Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Where to listen?
Podcasts in the app Replaio Radio Coming soonPodcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts
Episodes
Kalubalen Da Iyaye Ke Fuskanta Wajen Tarbiyyan 'Ya'yan Su 03.04.2025 27:12
Send us Fan Mail Duk wanda ya shekara arbain zuwa sama ya san irin tarbiyyan da ya samo daga wurin iyayen sa a da baya can, irin mu’amalan dake tsakanin sa da iyaye har ma da shakuwan dake tsakanin ‘ya’ya da iyaye. A yanzu kuwa abubuwa sun canza daga yadda aka san su, inda abubuwa suka rincabe sukayi wa iyaye yawa. Daya daga cikin manyan sauyin da aka samu sun hada da aikin gwamnati ko aikin wata...
Abubuwan Da Za Su Kwaɗaita Muku Azumtar Sitta Shawwal 01.04.2025 24:06
Send us Fan Mail Alqurani mai girma a cikin suratul Baqarah Allah ya wajabta wa musulmi da suka cika wasu sharudda azumtar watan Ramadana. Kamar yadda malamai suka sha fadi, wannan wata na dauke da wasu falala maras misaltuwa da bawa kan samu idan ya maida kai wajen ibada don samun rabauta daga ubangiji. Kazalika hadisai sun ruwaito kan falalar azumtar kwanaki shidda na watan shawwal, watan dake b...
Hanyoyin Komawa Cin Abinci Yadda Ya Kamata Bayan Watan Ramadana 31.03.2025 24:02
Send us Fan Mail Watan azumin ramadana kan zo da sauye sauye da dama da suka hada da kara kaimi wajen bauta wa ubangiji, samun lada ta hanyar ciyar da alumma da kuma falala masu yawa da basu misaltuwa . Wani sauyi da watan azumin watan ramadana ke zuwa dashi shine canjin yanayin ciman alumma, inda mutane ke canzawa daga cin abinci sau uku ko sama da haka a rana zuwa sahur da kuma bude baki. Bayan...
Abubuwan Da Ya Kamata Musulmi Su Yi Gabani Da Ranar Sallah 28.03.2025 27:32
Send us Fan Mail Lokutan sallah kamar yadda aka sani lokacin ne na farin ciki, nuna godiya ga ni’imar da Allah yayi mana da kuma bauta. Kazalika lokacin ne da zamu lura da tabbatar da aiyukan da zamu aikata su zama ingattattu. Ko wadanne irin abubuwa ne mutane ya kamata su aikata kafin da kuma ranar sallah? Wadanne hanyoyi za a bi don tabbatar da zaman lafiya yayin gudanar da bikin sallah? Shirin...
Halin Da Matasa Suka Tsinci Kan Su A Najeriya 27.03.2025 24:45
Send us Fan Mail Yau a Najeriya da yawa daga cikin matasa na fuskantar kalubale musamman wajen biya ma kan su bukatun su na yau da kullum sakamakon yanayin tattalin arzikin kasa, rashin aikin yi da kuma tsadar rayuwa. A wasu lokutan irin wadannan matasa sun yi karatu, wasu ma na da sana’oin su na hannu amma rashin aiki mai gwabi da zai biya musu bukatun su na cigaba da yin barazana da irin halin d...
Yadda Ake Yi Wa ‘Yan Majalisar Kasa Kiranye 25.03.2025 30:12
Send us Fan Mail Mulkin demokradiyya kamar yadda Hausawa ke cewa ‘yancin dan adam. A lokacin da ta baka damar tsayawa don a zabe ka kan wani mukami, kazalika ta baka damar zaben wanda kake so ya shugabance ka kuma ya wakilce ka. Wani abun da demokradiyyar ta baiwa alumma dama a kai kuma shine na yin kiranye ga wakilan da suka zaba musamman idan wadannan wakilan basa biya musu bukatun da suka tura...
Yadda Kasuwanci Ke Kasancewa Gabani Da Cikin Ramadana 24.03.2025 22:17
Send us Fan Mail Hausawa sunyi gaskiya da suka ce ‘yawan mutane sune kasuwa’. Yawan hada hadar da ake yi tsakanin ‘yan kasuwa da abokan cinikin su na daya daga cikin abun da zai tabbatar maka kasuwanci na gudana kamar yadda ake so. Sai dai da Zarar ance watan Ramadana ya kama wasu daga cikin kasuwanci kan samu nakasu, inda wasu kuma ke samun habbaka. Wasu kuwa kasuwar ce ke sauya salo, inda take d...
Illar Sare Itatuwa Ga Canjin Yanayi Da Lafiyar Mu 21.03.2025 30:13
Send us Fan Mail Shekaru da dama kenan da hukumomin duniya ke gudanar da tarurruka da dama kan zakulo hanyoyin da za a kawo karshen dumamar yanayi a duniya. Dumama ko canjin yanayi na cigaba da barazana ga duniya, inda ake samun sauye sauye ga yanayi da wasu abubuwa da masana ke bayyana ka iya kara ta’azzara in ba’ayi wani abu a kai ba. Daya daga cikin abubuwan da masana suka bayyana dake kawo wan...
Dalilan Da Ke Hana Wasu Teloli Cika Alƙawari 20.03.2025 23:03
Send us Fan Mail Sana’a na taka muhimmiyar rawa wajen habbaka tattalin arzikin alumma. Alumma da dama musamman a wannan lokacin na kara bayyana alfanun koyan sana’ar hannu don dogaro da kai maimakon dogara da aikin gwamnati ko na kamfani. Sai dai ana zargin wasu masu sana’ar hannu da rashin cika alkawari a wurin sana’ar su. Irin wadannan masu sana’ar hannun teloli na daga cikin su, wadanda a mafi...
Yadda Mai Karamin Karfi Zai Mallaki Muhalli Da Kudi Kalilan 18.03.2025 27:23
Send us Fan Mail Mallakan Muhalli na daya daga cikin burin kowanne dan Najeriya. Sai dai wannan buri a mafi yawan lokacin baya cika musamman ga masu matsakaitan samu. Kananan ma’aikata da mafi karancin albashin su yake naira dubu saba’in ba zai ciyar dasu, ko tufatar dasu ba, ballantana har suyi tunanin mallakan muhalli nasu na kashin kansu. Sai dai masana na bayyana cewa marasa karfin ma na iya m...
Guraben Aiki Da Aka Kasa Cikewa A Najeriya 17.03.2025 23:50
Send us Fan Mail Duk da kukan rashin aikin yi da ako da yaushe ke cigaba da addabar ‘yan Najeriya, a wasu lokutan ba rashin aikin yi ne matsalar ba, wadanda zasu cike guraben ayyukan ne suka yi karanci a Najeriya. Alkaluma na cigaba da bayyana dubban ‘yan Najeriya ne dai ke fito wa daga manyan makarantun kasar a kowace shekara. A yayin da da yawa basa samun aikin yi, so tari akwai dimbin guraben a...
Rashin Aikin Yi Da Hanyoyin Magance Su A Najeriya 14.03.2025 25:31
Send us Fan Mail Rashin aikin yi na daya daga cikin manyan kalubalen da najeriya ke fuskanta a wannan lokaci, musamman la’akari da yanda ake cigaba da samun matasa dake da karfi a jika amma babu aikin yi. Hukumar kididdiga ta kasa ta fitar da bayanan dake baiyana cewa rashin aikin yi ya karu a najeriya da kaso 5.3 a farkon wannan shekarar, kazalika binciken ya baiyana cewa wadanda basu yi karatu m...
Ko Yarjejeniya Da ’Yan Ta’adda Za Ta Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Arewa? 13.03.2025 27:15
Send us Fan Mail Masu iya magana kan ce dole uwar na ki. Matsalar tsaro da ta ki ci ta ki cinyewa musamman a Arewacin Najeriya tana tilasta wa wasu al’ummomi zakulo hanyoyin samun sa’ida ko yaya suke. Daya daga cikin wadannan hanyoyi da wasu al’ummomi suka runguma ita ce kulla yarjejeniya da ’yan bindigar dake addabar yankunansu. Shin ko cimma yarjejeniya da ’yan fashin daji mafita ce daga matsala...
Abubuwan Da Suke Shirin Faruwa A Fagen Siyasar Najeriya 11.03.2025 21:42
Send us Fan Mail Fagen siyasar Najeriya na ci gaba da daukar dumi yayin da ’yan kasa da dama suka yi kasake suna jiran girgiza ta gaba wadda wasu suke ganin tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai, ya diga mata dan ba. A baya-bayan nan dai an yi ta tsegunguma da rade-radi a kana bin da wasu jiga-jigan ’yan siyasar kasar nan, musamman ’yan adawa da ’ya’yan jam’iyya mai mulki wadanda suke...
Ladan Da Mai Aikin Karfi Yake Samu A Lokacin Azumi 10.03.2025 25:59
Send us Fan Mail Watan azumi lokaci ne da akan samu wasu ma’aikatu sun sassauta wa ma’aikata ta hanyar yi musu rangwame kamar rage musu yawan sa’o’in aiki. Sai dai a lokacin da wadannan mutane suke samun rangwame, akwai wadanda suke ayyuka ko sana’o’in da suka dogara da su ciyar da iyalansu. Sau da dama irin wadannan mutane sai sun fita sun yi aiki a rana, duk da suna azumi, suke samun abin da za...
Falalar Bude Baki Cikin Iyali A Lokacin Azumi 07.03.2025 26:50
Send us Fan Mail Hadisi ya tabbatar da yadda cin abinci tare yake kara dankon zumunci da kaunar juna da albarka a tsakanin al’umma. Mai yiwuwa wannan ne ya sa akan samu Karin kusanci da shakuwa a tsakanin duk iyalan da kan zauna su ci abinci. Ko kafin watan azumi dai, wasu magidantan kan mayar da cin abinci tare da tare da iyalin su al’ada. Shin ko mene ne matsayin bude-baki tare da iyali a watan...
Me Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Su Ga Ragi A Farashin Man Fetur Ba? 06.03.2025 20:26
Send us Fan Mail Fiye da wata guda ke nan tun bayan da Matatar mai ta Dangote ta sanar da rage farashin man fetur daga naira 890 zuwa naira 825 kowace lita. Bayan wannan ragi ne dai shi ma Kamafanin Mai na Kasa wato NNPCL ya sanar da rage nasa farashin. Sai dai har yanzu ba a ga ragin a gidajen mai ba. Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan wannan lamari.
Abin Da Ya Sa Ba Mu Bayar Da ‘Ramadan Basket’ Ba 04.03.2025 20:57
Send us Fan Mail A aladance, a duk lokacin da aka ce watan Ramadana ya karato samari da ‘yan mata kan yi musayar kyaututtuka don kyautata wa abokan zaman su. Misali, a lokacin azumi samari kan sayi kayan bude baki da suka hada da madara, kwai, da sauran kayan makulashe wanda ake yiwa lakabi da ‘’Ramadan Basket’’ a turance don kaiwa ‘yan matan su. Sai dai a wannan shekarar da alamun abun ya sauya s...
Yadda za ku yi girke-girken Azumi da kuɗi kaɗan 03.03.2025 14:49
Send us Fan Mail Yanayin tsadar rayuwa da ake ciki ya sa dole a yi tattalin kudin da ake kashewa. An saba da Ramadana ana yawan yin girke-girke da kayan buda baki iri-iri, amma kuma wannan azumin ya zo cikin yanayi na matsin tattalin arziki. Shirin Najeriya a Yau ya duba hanyoyin da za ku yi girke-girken da yawa yadda aka saba cikin sauki ba tare da kashe makudan kudade ba.
Ko Kun San Azumi Na Inganta Lafiyar Jiki? 28.02.2025 42:18
Send us Fan Mail Alumma na yin azumi ne bisa dalilan addini don samun lada kamar yadda Allah ya umurta a cikin Qurani mai girma. Sai dai daga baya binciken masana kimiyya ya gano cewa bayan lada da ake samu daga yin azumi, akwai wasu alfanu da mai azumi ke samu ga lafiyar jikin shi da suka hada da inganta karfi da zurfin tunani zuwa fitar da gurbatattun abubuwa da jiki baya bukata. A takaice dai,...
Halin da jama’a za su shiga idan Kamfanin Kaduna Electric ya ƙi sauraren ma’aikatansa 27.02.2025 22:58
Send us Fan Mail Wutan lantarki a Najeriya ya zama ginshikin rayuwa da alumma basa iya rayuwa ba tare dashi ba. A duk lokacin da aka ce an dauke shi zaka ga yadda alumma kan shiga cikin matsanancin hali, wasu da dama sun ta’allaka ne dashi wajen tafiyar da harkokin su na yau da kullum, kai har ma da kasuwanci. A kwanakin baya ne jihohin Kaduna, Sakkwato, Zamafara da kuma jihar Kebbi suka fuskanci...
Azumin Ramadana: Ko Kun San Dabinon Da Kuke Shan Ruwa Da Shi? 25.02.2025 26:29
Send us Fan Mail Ko kun san sunan dabinon da kuka fi so ku ci a lokacin shan ruwa? Dan Agadas ne, ko Ruwa-Ruwa, ko Annakhiyl? Yayin da ake shirye-shiryen tarbar watan Ramadana, shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan nau’ukan dabino da alfanunsa ga dan’Adam, musamman mai azumi.
Matakan Kariya Daga Cutar Ƙyandar Biri 24.02.2025 19:39
Send us Fan Mail Cutar kyandar biri da aka fi sani da Mpox ta kara bulla a Najeriya. Na baya bayan nan shine wanda ta bulla a jihar Filato inda aka samu wadanda suka kamu da ita mutum 11 da sai wanda ya rasa ransa mutum daya. Cutar ta kyandar biri ta bulla ne a kananan hukumomi biyar da suka hada da Jos ta Arewa, Bokkos, Shendam, Mangu da kuma Kenke. Ko wadanne irin matakai ya kamata alumma su dau...
Dalilan Da Ba Zamu Sauke Farashin Burodi Ba 21.02.2025 29:51
Send us Fan Mail A daidai lokacin da wasu alumma ke murnar saukar farashin kayayyakin abinci a kasuwanni kamar su shinkafa, masara da sauran kayan hatsi. Shima farashin flawa da ake amfani dashi wajen sarrafa biredi, gurasa da sauran makulashe ya sauka a kasuwa. Sai dai duk da saukar da farashin flawar tayi, alumma na cigaba da kokawa kan yadda har yanzu basu gani a kasa ba. Tun makonni biyu da su...
Tanadin Dokar Kasa Kan Kirkirar Gwamnatin Bibiya A Kano 20.02.2025 27:50
Send us Fan Mail Tun bayan bayyana kafa Gwamnatin Bibiya ko kuma Shadow government a turance da wata kungiya karkashin jamiyyar APC a jihar kano tace zata yi ne ne dai alumma da dama keta jefa ayar tambaya kan halascin wannan gwamnati. Kungiyar dai ta bayyana cewa zata kafa wannan gwamnati ne don bibiyan ayyukan gwamnatin gwamna Abba Kabir Yusuf don tabbatar da ana abin da ya kamata. Sai dai wan...
Similar podcasts
Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.