HumAngle

Birbishin Rikici

News HA ↓ 130 episodes

Kokarin nutsawa cikin wahalhalun da mutanen da ke zaune a yankunan da ake fama da tashe-tashen hankula ke fuskanta, yawanci yakan zo ne kawai ta fuskar kididdiga; Birbishin Rikici wani shiri ne na mako-mako akan waɗannan labarun sirri na wadanda rikici da tashin hankali suka shafa da HumAngle ke kawo muku.

Author

HumAngle

Category

News

Podcast website

rss.com

Latest episode

Jun 6, 2026

Where to listen?

Podcasts in the app Replaio Radio Coming soon

Podcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts

Get it on Google Play Install for free Android 5M+ downloads · 4.8 rating iOS soon

Episodes

Labaran Komawa Gidan 24.06.2023

 Wata mata ‘yar shekara 40, ta bayyana irin gwagwarmayar da ake fama da ita a kullum na samun kayan agaji a sansanin ‘yan gudun hijirar, yadda ba a ciyar da su tsawon shekara guda ba, kuma suna karbar bashi domin su biya bukatunsu.  Marubuciya: Hawwa Bukar Mohammad Muryoyin Shiri: Khadija Gidado Fassara: Rukayya Saeed    Edita: Aliyu Dahiru  Furodusa: Khadija Gidado Babban Furodusa: Anthony Asemot...

Ciwon Zama Dan Gudun Hijira A Inda Yaki Ya Wargaza 27.05.2023

Tun lokacin da aka fara rikicin Boko Haram a Arewa maso Gabashin Najeriya, rayuka da yawa sunyi muni ga miliyoyin mutane. Yakura Kumshe na daya daga cikin wadannan mutanen. Mun tambaye ta yadda take ji game da yadda al’amura suka sauya cikin sauri, tun daga ranar a Kumshe lokacin da ita da danginta suka san cewa dole ne su gudu zuwa Maiduguri. Tayi magana mei tsawo. Marubuciya: Hauwa Shaffi Nuhu M...

Tun Da Aka Kama Mamio Ba A San Inda Yake Ba! 20.05.2023

 Shekaru goma da suka gabata, yayin da rikicin Boko Haram ya yi kamari a Maiduguri, harkokin kasuwanci sun koma baya. Don haka, Alhaji Modu ya yanke shawarar tafiya zuwa birnin Legas da ke kudancin Najeriya, tare da fatan sayar da amfanin gonan sa. Bayan shekara goma, har yanzu bai dawo ba.  Marubuci: Kunle Adebajo Muryoyin shiri: Khadija Gidado Fassara: Rukayya Saeed    Edita: Aliyu Dahiru  Furod...

Komawa Gida Ko Sake Barinsa? 13.05.2023

A shekarar 2021, gwamnatin jihar Borno ta sanar da cewa za ta rufe dukkan sansanonin ‘yan gudun hijira da ke Maiduguri tare da fara tsugunar da mutanen garin a garuruwansu ko wasu garuruwa. Hakan dai ya kasance ne domin a rage yawan ‘yan gudun hijira a babban birnin kasar da kuma kara samun karfin gwiwa a tsakanin mutanen da suka dogara da kayayyakin agaji tsawon shekaru. Marubuciya: Yakura Kumshe...

'Ba Rai, Ba Mutuwa' 06.05.2023

Ragowar kuɗaɗen ayyukan jin kai ga ƴan gudun hijirar da ba su da mafita yana janyo shigarsu tsakiyar hatsarin hare-hare da ke faruwa idan sun fita gonaki don neman samun kudin siyan abinci.  Daya daga cikin irin wadannan mutanen shine Hagola Biya, mahaifi ga yara 14 kuma mijin mata biyu. Mai Gabatarwa: Rukayya Saeed Marubuci: Murtala Abdullahi Muryoyin shiri: Akila Jibrin Fassara: Rukayya Saeed   ...

Rayuwa A Daular Boko Haram 29.04.2023

Yaya rayuwa take a matsayin macen da aka sace a yankin Boko Haram? Yaya ya bambanta da rayuwa a cikin yankuna da ke ƙarƙashin ikon gwamnati? Saurari labarin Amina a cikin shiri na wannan mako. Mai gabatarwa: Rukayya Saeed Marubuciya: Anthony Asemota Muryoyin shiri: Khadija Gidado Fassara: Rukayya Saeed    Edita: Aliyu Dahiru  Furodusa: Khadija Gidado Babban Furodusa: Anthony Asemota Babban Mashiry...

Ta Rasa Matsuguni, Ta Kamu Da Cuta 22.04.2023

Mata a sansanin Malkohi da ke jihar Adamawa a arewa maso gabashin Najeriya na fuskantar wani yanayi na musamman daga amfani da wuraren da ba su da tsafta a sansanin.  Cututtukan farji, kaikayi da suke kira ‘cutar bayi’ na shafar rayuwarsu. Mai gabatarwa: Rukayya Saeed Marubuciya: Zubaida Baba Ibrahim Muryoyin shiri: Khadija Gidado, Zubaida Baba Ibrahim, Sabiqah Bello Fassara: Rukayya Saeed    Edit...

Mijinta Ya Bata Tana Cikin Shauƙinsa 15.04.2023

 Aisa Modu tana da shekara goma sha takwas da haihuwa kuma tana dauke da juna biyu a lokacin da ta zama yar gudun hijira. Bayan makonni da cikin, ta rabu da mijinta, Bulama Ali.  Mai gabatarwa: Rukayya Saeed Marubuciya: Kunle Adebajo Muryoyin shiri: Khadija Gidado Fassara: Rukayya Saeed    Edita: Aliyu Dahiru  Furodusa: Khadija Gidado Babban Furodusa: Anthony Asemota Babban Mashiryi: Ahmad Salkida

Yara Ne Ke Mutuwa Idan Aka Yi Ruwa A Nan 08.04.2023

A sansanin Wuro-Ahi da ke garin Fufore a jihar Adamawa a arewa maso yammacin Najeriya, an rufe wani asibitin da ke kula da ‘yan gudun hijira.   An rasa rayukan yara, ciki har da 'yar Safiratu. Mai gabatarwa: Rukayya Saeed Marubuciya: Zubaida Baba Ibrahim Muryoyin shiri: Khadija Gidado Fassara: Rukayya Saeed    Edita: Aliyu Dahiru  Furodusa: Khadija Gidado Babban Furodusa: Anthony Asemota Babban Ma...

Lokacin Da Farin Cikin Mahaifiya Ya Gushe 01.04.2023

A wani lokacin, Amsa ta  na ba kanta lefin abun da ya faru da danta. A can Kamaru, L7 ya so ya ci gaba da zama a kasar kuma ya yi wa me gidan sa aiki. Amma babban yayansa, Musa, ya rasu a can bayan gajeriyar rashin lafiya, Amsa ta ga hakan a matsayin mugun abu. Don haka ta dage kowa ya koma Najeriya.  Mai gabatarwa: Rukayya Saeed Marubuciya: Kunle Adebajo Muryoyin shiri: Khadija Gidado Fassara: Ru...

'Ko Gawarsa Ba Su Gani Ba' 25.03.2023

Yakawu ta nema mijinta a ko ina amman bata gan shi ba. Duk wanda ta tambaya, wanda zai iya sanin inda yake, sai su ce sun san shi, amma ba su da masaniyar inda yake. "Mutane sun ce ba su ga ko gawarsa ba," in ji ta. Mai gabatarwa: Rukayya Saeed Marubuciya: Kunle Adebajo Muryoyin shiri: Khadija Gidado Fassara: Rukayya Saeed    Edita: Aliyu Dahiru  Furodusa: Khadija Gidado Babban Furodusa: Anthony A...

Rayuwar Auren Wacce Ta Fada Hannun Boko Haram 18.03.2023

 Amina tana da shekaru 17 a duniya lokacin da wani dan ta'addan Boko Haram ya nuna wa mahaifiyarta bindiga, ya dora ta a saman babur dinsa, sannan ya tafi da ita. Sai da ta shekara takwas kafin ta sake ganin mahaifiyarta.  Mai gabatarwa: Rukayya Saeed Marubuciya: Zubaida Baba Ibrahim Muryoyin shiri: Khadija Gidado Fassara: Rukayya Saeed    Edita: Aliyu Dahiru  Furodusa: Khadija Gidado Babban Furod...

Sun Rasa Matsugunansu Don Tsira Daga Kisan Kiyashi 11.03.2023

A ranar Litinin, 2 ga watan Yuni, 2014, ‘yan kungiyar ta’addancin nan ta Boko Haram sun kashe kimanin mutane 400 a karamar hukumar Gwoza da ke jihar Borno, a arewa maso gabashin Najeriya, a wani abin da a yanzu aka fi sani da kisan gilla a Gwoza. Amma akwai wadanda suka tsira kuma wannan shine labarinsu. Mai gabatarwa: Rukayya Saeed Marubuciya: Zubaida Baba Ibrahim Muryoyin shiri: Mahdi, Zubaida B...

Me Ya Faru Da Bukar Mandara? 04.03.2023

Halimah Abba batasan inda mijinta yake ba. Bayan sun yi gudun hijira sakamakon rikicin Boko Haram a shekarar 2015, Bukar ya je Yola ne domin ya samu aikin yi da kuma shirya musu inda zasu zauna. Ya kira Halimah ya ce ya iso lafiya.  Mai gabatarwa: Ruqayya Saeed Marubuci: Kunle Adebajo Muryoyin shiri: Khadija Gidado Fassara: Rukayya Saeed    Edita: Aliyu Dahiru  Furodusa: Khadija Gidado Babban Furo...

Sun Rabu A Zahiri Amma Zuciyarsu Na Hade 25.02.2023

Adamu da Rahmatu suna soyayya da juna tun kafin kafa kungiyar ta'addanci na Boko Haram fiye da shekaru goma da suka wuce. Shekaru da dama da suka tsere daga gidajensu sakamakon tashin hankalin, har yanzu suna fama da illoli da rikicin da Boko Haram ya haifar.  Mai gabatarwa: Rukayya Saeed Marubuciya: Zubaida Baba Ibrahim Muryoyin shiri: Zubaida Baba Ibrahim, Aliyu Dahiru Fassara: Rukayya Saeed   ...

Dan Gudun Hijira Daga Najeriya Ya Bace A Kamaru 18.02.2023

Me ke faruwa idan mutanen da ke tserewa daga hare-haren ta'addanci a Arewa maso Gabashin Najeriya suka shiga cikin kasashen da ke makwabtaka da Afirka ta Yamma da Afirka ta Tsakiya? Amsar a takaice ita ce sun zama 'yan gudun hijira. Amma ba ko wani  lokaci bane suke samun mafakar da suke nema ba. Wani lokaci, ketare iyakokin zuwa cikin waɗannan ƙasashe kamar guduwa ne ba’a tsira ba.  Mai gabatarwa...

Bacewar Miji Nagari 11.02.2023

Da yawa daga cikin matan da suka rasa matsugunansu a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, wadanda aka tsare mazajensu ba bisa ka'ida ba ko kuma suka bace, suna kewar mazajen su da masu kula dasu da ya'yan su. Aisha tana kewar fiye da haka, ta yi kewar gaskiya da kyautatawa irin ta Umar. Mai gabatarwa: Ruqayya Saeed Marubuciya: Kunle Adebajo Muryoyin shiri: Zubaida Baba Ibrahim Fassara: Rukayya Sae...

Soja Ne Ya Daure Mijinta, Sannan Ya Nemi Aurenta 04.02.2023

Tsakanin shekara 2014 da 2015, Falmata Abubakar  ta shiga wani yanayi mai matukar raɗaɗi. Wani soja da ya tsare mijinta shi ne ya ci gaba da cutar da ita. Mai gabatarwa: Ruqayya Saeed Marubuciya: Hauwa Shaffi Nuhu Muryoyin shiri: Hawwa Bukar Fassara: Rukayya Saeed    Edita: Aliyu Dahiru  Furodusa: Khadija Gidado Babban Furodusa: Anthony Asemota Babban Mashiryi: Ahmad Salkida

Yadda Kisan Makiyaya Ke Yawaita A Hannun Yan Banga 28.01.2023

Ja'e Sanni, mai shekaru 50 ya zauna cikin nutsuwa yayin da yake ba da labarin yadda aka kashe dansa. Bai taba tunanin lamarin zai kai ga jama'a ba saboda babu wani rahoto da kafafen yada labarai suka bayar kan lamarin. Mai gabatarwa: Zubaida Baba Ibrahim Marubuciya: Kabir Adejumo Muryoyin shiri: Akila Jibrin, Attahiru Jibrin, Isaac Oritogun Fassara: Ruqayya Saeed Edita: Aliyu Dahiru  Furodusa: Kha...

Tashin Hankalin Wani Iyali Bayan Garkuwa Da Yan Uwansu 21.01.2023

 A lokacin da Azurfa John mai shekaru 21 da yar uwarta mai suna Peace Aboi  suka hadu a Abuja, babban birnin Najeriya, suka shiga jirgin Abuja zuwa Kaduna, ba su da masaniyar cewa za su shiga hannun 'yan ta'adda.  Mai gabatarwa: Zubaida Baba Ibrahim Marubuciya: Zubaida Baba Ibrahim Muryoyin shiri: Akila Jibrin, Isaac Oritogun Fassara: Ruqayya Saeed Edita: Aliyu Dahiru  Furodusa: Khadija Gidado Bab...

Kellu Haruna: Ta Fuskar Jama'ar Da Ta Nemarwa Yanci 14.01.2023

Kellu Haruna ta jagoranci kungiyar Knifar Movement, wata kungiyar mata masu fafutukar ganin an saki mazajensu da aka tsare ba bisa ka'ida ba tsawon shekaru ba tare da an gurfanar da su gaban kotu ba. A cikin shirin na yau, mun yi nazari kan rayuwar Kellu da kuma gudunmawar da ta bayar ga harkar kafin Allah ya yi mata rasuwa. Mai gabatarwa: Aliyu Dahiru Aliyu Marubuciya: Hauwa Shaffi Nuhu Muryoyin...

Yayin da Bakin Ciki Ya Cakuda Kokwanto Da Buri 07.01.2023

Bayan ta rasa danta, mijinta, da jikanta a cikin shekaru takwas, Amina ta yi ƙoƙari don daidaita begen sabuwar gaba da baƙin cikin abubuwan da suka faru a baya. Mai gabatarwa: Zubaida Baba Ibrahim Marubuci: Kunle Adebajo Muryoyin shiri: Ruqayya Saeed, Umar Yandaki Fassara: Ruqayya Saeed Edita: Aliyu Dahiru  Furodusa: Khadija Gidado Babban Furodusa: Anthony Asemota Babban Mashiryi: Ahmad Salkida

Yan Uwa Biyar Aka Sace, Daya Kawai Aka Samu! 31.12.2022

Yan Boko Haram ne suka sace Ummi da 'yan uwanta hudu a lokacin da suke debowa iyayensu itace. Bayan ta shafe kusan shekaru biyar a tsare, ita ce ’yar uwa daya tilo da ta tsira daga wannan mawuyacin hali. Mai gabatarwa: Aliyu Dahiru Aliyu Marubuciya: Zubaida Baba Ibrahim Muryoyin shiri: Ruqayya Saeed, Khadija Gidado Fassara: Ruqayya Saeed Edita: Aliyu Dahiru  Furodusa: Khadija Gidado Babban Furodus...

Damuwar Rasa Matar Aure Ga Harin Ta'addanci 24.12.2022

Bayan hare-haren ta'addancin da ake kaiwa a kai a kai, Ba abin da jama'ar Yanbuki ke fuskanta sai zaman damuwa da bakin ciki.  A cikin wannan shirin mun kawo muku  labarin bacin rai da raunin da ma'aurata ke fuskanta bayan sun rasa wasu muhimman abubuwa ga harin ta'addanci.  Mai gabatarwa: Aliyu Dahiru Aliyu Marubuciya: Zubaida Baba Ibrahim Muryoyin shiri: Umar Yandaki, Isaac Oritogun, Attahiru Ji...

Matan Da Yan Ta’adda Suka Mayar da Su Zawarawa 17.12.2022

Yawancin al’ummomi da rikicin tada kayar baya ya shafa a yankunan arewa maso yammacin Najeriya, sukan dogara da jami’an ‘yan banga wajen kare kansu. A cikin wannan shirin, mun ba da labarin zawarawan da mazajensu suka mutu wajen kare al’ummarsu. Mai gabatarwa: Zubaida Baba Ibrahim Marubuciya: Zubaida Baba Ibrahim Muryoyin shiri: Khadija Gidado, Ruqayya Saeed, Hajara Ibrahim Fassara: Zubaida Baba I...

Listen to the Birbishin Rikici podcast in Replaio

Radio and podcasts in one app - free, with no sign-up. Install today and do not miss the launch

Get it on Google Play

Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.