HumAngle
Birbishin Rikici
Kokarin nutsawa cikin wahalhalun da mutanen da ke zaune a yankunan da ake fama da tashe-tashen hankula ke fuskanta, yawanci yakan zo ne kawai ta fuskar kididdiga; Birbishin Rikici wani shiri ne na mako-mako akan waɗannan labarun sirri na wadanda rikici da tashin hankali suka shafa da HumAngle ke kawo muku.
Where to listen?
Podcasts in the app Replaio Radio Coming soonPodcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts
Episodes
Daga Hatsari Zuwa Matsi: 'Yan gudun hijira na Arewa maso Yamma Na Ci Gaba da Kokawa 18.06.2022 6:06
Ayyukan ‘yan ta’adda a sassa daban-daban na jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya, inda matsalar ‘yan fashi ta fara tayar da zaune tsaye, ya sanya al’umma sun koma masu zaman kansu. Amma yayin da ‘yan gudun hijirar ke ƙaura zuwa wurare masu aminci, sun hadu da sababbin ƙalubale kamar asarar rayuwa, kuncin rayuwa, da rashin sanya ƴaƴan su ci gaba da karatu. Mai gabatarwa: Zubaida Baba Ib...
Sun Matsu Da Samun Taimako Bayan Sun Rasa Matsugunansu A Arewa Maso Yamma 11.06.2022 6:23
'Yan ta'adda sun raba su da muhallansu, gwamnati ta yi watsi da su. Sai dai Ahmadu Tella, Muhammed Lawal da kuma Binta sun samu wani tsarin tallafi da ba a saba da shi ba wato tallafin Mangal da baya isarsu. Mai gabatarwa: Zubaida Baba Ibrahim Marubuci:‘Kunle Adebajo Muryoyin shiri: Akila Jibrin, Attahiru Jibrin, Ruqayya Saeed Fassara: Ruqayya Saeed Edita: Aliyu Dahiru Furodusa: Khadija Gidado...
Rayuwar Marasa Rinjaye A Tsakiyar Ta’addanci 04.06.2022 6:44
Tun bayan rikicin da aka kwashe shekaru 12 ana yi a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, mabiya addinin Kirista, wadanda suka yi hasarar gidajensu da rayuwarsu sanadiyyar rikicin suna kokawa da rayuwa a sansanonin ‘yan gudun hijira na tsiraru ba tare da kyakkyawar makoma ba. Mai gabatarwa: Zubaida Baba Ibrahim Marubuciya: Nathaniel Bivan Muryoyin shiri: Akila Jibrin, Attahiru Jibrin, Ruqayya Saee...
Suna Shan Taba Domin Su Rayu 28.05.2022 3:20
A sansanin 'yan gudun hijira na Tse-Yandev da ke Benue, a arewa ta tsakiyar Najeriya, mata suna shan taba idan aka yi ruwan sama domin shi ne kawai dumin da suke samu a yanzu; sun yi gudun hijira, suna rayuwa a bakin kasada. Mai gabatarwa: Zubaida Baba Ibrahim Marubuciya: Aishat Babatunde Muryoyin shiri: Khadija Gidado, Ruqayya Saeed, Hauwa Shaffi Nuhu, Attahiru Jibrin Fassara: Ruqayya Saeed Edit...
Ta Rasa Danta A Wurin Boko Haram, Ta Rasa Mijinta A Wurin Sojoji 21.05.2022 4:14
'Yan ta'addan Boko Haram sun kwace dan Maryam Muhammad mai shekaru 10 a duniya. Shi ma mijijnta ya gamu da sojojin Najeriya sun kamashi bisa zargin hada kai da yan Boko Haram bayan ya fita neman abinci wata rana. Tsawon shekaru, Maryam na ci gaba da wahala don tafiyar da rayuwarta ba tare da da ko miji ba. Mai gabatarwa: Zubaida Baba Ibrahim Marubuciya: Ihuoma Ilo Muryoyin shiri: Ruqayya Saeed...
Danginsa Sun Kasa Komai Tun da Sojoji Suka Nakasashi 18.05.2022 5:04
Sojojin Najeriya sun kama Bana ba a bisa ka’ida kuma suka tsare shi na shekaru biyu. Tunda ya samu ’yancinsa, ya na ta fama da lafiyar jiki da na hankali wanda ke shafar sauran danginsa. Mai gabatarwa: Zubaida Baba Ibrahim Marubuci: Anita Eboigbe Muryoyin shiri: Fatima Mustapha, Hawwa Bukar, Akila Jibrin Fassara: Rukayya Saeed Edita: Aliyu Dahiru Furodusa: Khadija Gidado Babban Furodusa: Antho...
Ta Samu Tabin Kwakwalwa Bayan An Kashe Mijinta 18.05.2022 4:45
Dangin Saraya sun shiga tashin hankali bayan da sojojin Najeriya suka kashe mijinta. Daga nan ta samu tabin hankali kuma har yanzu ba ta warke ba. Mai gabatarwa: Zubaida Baba Ibrahim Marubuci: Kunle Adebajo Muryoyin shiri: Rukayya Saeed Fassara: Zubaida Baba Ibrahim Edita: Aliyu Dahiru Furodusa: Khadija Gidado Babban Furodusa: Anthony Asemota Babban Mashiryi: Ahmad Salkida
Ta’adancin Boko Haram Ya Shafesu, Sojojin Najeriya Ta Dora Musu Laifi 18.05.2022 5:15
Sojojin Najeriya sun kama Mu’azu da Muhammad saboda zaton suna da alaka da Boko Haram. Bayan sunyi shekaru da yawa a tsare, an wanke su daga dukkan zarge-zargen amma hakan ya janyo musu sake sabuwar rayuwa daga farko. Mai gabatarwa: Zubaida Baba Ibrahim Marubuci: Kunle Adebajo Muryoyin shiri: Akila Jibrin, Attahiru Jibrin Fassara: Rukayya Saeed Edita: Zubaida Baba Ibrahim Furodusa: Khadija Gid...
Garkuwa ta Hanyar Ta’addanci 24.04.2022 5:20
Ta'addanci a yankin Arewa ta Tsakiyar Najeriya na kara dagula al'umma tare da raba mutane da matsuguninsu. ƙananan yara da ba su ji ba ba su gani ba suna fiskantan wannan tashin hankalin, abin da zai iya lalata ƙuruciyarsu. Mai gabatarwa: Zubaida Baba Ibrahim Marubuci: Muhammed Akinyemi Muryoyin shiri: Ruqayya Saeed, Akila Jibrin Fassara: Rukayya Saeed Edita: Aliyu Dahiru Furodusa: Khadija G...
Yan Makaranta da Yan Gudun Hijira na Zama a Aji Daya 16.04.2022 6:33
‘Yan ta’adda sun mamaye wata al’ummar Tabanni Gandi a jihar Sokoto, inda suka raba mutane da muhallansu. Yanzu suna kokawa da sabuwar rayuwa wacce ba su saba dashi ba. Mai gabatarwa: Zubaida Baba Ibrahim Marubuci: Muhammed Akinyemi Muryoyin shiri: Isaac Oritogun Fassara: Rukayya Saeed Edita: Aliyu Dahiru Furodusa: Khadija Gidado Babban Furodusa: Anthony Asemota Babban Mashiryi: Ahmad Salkida
Hangen Fata Ga Knifar Women 10.04.2022 7:07
A hankali matan Knifar sun fara samun kwanciyar hankali bayan an sako mazajensu sama da 30. Amma yayin da mutanen da aka tsare ke fita, sun shiga wata rayuwa ta daban. Mai gabatarwa: Zubaida Baba Ibrahim Marubuci: Muhammed Akinyemi Muryoyin shiri: Ruqayya Saeed, Hawwa Bukar, Hauwa Shafii Nuhu Fassara: Rukayya Saeed Edita: Aliyu Dahiru Furodusa: Khadija Gidado Babban Furodusa: Anthony Asemota...
Daga Garkuwa Zuwa Jami’a 02.04.2022 7:03
Sau uku Zarah ta kubuta daga hannun ‘yan ta’adda, kafin ta samu cikakken tsira daga wurin su. A yanzu Zarah tana jami’a. Mai gabatarwa: Zubaida Baba Ibrahim Marubuci: Anita Egboibe Muryoyin shiri: Ruqayya Saeed Fassara: Zubaida Baba Ibrahim Edita: Aliyu Dahiru Furodusa: Khadija Gidado Babban Furodusa: Anthony Asemota Babban Mashiryi: Ahmad Salkida
Kubuta daga dajin sambisa da cutan HIV 26.03.2022 7:27
An yi garkuwa da Hajiya sau dayawa tare da tilasta mata auren mayakan Boko Haram sau uku. Lokacin da ta kubuta daga hannun 'yan ta'addan, ta tafi da kwayar cutar HIV. Mai gabatarwa: Zubaida Baba Ibrahim Marubuci: Anita Egboibe Muryoyin shiri: Ruqayya Saeed Fassara: Ruqayya Saeed Edita: Aliyu Dahiru Furodusa: Attahiru Jibrin Babban Furodusa: Anthony Asemota Babban Mashiryi: Ahmad Salkida
Ba Su Da Gida Balle Samun Kulawa 08.03.2022 5:34
Yayin da damina ke karatowa, yan gudun hijirar da ke sansanin Tse Yandev suna zaman dar-dar saboda rashin mafakar da gwamnati ta kasa samar musu. Mai gabatarwa: Zubaida Baba Ibrahim Marubuci: Anita Egboibe Muryoyin shiri:Akila Jibrin, Hauwa Shaffi Nuhu, Ruqayya Sa’eed, Attahiru Jibrin Fassara: Zubaida Baba Ibrahim Edita: Aliyu Dahiru Furodusa: Khadija Gidado Babban Furodusa: Anthony Asemota Babban...
‘Ba Lallai Mu Dawo Gida Da Mazajenmu Ba Duk Da Tare Muka Fito’ 26.02.2022 9:00
Tun wajen 2015, Knifar Women ba su ga mazajensu da aka tsare ba a bisa ka’ida ba. Yanzu matan na kokawa ga wani sabon mataki na mayar da su garuruwansu ba tare da ’ya’yansu da mazajensu da aka tsare ba. Mai gabatarwa: Zubaida Baba Ibrahim Marubuci: Anita Egboibe Muryoyin shiri: Isaac Oritogun, Hafsah Abubakar, Khadija Gidado, Ruqayya Sa’eed Fassara: Zubaida Baba Ibrahim Edita: Aliyu Dahiru Furo...
Tabon Da Rikici Ya Samarwa Zuciya 19.02.2022 5:15
A karo na ƙarshe da Mary Amua ta ga ɗanta, ya taimaka mata ta kubuta daga hare-haren yan bindiga kuma ya koma ya taimaki wasu. Yanzu tana cikin tashin hankali da mutuwarsa. Mary na kwana a sansanin yan gudun hijira, tana kuma fatan da ace yana kusa don taimaka mata da iyalansa. Mai gabatarwa: Zubaida Baba Ibrahim Marubuci: Anita Egboibe Muryoyin shiri: Aquila Brisca, Khadija Gidado Fassara: Zubai...
Mai Cikin Da Ke Burin Samun Mu’ujiza 12.02.2022 4:29
Namsoor tana dauke da cikin wata shida. Cikin ta na biyu kenan a sansanin yan gudun hijira na Tse Yandev da ke jihar Benue. Jama'a sun damu da yadda za ta rayu idan ta haihu amma Namsoor na fatan ta ci gaba da haifar yara. Mai gabatarwa: Zubaida Baba Ibrahim Marubuci: Anita Egboibe Muryoyin shiri: Rukayya Saeed, Khadija Gidado Fassara: Zubaida Baba Ibrahim Edita: Aliyu Dahiru Furodusa: Attahiru...
Daga Ciyayi Zuwa Rairayi (Episode 13) 05.02.2022 5:23
Veronica manomiya ce da take ciyar da mutane da yawa kafin a kaiwa gonakinta hari. Yanzu haka rayuwarta a hargitse take a sansanin yan gudun hijira. Mai gabatarwa: Zubaida Baba Ibrahim Marubuci: Anita Egboibe Muryoyin shiri: Rukayya Saeed Fassara: Zubaida Baba Ibrahim Edita: Aliyu Dahiru Furodusa: Attahiru Jibrin Babban Furodusa: Anthony Asemota Babban Mashiryi: Ahmad Salkida
Ta Rasa ‘Ya’ya Biyu a Kokarin Tseratar da Daya 29.01.2022 5:11
Dorcas na gudu don ceto rayuwarta da na ‘ya’yanta a lokacin da mutuwa ta dauki ‘ya’yanta biyu. Mai gabatarwa: Zubaida Baba Ibrahim Marubuci: Anita Egboibe Muryoyin shiri: Rukayya Saeed, Isaac Oritogun Fassara: Zubaida Baba Ibrahim Edita: Aliyu Dahiru Furodusa: Attahiru Jibrin Babban Furodusa: Anthony Asemota Babban Mashiryi: Ahmad Salkida
Daga Ritaya zuwa Gudun Hijira: Rayuwar Wani Malamin Makaranta a Sansanin Yan Gudun Hijira 22.01.2022 5:30
Bayan ya yi ritaya, Ajir Godwin ya yi fatan zai kashe kudin fansho sa yana noma da hutawa. Sai dai rikicin jihar Benue bai sa hakan ya faru ba Mai gabatarwa: Zubaida Baba Ibrahim Marubuci: Anita Egboibe Muryoyin shiri: Aliyu Dahiru Fassara: Zubaida Baba Ibrahim Edita: Aliyu Dahiru Furodusa: Attahiru Jibrin Babban Furodusa: Anthony Asemota Babban Mashiryi: Ahmad Salkida
Ina Mijina? 15.01.2022 7:54
Sojojin Najeriya sun tsare mijin Falta Gambo, Modu Ngubdo a shekarar 2015. A yayin da yake jiran shari’a, Falta ta fada cikin alhini saboda ta samu ciki da wani namiji da ba nata ba. Yanzu haka ta haifi dan da ba na mijinta ba; abin da ya sakata a cikin rudani. Mai gabatarwa: Zubaida Baba Ibrahim Marubuci: Anita Egboibe Muryoyin shiri: Khadeeja Gidado Fassara: Zubaida Baba Ibrahim Edita: Aliyu Da...
Rayuwa Karkashin Gidan Sauro 08.01.2022 4:45
Ga mutanen da sukayi hijira zuwa sansanin Tse-Yandev, suna makotaka ne da dubban saurayen da suke zaune a kogo daya tare da su. Wadannan 'yan gudun hijirar suna rayuwa ne cikin fargabar ruwan sama wanda zai iya sa su zama marasa matsuguni idan ya yi tsanani. Kasancewar sun tsallake rijiya da baya a Benue, yanzu dole ne su yi rayuwa a cikin kunci da wahala. Mai gabatarwa: Zubaida Baba Ibrahim Marub...
Tsalle Daya: Daga Rashin Lafiya Sai Mutuwa 01.01.2022 5:14
Agule ta ga yayin da ‘danta ya mutu bayan wata gajeriyar rashin lafiya a sansanin yan gudun hijira domin ba ta samu kudin magani ba. Mutuwa ta sake zuwa dakin Agule lokacin da ‘yar ta tayi rashin lafiya amma likitocin agaji suka ceceta. Kamar Agule da ‘ya’yanta, ‘yan gudun hijira da dama a sansanonin dake fadin jihar Benue suna fama da rashin lafiyar da ka iya zama ajalinsu. Mai gabatarwa: Zubaid...
Matar da Ke Neman Soyayyar Dan Ta’adda 25.12.2021 6:52
'Yan ta'addan Boko Haram sun sace Aminata tare da yi mata aure da membansu Muhammad Bukar. Ta kamu da son Muhammad, wanda ta ce yana kyautata mata. Shekaru bayan tserewa daga sansanin ‘yan ta’adda, Aminata na kewar rayuwar jin dadin da tayi tare da mijinta yayin da take kokawa da rayuwa a matsayinta na ‘yar gudun hijira. Mai gabatarwa: Zubaida Baba Ibrahim Marubuci: Anita Egboigbe Muryoyin shiri:...
An Musu Ruwan Bomb Bisa Kuskure 18.12.2021 5:08
Yan gudun hijira a garin Rann da ke jihar Borno da ke Arewa maso gabashin Najeriya sun farka da karar wani jirgin yaki na shawagi a samansu. Ganinsa ya sanya suka nufi inda sojojin da aka ajiye a sansanin suke domin neman tsaro don kada a yi zargin yan ta’adda ne. Duk da haka, jirgin yakin ya harbe su da bam inda ya kashe mutane akalla 115. Ko ya yaya lamarin ya faru? Mai gabatarwa: Zubaida Baba I...
Similar podcasts
Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.