RFI Hausa
Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare
Shiri ne na musamman, da kan tattaunawa da bangarori daban-daban na Al’umma da ke sauraren Shirye shiryen RFI Hausa daga kowane kusurwa na fadin duniya, kan muhimman batutuwa, da suka shafi siyasa Tattalin’ariziki, al’adu da dai sauransu…
Be sure to visit the podcast's website and support the creator: www.rfi.fr
Where to listen?
Podcasts in the app Replaio Radio Coming soonPodcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts
Episodes
Ra'ayoyin masu sauraro kan batutuwa mabanbanta 13.11.2026 9:12
Yau juma'a kamar yadda aka saba rana ce da sashen Hausa na RFI ke bai wa masu sauraro damar bayyana ra'ayoyinsu kan batutuwan da ke ci musu tuwo a ƙwarya, kama daga fannoni a irinsu tattalin arziƙi, siyasa, zamantakewa da dai sauransu. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...
Ra'ayoyi kan takun-saƙar EU da Nijar kan batun jibge dakarun Algeria a Yamai 11.11.2026 10:08
An shiga takun-saƙa tsakanin Kungiyar Turai da mahukuntan Jamhuriyar Nijar, bayan da ƙungiyar ta ce tana buƙatar ƙarin bayani a game da yarjejeniyar tsaro da aka ƙulla tsakanin Nijar da Aljeriya. Mahukuntan Nijar sun ce furucin na EU ba wani abu ba ne face shiga sharo ba shanu, wanda ko da wasa ba za’a taɓa amince wa da shi ba. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...
Fadar shugaban Najeriya ta magantu kan zargin ciyo bashin Naira triliyan 120 09.11.2026 10:30
Fadar shugaban Najeriya, ta musanta alƙalumma da ke cewa bashin da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta a cikin shekaru uku, ya kai Naira tiriliyan 120, inda ta bayyana ikirarin da ke cewa shugabanni 16 da aka yi cikin shekaru 63 da suka gabata, duka-duka bashin da suka ciwo bai zarta Naira trililyan 46, ba wani abu ba ne face farfagandar ƴan adawa. Danna alamar sauti don sauraron cikakken shiri......
Ra'ayoyin masu sauraro kan yadda ƴan adawa ke cigaba da yaƙin neman zaɓe duk da ƙalubale 05.11.2026 10:36
A Najeriya yayin da ake ci gaba da yaƙin neman zaɓen gamma-gari da za a yi cikin shekara mai zuwa, ƴan adawa sun yi zagin cewa ana hana su samun damar isa ga filayen da suka dace don gudanar da tarukan gangami, da rashin samun damar wallafa manufofinsu a allunan tallace-tallace da kuma rashin ba su cikakkiyar kariya ta tsaro a wasu jihohin ƙasar. Wannan shine maudu'in da muka baiwa mai sauraro dam...
Ra'ayoyi kan gargaɗin IMF cewa kada a kuskura a dawo da tallafin mai a Najeriya 15.10.2026 9:17
Yayin da wasu daga cikin ƴantakarar neman shugabancin Najeriya ke bayyana yiyuwar sake dawo da tsarin biyan tallafin man fetur matukar suka yi nasarar lashe zaɓen shekara mai zuwa, a nasa ɓangare Asusun Bada Lamuni na Duniya IMF ya yi gargaɗin cewa ka da a kuskura a dawo da wannan tallafi. IMF ya bayyana cewa duk wani yunkurin sake dawo da tallafin, zai kasance mummunan koma-baya a maimakon cigaba...
Ra'ayoyi: Cikar Najeriya shekaru 10 ba tare da zartas da hukuncin kisa ba 13.10.2026 9:47
A Najeriya an cika shekaru goma cur ba tare da an aiwatar da hukuncin kisa ba wanda ya samu sahakewar gwamnati, wadda ita kaɗai ce take ɗaukar matakin ƙarshen wajen aiwatar da hukuncin da kotuna suka yanke dangane da haka. Wannan dai lamari ne da ya sake biijoro da kiraye-kirayen ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam da ke neman a samar da doka da za ta dakatar da aiwatar da hukunci a Najeriya.
Ra'ayoyin masu sauraro kan jingine shirin ƙara kuɗin mai a Nijar 12.10.2026 9:21
Mahukuntan Jamhuriyar Nijar sun jingine batun ƙara farashin mai duk da cewa Majalisar Dokokin Riƙon Kwaryar ƙasar ta bayar da shawarar yin wannan ƙari don magance ƙaracin makamashi da ake fama da shi a ƙasar. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Najeriya ta sanar da wani shirin rage farashin mai a tsawon wata ɗaya domin sauwaƙa wa jama’a. Latsa alamar sauti don sauraren ra'ayoyin jama'a...
Ra'ayoyin masu saurare kan kawo ƙarshen wasa da Argentina da Messi yayi 08.10.2026 9:28
Ra'ayoyin masu saurare kan wasan ƙarshe da Ɗan wasa Lionel Messi ya bugawa ƙasarsa. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Kabiru Muhammad Dan Bauchi.
Ra'ayoyin masu saurare kan fatan ci gaba da haƙo man fetur a wasu sassan arewacin Najeriya 06.10.2026 10:45
Taron gwamnonin jihohin Arewa maso Gabashin Najeriya da ya gudana a ƙarshen mako, ya buƙaci gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta gaggauta farfaɗo da aikin binciken man fetur da aka faro tsawon shekaru a yankin. Kazalika taron ya buƙaci gwamnatin da ta mayar da hankali wajen gyara layin dogon da ya haɗa biranen Port-court-Jos-Bauchi-Gombe zuwa Maiduguri saboda muhimmancinsa wajen buƙasa tattalin arzikin...
Ra'ayoyin masu sauraro kan ƙarancin makamashi a wasu ƙasashen yammacin Afrika 29.09.2026 9:42
Yayin da kusan a kowane mako ana iya a wayi gari da sabon farashin man fetur a Najeriya, a Jamhuriyar Nijar ana fama da ƙaranci da kuma tsadarsa ne a wasu jihohin ƙasar, yayin da ake fama da gagarumar matsalar ƙarancin gaz da ake amfani da shi domin girki. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.
Ra'ayoyin masu sauraro kan batutuwa mabanbanta 18.09.2026 10:59
Yau juma'a kamar yadda aka saba, sashen Hausa na RFI na bai wa masu sauraro damar bayyana ra'ayoyinsu kan batutuwan dake ci musu tuwo a ƙwarya, kama daga siyasa, tattalin arziƙi, tsaro, zamantakewa da dai sauransu. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...
Ra'ayoyin masu sauraro kan ƴan aikin jarida dake fuskantar tarnaƙi a Afrika 16.09.2026 10:15
Ƴancin aikin jarida na ci gaba da fuskantar tarnaƙi a wasu ƙasashen Afirka, saboda yayin da wasu ke fuskantar tursasawa a Najeriya, a Jamhuriyar Nijar kuwa ana tsare da Moussa Tchangari kusan shekaru biyu ba tare da shara’a ba, yayin da a hannu ɗaya, wani ɗanjaridar wato Moussa Kaka ya ɓata yau kwanaki 16 kenan. A can kuwa Mali ko shekaran jiya litinin ma an yanke wa wani ɗanjaridar hukuncin ɗauri...
Ra'ayoyin masu sauraro kan hauhawar farashin man fetur a Najeriya 15.09.2026 9:49
Hauhawar farashin man fetur na ci gaba da haifar da tarin matsaloli ga al’ummar Najeriya, inda a jihohi irinsu Sokoto, Kebbi da Zamfara, farashin lita ya doshi Naira dubu ɗaya da 500 a halin yanzu kuma kusan hakan farashin yake a mafi yawan jihohin arewacimn ƙasar. Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a kai yau, musamman game da yadda ake samun hauhawar farashin akai-a...
Ranar yaƙi da jahilci ta duniya a bana ya duba yadda za a inganta ilimin manya 08.09.2026 10:09
Ranar takwas ga watan Satumban kowacce shekara, rana ce da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware, tun a shekarar 1960 a matsayin ranar yaƙi da jahilci, inda ake mayar da hankali wajen faɗakar da jama'ar a sassan duniya mahimmancin ilimi da samar da tsari ko dabarun koyar da mutanen da basu samu dama ba. A mafi yawan ƙasashe dai an sha aiwatar da tsarin yaƙi da jahilci da ke bai wa dattijai ko masu many...
Ra'ayoyin masu sauraro kan batutuwa mabanbanta 28.08.2026 11:04
Kamar yadda aka saba ko wace rana irin ta yau Juma’a, muna baku damar tofa albarkacin bakin ku kan wasu abubuwa da ke ci muku tuwo a ƙwarya kama daga siyasa da tattalin arziƙi da zamantakewa da dai sauransu. To yau ba ta sauya zani ba, sai ku latsa alamar sauti don sauraren shirin...
Ra'ayoyin masu sauraro kan kalaman tinzira jama'a da wasu ƴan siyasa suke 27.08.2026 10:59
A Najeriya ana ci gaba da mayar da martani mai zafi sakamakon kalaman da shugaban ƙaramar hukumar Kuje da ke birnin Abuja Mista Samuel Shekwolo ya furta, kan cewa duk wanda baya goyon bayan jam’iyya mai mulki ta APC ya fice daga karamar hukumar. Yayin da ake tunkarar zabe a Najeriya, sannu a hankali kalaman tunzuri da yiwa jama’a barazana a karuwa a tsakanin yan siyasa musamman daga bangaren jam’i...
Ra'ayoyin masu sauraro kan sace masallata 600 a jihar Neja 25.08.2026 9:44
A Najeriya al’umma na cike da zullumi a jihar Neja musamman bayan ƴan ta’adda sun saki wani bidiyo a kafafen sada zumunta wanda ke nuna mutane kusan 600, galibinsu mata da yara da kuma dattijai, waɗanda suka bayyana a matsayin masallatan da suka sace a gari na Borgu a Juma’ar da ta gabata. Mahukunta sun ce suna ƙoƙarin ceto su, amma hankula ba su kwanta ba gannin an saba ruwa ƙasa na shanyewa. Lat...
Ra'ayoyi kan yadda rashin bin ƙa'idojin gini ya haifar da ambaliya a Abuja da Kano 18.08.2026 10:30
A Najeriya duk da gargaɗin da hukumar yanayi ta NIMET ta riƙa yi a lokuta da dama game da ambaliyar da wasu sassan ƙasar zasu fuskanta a damunar bana, wajen ganin an ɗauki matakan daƙile illar da hakan zai haifar. Tuni aka ga wannan ambaliya a birane da dama ciki har da Abuja fadar gwamnatin ƙasar, birnin da ruwa ya shanye sassa da dama da ke matsayin ambaliya mafi muni da aka gani, wanda ake alaƙ...
Ra'ayoyin masu sauraro kan yadda zaɓen gwamnan Osun ya gudana Najeriya 17.08.2026 10:18
A Najeriya, Gwamna mai ci kuma ɗan takarar jam’iyar Accord Ademola Deleke ya lashe zaɓen jihar Osun da aka gudanar a ranar Asabar da ƙuri’u sama da dubu 511, yayin da ɗan takarar jam’iya APC mai mulkin ƙasar Bola Oyebamiji yazo na biyu da ƙuri’u dubu 444,815. Kafin ranar zaɓen dai an fuskanci dambarwar siyasa da rikice-rikice da suka yi sanadin mutuwar mutane sama da 40. Latsa alamar sauti don sau...
Ra'ayoyin masu saurare kan yadda gwamnonin Najeriya suka yi buris da kudaden UBEC 13.08.2026 10:00
A Najeriya, Hukumar Kula da Ilimin Firamare ta Kasa ta roƙi gwamnonin jihohi da su yi wa Allah su gaggauta karɓar sama da Naira biliyan 332 na kuɗaɗen tallafin daidaita tsarin ilimi. Shugabar Hukumar Aisha Garba wanda ta yi wannan kira, ta ce bayaga Naira biliyan 65 da aka ware akwai kuma wasu Naira biliyan 267 da aka ware domin inganta makarantun firamare a ƙananan hukumomin faɗin ƙasar. Ku dann...
Ra'ayoyin masu sauraro kan yunƙurin haɗa kan ƴan adawa a Najeriya don fiida ɗan takara ɗaya 12.08.2026 9:59
A Najeriya, ƙungiyar G –100 ta gamayyar wasu fitattun ƴan ƙasar kimanin 100 ta jagorancin wani sabon yunkurin ganin lallai sai jam’iyyun adawa sun yi haɗin guiwa domin fitar da ɗantakara ɗaya tilo da zai fafata da shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shekara mai zuwa. Ku danna alamar sauraro dimin jin cikakken shirin tare da Oumar Sanni.
Ra'ayoyin masu sauraro kan haramtawa yara amfani da kafafen sadarwa a wasu ƙasashe 22.07.2026 10:04
Ana ci gaba da samun ƙarin ƙasashe a sassan Duniya da ke ɗaukar matakin taƙaitawa ko kuma haramta wa yara amfani da shafukan sada zumunta don basu kariya daga illolinsu. A halin yanzu dai fiye da ƙasashe 20 ne ciki har da India, da China da Faransa da Ingila, suka ɗauki wannan mataki, tun bayan da Australia ta zama ƙasa ta farko da ta bayar da misalin hana yara ‘yan ƙasa da shekaru 16 shiga shafuk...
Ra'ayoyin masu sauraro kan lashe kofin duniya da Spain ta yi 20.07.2026 10:51
Tawagar ƙasar Spain ta lashe gasar kofin duniya karo na biyu a tarihi, bayan ta doke Argentina da ke kare kambun a wasan ƙarshe da suka gudanar a daren jiya. Ita kuma Ingila ta ƙare a matsayi na 3 ne inda ta lashe kyautar tagulla da ke zama kyauta ta farko da ta lashe a kofin duniya cikin shekaru 60, ya yin da Faransa ta ƙare a matsayi na 4. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...
Ra'ayoyin masu sauraro kan batutuwa mabanbanta 17.07.2026 10:09
Yau juma'a, rana ce da sashen Hausa na RFI ke bai wa masu sauraro damar bayyana ra'ayoyinsu kan batutuwan da ke ci musu tuwo a ƙwarya, kama daga tsaro, tattalin arziƙi, siyasa, zamantakewa, da dai sauransu. Latsa alamar sauti don sauraren ra'ayoyi mabanbanta...
Ra'ayoyin masu sauraro kan batutuwan mabanbanta 10.07.2026 10:58
Kamar yadda aka saba, yau rana ce da sashen Hausa na RFI ke bai wa masu sauraro damar bayyana ra'ayoyinsu kan batutuwan da ke ci musu tuwo a ƙwarya, kama daga tsaro, siyasa, tattalin arziƙi da dai sauransu. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...
Similar podcasts
Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.