.2021 26:43
Wasu alkaluma da Hukumar Kiyaye Hadurra ta Tarayya (FRSC) ta fitar sun nuna cewa a wata guda kawai mutane 1,059 ne suka riga mu gidan gaskiya sakamakon hadurran mota a Najeriya. A wannan karon, "Daga Laraba" ya duba yawan hadurra da dalilan da ke haddasa su da masu haddasa su da yadda za a yi a rage su.
Yadda Cin Hanci Da Rashawa Ke Kassara Rayuwar Al'umma 07.07.2021 34:26
Ko kun san cewa da dama daga cikin matsalolin da talakan Najeriya ke fuskanta a yanzu haka cin haanci da rashawa ne suka haddasa su? A wannan karon, shirin "Daga Laraba" ya yi nazari a kan alakar wadannan abubuwa - wato cin hanci da rashawa da kuma bakin talaucin da wahalar da al'umma ke fama da su. Ku biyo mu don jin yadda aka yi aka haihu a ragaya.
Yadda kwacen waya ke ajalin jama'a a Najeriya 30.06.2021 31:58
A wasu sassan Najeriya, rike wayar salula kan zama hadarin da ka iya haifar da sara ko suka ko ma mutuwa idan ajali ya yi. A wannan karon, "Daga Laraba" ya duba yadda wannan matsala ke karuwa da illar da take haifarwa da kuma hanyoyin magance ta ko kauce wa fada mata.
Hidimar aure: Wa ya fi jin jiki tsakanin dangin ango da na amarya? 23.06.2021 23:41
Sau da yawa, iyayen yarinya kan dage ranar aure saboda ba su kammala shirye-shiryen biki ko sayen kayan daki ba. Samari da dama kan bayar da uzuri cewa tsarabe-tsarabe - kama daga dukiyar aure, zuwa ga sadaki zuwa ga lefe - sun yi yawa shi ya sa suka kasa aure. Wai shin, a tsakanin dangin amarya da na ango, wa ya fi shan wahala ko kashe kudi yayin bikin aure? Wannan ne batun da shirin Daga Laraba...
Shin Ana Damawa da Nakasassu a Najeriya? 16.06.2021 22:56
A wannan makon, shirin DAGA LARABA ya yi nazari a kan halin da masu nakasa suke ciki a Najeriya da kuma inda aka kwana game da aiwatar da dokar kyautata rayuwarsu a kasar.
Similar podcasts
Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.