Najeriya a Yau

News HA ↓ 958 episodes

Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.

Category

News

Podcast website

www.buzzsprout.com

Latest episode

Jun 23, 2026

Where to listen?

Podcasts in the app Replaio Radio Coming soon

Podcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts

Get it on Google Play Install for free Android 5M+ downloads · 4.8 rating iOS soon

Episodes

Halin Da Alummar Mokwa Ke Ciki Wata Guda Bayan Ambaliya 01.07.2025

Send us Fan Mail Tun bayan da ambaliyan ruwa ya ci wasu sassan garin Mokwa ne dai alummar garin suka fada halin neman taimako. A yayin da gwamnatin tarayya da ma wasu daidakun mutane suka taimaka ma wadanda abun ya shafa da kudi da ma wasu kayayyakin masarufi, wasu daga cikin alummar sun bayyana rashin jin dadin su ga yadda alamura ke gudana a garin Mokwa. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci za...

Yadda Za A Kawo Karshen Daukar Doka A Hannu A Najeriya 30.06.2025

Send us Fan Mail Kisa ta hanyar daukar doka a hannu na kara ta’azzara da saka damuwa a zukatan ‘yan Najeriya. Yayin da wasu ke ganin daukar doka a hannu daidai ne, wasu kuwa na ganin hakan zai cigaba da haifar da rashin doka da oda a kasa. Shin ko me doka ta ce a kan daukar doka a hannu da wasu ‘yan Najeriya su’ke yi? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan hanyoyin da za a bi...

Ko Wadanne Dalilai Ne Ke Hana Mata A Arewa Koyon Ilimin Kimiyya? 27.06.2025

Send us Fan Mail Doctor Zainab Muhammad na daya daga cikin mata a Arewacin Najeriya da ta jajirce tare da kudirin cika burinta na karantar kimiyya duk da kalubalen da wasu matan dake yankin Arewa suke bayyanawa suna fuskanta wurin karantar fannin.  Doctor Zainab ba kimiyya kawai ta karanta ba, ta karanci daya daga cikin kimiyyoyin da ake ganin sun fi kowanne wahala wanda a mafi yawan lokuta ba mat...

Yadda 'Yan Najeriya Za Su Kula Da Lafiyar Jikin Su 26.06.2025

Send us Fan Mail Kula da lafiya na nufin yin abubuwa da ke kare mutum daga kamuwa da cututtuka da kuma tabbatar da cewa jiki na aiki yadda ya kamata.     Wannan ya haɗa da cin abinci mai gina jiki, motsa jiki akai-akai, da dai sauran su.   Sai dai a wannan zamani ‘yan Najeriya ba kasafai suke kula da lafiyar jikin su ba, a mafi yawan lokuta ma sai ciwo ya kwantar da mutum sannan yake tunawa da lik...

Ko Najeriya Na Da Kudin Renon Sabbin Jihohi? 25.06.2025

Send us Fan Mail Da za a kirkiri sabuwar jiha a Najeriya a yanzu, to da dole a samar da karin gwamna daya da sabuwar majalisar dokoki, da sababbin ma’aikatun gwamnati, da sauransu. Samar da wadannan kuwa abu ne da yake bukatar makudan kudi – akalla Naira biliyan 30 duk shekara. Ko da jihar za ta iya sama wa kanta kudin shiga kuma, za ta bukaci tallafi daga Gwamnatin Tarayya kafin ta tsaya da kafaf...

Dabarun Samun Kuɗaɗe Ta Hanyar Amfani Da Wayar Hannu 24.06.2025

Send us Fan Mail A zamanin yau, ba kira da tura saƙo kawai ake yi da wayar hannu ba; baya ga haka, muhimmiyar hanya ce ta samun kuɗi da bunƙasa sana’o’i.  Ko kun san dabarun amfani da wayoyinku don samun kuɗaɗen shiga?   Idan ba ku sani ba, ko kuma kuna buƙatar ƙarin sani, ku biyo mu a shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci.

Matakan Dakile Kisan Matafiya A Hanyoyin Kasar Nan 23.06.2025

Send us Fan Mail Matsalar tare fasinjoji da kashe su a hanyoyin Najeriya na kara tsananta, musamman a yankunan Arewa.  Misali, a shekarun baya an sha tare matafiya tare da kashe wasu daga cikin su a hanyar Abuja zuwa Kano, a kwanakin baya ma an kashe wasu matafiya a garin Uromi dake jihar Edo a hanyar su ta komawa gida, sai na kwanan nan da ya faru a jihar Filato inda aka kashe wasu matafiya dake...

Yadda Tsarin Ilimi Ke Karya Gwiwar ’Yan Najeriya 20.06.2025

Send us Fan Mail ’Yan Najeriya da dama ne dai da suka yi ilimin zamani dole ta sa suka rungumi sana’o’in da a baya ake ganin na kaskantattu ne don su samu na sakawa a bakin salati.  Mai yiwuwa hakan ne ya sa wasu, musamman matasa, suka yanke kauna da cewa shafe lokaci ana karatun kan iya taimaka wa mutum magance bukatunsa nay au da kullum.  Wannan shi ne batun da shirin Najeriya a Yau na wannan lo...

''Yadda Cutar Amosanin Jini Ta Hana Ni Cimma Buri Na'' 19.06.2025

Send us Fan Mail Cutar amosanin jini wacce aka fi sani da cutar sikila na cigaba da barazana ga rayukan masu dauke da ita. Wannan cuta na saka masu ita da ‘yan uwan su cikin halin ha’ula’i, a wasu lokutan ma tana haifar da rasa rayukan wasu dake dauke da ita. Rahotannin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) sun nuna cewa, kusan yara 300,000 ne ake haifa da cutar Sikila a duk shekara a fadin duniya, inda...

Yadda Cin Ganyayyaki Ke Yi Wa 'Yan Najeriya Wahala 17.06.2025

Send us Fan Mail Karancin kayan ganyayyaki na cigaba da barazana ga lafiyar ‘yan Najeriya. Masana sun bayyana cewa akwai gibi mai girma na rashin kayan ganyayyaki da ya kamata cike. Sai dai hakan na fuskantar tasgaro sakamakon wasu dalilai. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan wannan matsala da zummar nemo hanyoyin magance ta.

Dalilan Durƙushewar Sababbin Sana'o'i Tun Ba A Je Ko'ina Ba 16.06.2025

Send us Fan Mail Sabbin masu sana’oi na tafka kurarai da suka hada da rashin kyakkyawar tsari, karancin jari, rashin shawarwarin kwararru da wasu kalubalen na daban. Sai dai masana suna ganin idan sabbin masu sana’oi za su yi amfani da shawarwarin da suke badawa zai taimaka wajen dorewar sabbin sana’oin su. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan irin wadannan kura-kurai da kum...

Rashin Aikin Yi Da Hanyoyin Magance Su A Najeriya 13.06.2025

Send us Fan Mail Rashin aikin yi na daya daga cikin manyan kalubalen da najeriya ke fuskanta a wannan lokaci, musamman la’akari da yanda ake cigaba da samun matasa dake da karfi a jika amma babu aikin yi.    Hukumar kididdiga ta kasa ta fitar da bayanan dake baiyana cewa rashin aikin yi ya karu a najeriya da kaso 5.3 a farkon wannan shekarar, kazalika binciken ya baiyana cewa wadanda basu yi karat...

Hanyoyin Magance Matsalar Kwacen Waya 10.06.2025

Send us Fan Mail ’Yan Najeriya suna ci gaba da nuna damuwa da yadda rahotannin kwace-kwacen waya suke karuwa a sassan daban-daban na kasa. Daya daga cikin rahotanni na baya-bayan nan shi ne inda a birnin Kaduna aka bayar da rahoton cewa wani matashi ya daba wa wani babban soja wuka saboda jami’in ya ki ya mika wayarsa. Ko me mahukunta suke yi don hana aikata wannan laifi? Wannan shi ne batun da sh...

Hanyoyin Fara Sana’a Ba Tare Da Jari Ba 09.06.2025

Send us Fan Mail Fara sana’a na cikin manyan jerin kalubalen da ’ƴan Najeriya suke fuskanta sakamakon wasu dalilai wadanda suka hada da rashin ilimi, ko Rashin wanda zai ba su shawara ko kuma, uwa uba, rashin jari. Wasu bayanai da Hukumar Ƙididdiga Ta Kasa – NBS – ta fitar sun nuna cewa fiye da kashi 40 cikin 100 na matasan Najeriya suna sha’awar fara sana’a, amma sun kasa saboda rashin jari. Haka...

Abubuwan Da Suka Fara Bacewa Yayin Bukukuwan Sallah 06.06.2025

Send us Fan Mail Yau mutane na kallon bukukuwan Sallah da ido daban—yayin da wasu ke ganin ta zama lokaci na shakatawa nishadi kawai, wasu kuwa na cewa an bar al’adun da ke nuna kimar wannan babban lokaci na Musuluncin. Wadanda suka manyanta na ganin akwai abubuwa da dama da a yanzu matasa sukayi watsi da su wadanda kuma na da muhimmanci yayin bukukuwan sallah a da can baya wanda kuma suke ganin b...

Yadda Mayar Da Unguwa Mayanka Ke Shafar Lafiyar Al’umma 05.06.2025

Send us Fan Mail Wata dabi’a da ta zama ruwar dare ita ce yadda matasa suke yankawa suke kuma da fige kaji a unguwanni, musamman a lokutan shagulgulan sallah. A da can akwai kebabbun wurare da ake gudanar da irin wadannan abubuwa. Sai dai masana suna ganin hakan na tafe da illolin kiwon lafiya da ma gurbata muhalli. Wannan ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai yayin...

Hanyoyin Kauce Wa Barnar Ambaliyar Ruwa 03.06.2025

Send us Fan Mail Ambaliyar ruwa na ci gaba da raba dubban mutane tare da lalata dukiyoyi a fadin Najeriya.  Ko a makon da ya gabata, wasu al’ummomi a Karamar Hukumar Mokwa dake Jihar Neja sun fuskanci irin wannan ambaliya da ta yi sanadiyyar rasa rayuka da dukiyoyi masu yawa. Ko wadanne hanyoyi za a bi don kauce wa barnar ambaliya a Najeriya? Wannan ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan loka...

Mokwa: Tsakanin Taraddadin Rashin Matsuguni Da Jimamin Rashin ’Yan-Uwa 02.06.2025

Send us Fan Mail Shin wanne ya fi zafi – takaicin rasa matsuguni ko alhinin Rashin sanin halin da dan uwa na jini yake ciki? Wannan ne halin da wasu al’ummomi a Karamar Hukumar Mokwa ta Jihar Neja suke ciki, bayan da suka tsinci kansu tsamo-tsamo a tsakiyar wata mummunar ambaliyar ruwa. Wasu mutanen da dama dai sun yi batan dabo a wannan ibitila’i, wanda ya yi sanadiyyar rayukan mutanen da adadins...

Yaya Girman Matsalar Rashin Tsaro A Shekaru Biyun Tinubu? 30.05.2025

Send us Fan Mail Rashin tsaro na cikin matsalolin da suke ci gaba da ci wa ’yan Najeriya da dama tuwo a kwarya, har a wannan lokaci da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu yake cika shekara biyu a kan mulki. Wasu rahotanni da wasu kungiyoyi masu zaman kansu suka fitar dai sun koka da yadda suke ganin matsalar ta kara kamari a wadannan shekarun. Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi duba ne a ka...

Sai Yaushe ’Yan Najeriya Za Su Ci Gajiyar Manufofin Shugaba Tinubu? 29.05.2025

Send us Fan Mail A yau shekara biyu ke nan cif  tun bayan da  shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karɓi mulkin Najeriya a matsayin shugaban ƙasa na 16 tun bayan samun ‘yancin kai.  Daya daga cikin abubuwan da shugaban kasar ya fara yi yayin jawabin karbar mulkin shi ne sanar da kawar da tallafin man fetur. Yayin da yake cika shekaru biyu, ana ci gaba da muhawara mai zafi game da irin nasarorin da aka sam...

Matsalolin Da Suke Tarnaki Ga Kananan Yara A Najeriya Da Hanyoyin Magance Su 27.05.2025

Send us Fan Mail Najeriya tana cikin ƙasashen da suka fi yawan yara a duniya, a cewar Hukumar Kula da Kananan Yara ta Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF). Sai dai a cewar Hukumar ta UNICEF, kusan rabin wadannan yara suna fuskantar kalubale, kama daga cin zarafi zuwa rashin samun kulawa da dai sauran su. Wadannan matsaloli da yara suke fuskanta dai sun dade suna ci wa masu ruwa da tsaki tuwo a kwarya....

Tasirin Dangantaka Tsakanin Bangaren Zartarwa Da Na Majalisa A Kan Talaka 26.05.2025

Send us Fan Mail A tsarin mulkin dimokuraɗiyya, dangantaka tsakanin bangaren zartarwa da majalisun dokoki tana taka muhimmiyar rawa wajen gudanar da shugabanci a tsakanin al’umma. A galibin kasashe masu bin tsarin na dimokuraɗiyya, ’yan majalisa kan kasance masu wakiltar al’umma da kare muradunta, da sa ido da kuma bayar da shawarwarin da suka dace ga bangaren zartarwa domin ci gaban kasa. Sai dai...

Dalilin ’Yan Adawar Najeriya Na Kulla Kawance A Karkashin Inuwar ADC 23.05.2025

Send us Fan Mail Mene ne ya sa jiga-jigan ’yan siyasar Najeriya bangaren adawa suka zabi inuwar jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) don hada hannu da nufin kawar da Shugaban Kasa Bola Tinubu da APC dagga mulki? Da daren Talata ne dai jigogin adawar, wadanda suka hada da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar, da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir Ahmed El-Rufai da kuma dan tak...

Illar Sare Itatuwa Ga Canjin Yanayi Da Lafiyar Mu 22.05.2025

Send us Fan Mail Shekaru da dama kenan da hukumomin duniya ke gudanar da tarurruka da dama kan zakulo hanyoyin da za a kawo karshen dumamar yanayi a duniya.  Dumama ko canjin yanayi na cigaba da barazana ga duniya, inda ake samun sauye sauye ga yanayi da wasu abubuwa da masana ke bayyana ka iya kara ta’azzara in ba’ayi wani abu a kai ba.  Daya daga cikin abubuwan da masana suka bayyana dake kawo w...

Yadda 'Yan Najeriya Za Su Kula Da Lafiyar Jikin Su 20.05.2025

Send us Fan Mail Kula da lafiya na nufin yin abubuwa da ke kare mutum daga kamuwa da cututtuka da kuma tabbatar da cewa jiki na aiki yadda ya kamata.  Wannan ya haɗa da cin abinci mai gina jiki, motsa jiki akai-akai, da dai sauran su.  Sai dai a wannan zamani ‘yan Najeriya ba kasafai suke kula da lafiyar jikin su ba, a mafi yawan lokuta ma sai ciwo ya kwantar da mutum sannan yake tunawa da likita....

Listen to the Najeriya a Yau podcast in Replaio

Radio and podcasts in one app - free, with no sign-up. Install today and do not miss the launch

Get it on Google Play

Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.