HumAngle
Birbishin Rikici
Kokarin nutsawa cikin wahalhalun da mutanen da ke zaune a yankunan da ake fama da tashe-tashen hankula ke fuskanta, yawanci yakan zo ne kawai ta fuskar kididdiga; Birbishin Rikici wani shiri ne na mako-mako akan waɗannan labarun sirri na wadanda rikici da tashin hankali suka shafa da HumAngle ke kawo muku.
Where to listen?
Podcasts in the app Replaio Radio Coming soonPodcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts
Episodes
Fatima Ta Yi Burin Zama Ma'aikaciyar Asibiti, Yan Ta'adda Ne Suka Hanata 10.12.2022 9:10
Kamar sauran ‘yan matan da aka yi garkuwa da su a Dapchi, Fatima ta yi watsi da burinta na samun ilimi. A cikin wannan shirin na Birbishin Rikici ta bayyana abin da ya faru tun daga kwashesu daga makaranta har zuwa kaisu ga Tafkin Chadi, abin da ya kai ga mutuwar wasu 'yan mata, da kuma yadda aka yi garkuwa da Leah Sharibu. Mai gabatarwa: Zubaida Baba Ibrahim Marubuciya: Zubaida Baba Ibrahim Mury...
Akan Zuwa Makaranta Rayuwarsu Ta Salwanta! 03.12.2022 6:30
A shekarar 2018, an sace ‘yan mata sama da 115 daga dakunan kwanansu a Dapchi. Wasu daga 'yan matan da suka je neman ilimi a makaratar da aka kwashesu sun biya farashi da rayukansu. A cikin wannan shiri na Birbishin Rikici, HumAngle ta bayar da labarin waɗannan da aka kashe da kuma firgicin da suka yi ta fama. Mai gabatarwa: Zubaida Baba Ibrahim Marubuciya:Zubaida Baba Ibrahim Muryoyin shiri: Isaa...
Sun Cika Alkawarinsu Na Kai Harin Ta'addanci 26.11.2022 5:37
Wasu daruruwa dauke da makamai sun kai hari garin Kagoro dake Kudancin Kaduna a daren ranar Lahadi, 20 ga watan Maris, 2022, inda suka dawo da safiyar ranar Litinin 21 ga watan, suka kashe mutane da dama tare da kona dukiyoyi duk da kasancewar sojoji. Mai gabatarwa: Zubaida Baba Ibrahim Marubuciya:Zubaida Baba Ibrahim Muryoyin shiri: Khadija Gidado, Hawwa Bukar, Umar Yandaki Fassara: Ruqayya Saeed...
Zalincin Da Ya Biyo Bayan Kisan Kiyashin Da Akai A Zaria 19.11.2022 5:54
Tsakanin ranar 12 zuwa 14 ga watan Disambar 2015, sojojin Najeriya sun kai wa kungiyar 'yan Shi'a wadanda galibinsu 'ya'yan kungiyar IMN ne, a daidai lokacin da suke murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (SAW). Mutane da dama da aka kama yayin kisan gilla sun shafe shekaru a gidan yari ba tare da samun wani hukunci ba da kuma samun adalci. Mai gabatarwa: Zubaida Baba Ibrahim Marubuciya...
Har Yanzu Wasu Na Jinya Tun Bayan Kisan Kiyashin Da Aka Yi A Zaria 12.11.2022 6:10
A watan Disambar 2015 ne sojojin Najeriya suka kai hari gidan Ibrahim El-Zakzaky, jagoran Harkar Musulunci Ta Najeriya, a lokacin kisan kiyashin da aka yi a Zaria. Shekaru da yawa bayan faruwar lamarin, yawancin wadanda abin ya shafa na ci gaba da rayuwa tare da nakasu da zafi yayin da suke kokarin murmurewa. Mai gabatarwa: Zubaida Baba Ibrahim Marubuciya:Tracy-Allen Ezechukwu Muryoyin shiri: Akil...
Har Yanzu Yara Na Dauke Da Tabon Kisan Kiyashin Da Aka Yi A Zaria 05.11.2022 5:08
Yaran ‘yan kungiyar Islamic Movement of Nigeria (IMN) da sojoji suka kai wa hari gidan Ibrahim El-Zakzaky, har yanzu suna da tabo na kisan kiyashin da akayi shekaru bayan harin. A cikin wannan shirin, za mu kalli fadace-fadacen tunani da firgici da aka tilasta wa wadannan yara shiga bayan sun shaida mutuwar ‘yan uwansu. Mai gabatarwa: Zubaida Baba Ibrahim Marubuciya: Tracy-Allen Ezechukwu Muryoyi...
An Musu Dirar Mikiya, An Sace Dabbobinsu 29.10.2022 4:46
Tsakanin ranar 12 zuwa 14 ga watan Disambar 2015, sojojin Najeriya sun kai farmaki kan 'yan uwa musulmi na Harkar Musulunci a Zariya. Lokacin da lamarin ya faru, rundunar sojin ta yi ikirarin cewa ‘yan Shi’a sun yi yunkurin kashe tsohon babban hafsan sojojin kasa, Tukur Buratai. Shekaru da yawa bayan haka, iyalai har yanzu suna shan wahala sakamakon kisan kiyashin. Mai gabatarwa: Zubaida Baba Ibra...
Me Yake Faruwa Idan Aka Ji Gwara Yaki Akan Yunwa? 22.10.2022 5:22
A Maiduguri babban birnin jihar Borno an samu raguwar adadin tallafin da ake samu a sansanonin 'yan gudun hijira. A cikin matsananciyar yunwa, rashin tsaro, da cin zarafi ta hanyar jima'i, yawancin 'yan gudun hijira yanzu sun gwammace su koma yankunansu, duk da rashin tsaro. Mai gabatarwa: Zubaida Baba Ibrahim Marubuciya: Tracy-Allen Ezechukwu Muryoyin shiri: Ruqayya Saeed, Hawwa Bukar, Khadija Gi...
An Dawo Da Su Gida ne Ko Kuma An Canja Musu Matsuguni ne? 15.10.2022 6:10
Gwamnatin jihar Borno ta kuduri aniyar mayar da ‘yan gudun hijira daga sansanonin ‘yan gudun hijira zuwa sabbin wuraren tsugunar da jama’a ko kuma kananan hukumominsu. Duk da alkawuran samar da tsaro da abinci, shirin na sake tsugunar da jama'a ya fuskanci kalubale da dama. Da alama 'yan gudun hijirar dole ne su fuskanci wani nau'i na sabuwar rayuwa a yanzu. Mai gabatarwa: Zubaida Baba Ibrahim Mar...
Ina Amfanin Gida Idan Babu Zaman Lafiya? 08.10.2022 6:29
Al’ummomin da ke karkashin karamar hukumar Chikun A Arewa maso Yammacin Najeriya, ba su da tsaro. A wasu kauyukan dake fadin karamar hukumar, gidajen da babu kowa a cikinsu sun zama ruwan dare gama gari. Yawancin wadannan al'ummomi a kullum 'yan ta'adda suna kaiwa hari da garkuwa da mutane da lalata dukiyoyi. Mazauna suna ci gaba da barin gidajensu zuwa wasu al'ummomi, amma har yaushe sabbin gidaj...
Ta'addanci Bai Hanata Neman Ilimi Ba 01.10.2022 5:18
Zarah na ganin Bama garin al'umma ne mai cike da ban tsoro. A baya, garin ya taba zama cibiyar kasuwanci a jihar Borno. Amma yanzu ya zama tarihi bayan hare-haren da 'yan ta'adda ke kaiwa sama da shekaru goma da suka wuce. Duk da tserewa da ta yi daga sacewa da cin zarafi daga kungiyoyin 'yan ta'adda, amma yanzu yanayi ya tilastawa wannan budurwa komawa garin da ya tara mata bakin ciki hade da ru...
Kirsimeti A Hannun Masu Garkuwa 24.09.2022 6:03
21 ga Satumbar 2021 rana ce da al'ummar Unguwan Gwari dake Kaduna ba za su manta da ita ba. Sama da mazaunanta 20 ne suka fada hannun masu garkuwa da suka nemi kudin fansa. Sun yi rayuwa a hannunsu har tsawon kwanakin da ya kai ga bikin kirsamati da sabuwar shekara. Wannan ya saka yan uwa da abokan wadanda aka kama din cikin tsananin damuwa. Abin da ya biyo bayan wannan tashin hankali shi ne ya ca...
Daga Kurkuku Mai Ban Tsoro Zuwa Bakon Gida 17.09.2022 6:02
Rayuwar Baana Alhaji Ali ta ruguje bayan daurin shekara shida a karkashin zargin da ake yi masa na dan ta’adda ne, ya jure gallazawar Barikin Giwa, yayin da matarsa ke fafutukar ganin an sake shi. Mai gabatarwa: Zubaida Baba Ibrahim Marubuciya:Hauwa Shafii Nuhu Muryoyin shiri: Umar Yandaki, Ruqayya Saeed Fassara: Ruqayya Saeed Edita: Aliyu Dahiru Furodusa: Khadija Gidado Babban Furodusa: Antho...
Rayuwa Da Tabon Cuta Mai Yaduwa 10.09.2022 6:09
Sakin Adam Modu da sojojin Najeriya suka yi ya kamata ya zama albishir da abun jin dadi ga matarsa da mahaifiyarsa da ke jira. Amma wata cuta da ya kamu da ita a lokacin da ake tsare da shi har yanzu tana addabarsa. A yanzu ya zama wani abin dawainiya ga danginsa da ke fama da talauci. Mai gabatarwa: Zubaida Baba Ibrahim Marubuci: Kunle Adebajo Muryoyin shiri: Umar Yandaki, Ruqayya Saeed Fass...
Sun Masa Alkawarin Sana'a Amma Suka Kaishi Kurkuku 03.09.2022 5:03
A jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya, sojojin Najeriya sun kama dubban mutane a tsakanin shekarar 2015 zuwa 2016, a yunkurinsu na dakile hare-haren Boko Haram. Da yawa daga cikin wadanda aka kama ‘yan gudun hijira ne. Modu Bukar na daya daga cikinsu. Ya ce sojoji a sansanin ‘yan gudun hijira ne suka shaida masa cewa an dauke shi ne domin ya koyi sana’a har na tsawon watanni uku. Daga ka...
Doguwar Tafiya A Iyakokin Kasashe Don Tserewa Boko Haram 27.08.2022 7:36
Hannatu ta samu kwanciyar hankali a matsayinta na malama a jihar Borno har sai da Boko Haram ta afka musu; An tilasta mata barin waccan rayuwar ne yayin da ta yi tattaki kimanin kilomita 300 don tserewa daga fushin maharan. Mai gabatarwa: Zubaida Baba Ibrahim Marubuciya: Chigozie victor Muryoyin shiri: Ruqayya Saeed Fassara: Ruqayya Saeed Edita: Aliyu Dahiru Furodusa: Khadija Gidado Babban Furodu...
Munje Neman Taimako Gurin Sojoji Amma Sai Suka kama Mazajenmu 20.08.2022 3:49
A jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, sojojin Najeriya sun kama dubban mutane ba bisa ka'ida ba tsakanin shekarar 2015 zuwa 2016, a yunkurinsu na yaki da 'yan ta'adda a lokacin da Boko Haram ke kai hare-hare. Yawancin wadanda aka kama ba su da laifi. Mijin Zarah na daya daga cikinsu. An gaya mata cewa ya mutu a tsare. Yanzu ta sake yin aure, amma labarin da ya zo mata shi ne yana raye....
Daga Kamu Ba Dalili Zuwa Rasa Matsuguni 13.08.2022 5:50
A jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, sojoji sun kama dubban mutane ba bisa ka'ida ba a tsakanin shekarar 2015 zuwa 2016 a yunkurinsu na yaki da 'yan ta'adda a lokacin da Boko Haram ke yawaita kai hare-hare. Yawancin wadanda aka kama ba su da laifi. Kaadi Aji yana daya daga cikinsu. Bayan shekaru shida a tsare ba bisa ka'ida ba, a karshe an sake shi ba tare da tuhumar sa ba amma yanzu...
Ta Gudarwa Hari A Gona Ta Yi Jinya A Sansanin Gudun Hijira 06.08.2022 4:53
Rikicin manoma da makiyaya a jihar Benue dake arewa ta tsakiyar Najeriya na ci gaba da raba mutane da gidajensu, wadanda galibinsu mata ne da suka tsira daga mutuwa kuma har yanzu suna fama da tashin hankali. Mai gabatarwa: Zubaida Baba Ibrahim Marubuciya:Anita Eboigbe Muryoyin shiri: Ruqayya Saeed, Hauwa Shaffii Nuhu, Khadija Gidado, Hawwa Bukar Fassara: Ruqayya Saeed Edita: Aliyu Dahiru Furodus...
Ya Gudarwa Yan Boko Haram Karshe Aka Ce A Cikinsu Yake 30.07.2022 5:42
A jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, sojojin Najeriya sun kama dubban mutane ba bisa ka'ida ba a tsakanin shekarar 2015 zuwa 2016, a yunkurinsu na yaki da 'yan ta'addan a lokacin da suka yawaita kai hare-hare. Yawancin wadanda aka kama ba su da laifi. Gambo Modu na daya daga cikinsu. Bayan ya shafe shekaru shida yana tsare ba bisa ka'ida ba, daga karshe an wanke shi daga zargin Boko...
Ya Kubucewa Masu Garkuwa Ba Tare Da Biyan Fansa Ba 23.07.2022 5:51
A Arewa maso Yammacin Najeriya, yin garkuwa da mutane yana iya faruwa a ko'ina, ba wai zama a wurin da bai dace ba ne a lokacin da bai dace ba. Wani manomin shinkafa da masara mai suna Mustapha Shafi’i a garin ‘Yarkofoji na jihar Zamfara, yana cikin gidansa ne ‘yan ta’adda suka fasa masa kofarsa, suka kutsa kai, suka tafi da shi a lokacin da matarsa ke kallonsu tana rokon su sakeshi. Yayi sa'a, ya...
Kadaici Saboda Rashin Miji 16.07.2022 5:16
Mata a sansanin ‘yan gudun hijira na Dalori II da ke jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya sun ce Jami’ai ' suna duba matsayin auren su ko rashinsa ne kafin su zaɓi wadanda zasu bawa kayan agaji. Mai gabatarwa: Zubaida Baba Ibrahim Marubuciya: Zubaida Baba Ibrahim Muryoyin shiri: Ruqayya Saeed, Khadija Gidado Fassara: Zubaida Baba Ibrahim Edita: Aliyu Dahiru Furodusa: Khadija Gidado Babban F...
Rashin Lafiya A Sansanin En Gudun Hijira 09.07.2022 5:35
Yan gudun hijira a sansanin Tse-Yandev da ke Makurdi a arewa ta tsakiyar Najeriya na fuskantar matsalar rashin lafiya. Maza da mata musamman ma tsofaffin, suna fama da rashin lafiya. Yara kuma suna mutuwa bayan rashin lafiya. Gwamnati ta gaza musu kuma suna cigaba da amfani da maganin gargajiya, da fatan ta zasu samu sauki. Mai gabatarwa: Zubaida Baba Ibrahim Marubuci: Jarius Awo Muryoyin shiri: H...
Siyen Rayuwa da Kudin Fansa a Arewa Maso Yamman Najeriya 02.07.2022 6:25
Biyan kuɗaɗen fansa don tsira daga hannun 'yan ta'addan da ake kira da yan fashin daji, ya zama ruwan dare a Sokoto da ke Arewa maso Yammacin Najeriya. Abubakar Sanusi, dan shekara 22, ya ba da labarin abin da ya faru da shi mai ban takaici da ya kai ga rashin abokinsa Farouk. Mai gabatarwa: Zubaida Baba Ibrahim Marubuci: ‘Abiodun Jamiu Muryoyin shiri: Akila Jibrin, Attahiru Jibrin Fassara: Zubaid...
#ENDSARS: Iyalan wadanda suka rasu suna fama da radadin jinkirin shari'a 25.06.2022 7:48
Zanga-zangar #EndSARS ta samo asali ne sakamakon korafe-korafen da suka taso daga shekaru da dama da jami'an rundunar 'yan sanda ta SARS ke aikinta. Da yawa daga cikin matasan Najeriya sun fito kan tituna domin nuna adawa da kisan gilla da sauran laifuka da rundunar 'yan sanda ke yi. Da yawa sun rasa rayukansu kuma har yanzu ba su sami adalcin da ake bukata ba. Mai gabatarwa: Zubaida Baba Ibrahim...
Similar podcasts
Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.