Najeriya a Yau

News HA ↓ 958 episodes

Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.

Category

News

Podcast website

www.buzzsprout.com

Latest episode

Jun 23, 2026

Where to listen?

Podcasts in the app Replaio Radio Coming soon

Podcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts

Get it on Google Play Install for free Android 5M+ downloads · 4.8 rating iOS soon

Episodes

‘Halin Kunci Ya Sa Muke Zama A Baca A Abuja’ 06.10.2025

Send us Fan Mail Halin matsin tattalin arziki ya tilasta da yawa daga cikin mutane zama a bacoci a garin Abuja da wasu biranen Najeriya. Mutane a birane kamar Abuja da Legas Da Fatakwal na cikin halin matsi sakamakon rashin ingattaccen muhalli. Ko wannen irin rayuwa irin wadannan mutanen ke yi? Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai a yau da ake bikin rana...

Yadda Fasahar AI Ke Barazana Ga Sana’ar Masu Shagunan Daukar Hoto 03.10.2025

Send us Fan Mail A zamanin yau na fasahar zamani, musamman fasahar kirkirarriyar basir ta (AI) , harkokin sana’o’i da dama suna fuskantar sauye-sauye masu girma. Daya daga cikin sana’o’in da ke cikin babban hadari shi ne sana’ar ɗaukar hoto musamman irin wadanda ke kashe makudan kudi wajen sayen kyamara da bude katafaren gidajen daukar hoto. A da, mutane kan je shagon daukar hoto domin samun hoto...

Hanyoyin Da Dangote, PENGASSAN Ba Su Bi Ba Don Magance Takaddamarsu 29.09.2025

Send us Fan Mail Gwamnatin Tarayya ta gayyaci Kungiyar Manyan Ma’aikatan Man Fetur da Iskar Gas ta Najeriya (PENGASSAN) da Matatar Dangote don a sasanta a yau. Hakan ya biyo bayan umarnin da ’yan kwadagon suka bai wa mambobinsu ne na shiga yajin aiki bayan da Matatar Dangote ta salami ma’aikata fiye da 800. Sai dai wasu masana suna ganin tun farko bai kamata lamarin ya kai ga haka ba da an bi wasu...

Hanyoyin Magance Gubar Cikin Abinci 26.09.2025

Send us Fan Mail Cin guba ta hanyar abinci (food poisoning) wata cuta ce da ke faruwa idan mutum ya ci abinci ko ya sha abin sha da ya gurɓace. Gurɓacewar abincin na iya fitowa daga ƙwayoyin cuta kamar Salmonella, E. coli, ko Listeria, ko kuma daga ƙwayoyin cutar virus, ƙwari (parasites), ko sinadarai masu guba. Alamomin cutar sun haɗa da ciwon ciki, amai, zazzabi, gudawa, da rashin jin daɗin jiki...

Dalilan Da Suke Sa Dalibai Cin NECO Fiye da WAEC 25.09.2025

Send us Fan Mail Yayin da dalibaI da dama da suka rubuta jarrabawar kammala karatun sakandare suka fitar da zaton samun gurbi a makarantun gaba a bana bisa la’akari da sakamakon WAEC, sai ga sakamakon NECO ya taho musu da sabon albishiri. Yayin da sakamakon WAEC ya bar baya da kura, inda galibi suka kasa samun makin da ake bukata a mafi karancin adadin darussa, na NECO ya yi nuni da cewa galibi su...

Abin Da Doka Ya Ce Kan Kisan Jami’an ‘Yan Sanda 23.09.2025

Send us Fan Mail Kisan jami’an tsaro na cigaba da zama ruwan dare a Najeriya, lamarin da ya daɗe yana tayar da hankali, amma a ‘yan kwanakin nan abin ya ƙara muni. Misali, kwanan nan a an kashe wasu jami’an ‘yan sanda a kananan hukumomin Katsina-Ala da Ukum a jihar Benue , inda ‘yan bindiga suka kai hari tare da kashe ‘yan sanda uku inda suka kuma sace wasu bakwai.  Shirin Najeriya A Yau na wannan...

Yadda Wata Bakuwar Cuta Take Cin Naman Jikin Mutanen Malabu 22.09.2025

Send us Fan Mail Wata cuta mai cin naman jikin dan’Adam ta yi sandin mutuwar mutum takwas yayin da wasu fiye da 60 suke kwance a asibiti a garin Malabu dake Karamar Hukumar Fufure ta Jihar Adamawa. Wannan lamari dai ya jefa fargaba a zukatan mazauna yankin. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi bincike a kan yadda wannan cuta take yaduwa da matakan da ya kamata a dauka don kauce wa kamuwa...

Ayyukan Da Fasahar AI Za Ta Raba Mutane Da Su Nan Ba Da Jimawa Ba 22.09.2025

Send us Fan Mail Mutane da dama na nuna damuwa game da mmakomar ayyukansu tun bayan fitowar fasahar AI. Sai dai yayin da wasu manazarta suke ganin fasahar za ta raba mutane da ayyukansu, wasu kuwa gani suke yi wannan ba abu ne mai yiwuwa ba. Shirin Najeriya  A Yau na wanna lokaci zai yi nazari ne kan sayyukan da fasahar AI za ta iya raba mutane da su.

Wadanne Kalubale Gwamna Fubara Zai Fuskanta Bayan Dawowa Mulkin Ribas? 18.09.2025

Send us Fan Mail A yau ne Gwamna Siminalaye Fubara ke dawowa kujerarsa a matsayin gwamnan Jihar Ribas bayan dakatarwa da ayyana dokar ta baci na watanni shidda da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi a jihar. Manazarta dai na hasashen wannan dawowar zata bude wani sabon babi a siyasar jihar Ribas. Yayin da wasu ke ganin gwamna Fubara zai koma bakin aiki ne ya cigaba da gudanar da mulkin jihar kam...

Matsayin Doka Kan Hawa Mumbari Ba Tare Da Izinin Gwamnati Ba 16.09.2025

Send us Fan Mail Matakin hana malaman da ba su da rajista hawa mumbari a Neja yana ci gaba da yamutsa hazo a ciki da wajen jihar. Yayin da wasu suke ganin wannan mataki bai dace ba, wasu kuwa gani suke faduwa ta zo daidai da zama, wato matakin ya zo a daidai lokacin da ake bukata. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kan tanadin Dokar Kasa game da wannan batu.

Yadda Wasu Al'ummomi Suke Kare Kansu Daga Barnar Ambaliyar Ruwa 15.09.2025

Send us Fan Mail Ambaliyar ruwa na cigaba da salwantar da dukiyoyi da rayukan al’ummomi da dama a sassa daban-daban na Najeriya. Ko a farkon makon nan, hukumomi sun yi gargadin cewa akwai yiwuwar samun ambaliyar a jihohi akalla 11. Sai dai wasu alummomin tuni suka dauki matakai don rage barnar da ambaliyar ka iya yi musu. A kan wadannan matakai shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari.

Rayukan Da Aka Rasa Sakamakon Ambaliyan Wannan Shekarar 11.09.2025

Send us Fan Mail Duk shekara rayuka da dukiyoyi na kara salwanta sakamakon ambaliyar ruwa. Duk da jan kunne da hukumomi a matakai daban-daban keyi, rayukan mutane da dukiyoyi na kara salwanta. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan rayukan da suka salwanta a damunan wannan shekarar.

Tasirin Takaddamar NUPENG Da Dangote A Kan Tattalin Arzikin Najeriya 09.09.2025

Send us Fan Mail ’Yan Najeriya sun shiga taraddadin abin da ka iya biyo bayana kudurin Kungiyar Ma’aikatan Man Fetur da Iskar Gas ta Najeriya (NPENG) na tsunduma yajin aiki. Hakan dai ya biyo bayan tashi da aka yi daga zaman da Gwamnatin Tarayya ta kira don sasanta kungiyar, mai samun goyon bayan sauran kungiyoyin kwadago, da rukunin kamfanonin Dangote, ba tare da cimma wata matsaya ba. Ministan K...

Yadda Ilimi Ke Kara Tsada Yayin Komawar Yara Makaranta 08.09.2025

Send us Fan Mail Iyaye na ci gaba da kokawa kan yadda ilimi ke kara tsada yayin komawan yaransu makaranta a sabon zango. Makarantu na kara fidda sabbin hanyoyin karbar kudi daga hannun yara da sunan koyarwa. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan dalilan dake sa ilimi kara tsada yayin da yara ke komawa makaranta.

Yadda Ake Gudanar Da Bukukuwar Sallar Gani Yayin Mauludi 05.09.2025

Send us Fan Mail Yayin da ake gudanar da bukukuwar Mauludi a sassa daban daban a garuruwan kasar nan, wasu yankunan na da tasu bukukuwar ta daban. Ko yaya ake gudanar da bikin Sallar Gani? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan yadda ake gudanar da bikin sallar Gani.

Hanyoyin Da Mutane Zasu Bi Wajen Neman Diyya 02.09.2025

Send us Fan Mail Sau da dama ibti’lai kan faru da wasu mutane wanda ya kamata ace sun bi hanyoyi don a biya su diyya. Sai dai masana na bayyana cewa sau da dama mutane basu san honyoyin da ya kamata subi don neman hakkokin su ba. Shirin Najeriya  A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan hanyoyin da mutane zasu bi don neman diyya idan an zalunce su.

Me Sakamakon Zaben Ribas Ke Nunawa Game Da Sulhun Wike Da Fubara? 01.09.2025

Send us Fan Mail Yadda Gwamnan Jihar Ribas da aka dakatar, Siminalayi Fubara, da magoya bayansa suka kaurace wa zaben kananan hukumomin jihar, da yadda APC ta lashe kujeru 20 a cikin 23 sun haifar da muhawara a tsakanin ’yan Najeriya. Shin wannan sakamako alama ce ta yarjejeniyar sulhu da aka cimma a tsakanin Gwamna Fubara da Minsitan Abuja Nyesom Wike a Fadar SHugaban Kasa? Amsar wannan tambaya s...

“Abin Da Ya Sa Muka Dawo Daga Rakiyar Kirifto” 29.08.2025

Send us Fan Mail A ’yan watanni da suka gabata, matasa da yawa a Najeriya sun dukufa don ganin hakar su ta cimma ruwa wajen samun kudaden kirifto. Amma alamu na cewa a baya-bayan nan wasu daga cikinsu sun sare sun kuma saduda sun dawo daga rakiyar harkar. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan dalilan wasu matasan na yin watsi da harkar kirifto.

Matakan Da Ciwon Suga Ke Bi Kafin Yin Illa 28.08.2025

Send us Fan Mail Mutane da dama basa sanin suna dauke da ciwon suga ballantana su san hanyoyin magance ta kafin tayi tsanani. Sau da yawa ciwon sai ta kai wani matakin da zatayi wa mutum illa sannan yake sanin yana dauke da ita. Shirin Najeriya  A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan matakan da ciwon suga ke bi kafin tayi tsanani da kuma hanyoyin magance ta.

Ci Gaban Da Harshe Da Al’adun Hausa Suka Samu A Shekaru 10 26.08.2025

Send us Fan Mail Tun bayan fara bikin harshen Hausa ta duniya shekaru goma da suka gabata ne dai manazarta suke bayyana irin cigaba da habbakar da yaren ya samu. Harshen Hausa ya samu zama a mataki na 11 cikin harsunan da ake amfani dasu a fadin duniya tare da fatan nan bada jimawa ba zai dara hakan. Shirin Najeriya  A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan irin cigaba ko akasin haka da harshen...

Kalubalen Da Iyaye Ke Fuskanta Wajen Tarbiyyan 'Ya'yan Su 25.08.2025

Send us Fan Mail Duk wanda ya shekara arbain zuwa sama ya san irin tarbiyyan da ya samo daga wurin iyayen sa a da baya can, irin mu’amalan dake tsakanin sa da iyaye har ma da shakuwan dake tsakanin ‘ya’ya da iyaye.   A yanzu kuwa abubuwa sun canza daga yadda aka san su, inda abubuwa suka rincabe sukayi wa iyaye yawa. Daya daga cikin manyan sauyin da aka samu sun hada da aikin gwamnati ko aikin wat...

Ayyukan Da Fasahar AI Za Ta Raba Mutane Da Su Nan Ba Da Jimawa Ba 22.08.2025

Send us Fan Mail Mutane da dama na nuna damuwa game da mmakomar ayyukansu tun bayan fitowar fasahar AI. Sai dai yayin da wasu manazarta suke ganin fasahar za ta raba mutane da ayyukansu, wasu kuwa gani suke yi wannan ba abu ne mai yiwuwa ba. Shirin Najeriya  A Yau na wanna lokaci zai yi nazari ne kan sayyukan da fasahar AI za ta iya raba mutane da su.           

Halin Kunci Da Wadanda Hare-haren Ta'addanci Ya Rutsa Da Su Ke Ciki 21.08.2025

Send us Fan Mail A yau, ta’addanci ya zama babban kalubale ga tsaron rayuka da dukiyoyi, ya raba iyalai, ya tilasta dubban mutane barin gidajensu, ya hana yara zuwa makaranta, kuma ya durƙusar da tattalin arzikin yankuna da dama.  Baya ga haka, ta’addanci ya bar raunuka masu zurfi na damuwa da tsoro a zukatan waɗanda suka tsira, wanda sau da yawa ba sa samun kulawar kwararru. Shirin Najeriya A Yau...

Halin Da Muke Ciki Bayan Rasa ‘Yan Uwanmu A Hadarin Kwale-Kwale A Sakkwato 19.08.2025

Send us Fan Mail ‘Yan uwan wadanda suka rasa rayukansu a hatsarin jirgin ruwa da ya faru a garin Kojiyo dake karamar hukumar Goronyo a jihar sakkwato sun samu kansu cikin damuwa. Yayin da kalilan daga cikin wadanda abun ya rutsa dasu suka tsira da ransu, wasu da dama sun mutu, a gefe guda kuma an kasa gano inda sauran da abun ya rutsa dasu suke. Wannan lamari ya tayar da hankulan jama’a, musamman...

Dalilan Karyewar Farashin Hatsi A Kasuwanni 18.08.2025

Send us Fan Mail Manoma da dillalan hatsi suna ci gaba da nuna damuwa a kan yadda farashin kayan abinci yake kara karyewa a kasuwanni. Su kuwa wasu ‘yan Najeriya jin dadi suke yi saboda yadda farashin yake ta sauka. Ko wadanne dalilai ne suka sa farashin hatsin yake kara sauka a kasuwanni? Wannan shi ne batun da shiriin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai tattauna a kai.

Listen to the Najeriya a Yau podcast in Replaio

Radio and podcasts in one app - free, with no sign-up. Install today and do not miss the launch

Get it on Google Play

Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.