RFI Hausa

Al'adun Gargajiya

News HA ↓ 24 episodes

Kawo al’adu na zamani da wadanda suka shude daga sassan kasashen duniya domin mai sauraro ya san cewa, duniyarmu tana da girma da yawan jama’a masu al’adu daban-dabam.  Akwai kuma Shirin al'adunmu na musamman na karshen mako da mu ke gabatarwa a ranakun Asabar da lahadi.

Author

RFI Hausa

Category

News

Podcast website

www.rfi.fr

Latest episode

Jun 30, 2026

Where to listen?

Podcasts in the app Replaio Radio Coming soon

Podcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts

Get it on Google Play Install for free Android 5M+ downloads · 4.8 rating iOS soon

Episodes

Makomar makarantun gwaji na harsunan gida a Jamhuriyar Nijar. 30.06.2026

Shirin wannan makon zai duba makomar makarantun gwaji na harsuna  gida da suka haɗa harshen Hausa. A waɗannan makarantu, za a riƙa koyarwa da harsunan gida.  Za a koya wa yara sana'o'i irin na gargajiya, a kuma koya musu adabin harsshe da sauransu.

Yadda Hausawa ke cin kasuwar abincin gargajiya a Saudiyya 23.06.2026

Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoullaye Issa a wannan mako ya yi duba kan yadda Hausawa ke ɗabbaƙa al'adunsu ta hanyar hada-hadar abincin gargajiya a ƙasa mai tsarki ko kuma Saudi Arabiya. Kamar yadda ya ke sanannen abu, Hausawa kan rungumi mabanbantan sabbin al'adu amma yana matuƙar wahala a garesu su yi watsi da abincin da suturarsu, wannan ya sanya samun kasuwannin abincin gargajiya da dama...

Yadda kiɗan Gurmi ke neman ɓacewa a ƙasar Hausa 16.06.2026

Shirinmu na yau ya leƙa sassan arewacin Najeriya da Jamhuriyar Nijar, tare da duba yadda wani fitaccen kiɗan gargajiya, wato kiɗan Gurmi, ke fuskantar barazanar bacewa a fadin ƙasar Hausa. Shin me ke janyo haka, kuma wane canji fasahar zamani ta kawo? Gurmi, kayan kiɗa ne da aka sani tun kaka da kakanni, wanda ƙera ta hanyar amfani da ƙoƙon ƙwarya da aka rufe shi da fatar dabba, musamman fatar guz...

Yadda Hausawa mazauna Jamus suka gudanar da gagarumin taron sada zumunci 09.06.2026

Shirin Al'adun mu na Gado na wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda Hausawa mazauna Jamus suka gudanar da wani gagarumin taro. Ku danna alamar Saurare domin jin cikakken shirin tare da Abdullahi Isa.

Gombe: Fulani sun yi taro kan warware matsalolin da ke ɓata musu suna 28.05.2026

Shirin Al'adunmu na Gado a wannan mako, yayi tattaki ne zuwa garin Gombe, inda Al'ummar Fulani suka gudanar da wani taro na farfaɗo da Al'adunsu na Gargajiya, da kuma tattaunawa a kan hanyoyin da za a bi wajen maido da Tarbiyya, gami da zamantakewa kyakkyawa a tsakanin Fulanin da kuma sauran Ƙabilu.

Yadda al'ummar wani gari suka riƙe Al'adar da suke kira da "Sai kowa ya zo" 12.05.2026

Shirin Al'adunmu na Gado na wannan mako tare da Abdoulaye Issa ya yi duba kan wata Al'ada da ake kira "sai kowa ya zo" a tsakanin al'ummar wani gari da ke Yankin Arewacin  Najeriya. Shiga alamar sauti don sauraron karin bayani.......

Tasirin karance-karance Littattafan Hausa wajen ɗabbaƙa al'adun Hausawa 05.05.2026

Shirin Al'adunmu na Gado tare da Abdoulaye Issa a wannan makon, ya mayar da hankali ne kan tasirin karance-karancen Littattafan Hausa a zamantakewar Al'ummar yankin. Irin waɗannan Littafai kuwa sun ƙunshi Magana Jari da jiki Magayi baya da Uwar Gulma da Shehu Umar kana Ruwan Bagaja, waɗanda dukkaninsu suka taimaka wajen fito da Al'adar Hausawa a fili. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken sh...

Rawar da mayaƙa suka taka zamanin da a Masarautun ƙasar Hausa 21.04.2026

Shirin Al’adun mu na Gado a wannan makon ya leka Jamhuriyar Nijar ne, inda ya duba batun da ya shafi mazajen dauri, musaman mayaƙan gargajiya a wannan zamani, jaruman da ke ƙarƙashin inuwar sarakunan gargajiya.  Duk inda akwai masarautun gargajiya an san su da tarin mayaƙa da ke yin tsarin daka a cikin kowane irin hali don kare su. Wannan tsarin ne da ya samo sali tun zamani da ake yaƙe-yaƙe tsaka...

Yadda kiɗan shantu ke ƙoƙarin ɓacewa duk da shaharar da ya yi a shekarun baya 07.04.2026

Shirin Al'adun mu na gado na wnnann mako ya waiwayi kiɗan Shantu ne da ya shahara tsakanin Mata a shekarun baya, wanda bayan tasirin da ya yi a waccan lokaci a fagen nishaɗantarwa, kiɗan na Shantu ke neman ɓacewa a yanzu. A shekarun baya dai wannan kiɗa na Shantu ya shahara ne tsakanin mata a yankunan arewacin Najeriya musamman a makarantu ko ɗalibai da kuma wasu sassan Jamhuriyar Nijar. Ku latsa...

Yadda bikin addinin gargajiya na Vodun ke gudana a Jamhuriyar Benin (2) 27.01.2026

Shirin Al'adunmu na Gado tare da Abdoulaye Issa a wannan makon, ya ɗora ne a kan yadda aka gudanar da bukukuwan addinin gargajiya na Vodun a Jamhuriyyar Benin, bikin addinin gargajiya da ke da muhimmanci a ƙasar.

Yadda bikin addinin gargajiya na Vodun ke gudana a Jamhuriyar Benin 20.01.2026

Shirin Al'adunmu na Gado tare da Abdoulaye Issa a wannan makon, ya yi tattaki ne zuwa Jamhuriyar Benin, inda ya halarci bukukuwan addinin gargajiya na Vodun, bikin da ke da muhimmanci matuƙa a ƙasar. Tun a bara ne aka ƙara wa'adin ranakun gudanar da wannan biki wanda ke samun mahalarta daga sassa daban-daban na duniya, inda alƙaluma suka nuna cewar a shekarar bara baƙi fiye da dubu 100 ne suka hal...

Hausawan Turai na fuskantar barazanar ɓacewar harshe da al'adunsu 13.01.2026

Shirin "Al'adunmu na gado" a wannan makon tare da Nura Ado Suleiman ya leƙa ne Masarautar Hausawa da ke nahiyar Turai, inda a makon Masarautar ta karɓi baƙuncin Mai Martaba Sarkin Daura Dakta Umar Faruk Umar da ya yi tattaki daga Tarayyar Najeriya, domin halartar bikin karrama Sarkin Hausawan na Turai da kuma naɗin wasu sabbin muƙaman na sarauta da suka shafi sassan nahiyar. Daya daga cikin kaluba...

Yadda aka gudanar da bikin nuna al'adu na masarautar Jiwa a Abuja 06.01.2026

Shirin Al'adun gargajiya na wanan makon tare da Abdoulaye Issa ya yi duba game da yadda aka gudanar da bikin al'adu na masarautar Jiwa a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya. Shiga alamar sauti domin sauraron cikakken shirin.......

Yadda aka gudanar da bikin naɗin sarautar sarkin Komadugu a Maraɗi 02.12.2025

Shirin na yau ya yada zango jihar Diffa dake Jamhuriyar Nijar,yankin da aka gudanar da bikin nadin sabon sarkin Komadugu, wanda ya samu halartar baƙi daga ciki da wajen ƙasar. Diffa dai kamar dai yadda masana tarihi suka tabbatar, ana na nufin Diwa a harshen Kanuri kenan. Kalmar ta samo asali ne daga kalmar "Di wa Nallé wa," wadda ke nuna tsabtar jiki da dai sauran abubuwan da suka shafi maza da m...

Yadda sana'ar sassaƙar Turmi ke fuskantar koma baya sabida ci gaban zamani 25.11.2025

Shirin "Al'adun mu na Gado" na wannan makon ya yi duba ne akan sana'ar nan ta sassaƙar Turmin, wadda ke a matsayin sana'ar al'adun gargajiya, ko da yake a yanzu samar da na'urori da ke amfanin da Turmin keyi ya mayar da sana'ar baya matuka gaya.    A baya duk macen da za'a kai gidan miji, akan hadata da Turmin babba da ƙarami kana da kuma na ƙarfe wanda za ta rika daka kayan ƙanshi wasu ma hatta K...

Yadda ƴan siyasa ke katsalandan a harkokin masarautu a Najeriya 18.11.2025

Shirin al'adun mu na gado na wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda ƴan siyasa ke katsalandan a masarautun gargajiya a Najeriya. Danna alamar sauarre domin jin cikakken shirin tare da Abdullahi Isa

Bikin Kalankuwar farfaɗo da al'adun Hausawa a jihar Kano ta Najeriya 04.11.2025

Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya mayar da hankali ne kan Kalankuwar farfaɗo da al'adunmu Hausawa a jihar Kano ta arewacin Najeriya, a wani yanayi da al'umma ke fuskantar matsalar gushewar tarin al'adu a mataki daban-daban. Yayin wannan bikin Kalankuwa dai an duba fannoni daban-daban na al'adu kama daga Kiɗan gargajiya da Waƙa baya ɓangarorin wasanni da dama, bikin d...

Yadda al'adar ''Ƴar zaman Ɗaki'' ta zama tarihi tsakanin hausawa 28.10.2025

Shirin Al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya mayar da hankali kan yadda sananniyar al'adar nan ta zaman ɗaki ke ƙoƙarin shuɗewa tsakanin al'ummar Hausawa. Shekaru aru-aru, da zarar an yi auren budurwa a ƙasar Hausa akan haɗata da ƙaramar yarinya da za ta yi mata zaman ɗaki, wanda a wasu lokutan anje kenan domin galibi aure ke raba wannan ƙaramar yarinya da gidan, kodayake wasu...

Yadda aka gudanar da bikin makiyaya na Cure Salee a Jamhuriyar Nijar 21.10.2025

Shirin a wannan mako ya yi tattaki ne, zuwa ƙauyen Ingal da ke Yankin Agadez a jamhuriyyar Nijar, domin waiwayar gagarumin bikin makiyaya da ƙabilu daban-daban da ake yi wa laƙabi da 'Cure Salee' wanda aka saba yi duk shekara. Bikin makiyayan na Cure Salee ya gudana ne a tsakanin ranakun 4 zuwa 6 ga watan da muke ciki na Oktoba. Manufar bikin ita ce yadda za a ƙarfafa haɗin kai tsakanin makiyaya d...

Yadda sana'ar kaɗi ke gab da gushewa tsakanin al'ummar Hausawa 14.10.2025

Shirin al'adunmu na gado tare da Nura Ado Suleiman a wannan makon ya mayar da hankali ne kan gushewar sana'ar kaɗi a ƙasar Hausa duk da kasancewarta guda cikin sana'o'in Hausawan suka gada kaka da kakanni. Galibi sana'o'in Hausawa na tafiya ne da tsarin rayuwa da zamantakewar jama'a, cikin wannan kuwa har da sana'ar kaɗi wadda galibi dattawa Mata suka fi ƙwarewa akai, kodayake wannan sana'a na gab...

Banbanci tsakanin maita da tsafi a mahangar al'adu da addini 07.10.2025

Shirin Al'adunmu na Gado tare da Nura Ado Suleiman a wannan mako, ya mayar da hankali kan manufar Maita da kambun baka a mahangar al'adu da kuma addini, a wani yanayi da ake yiwa wannan abubuwa biyu mabanbantan kallo. Duk da cewa wasu na yiwa waɗannan abubuwa biyu kallon abu guda, amma a wasu na kallon abubuwan biyu a matsayin mabanbanta kasancewar guda akan sameshi ne haka suddan yayinda ɗayan ku...

Yadda aka bar baya da ƙura a girmamawar da ka yiwa Rarara da digirin Dakta 23.09.2025

Shirin Al’adunmu na Gargajiya tare da Nura Ado Suleiman a wannan makon ya sake waiwayar fagen Waƙa guda daga cikin fannoni masu tasiri a Adabin Harshen Hausa la’akari da gudunmawar waƙoƙin da kuma mawaƙan da ke rera su wajen bunƙasa harshen. Tun cikin makon jiya masana da sauran jama’ar gari ke tofa albarkacin bakunansu akan karramawar  da wata Jami’a mai suna European-American University ta yi wa...

Sannu a hankali sana'ar ƙira na shuɗewa a jihar Agadez ta Jamhuriyar Nijar 16.09.2025

Shirin Al'adunmu na Gado na wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda sannu a hankali sana'ar kira ke shudwa musamman ta ƴan Kabilar Abzinawa da ke jihar Agadez a jamhuriyar Nijar. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Abdullahi Issa.

Bikin cika shekaru 10 da fara Ranar Hausa ta Duniya - kashi na biyu 02.09.2025

Shirin Al’adunmu na Gado a wannan makon ya ɗora ne akan Bikin ranar Hausa ta Duniya, bikin da yake mayar da hankali wajen bunƙasawa da faɗaɗa harshe da kuma al’adun Hausawa a fadin Duniya. A watan Agustan shekarar 2015 aka fara gudanar da wannan biki na ranar Hausa ta Duniya a Najeriya da sauran ƙasashen da ke da al’ummar Hausawa, bikin da sannu a hankali ya riƙa samun karɓuwa gami da faɗaɗa har z...

Listen to the Al'adun Gargajiya podcast in Replaio

Radio and podcasts in one app - free, with no sign-up. Install today and do not miss the launch

Get it on Google Play

Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.