HumAngle
Birbishin Rikici
Kokarin nutsawa cikin wahalhalun da mutanen da ke zaune a yankunan da ake fama da tashe-tashen hankula ke fuskanta, yawanci yakan zo ne kawai ta fuskar kididdiga; Birbishin Rikici wani shiri ne na mako-mako akan waɗannan labarun sirri na wadanda rikici da tashin hankali suka shafa da HumAngle ke kawo muku.
¿Dónde escuchar?
Podcasts en la app Replaio Radio Muy prontoLos podcasts llegarán muy pronto a la app. Instálala ahora y sé el primero en descubrir una forma totalmente nueva de vivir los podcasts
Episodios
Yadda Uwa Ta Yi Jiran Labarin Garkuwa Da Yayanta 06.06.2026 8:09
Lokacin Ramadan ne, kuma Bintu Suleiman, wata uwa kuma ‘yar kasuwa mai shekaru 55 daga Ngoshe a Jihar Borno, Arewa maso Gabashin Najeriya, tana shirin buɗe baki tare da iyalanta. Sai harbe-harbe ya fara, kuma cikin awa guda gidanta ya kama da wuta. Yayin da ‘yan ta’adda ke tattara mutane, ta samu damar tserewa tare da wasu daga cikin ‘ya’yanta da jikokinta zuwa cikin daji. Daga baya, ta gane cewa...
Bauta A Matsayin Ungozama 09.05.2026 6:10
Adisu Abba wata mata ce mai shekaru 45 kuma uwa ga ‘ya’ya biyar. Ta fito daga Dikwa, Jihar Borno, a arewa maso gabashin Najeriya. Tun kafin rikici ya tarwatsa rayuwarta, ta riga ta fara koyon aikin da zai zama ginshiƙin rawarta a cikin al’ummarta—ta koyi yadda ake taimaka wa mata wajen haihuwa. An yi garkuwa da Adisu a hannun ‘yan ta’adda na tsawon shekaru uku,a wannan lokacin, ta taimaka wajen ha...
Sabuwar Rayuwa Bayan Yaki 06.05.2026 8:14
Christie Garba mace ce mai shekaru 38, uwa ga yara bakwai, wadda ke zaune a Billiri, Jihar Gombe, a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya. Ta kasance tana zaune a Jihar Yobe tare da iyalinta kafin rikicin Boko Haram ya addabi yankin. A wancan lokacin, hare-hare sun riga sun faru a wasu wurare kusa da su, amma ba su kai ga al’ummarsu kai tsaye ba. Christie da iyalinta sun zauna kimanin watanni huɗu b...
Ta Rasa Komai Dalilin Boko Haram 08.03.2026 7:11
Gina Bashir manomiya ce mai shekaru 46 daga Askira Uba a jihar Borno, arewa maso gabashin Najeriya. A lokacin da rikicin Boko Haram ya kai kololuwa, tana zaune a Benisheik, wani karamin gari a Borno, tare da mijinta da ‘ya’yanta shida. A lokacin wannan rikici, ta rasa dan’uwanta, dan dan’uwanta, da wasu ‘yan uwa shida. A cikin wannan bidiyo, mun tattauna game da yadda ta tsira da kuma burinta ga ‘...
Gudun Tsira 07.02.2026 7:15
Kina dauke da ciki na watanni tara, ba takalmi a ƙafa, kina gudu cikin ƙaya, kura da tsoro. Kusan shekaru goma, Ya Busam Ali ta shafe tana rayuwa a matsayin yar gudun hijira, tana tafiya me nisa a kowace kakar noma zuwa gonakin da ‘yan ta’adda ke iko da su, domin kawai ta kula da kanta da ‘ya’yanta. Wannan shirin na #BirbishinRikici ya bi labarin yadda ta tsira, juriyarta, da ƙarfin zuciyar da ke...
Hatsarin Noma A Inda Babu Tsaro 03.01.2026 7:14
Da can kana shafe tsawon kwanaki a gona, kana shuka iri-iri na amfanin gona kana dawowa gida da girbi mai yawa. Yanzu kuma, sa’o’i kaɗan kacal kake aiki, a ƙarƙashin sa ido na sojoji. Ba za ka iya yin nesa da gari ba, kuma ba za ka ƙara shuka amfanin gona masu tsawo ba domin suna iya ɓoye ’yan ta’adda. Saboda haka kana shuka wake da gyada kawai, amma amfanin da kake samu ba ya taɓa isa. Kuma duk l...
Lokacin Da Mai Taimakonta Ya Bace 06.12.2025 6:31
Ka gudu don ceton rayuwarka lokacin da Boko Haram suka kai hari a garinku a Adamawa, arewa maso gabashin Najeriya. Da ka dawo, sai ka tarar da makwabci ya fara gina gida a kan filin ka. Lokacin da ka nuna rashin amincewa, ya ba wa jami’ai cin hanci kuma ya kore ka, yana cewa ba ka da wani da zai gaji gidan. Ɗanka, wanda shi ne babban mai kula da kai, ya ɓace a lokacin yaƙin, kuma har yanzu ba ka j...
Neman Yanci Da Kudin Fansa 01.11.2025 7:01
kuna gida kuna shirye-shiryen dare, bayan sallar isha'i. Rayuwarku na cike da kalu-bale, amma aƙalla kuna tare da iyalan ku. kwatsam, ba tare da gargadi ba, mahara dauke da makamai suka mamaye kauyen ku. Suna baku umarni da ihu har baku iya gane me suke fada. Tsoro ya ratsa jikinku. Kuna gudu cikin duhu, zuciyar ku tana bugawa tare da fatan tsira, kuna ta addu'a. Amma duhun dare be baku abin da ku...
Kwana Na Karshe A Gida 04.10.2025 5:59
kina gida tare da mijinki da 'ya'yanku hudu, kuna shirya abincin rana kamar kowace rana. Kwatsam sai kuka ji 'yan ta'adda dauke da makamai sun kewaye garinku. Suna afkawa gidaje, suna sace amfanin gona, suna kashe duk wanda ya musu gadara. Take kuka fita da gudu zuwa cikin daji. Jama'a duk an watse zuwa wurare daban-daban. A wannan yanayi kika nemi mijinki kika rasa, sai bayan lokacin da abun ya l...
Kwana Na Karshe A Gida 04.10.2025 5:59
kina gida tare da mijinki da 'ya'yanku hudu, kuna shirya abincin rana kamar kowace rana. Kwatsam sai kuka ji 'yan ta'adda dauke da makamai sun kewaye garinku. Suna afkawa gidaje, suna sace amfanin gona, suna kashe duk wanda ya musu gadara. Take kuka fita da gudu zuwa cikin daji. Jama'a duk an watse zuwa wurare daban-daban. A wannan yanayi kika nemi mijinki kika rasa, sai bayan lokacin da abun ya l...
Kwana Na Karshe A Gida 04.10.2025 5:59
kina gida tare da mijinki da 'ya'yanku hudu, kuna shirya abincin rana kamar kowace rana. Kwatsam sai kuka ji 'yan ta'adda dauke da makamai sun kewaye garinku. Suna afkawa gidaje, suna sace amfanin gona, suna kashe duk wanda ya musu gadara. Take kuka fita da gudu zuwa cikin daji. Jama'a duk an watse zuwa wurare daban-daban. A wannan yanayi kika nemi mijinki kika rasa, sai bayan lokacin da abun ya l...
Masu Kewa Da Wadanda Suke Kewarsu 15.09.2025 6:42
Lokacin da wanda kuke ƙauna ya ɓace, kuma bayan shekaru ba ku gan shi ko ji daga gare shi ba, baku cire ran sake haɗuwa, se ya zama wani jinkirin me zafain jira. Amma me zai faru idan an shafe fiye da shekaru goma ana jira bayan tuna su shine kadai alama ta cewa sun taba rayuwa?
Danta Ya Taka Bom! 25.08.2025 6:37
Kin yi aure da wani soja wanda kuka gina rayuwa da shi kuma kuka haifi ’ya’ya shida. wata rana, an tura shi yaki ba sake dawowa ba. Shekaru da yawa bayan haka, yayin da barazanar tayar da kayar baya ta fara bayyana a cikin garinku, ɗanku ya taka bam da ya fashe. Ba ku da tabbas ko zai tsira, kuka garzaya da shi asibiti a babban birnin tarayyar Najeriya, da fatan ba shi damar yin rayuwa. Bayan shek...
Gwagwarmayar Rayuwa 25.08.2025 8:19
Ke uwa ce mai yara takwas, kina rainon ‘ya’yanki a sansanin ‘yan gudun hijira dake babban birnin tarayyar Najeriya bayan tserewa mummunan harin da kungiyar ta’addancin Boko Haram ke kaiwa. Ta yaya zaki iya tinkarar barazanar rugujewar sansaninku, da kama danki, da kuma kwace baburan acabar da ki ka siya don samun abin rike rayuwa bayan duk kokarin ki na ganin kun samu rayuwa mai kyau na neman ya c...
Labarin Jajircewa 25.08.2025 6:39
Me za ku yi a lokacin da ’yan Boko Haram suka sace danku suka kuma koya mishi musu yaki, alhali kuna fuskantar kora a gidanku? Wannan jigon na #BIRBISHINRIKICI ta bibiyi rayuwar Ya Hauwa, wacce ta zama mace tilo da ke aiki a matsayin wakiliya a Borno, arewa maso gabashin Najeriya.
Gudun Tsira Dauke Da Juna Biyu 03.05.2025 5:34
Jummai mai dauke da cikin wata tara ta tsere daga garinsu da ke Nassarawa a Arewacin Najeriya bayan jin karar harbe-harbe! Wannan ba shine karo na farko da take tserewa tashin hankali ba. A cikin wannan shirin na #BIRBISHINRIKICI, mun ba da labarin asarar da sukayi da kuma gudun hijira.
Daren Tashin Hankali 05.04.2025 5:34
A cikin dare a cikin watan Disamba, 'yan ta'adda sun kai hari kan wata karamar al'umma a garin Gombe da ke arewa maso gabashin Najeriya, inda suka bar gidaje a kone! Wannan shirin na #BirbishinRikici ya ba da labarin wata mata mai suna Tabitha mai shekaru 58, wadda ta rasu a daren.
Sau Goma Sha Uku Tana Gudun Hijira 01.03.2025 4:50
Sakamakon tashe-tashen hankula a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, an tilasta wa Binta Bukar mai shekaru 54 yin kaura sau 13. Wannan shirin na #BirbishinRikici ya ba da labarin gudun hijirar da ta yi, da asarar gida, da 'ya'yanta guda biyu.
Shekaru Goma Sha Daya A Daure 01.02.2025 6:08
Wannan shirin #BirbishinRikici ya ba da labarin Aisha, wacce kamar mijinta, sojojin Najeriya suka kama. Ta yi shekara 11 tana a tsare ba tare da jin ko ganin ’ya’yanta da al’umma ba. Yanzu ta sami 'yanci, tana gwagwarmayar sake shiga cikin al'umma. Mai Gabatarwa: Rukayya Saeed Marubuciya: Sabiqah Bello Muryoyin Shiri: Sabiqah Bello Fassara: Rukayya Saeed Edita: Aliyu Dahiru Furodusa: Alamin Umar B...
Rashin Mahaifiya Yayin Rikici 18.01.2025 5:50
Pwajeldi Lazarus ‘yar shekara 19 ta rasa mahaifiyarta sakamakon rikicin manoma da makiyaya a Numan da ke arewa maso gabashin Najeriya. Wannan shirin na #BIRBISHINRIKICI ya ba da labarin rabuwar Pwajeldi da mahaifiyarta. Yayin da take rayuwa tare da raɗaɗin harin, tana kuma baƙin cikin rasa wacce hankalin ta yafi kwanciya da. Mai Gabatarwa: Rukayya Saeed Marubuciya: Sabiqah Bello Muryoyin Shiri: Sa...
Rayuwar Manomiya A Arewa Maso Yammacin Najeriya 14.12.2024 5:48
Mata a Arewa maso yammacin Najeriya sun dena zuwa gona domin ciyar da iyalinsu. Wannan ya faru ne saboda yan ta’adda na zuwa su yi musu fashi kuma su kashe wasu. Sakamakon haka ya janyo ba su da abin dogaro wajen ciyar da iyalinsu a yanzu. Mai Gabatarwa: Rukayya Saeed Marubuci: Abubakar Gumi Muryoyin Shiri: Khadija Gidado Fassara: Rukayya Saeed Edita: Aliyu Dahiru Furodusa: Khadija Gidado Babban F...
Mijinta Yana Son Ta Bishi Sambisa 09.11.2024 5:27
Tare da goyon bayan @pulitzercenter, wannan shirin na #BIRBISHINRIKICI ya duba labarin wata mata da ta auri wani dan kungiyar #BokoHaram Wanda yanzu aka ma gyaran hali, da kuma yadda abin da ya faru a baya ke shiga tsakani halin da suke ciki a yanzu a yankin da aka sake tsugunar da su a jihar Borno. Mai Gabatarwa: Rukayya Saeed Marubuciya: Hauwa Shaffii Nuhu Muryoyin Shiri: Khadija Gidado Fassara:...
Kubuta Daga Harin Yan Ambazonia 19.10.2024 5:20
A watan Disambar 2023, wasu da ake zargin mayakan Ambazoniya ne suka kai hari kan al'ummar Belegete a Cross River, Kudu-maso-Kuducin Najeriya, wani ƙauye mai iyaka kusa da Kamaru. A cikin wannan shirin na #BirbishinRikici, za mu ba da labarin Elizabeth, mahaifiyar 'ya'ya shida, wacce ta tsere daga harin kuma ta sami mafaka a wani wurin kiwon dabbobi da ke kusa. Mai Gabatarwa: Rukayya Saeed Muryoyi...
Rayuwar Shekara Takwas Da Yaya Hudu A Hannun Boko Haram 07.09.2024 6:57
A cikin shirin #BirbishinRikici, za mu kawo muku labarin Aisha, wacce aka yi garkuwa da ita tana da shekaru sha takwas, aka yi mata auren dole da wani dan Boko Haram. Bayan shekaru takwas, ta tsere a matsayin mahaifiyar 'ya'ya hudu. Yanzu, tana bin burinta da kwato 'yancinta. Mai Gabatarwa: Rukayya Saeed Muryoyin Shiri: Khadija Gidado Fassara: Rukayya Saeed Edita: Aliyu Dahiru Furodusa: Khadija Gi...
Bayan Kubutar Amaryar Da Yan Garkuwa Suka Yi Wa Fyade 17.08.2024 6:10
A shirin #BirbishinRikici na yau, muna ba da labarin Hauwa Abbagana, wata budurwar amarya da aka sace. Bayan tserewa daga zaman talala, ta dawo gida ciki da ɗan wanda ya zalunce ta, cikin fargabar kyama da ƙi da za ta iya fuskanta. Mai Gabatarwa: Rukayya Saeed Muryoyin Shiri: Khadija Gidado, Samir Sheriff Fassara: Rukayya Saeed Edita: Aliyu Dahiru Furodusa: Khadija Gidado Babban Furodusa: Anthony...
Podcasts similares
Replaio no es editor de podcasts; los nombres de los programas, las portadas y el audio pertenecen a sus autores y se distribuyen a través de canales RSS públicos