Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Where to listen?
Podcasts in the app Replaio Radio Coming soonPodcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts
Episodes
Halin Kunci Da ‘Yan Fansho Ke Ciki A Wasu Sassan Najeriya 15.08.2025 20:29
Send us Fan Mail A wasu jihohin Arewacin Najeriya, masu karɓar fansho suna cikin mawuyacin hali sakamakon ƙarancin kuɗin da suke samu duk wata. Wasu daga cikinsu sun bayyana yadda suke karbar naira dubu 5 a kowane wata a matsayin kudin fansho bayan kwashe shekaru suna aiki. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan irin halin da ‘yan fansho ke ciki a wasu jihohin Arewacin Najeri...
Dalilan Karuwar Mace-Mace A Hanyoyin Najeriya 14.08.2025 25:50
Send us Fan Mail Duk da kara wayar da direbobi da fasinjoji da hukumar kiyaye hadura ta tace tana yi, ana kara samun hauhawar wadanda ke rasa rayukansu sakamakon haddura a titin kasar nan. A shafinta na internet, hukumar kiyaye haddura ta kasa tace a watanni uku na farko na shekarar 2024, mutane 1,471 ne suka rasa rayukansu sakamakon hatsarin mota, kazalika, a watanni uku na farko na wannan shekar...
Yadda Matasa Ke Bada Gudunmawar Cigaban Al’ummarsu 12.08.2025 24:21
Send us Fan Mail Samun matasan dake bada gudunmawa a alummomin da suke rayuwa a cikin ta yana da matukar wuya a wannan zamani. Amma duk da haka, wasu matasa sun sadaukar da rayuwarsu wajen bada gudunmawarsu wajen cigaban alummarsu. Shirin Najeirya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan irin gudunmawar da matasa ke badawa wajen cigaban alummarsu
Yadda Damina Ke Shafar Masu Kananan Sana’o'i 11.08.2025 25:39
Send us Fan Mail Damina lokaci ne da dan'Adam yake matukar bukata - da za ta yi jinkiri, sai a ga hankalin kowa ya tashi. A lokaci guda kuma yadda damina kan hana wasu harkoki gudana kan jefa wasu mutane cikin wani irin yanayi.. Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan yadda damina kan shafi rayuwar kananan 'yan kasuwa da masu kananan sana’oi.
Shekara Nawa Shugabanni Ke Bukata Don Cika Alkawarin Da Suka Dauka? 08.08.2025 27:00
Send us Fan Mail Duk bayan shekaru hudu, Najeriya na kara yin zabe kuma ko wanne lokaci 'yan takara kan dauki alkawurika. Ko shekaru nawa wadanda ake zabe ke bukata don cika alkawuran da suka dauka? wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.
Mummunan Tasirin Rashin Bambance Zazzabin Lassa Kan Lafiyar Al’umma 07.08.2025 28:12
Send us Fan Mail A cewar masana harkar kiwon lafiya, rashin tantancewa balle a bayar da kulawar da ta dace a kan lokaci na cikin dalilan ta’azzarar barazanar da Zazzabin Lassa ke yi ga bangarori da dama na rayuwar al’ummar Najeriya, musamman a yankunan karkara. Wani bincike a kan tasirin Zazzabin Lassa a kan rayuwar ‘’yan Najeriya wanda aka wallafa bara a mujallar Springer ya nuna gudunmawar da ja...
Yadda Ayyuka Suka Ragu A Jihohi Bayan Kudin Shiga Ya Karu 05.08.2025 24:38
Send us Fan Mail Duk da karin kudin da gwamnatoci a matakin jiha suke samu daga asusun tarayya, ’yan Najeriya da dama suna korafin ba sa gani a kas. Manazarta dai sun ce ko kafin karin ma ya kamata ya yi a ce ayyukan da gwamnatcin jihohi suke yi sun fi da ake gani Ko mene ne ya sa jihohi “ba sa kashe karin kudaden da suke samu yadda ya kamata”? Wannan shi ne batun da shirin Najeriya a Yau na wann...
Yadda Talauci Ke Hana Shayar Da Yara Nonon Uwa Zalla A Najeriya 04.08.2025 25:32
Send us Fan Mail Ga alama kwalliya ba ta biyan kudin sabulu a fafautukar da ake yi ta ganin iyaye mata sun shayar da jariransu nono Zalla a wata shida na farko. Rahotanni sun ce duk da dadewar da aka yi ana wayar da kai har yanzu matan da suke shayar da yara nono uwa Zalla ba su haura kashi 29 cikin dari ba. Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan dalilan da suke hana mata shay...
Me Dokar Kasa Ta Ce Kan Karin Wa’adin Aiki Da Shugaban Kasa Keyi? 01.08.2025 22:59
Send us Fan Mail Bayan Karin wa’adin aiki da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yayi ga kwanturola janar na hukumar hana fasa kwauri ta kasa Bashir Adewale Adeniyi ne dai lamarin ke ta shan suka daga mutane daban-daban. Yayin da wasu ke ganin abinda shugaban kasan yayi daidai ne, wasu kuwa na ganin hakan yayi hannun riga ga tanade-tanaden kundin tsarin mulkin kasa. Ko me dokar kasa tace game da wanna...
Tinubu Ya Yi Adalci Ga Ayyuka Da Mukamai Tsakanin Kudu Da Arewa—Bayo Onanuga 31.07.2025 27:48
Send us Fan Mail Kungiyar tuntuba ta Arewa ta zargi shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da kin yin daidaito wurin ayyuka da raba mukamai tsakanin Arewa da Kudancin Kasar nan. Wadannan zarge-zarge suka sa fadar Shugaban Kasa ta hannun mai taimaka masa na musamman kan kafofin yada labarai Bayo Onanuga maida martani ga Kungiyar ACF. Ko wadanne irin martani fadar shugaban kasar ta mayar ga kungiyar Tuntub...
Yadda Za A Dama Da Matan Arewa A Fannin Kimiyya 29.07.2025 30:00
Send us Fan Mail Mata a Arewacin Najeriya na fuskantar kalubale da dama a fannin karantar kimiyya Akwai darussan da a mafi yawan lokuta ba mata kadai ba, har da mazan na kaurace musu. Shirin Najeriya a Yau ya yi nazari ne kan dalilan da suka sa matan Arewacin Najeriya ke tsoron karantar ilimin kimiyya.
Matakan Karfafa Gwiwar 'Yan Najeriya Kan Zabe—INEC 28.07.2025 19:46
Send us Fan Mail ‘Yan Najeriya da dama ne dai aka bayyana basa fitowa kada kuri’a a duk lokacin da zabe ya zagayo. Wasu daga cikin ‘yan Najeriya sun bayyana dalilan su da suka hada da rashin jin dadin abun da hukumar zabe keyi, rashin yadda da sakamakon zabannin da suka gabata da dai sauran su a matsayin dalilan su. Ko wadanne matakai hukumar zabe INEC take dauka don karfafawa ‘yan Najeriya gwiwan...
Cutukan Da Rumar Daki Ke Haifarwa Ga Jikin Mutum 24.07.2025 22:14
Send us Fan Mail Malaman kiwon lafiya sun bayyana yadda ruma ke yada matsalolin rashin lafiya ga lafiyar jikin mutum. Musamman a lokuta irin na ruwa, ruma kan dabaibaye gidajen mutane da dama na tsawon lokaci wanda ka iya jawo matsaloli daban daban ga lafiya da kuma gidajen mu. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan irin matsalolin da ruma ke haifarwa ga lafiyar jikin mu.
Yadda Farashin Taki Ke Hana Noman Masara Da Shinkafa 22.07.2025 25:57
Send us Fan Mail Tashin farashin takin zamani yana hana manoma da dama noman wasu nau’ukan abinci. Manoma da dama dai suna kauracewa shukan masara da shinkafa da aka fi amfani da su a Najeriya sakamakon tsadar takin zamani, inda masana suke ganin in ba’a dauki mataki ba hakan zai kawo karancin abinci a Najeriya. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan dalilan da suka sa farashi...
Abin da ya sa muke yi wa PDP zagon ƙasa — Sule Lamiɗo 21.07.2025 26:40
Send us Fan Mail Zagon kasa da wasu ‘ya’yan PDP ke yi mata na kara ta’azzara, inda wasu ke zama a cikin ta amma suke wa jam’iyyun adawa aiki. Ko a kwanan nan, an hangi wasu daga cikin ‘ya’yan jam’iyyar a taron hadakar ADC, wadda hakan ke jaddada har yanzu PDP ta kasa kawo karshen wannan matsala. Ko me yasa ‘ya’yan PDP ke yiwa jam’iyyun adawa aiki? Wannan ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan...
Shin Ya Kamata A Samar Da Dokokin Da Za Su Sa Ido Kan Amfani Da AI? 18.07.2025 22:58
Send us Fan Mail Tun bayan bayyanar kirkirarrriyar basira wato AI ne dai wasu mutane suke amfani da ita ta hanyar da da bai kamata ba. Wasu sukan yi amfani da ita wajen saka hoto ko kirkirar faifan bidiyo wanda zai nuna wani yana yin abun da bai kamata ba. Hakan dai ya sa wasu suna ganin ya kamata a samar da dokokin da za su rinka lura da yadda ake amfani da kirkirarriyar basirar. Shirin Najeriya...
Dalilan Da Suka Sa 'Yan Najeriya Ba Sa Samun Adalci 17.07.2025 19:54
Send us Fan Mail Rashin samun adalci a Najeriya ba ya rasa nasaba da cin hanci da rashawa a bangaren shari’a, inda ake zargin wasu jami’ai suna karɓar kuɗi kafin su yanke hukunci, kamar yadda manazarta suka bayyana. Ko mece ce gaskiyar wannan lamari? Wannan ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.
Wa Zai Gaji Buhari A Fagen Siyasar Najeriya? 15.07.2025 24:14
Send us Fan Mail Gaskiya da rikon amana suna cikin dalilan da suka sa tsoon Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi fice a siyasar Arewacin Najeriay. Wasu masana da ma makusantar tsohon Shugaban kasar dai suna ganin Arewa ta yi rashi kuma zai yi wuya a samu makwafansa. Yayin da ake binne marigayin, hankalin wasu 'yan Najeriya ya fara komawa ga yiwuwar samun wanda zai iya maye gurbinsa a fagen...
Abin Koyi Daga Rayuwar Marigayi Muhammadu Buhari-- Makusantansa 14.07.2025 24:40
Send us Fan Mail Rasuwar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ta sa 'yan Najeriya da dama kaduwa duk da cewa ya jima yana fama da rashin lafiya. Sanar da rasuwar ke da wuya, 'yan kasa suka fara bayyana ra'ayoyi daban daban akan abin da suka gani game da rayuwar tsohon shugaban. Amma makusantansa sun bayyana wasu halaye game da shi wadanda ba kowa ne ya sani ba. Sune kuma shirin Naj...
Dalilan Da Wasu Matasa Ba Sa Aiki Tukuru Wajen Neman Arziki 11.07.2025 24:47
Send us Fan Mail Matasan Najeriya da dama suna son yin arziki amma ba tare da sun sha wahala ba. Sau da yawa matasa sun fi neman hanya mafi sauki da za ta basu arziki ba tare da sun sha wahala ba. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan dalilan da suka sa wasu matasa bin yanke don tara abin duniya.
Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Sa Cin Kifi Yadda Ya Kamata 10.07.2025 27:52
Send us Fan Mail Duk da amfanin kifi ga lafiyar jikin mutum da kuma samar da kudin shiga masana sun ce ba a amfani da shi yadda ya kamata a Najeriya. Baya ga bai wa jiki lafiya, kifi ka iya samar da kudaden shiga ga daidaikun ’yan Najeriya da ma kasar gaba daya. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan dalilan da suka sa ’yan Najeriya basa samun cin kifi kamar yadda ya kamata.
Sarkakiyar Dake Gaban Hadakar ADC -- Atiku Ko Peter Obi? 08.07.2025 26:30
Send us Fan Mail 'Yan Najeriya suna ci gaba da tafka muhawara a kan wanda jamiyyar hadaka ta ADC zata tsayar takarar Shugaban Kasa a zaben 2027. Yayin da wasu suke ganin Atiku Abubakar yana da dimbin magoya baya, wasu kuwa gani suke yi shi ma Peter Obi ba kanwar lasa bane. Ko me zai faru idan daya daga cikin su ya samu tikitin tsayawa takara a 2027? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai...
Mene Ne Tasirin Nadin Mataimaka Na Musamman A Rayuwar Jama’a? 07.07.2025 25:37
Send us Fan Mail Wadanda aka zaba su rike mukaman gwamnati kan nada wasu mukarrabai don su taya su sauke nauyin da aka dora musu. Wasu na zargin nadin baya rasa nasaba da sakayya ga irin rawar ga wadanda aka nada saboda rawar da suka taka yayin yakin neman zabe. Ko irin wadannan nade-nade na da wani tasiri ga rayuwar alumma? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan nade-naden ma...
Shin Ko Hadakar Sabuwar Jamiyyar ADC Za Ta Fidda Wa ‘Yan Najeriya Kitse Daga Wuta? 04.07.2025 27:27
Send us Fan Mail Yan Najeriya da dama na ta bayyana mabanbantan ra’ayoyi kan sabon hadakar ‘yan siyasa zuwa sabuwar jami’yyar ADC. A yayin da wasu ke ganin wannan hadaka za ta cire musu kitse daga wuta, wasu kuwa gani suke yi duk kanwar ja ce. A ranar laraban nan ne dai gaggan ‘yan siyasa daga jamiyyu daban daban suka hadu don dinkewa wuri daya da niyyar kalubalantar jamiyya mai mulki ta APC, a ce...
Boyayyun Kalubalen Da Sabuwar Hadakar ADC Za Ta Iya Fuskanta 03.07.2025 28:10
Send us Fan Mail Tun kafin sanar da sabuwar kawance da suka hada da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da Peter Obi da Nasir El’rufai da wasu manyan ‘yan siyasa ne aka fara zargin yiwa wannan hadaka zagon kasa da kawo cikas ga tafiyar wannan hadaka. Daya daga cikin irin wadannan zagon kasa da ake zargin wasu da yiwa wannan sabuwar hadaka itace na sanar dasu rashin samun dakin taron da...
Similar podcasts
Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.