HumAngle
Birbishin Rikici
Kokarin nutsawa cikin wahalhalun da mutanen da ke zaune a yankunan da ake fama da tashe-tashen hankula ke fuskanta, yawanci yakan zo ne kawai ta fuskar kididdiga; Birbishin Rikici wani shiri ne na mako-mako akan waɗannan labarun sirri na wadanda rikici da tashin hankali suka shafa da HumAngle ke kawo muku.
Where to listen?
Podcasts in the app Replaio Radio Coming soonPodcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts
Episodes
Kisan Kiyashi A Ranar Kirsamati 06.07.2024 6:22
Babu wanda ya ga hakan yana zuwa, yayin da mutanen kauyen suka shirya kansu domin murnar bukukuwan, ‘yan bindiga na kan hanyarsu ta zuwa yanka su. An kai wa kananan hukumomi uku hari a jihar Filato a Najeriya, inda aka kashe mutane kusan 195 da kuma abubuwan tunawa da mutane suka yi a kusa da gidajensu. Mai Gabatarwa: Rukayya Saeed Muryoyin Shiri: Khadija Gidado, Hajara Ibrahim, Akila Jibrin Fassa...
An Kone Musu Gida, An Kone Duk Burikansu 08.06.2024 3:55
A shiri na yau, zamu ba da labarin Rukayya Saidu, wata uwa mai yara biyu da aka kona gidanta a Kaku, amma tana sake gina rayuwarta yanzu a Kajuru, Arewa maso Yammacin Najeriya. Mai Gabatarwa: Rukayya Saeed Muryoyin Shiri: Khadija Gidado Fassara: Rukayya Saeed Edita: Aliyu Dahiru Furodusa: Khadija Gidado Babban Furodusa: Anthony Asemota Babban Mashiryi: HumAngle Media
Yadda Ake Yi Wa Yan Kabilu Kudin Goro A Arewa Maso Yammacin Najeriya 04.05.2024 4:32
A yau za mu ji labarin Umar, wani Bafulatani da ya sha fama da hare-haren ta’addanci a kauyensu, sannan ya ga al’ummar da yake zaune a cikinsa sun juya masa baya ba gaira ba dalili sai asalinsa. Umar, kamar sauran jama’a, ya kasance wanda aka zalunta dan kabilanci. Mai Gabatarwa: Rukayya Saeed Muryoyin Shiri: Akila JibrinFassara: Rukayya Saeed Edita: Aliyu Dahiru Furodusa: Khadija Gidado Babban Fu...
Rayuwa Tare Da Warin Gawa 13.04.2024 5:31
A lokacin da ake fama da hare-haren Boko Haram a Najeriya, an samu asarar rayuka da dama. Binciken HumAngle ya gano cewa ana jibge gawarwaki da dama da ba a san ko su waye ba a asibitin kwararru na jihar Borno. Kusa da asibitin al’ummar Hausari ne, kuma suna da koke-kokensu. Muryoyin Shiri: Akila Jibrin, Samir Sherrif, Aliyu Dahiru Fassara: Rukayya Saeed Edita: Aliyu Dahiru Furodusa: Khadija G...
Rashin Matsuguni 09.03.2024 5:02
Wani magidanci mai suna David Jafaru mai shekaru 35 yana zaune ne a Kaduna, yana sana’ar tuka babur ne a lokacin da ya yi hatsari ya karya kafarsa. Hakan ya tilasta masa komawa gida a garin Dogon Noma don jinya. Mai Gabatarwa: Rukayya Saeed Muryoyin Shiri: Akila Jibrin Fassara: Rukayya Saeed Edita: Aliyu Dahiru Furodusa: Khadija Gidado Babban Furodusa: Anthony Asemota Babban Mashiryi: HumAng...
Ƙaramar Uwa Mai Jin-Ƙai 03.02.2024 4:50
Maryam Adam, mace mai tsananin rashin son kai ta dauki matsayin uwa da uba tun tana karama. An tilasta mata zama uwa tana da shekaru 13, an tilasta mata barin makaranta, ta gudu daga tashin hankali, kuma ta koma gudun hijira. Da duk abin da ta shiga, ta kuduri aniyar baiwa 'ya'yanta rayuwa mai inganci. Mai Gabatarwa: Rukayya Saeed Muryoyin Shiri: Khadija Gidado Fassara: Rukayya Saeed Edita: Ali...
Kwana 105 A Hannun Masu Garkuwa 06.01.2024 5:50
Kwanaki 105 Bilyaminu yana hannun masu garkuwa da mutane. A lokacin, iyalinsa sun yi duk abin da za su iya don tara kudin fansa da suka nema, ciki har da sanya gidajensu da gonakinsu don sayarwa. Amma hakan ya kasance da wahala sosai saboda manufar sake fasalin Naira ta Najeriya a wancan lokacin. Mai Gabatarwa: Rukayya Saeed Muryoyin Shiri: Akila Jibrin Fassara: Rukayya Saeed Edita: Aliyu Dahi...
Kwana 40 A Hannun Garkuwa 31.12.2023 5:04
Wannan shiri na #BirbishinRikici ya koma ne a lokacin da Najeriya ke fama da matsalar kudi inda a wani yunkuri na dakile tallafin ayyukan ta'addanci, babban bankin Najeriya ya bullo da sabbin tsare-tsare. Muna nazarin nasarorin manufofin yayin da wadanda suka tsira kamar Maimuna suka kwashe kwanaki a tsare har sai an biya kudin fansa. Mai Gabatarwa: Rukayya Saeed Muryoyin Shiri: Khadija Gidado F...
Tana Tsaka Da Gudu Ta Haihu! 23.12.2023 4:14
Salamatu Buhari, mai shekaru 20, tana aiki a gonarta, tana da juna biyu, a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka mamaye kauyensu. Sai suka fara kashe mazaje suna yiwa mata fyade, ta ji sai ta ruga don ta kare kanta. A tsakiyar daji ta shiga naƙuda. Mai Gabatarwa: Rukayya Saeed Marubuciya: Zubaida Baba Ibrahim Muryoyin Shiri: Khadija Gidado Fassara: Rukayya Saeed Edita: Aliyu Dahiru Furodusa: Kha...
Wasikar Bakin Ciki Daga Wacce Aka Yi Garkuwa Da Ita 25.11.2023 5:13
An sace Lilian Daniel, ‘yar shekara 20 daliba a Jami’ar Maiduguri a shekarar 2020 a lokacin da take komawa makaranta daga Jos a arewa ta tsakiyar Najeriya. Har yau babu wata magana kai tsaye daga gare ta. Wasiƙar baƙin ciki ɗaya kaɗai daga bauta. Mai Gabatarwa: Rukayya Saeed Marubuciya: Hauwa Shaffi Nuhu Muryoyin Shiri: Khadija Gidado Fassara: Rukayya Saeed Edita: Aliyu Dahiru Furodusa: Khad...
Abin Da Ya Faru A Gidajen Ma'aikata A Lokacin Kisan Kiyashi A Buni Yadi 11.11.2023 5:04
A ranar 25 ga Fabrairu shekarar 2014, 'yan ta'addar Boko Haram sun kai hari a Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Buni Yadi a Arewa maso Gabashin Najeriya. Sun kashe akalla ’yan makaranta matasa 29 a lokacin da suke kwana a dakunan kwanansu tare da kona dukkan gine-gine tun daga dakunan kwanan dalibai har zuwa ajujuwa. Sai masallacin ya tsira. Mai Gabatarwa: Rukayya Saeed Marubuciya: Hauwa Shaffi Nuh...
Gudun Tsira 28.10.2023 3:05
Labarin Jummai da aka yi garkuwa da ita ya nuna wa daruruwan wasu mata da ake sacewa daga gidajensu, dakunan kwanan su, filayen gonaki, ko kuma lokacin da suke tafiya a yankuna da dama na arewa maso gabas. Saurari labarin juriya da jarumtaka da tayi akan wadanda sukayi garkuwa da ita. Mai Gabatarwa: Rukayya Saeed Marubuci: Ahmad Salkida Muryoyin Shiri: Khadija Gidado Fassara: Rukayya Saeed Edit...
Wata Rayuwa! 22.10.2023 5:56
Ahmadu Aga ya tuna rayuwarsa a baya a garin Boboshe, al’ummar da ke tsakiyar Borno da shauki. Yana daya daga cikin sama da mutane miliyan biyu da aka tilastawa barin garuruwansu zuwa wuraren da suka fi tsaro a Najeriya da kasashen makwabta na Chadi, Nijar da Kamaru. Mai Gabatarwa: Rukayya Saeed Marubuci: Murtala Abdullahi Muryoyin Shiri: Akila Jibrin Fassara: Rukayya Saeed Edita: Aliyu Dahiru ...
A Najeriya Aka Siyar Da Shi Kamar Wani Bawa 14.10.2023 4:10
Aminu manomi ne a Daki Takwas, wani gari da ke Arewacin Najeriya. Amma ya kasa zuwa gonarsa saboda yawaitar sace mutane da ake da yaki karewa. Don haka rayuwa ta yi masa tsauri. Mun bibibiyi labarin Aminu, wanda dalibi ne da ya dogara da aikin gona don biyan kudin makaranta. Anma wuyar aikin a yanzu saboda tashin hankali ta janyo masa abin da ba zai manta ba. Mai Gabatarwa: Rukayya Saeed Marubuc...
Shi Ya Yi Mata Fyade Kuma Yake Tsokanarta Akai 07.10.2023 6:31
Wataƙila mutanen da suka rasa matsugunansu sun riga sun yi asara mai yawa saboda tashe-tashen hankula a arewa maso gabashin Najeriya, ‘yan uwansu, gidajensu, rayuwarsu, hankalinsu… Ta hanyar abubuwan da Hauwa, 14, da Adama, 22, za mu ga yadda yake da wuya a sami adalci ga wadanda aka yi wa fyade da kuma yadda rayuwarsu ta canza ba tare da jin dadi ba bayan cin zarafi. Mai Gabatarwa: Rukayya Saeed...
Rashin Miji da Rashin Matsuguni A Lokacin Rikici 30.09.2023 3:57
Kusan shekaru goma ke nan da Hauwa ta bar garinsu na Gwoza, har zuwa yau ta kasance ‘yar gudun hijirar da ke fuskantar kuncin rayuwa da ba za ta iya jurewa ba a babban birnin tarayyar Najeriya. Mai Gabatarwa: Rukayya Saeed Marubuciya: Rukayya Saeed Muryoyin Shiri: Khadija Gidado Fassara: Rukayya Saeed Edita: Aliyu Dahiru Furodusa: Khadija Gidado Babban Furodusa: Anthony Asemota Babban Mashiryi...
Ganin Kisan Kiyashi A Buni Yadi 24.09.2023 5:40
A wannan jerin da yake kunshe da labaran kisan Kiyashi na Buni Yadi, za mu ji daga bakin wani ma’aikaci akan halin da aka shiga kafin a kawo harin da kuma bayan harin. Mai Gabatarwa: Rukayya Saeed Marubuciya: Hauwa Shafii Nuhu Fassara: Rukayya Saeed Edita: Aliyu Dahiru Furodusa: Khadija Gidado Babban Furodusa: Anthony Asemota Babban Mashiryi: HumAngle Media
Kisan Kiyashi A Buni Yadi: Wasu Yan Mata Da Ba A Tabata Ba 16.09.2023 4:56
A wannan labarin na kisan kiyashin da aka yi a Buni Yadi, za mu ji daga bakin daya daga cikin yan matan wadanda yan ta'addan ba su yi musu komai ba. Mai Gabatarwa: Rukayya Saeed Marubuci: Hauwa Shafii Nuhu Muryoyin Shiri: Khadija Gidado Fassara: Rukayya Saeed Edita: Aliyu Dahiru Furodusa: Khadija Gidado Babban Furodusa: Anthony Asemota Babban Mashiryi: HumAngle Media
Wadanda Suka Ɓata Da Waɗanda Ke Nemansu 11.09.2023 6:13
Gibin da bacewar mutane ya samar a Arewa Maso Gabashin Najeriya ba karami ba ne. Wadansu giɓɓan manya ne da suka shanye mutane da yawa kuma suka jefasu rayuwar kunci. Saurari muryoyin yan uwan wadanda suka bata da kuma radadin da suke ciki. Mai Gabatarwa: Rukayya Saeed Marubuci: Kunle Adebajo Muryoyin Shiri: Khadija Gidado Fassara: Rukayya Saeed Edita: Aliyu Dahiru Furodusa: Khadija Gidado Ba...
Ranar Fargaba 26.08.2023 5:51
Mansura Zubairu, Naja'atu Muhammad, da Khadijat Aminu na daga cikin daliban da suka yi sa'a. Da kyar suka tsallake rijiya da baya a lokacin da 'yan ta'adda suka kai hari a Kwalejin Gwamnatin Tarayya (FGC) a Birnin Yauri, a watan Yunin 2021. Har yanzu suna tunawa da ranar ta'addanci da ba a saba gani ba. Mai Gabatarwa: Rukayya Saeed Marubuciya: Rukayya Saeed Muryoyin Shiri: Khadija Gidado, Hauwa S...
Rashin Matsuguni Agun Matar Dan Gudun Hijira 12.08.2023 3:49
A shekarar 2014, Furaira da danginta sun gudu daga gidansu da ke Gwoza a Arewa maso Gabashin Najeriya zuwa Girei da ke makwabtaka da Adamawa. Bayan shekara guda ta daidaita da sabon yanayi, mijinta ya yanke shawarar yin ƙaura don ya sami aiki mai kyau. Amma yau shekara bakwai kenan bai dawo ba ko aika tallafin kudi ba. Mai Gabatarwa: Rukayya Saeed Marubuciya: Rukayya Saeed Muryoyin Shiri: Khadija...
Daga Gona Zuwa Kurkuku 22.07.2023 3:30
Yeri Kambari, mai shekaru 40, ya bace ne a shekarar 2014 bayan da jami’an rundunar hadin gwiwa ta Civilian Task Force (CJTF) suka kama shi a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya. Bai shiga kungiyar ta'addanci ta Boko Haram ba. Babu wani abu da ke nuna ya cutar da kowa. Ya tafi gona ne kawai kuma ya kasance abin ya shafe shi. Ya Kodo Alli, yayarsa, ta tuna abubuwan da suka faru kamar sun faru kwanan...
Neman Tsira 15.07.2023 3:39
Ga mutanen da suka rasa muhallansu daga tashe tashen hankula a arewa maso gabas, damarsu ta tsira ta kasance ne wajen zabar ko su zauna a gidajensu ko kuma su fice. Yayin da tserewar Mary Oyuba tayi nasara, wasu da yawa ba su yi sa'a ba. Marubuciya: Zubaida Baba Ibrahim Muryoyin Shiri: Khadija Gidado Fassara: Rukayya Saeed Edita: Aliyu Dahiru Furodusa: Khadija Gidado Babban Furodusa: Anthony...
Yan Gudun Hijira Masu Kai Kudin Fansa 08.07.2023 6:34
A cikin wannan shirin namu na Birbishin Rikici , za mu saurari labarin wani matashin dan gudun hijira a Maiduguri da ke Arewa maso Gabashin Najeriya, wanda ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da shi kwanan nan, da kuma labarin wata mata da aka yi amfani da ita wajen kai kudin fansa. Marubuciya: Hauwa Shaffi Nuhu Muryoyin Shiri: Mahdi Garba, Khadija Gidado Fassara: Rukayya Saeed Edita: Aliyu Dahiru ...
Yakin Da Ya Tafi Da Komai 01.07.2023 6:31
Labarin Yagana Mamanaye na rashi ne mai ban mamaki. Kamar miliyoyin mutane a arewa maso gabashin Najeriya, za ta iya raba rayuwarta kashi biyu cikin sauki. Kafin tashin hankalin Boko Haram na 2009 da kuma bayan sa. Amma ba kamar yawancin mutane ba, a gare ta, yakin ba wai kawai ya ɗauki wannan ko wancan masoyin bane, - ya ɗauke duk abin da take da shi. Marubuciya: Kunle Adebajo Muryoyin Shiri: K...
Similar podcasts
Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.