Najeriya a Yau

News HA ↓ 958 episodes

Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.

Category

News

Podcast website

www.buzzsprout.com

Latest episode

Jun 23, 2026

Where to listen?

Podcasts in the app Replaio Radio Coming soon

Podcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts

Get it on Google Play Install for free Android 5M+ downloads · 4.8 rating iOS soon

Episodes

Mece ce Makomar Dimokuraɗiyya Idan Aka Wajabta Kada Kuri’a? 19.05.2025

Send us Fan Mail Daya daga cikin ginshikan tsarin dimokuradiyya shi ne zabi – bai wa jama’a dama su zabi abin da suke so, ko kuma wanda suke so ya shugabance su. Wannan ne ya sa daya daga cikin muhimman matakai a kafuwar tsarin shi ne zabe. Sai dai kuma abin tambaya shi ne, zabin ya hada har da na yin zabe ko kaurace masa? Mene ne matsayin tsarin dimokuardiyya idan aka wajabta wa al’umma kada kuri...

Shin Jam’iyyar NNPP Za Ta Kai Labari A 2027? 16.05.2025

Send us Fan Mail Jam’iyyar NNPP wadda Dr. Boniface Aniebonam ya kafa a shekarar 2001, ta samu karfi sosai a Jihar Kano bayan tsohon gwamna Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya shiga cikinta a shekarar 2022 tare da mabiyansa na Kwankwasiyya.  Shigowarsa ta farfado da jam’iyyar, inda ta samu gagarumar nasara a zaɓen 2023 ta hanyar lashe kujerar gwamna da wasu kujerun majalisa.  Sai dai rikicin cikin gida...

Kuskuren JAMB Da Ya Haddasa Faduwar Dalibai A Jarabawa 15.05.2025

Send us Fan Mail Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB) ta yi amai ta lashe. Bayan ta musanta dukkan zarge-zargen da aka yi cewa tana da hannu a rashin kyawun sakamakon jarrabawar da ta shirya, Shugabanta ya fito ya amsa laifi. Yayin wata ganawa da ya yi da manema labarai, Farfesa Is-haq Oloyede ya ce dalibai 379,997 abin ya shafa, kuma hukumar zata sake shirya musu wata jarabawar....

’Yan Najeriya Sun Yi Tir Da Biyan Diyya Ga Kwastomomin Rukunin Band A 13.05.2025

Send us Fan Mail Wasu ’yan Najeriya sun yi Allah-wadai da wani umarni da Hukumar da ke Kula da Harkar Wutar Lantarki a Najeriya, wato NERC, ta bai wa kamfanonin rarraba wutar lantarki da su biya diyya ga abokan huldarsu da ke rukunin Band A. Hukumar ta NERC ta bai wa kamfanoni rarrabar wutar, wato DisCos, wannan umarni ne saboda rashin samar wa Band A din lantarki na akalla sa’a 20 a kullum a wata...

Abun Da Yasa Muka Ƙasa Kawo Karshen Tamowa A Wasu Jihohin Arewa Maso Gabas 09.05.2025

Send us Fan Mail Hukumomi a jihar Yobe sun dora alhakin kazancewar matsalar tamowa a kan rikicin Boko Haram da rashin shayar da jarirai nonon uwa yadda ya kamata da kuma gurbacewar harkar kiwon lafiya, da sauran su. Bayanin hakan na zuwa ne bayan ambato Babban Jami’i mai Kula da Ayyukan Jinkai na Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya, Mista Mohamed Malick Fall, yana  yara miliyaan daya a jihohin Born...

Kalubalen Da Iyaye Ke Fuskanta Wajen Tarbiyyan 'Ya'yan Su 08.05.2025

Send us Fan Mail Duk wanda ya shekara arbain zuwa sama ya san irin tarbiyyan da ya samo daga wurin iyayen sa a da baya can, irin mu’amalan dake tsakanin sa da iyaye har ma da shakuwan dake tsakanin ‘ya’ya da iyaye. A yanzu kuwa abubuwa sun canza daga yadda aka san su, inda abubuwa suka rincabe sukayi wa iyaye yawa. Daya daga cikin manyan sauyin da aka samu sun hada da aikin gwamnati ko aikin wata...

Me Ya Sa ‘Yan Gwagwarmaya Ke Shiga Tasku A Najeriya? 06.05.2025

Send us Fan Mail Yin gwagwarmaya ko fafutuka wani abu ne da ke cikin jinin dan Adam, musamman idan yana kokarin ganin an samu sauyi ko cigaba a al'umma.  Sai dai a Najeriya, sau da yawa ana danganta kalmar "gwagwarmaya" da rikici ko sabani da gwamnati. Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari ne kan yadda za a yi gwagwarmaya ba tare da an taka doka ba.

Abin da ke kai matasan Najeriya ci-rani wasu ƙasashen Afirka 05.05.2025

Send us Fan Mail A ko’ina a Nahiyar Afirka za a iya samun ɗan Najeriya da ya bar ƙasar sa domin rayuwa a wata ƙasa.  A yau ba sai an je Turai ko Amurka ba – kasashe irin su Mali, Ghana, Libya, Sudan da sauran su suna cike da matasa ’yan Najeriya wadanda suka je ci-rani. Shin me ya sa wadannan matasa suke barin Najeriya – uwa ga Afirka, mai albarkatu da dama? Me suke samu a waje da ba za su iya sam...

Yadda Naira Biliyan Daya Ta Salwanta A Gobarar Kasuwar Jos 02.05.2025

Send us Fan Mail Kusan Naira biliyan day ace aka kiyasta ta salwanta sakamakon gobarar da ta kone wane sashe na babbar kasuwar dake tsakiyar Jos babbar birnin jihar Filato. An rawaito cewar gobarar ta lakume shaguna fiye da dari biyar, galibinsu na masu sayar da kayan gwanjo. Mutane da dama dai sun rasa hanyar cin abincinsu, kasancewar galibinsu sun sun dogara ne da samun da suke yi a kullum a wan...

Dalilan Kamuwa Da Cutar Hawan Jini Da Hanyoyin Magance Ta 01.05.2025

Send us Fan Mail Cututtuka da dama suna Kamari a Najeriya wanda a mafi yawancin lokuta ma wadanda ke dauke da irin wadannan cututtukan basu da masaniyar suna dauke da su.  Kamar yadda majalisar dinkin duniya ta bayyana, zaman lafiya, rashin matsalar kwakwalwa, da samun wadata na daga cikin abubuwan dake tabbatar da lafiyar bil’adama.  Wata cuta da ta addabi da yawa daga cikin al’umma itace cutar H...

Dalilin Karyewar Farashin Shinkafa A Wasu Kasuwannin Najeriya 29.04.2025

Send us Fan Mail Rahotanni suna nuna cewa farashin shinkafa, daya daga cikin nau’ukan abincin da ’yan Najeriya suka fi ci, ya karye a wasu sassan kasar. Sauyin farashin ya sa ana tambayoyi – shin me ya haifar da wannan sauyi? Kuma me hakan ka iya haddasawa a rayuwar talaka? A kan wannan sauyi da dalilansa ne shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari.

“Dalilan Da Suka Sa Muke Sauya Sheƙa Zuwa Jam’iyya Mai Mulki” 28.04.2025

Send us Fan Mail Fagen siyasar Najeriya na ci gaba da jijjiga sakamakon sauya shekar da ’yan siyasa daga banarori daban-daban suke yi. A baya-bayan nan tsallakawar da wasu jiga-jigan jam’iyyun adawa suka yi zuwa jam’iyyar APC mai mulki ta jawo diga ayar tambaya a kan dalilansu da kuma makomar hamayya a zaben 2027. Hakan dai yana faruwa ne a daidai lokacin da wasu ’yan Najeriya suke kokawa da yadda...

Dalilan Da Suka Sa Zazzabin Cizon Sauro Ba Ya Jin Magani 25.04.2025

Send us Fan Mail Zazzabin cizon sauro, wato malaria, na cikin cututtuka mafiya shahara da kuma hadari a Najeriya. Wani rahoton Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ya nuna cewa Najeriya na da kaso mafi girma na mace-macen da cutar take haifarwa a duniya. Sau da yawa wanda ya kamu da cutar ta malaria kan sake kamuwa da ita bayan ya warke. Ko me ya sa magungunan zazzabin cizon sauro suka daina aiki a jiki...

Hanyoyin Amfani Da Kafafen Sada Zumunta Wajen Habbaka Kasuwanci 24.04.2025

Send us Fan Mail Tun zamanin kaka da kakanni ake gudanar da kananan sana’oi, wanda alumma ke dogaro dasu don biyan bukatun su na yau da kullum. Irin wadannan sana’oi sun hada da saka, jima, balangu, suyan kosai ko masa da dai sauran sana’oi da alumma keyi. A da can baya irin masu wadannan sana’a sun dogara ne da masu wucewa a bakin hanya don siyar da abun da suke sana’antawa ko kuma wadanda suka s...

Mene ne Matsayin Mataimakin Shugaban Ƙasa A Kundin Tsarin Mulkin Najeriya? 22.04.2025

Send us Fan Mail Ko kun san tanadin da Kundin Tsarin Mulkin Kasa ya yi game da Ofishin Mataimakin Shuaban Kasa da ayyukansa da alhakin da ya rataya a wuyansa? Kundin na Tsarin Mulkin Kasa ne dai kundin dokoki mafi karfi a Najeriya wanda ya kunshi tanade-tanade a kan dukkan al’amuran da suka shafi alhakin da ya rataya a wuyan shuggabanni da ma al’ummar kasa. Kuma kamar yadda ya tanadi yadda ake gud...

Me Ya Sa Matsalar Tsaro “Ta Gagari Gwamnati” A Najeriya? 21.04.2025

Send us Fan Mail A daidai lokacin da ake tunanin samun sauƙi daga ɗimbin matsalolin tsaro da na tada ƙayar baya a Najeriya, sai ga wasu matsalolin na ƙara Kunno Kai. Yayin da a wannan lokaci ake fuskantar kalubale iri-iri kama daga hare-haren da ake zargin na kungiyar Boko Haram ne a Arewa maso Gabas, zuwa ga sabbin kashe-kashe a wasu garuruwan jihohin Filato da Binuwai sai kuma ga wata sabuwar ƙu...

Sabbin Dabarun Hana Matasa Aikata Laifuffuka 18.04.2025

Send us Fan Mail Masu iya magana kan ce banza ba ta kai zomo kasuwa.  Mai yiwuwa hakan ne ya sa matasan da ake zargi da aikata manyan laifuffuka shiga ofishin ’yan sanda, su kuma fita ba tare da wani ya harare su ba, balle ya kama su. ’Yan sandan dai sun ce wannan wata dabara ce ta yakar aikata manyan laifuka irin su sata da fashi da makami da kwacen waya da fyade kai har ma da satar mutane don ku...

Ko Wadanne Dalilai Ne Ke Hana Mata A Arewa Koyon Ilimin Kimiyya? 17.04.2025

Send us Fan Mail Doctor Zainab Muhammad na daya daga cikin mata a Arewacin Najeriya da ta jajirce tare da kudirin cika burinta na karantar kimiyya duk da kalubalen da wasu matan dake yankin Arewa suke bayyanawa suna fuskanta wurin karantar fannin.  Doctor Zainab ba kimiyya kawai ta karanta ba, ta karanci daya daga cikin kimiyyoyin da ake ganin sun fi kowanne wahala wanda a mafi yawan lokuta ba mat...

Dalilan Rikice – Rikice A Jihar Filato 15.04.2025

Send us Fan Mail A yanzu haka, al’ummar jihar Filato na cikin fargaba da tashin hankali sakamakon jerin hare-haren da suka afku a wasu sassan jihar, inda daruruwan mutane suka rasa rayukansu, wasu kuma suka tsere daga muhallansu. Ko mene ne dalilin sake fitowar rikice-rikicen da suka dabaibaye yankin da ake ganin an fara samun zaman lafiya? Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari ne kan...

Dalilan "Farfaɗowar Boko Haram" A Jihar Borno 14.04.2025

Send us Fan Mail A yanzu haka al’ummar Borno na cikin zulumi sakamakon wasu hare-haren da ake zargin kungiyar Boko Haram ce ta kai a wasu sassan jihar.  Wadannan hare-hare dai suna faruwa ne bayan shekaru da dama da ikirarin Gwamnati na cewa an yi nasarar nakasa kungiyar. Ko mene ne dalilin sake farfadowar kungiyar ta Boko Haram a wannan lokaci? Wannan ne batun shirin Najeriya a Yau na wannan loka...

Yadda Faɗuwar Farashin Ɗanyen Mai Za Ta Shafi Rayuwar 'Yan Najeriya 11.04.2025

Send us Fan Mail A Najeriya ana tafka muhawara a kan yadda farashin danyen man fetur yake kara faduwa a kasuwannin duniya.  Wannan lamari dai ya haddasa damuwa a zukatan wasu ’yan Najeriya, kama daga masana tattalin arziki zuwa ga jami’an gwamnati, kasancewar danyen mai ne mafi muhimmanci a cikin hanyoyin samun kudin shiga. Sai dai tambayar da wasu ’yan kasa suke yi ita ce: shin yaya wannan faduwa...

Tasirin Da Dangantakar Yan Uwa Yake Ga Rayuwar Alumma 10.04.2025

Send us Fan Mail Irin dangantakar dake kasancewa tsakanin abokai na da matukar tasiri ga farin cikin wadannan abokai, ta yadda a wasu lokutan ma baka iya banbancewa tsakanin ‘yan uwan su na jini da kuma abokai. Irin wannan dangantaka ya kamata ne ace ana samun shi a wurin wadanda suke uwa daya uba daya ko kuma wadanda suke uba daya. Sai dai a yayin da wasu ke samun kyakkyawan dangantaka tsakanin s...

Dabarun Samun Kuɗaɗe Ta Hanyar Amfani Da Wayar Hannu 08.04.2025

Send us Fan Mail A zamanin yau, ba kira da tura saƙo kawai ake yi da wayar hannu ba; baya ga haka, muhimmiyar hanya ce ta samun kuɗi da bunƙasa sana’o’i. Ko kun san dabarun amfani da wayoyinku don samun kuɗaɗen shiga?  Idan ba ku sani ba, ko kuma kuna buƙatar ƙarin sani, ku biyo mu a shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci.

Mene Ne Tasirin NYSC Bayan Shekaru 50 Da Kafa Shi? 07.04.2025

Send us Fan Mail Shirin bautar ƙasa wanda aka kafa tun a shekarar 1973, an kirkire shi da nufin haɗa kan matasa daga kowane lungu da saƙo na ƙasar nan, domin fahimtar juna da kawar da wariyar yanki da kabilanci. Amma a yau, bayan shekaru fiye da arba'in da biyar da fara wannan shiri, jama’a da dama na tambaya:  ko har yanzu shirin na da tasirin da aka kirkire shi domin shi? Ko har yanzu bauta...

Dalilan Kamuwa Da Cutar Hawan Jini Da Hanyoyin Magance Ta 04.04.2025

Send us Fan Mail Cututtuka da dama suna Kamari a Najeriya wanda a mafi yawancin lokuta ma wadanda ke dauke da irin wadannan cututtukan basu da masaniyar suna dauke da su. Kamar yadda majalisar dinkin duniya ta bayyana, zaman lafiya, rashin matsalar kwakwalwa, da samun wadata na daga cikin abubuwan dake tabbatar da lafiyar bil’adama. Wata cuta da ta addabi da yawa daga cikin al’umma itace cutar Haw...

Listen to the Najeriya a Yau podcast in Replaio

Radio and podcasts in one app - free, with no sign-up. Install today and do not miss the launch

Get it on Google Play

Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.