Najeriya a Yau

News HA ↓ 958 episodes

Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.

Category

News

Podcast website

www.buzzsprout.com

Latest episode

Jun 23, 2026

Where to listen?

Podcasts in the app Replaio Radio Coming soon

Podcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts

Get it on Google Play Install for free Android 5M+ downloads · 4.8 rating iOS soon

Episodes

Cigaban Da Hukumomin Raya Shiyyoyi Zasu Samar 18.02.2025

Send us Fan Mail A kwanakin baya ne dai shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kirkiri sabbin hukumomin shiyyoyin kasar nan da nufin kawo cigaba ga wadannan shiyyoyi. Gabanin kirkirar wadannan hukumomin, gwamnatin da ta gabata karkashin jagorancin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ce ta fara kirkirar hukumar raya yankin Neja Delta bayan wasu kalubale da suka dabaibaye yankin. Na baya bayan nan sh...

Dalilan Saukar Farashin Kayan Masarufi A Kaswanni 17.02.2025

Send us Fan Mail Bayanai daga sassa daban-daban na Najeriya suna nuni da cewa farashin kyayyakin masarufi na ta faduwa a kasuwanni. Kafin hakan dai farashin ya yi ta tashi, har ya kai ga duk abin da mutum ya saya a yau, idan ya koma kasuwa bayan kwana biyu zai ji an ce ya tashi. Ko wadanne dalilai ne suka sa farashin kayayyakin masarufi suke ta sauka a yanzu? Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci...

Tasirin Da Kyauta Ke Dashi A Soyayya 14.02.2025

Send us Fan Mail A duk lokacin da aka ce soyayya ta kullu a tsakanin mutane biyu, hakan na tafe da wasu hidimomin da soyayyar ke zuwa dasu. Cikin irin wadannan hidimomi akwai kyauta da masoya ke baiwa junan su. Wadannan kyaututtuka sun hada da turare, agogon hannu, sarka ko zobe da dai sauransu.

Kalubalen Dake Neman Durkushe Kafafen Rediyo A Arewa 13.02.2025

Send us Fan Mail Rediyo na daga cikin kafofin da alumma da dama suka dogara dasu don jin labarai, shirye shirye da kuma nishadi. Rediyo na taka muhimmiyar rawa wajen wayar wa da alumma dama kai musamman duba da yadda aka bada shaidar cewa tafi kowace kafar media saurin yada bayanai ba a cikin birane ba, har ma da yankunan karkara. Sai dai a wannan gaba ana ganin rediyo a Arewacin kasar nan na samu...

Ko Wadanne Dalilai Ne Ke Hana Mata A Arewa Koyon Ilimin Kimiyya? 11.02.2025

Send us Fan Mail Doctor Zainab Muhammad na daya daga cikin mata a Arewacin Najeriya da ta jajirce tare da kudirin cika burinta na karantar kimiyya duk da kalubalen da wasu matan dake yankin Arewa suke bayyanawa suna fuskanta wurin karantar fannin. Doctor Zainab ba kimiyya kawai ta karanta ba, ta karanci daya daga cikin kimiyyoyin da ake ganin sun fi kowanne wahala wanda a mafi yawan lokuta ba mata...

Har Yanzu Akwai Masu Rufin Asiri A Najeriya? 10.02.2025

Send us Fan Mail A tsakanin al’umma akan karkasa mutane gida-gida a bisa mizani na tattalin arziki, musamman a tsarin jari-hujja: akwai mawadata, akwai matalauta. A tsakanin al’umma akwai aji na mutane masu matsakaicin samu wanda ake kira “Middle Class”. Akan saka mutane a wannan aji ne galibi bisa la’akari da aiki ko sana’ar da suke yi, da kudin da suke samu, da matakin ilimin da suka kai, da ma...

Dalilin Faduwar Farashin Tumatur A Kasuwa 07.02.2025

Send us Fan Mail Shin mene ne dalilin faɗuwar farashin tumatir warwar a kasuwa?  Idan ba a manta ba, a watannin baya farashin Tumatur yayi tashin gwauron zabo wanda aka dade ba’a ga irin sa ba. A wancan lokacin, sai da farashin tumaturin ya kai ga iyalai da dama sun hakura dashi sun koma sayen na gwangwani ko na leda.  Wannan ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokacin zai yi nazari a kai.

Tasirin Yankan Angurya A Rayuwar Mata 06.02.2025

Send us Fan Mail A tsakanin Hausawa  akan yi wa jaririya wani nau’i na kaciyar mata, wanda ake kira yankan angurya, kwana bakwai da haihuwarta. Ko menene alfanu ko illar wannan al’ada ga ’ya’ya mata? Albarkacin Ranar Yaki da Kaciyar Mata ta Duniya, shirin Najeriya  A Yau zai yi nazari a kan wannan al’ada da tasirinta a rayuwar mata.

Hanyoyin Noma Ba Tare Da Kashe Kudi Da Yawa Ba 04.02.2025

Send us Fan Mail Mutanen dake da sha’awar shiga harkar noma kodai don sama wa kansu abin da za su ci ko kuma don samun kudaden shiga na fuskantar kalubale. Wannan kalubale ya hada da karancin ilimin noman, da na irin shuka, da rashin gonaki da dai sauran su. Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan wannan batu tare da samar da hanyoyin noma ba tare da kashe kudi masu yawa ba.

Dalilan Da Suka Sa Zamu Kashe Naira Biliyan Biyu Da Rabi Kan Auratayya A Kano 03.02.2025

Send us Fan Mail Tun bayan da jihar kano ta fitar da rahoton ware zunzurutun kudi har naira biliyan biyu da rabi don auratar da marasa aure a jihar ne dai batun ke ta shan suka daga bangarori daban daban a fadin Najeriya. Wasu na ganin jihar na da wasu bukatun da suka fi auratar da alumma muhimmanci da ya kamata ace gwamnatin ta mayar da hankali a kai. Shirin Najeriya A Yau na wannan rana yayi naz...

Anya Jam’iyyar PDP Za Ta Kai Labari A Fagen Siyasar Najeriya Kuwa? 31.01.2025

Send us Fan Mail Shin shure-shure PDP take yi da ba ya hana mutuwa, ko kuwa motsi ne na alamun samun lafiya? Wannan ce tambayar da wasu ’yan Najeriya suke yi game da fito-na-fito da shugabannin jam’iyyar suka jima suna yi da juna. Tuni wasu ma suka fara diga ayar tambaya a kan makomar jam’iyyar bisa la’akari da tarin rikice-rikicen da suka dabaibaye ta. Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai n...

Hakikanin Dalilan Takaddama Kan Kafa Kotunan Shari’ar Musulunci A Kudu 30.01.2025

Send us Fan Mail Ana ci gaba da zazzafar muhawara a shiyyar Kudu maso Yammacin Najeriya a kan batun samar da kotunan Shari’ar Musulunci. Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci a yankin ce dai ta buƙaci hakan. Sai dai wasu ƙungiyoyi da ma ɗaiɗakun mutane a yankin suna adawa da wannan buƙata. Wannan ne batun da shirin Najeriya a Yau na wannan lokacin zai yi nazari a kai.

Dabarun Noma Don Samun Kuɗaɗen Shiga 28.01.2025

Send us Fan Mail Akan ce “Noma tushen arziki”. Mutane da dama za su iya bayar da labarin da ke tabbatar da hakan; domin kuwa ko ba komai idan mutum ya samu abinci ya ci ya koshi babban arziki ne. Wasu ’yan Najeriya kan shuka kayan abinci a unguwannin su don sama wa kan su abincin da za su ci. Sai dai masana na ganin da wadannan mutane za su inganta wannan noma da sun sama wa kansu kudaden shiga. S...

Dabarun Bunƙasa Kasuwanci Ta Hanyar Intanet 27.01.2025

Send us Fan Mail Ci gaban zamani ya zo da sauye-sauye da dama a fannonin rayuwa daban-daban ciki har da kasuwanci. A yanzu hanyar sadarwa ta zamani, ko intanet, tana taka muhimmiyar rawa wajen tallata haja ko saye da sayarwa da banarori da dama.  Tuni ’yan Najeriya da dama suka yi balaguro suka koma intanet da kasuwancinsu. Shrin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan kalubale da k...

Matakan Samun Abinci A Kan Farashi Mai Rahusa A Najeriya 24.01.2025

Send us Fan Mail Wadatar da al’umma da abinci abu ne mai matukar muhimmanci ga duk ƙasar dake son zama lafiya cigaba. Sai dai a Najeriya cimma wannan buri na cin karo da ƙalubale, kama daga sauyin yanayi zuwa ambaliyar ruwa, daga rashin tsaro zuwa karancin zuba jari a bangaren noma. Rahotanni sun nuna cewa adadin abincin da aka samar bai kai yadda ya kamata a ce an samu ba ta dalilin wadannan mats...

Yadda Kuɗin Crypto Zai Haɓɓaka Tattalin Arzikin Najeriya 23.01.2025

Send us Fan Mail Kudaden crypto na cikin hanyoyin da zamani ya zo da su da nufin sauƙaƙa hada-hada a tsakanin alumma, musamman a ƙasashen da suka ci gaba. Sai dai a Najeriya, har yanzu ba kowa ne ya san wannan harka da kuma yadda ya kamata a yi ta ba, musamman duba da yadda kudin na crypto  ya yi daraja a fadin duniya. Shirin Najeriya a Yau na wannan lokacin zai yi nazari ne a kan alfanun da ’yan...

Yadda Kuɗin Kujera Yake Neman Hana Maniyyata Sauke Farali 21.01.2025

Send us Fan Mail Yanzu haka, saura mako biyu wa’adin  da aka deba wa maniyyata Hajjin bana su biya kudin kujerar ya cika, amma rahotanni daga wasu sassan kasar nan na nuna cewa kalilan ne suka iya biyan. Kudin kujerar hajjin ya tsorata ’yan Najeriya a bana, bayan da hukumomi suka ce duk mai sha’awar sauke farali sai ya biya zunzuruntun kudi sama da Naira miliyan takwas. Wannan shine batun da shiri...

Yadda Rashin Ɗaukar Darasi Ya Haddasa Gagarumin Asara A Suleja 20.01.2025

Send us Fan Mail Ƙiyasi ya nuna cewa an yi asarar miliyoyin Naira bayan da shaguna makare da kayayyaki da motocin hawa da na haya suka ƙone ƙurmus, uwa uba kuma rayuka aƙalla 80 suka salwanta sakamakon fashewar tankar mai a Marabar Dikko da ke kusa Suleja a Jihar Neja. Wannan dai ba shi ne karo na farko ba da faɗuwar tanka  ta haddasa asarar dukiya da rayukan mutane masu yawa.  Ko me ya sa ya sa h...

Dalilan Da Suka Sa Farashin Citta Ta Yi Tashin Gwauron Zabo 17.01.2025

Send us Fan Mail A kwanakin baya farashin tumatir yayi tashin gwauron zabo a kasuwani, bayan watanni kadan kuma albasa ta tsefe kai. Ana cikin jimamin tashin farashin albasar ne sai ga na itta ya zabura. Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan abubuwan da suka sa farashin citta ya yi tashin gwauron zabo a kasuwanni.

Yadda Birnin Abuja Ya Zama Yanki Mai Hatsari Ta Fuskar Tsaro 16.01.2025

Send us Fan Mail Rashin tsaro na ci gaba da addabar ’yan Najeriya a matakai daban-daban, a sassan kasar nan daban-daban. Yayin da a wasu yankuna ake fuskantar hare-haren ‘yan ta’adda da masu tayar da kayar baya, a Abuja ana fama ne da masu kwacen motoci, da ’yan damfara, da sauran su. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba ne a kan wuraren da suka zama ihun-ka-banza a birnin na Abuja d...

"Wannan Ce Daya Daga Cikin Ummul Haba'isin Lalacewar Najeriya" 14.01.2025

Send us Fan Mail Saye ko sayar da guraben aiki wani abu ne da yake karuwa kuma yake barazana ga ci-gaban al’umma a Najeriya. Akan yi zargin cewa mutane suna bin wasu hanyoyin da ba su dace ba kafin a ba su aiki a gwamnati. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan wadannan hanyoyi da illar da suke haifar wa al’umma da kuma dabarun kawo karshensu.

Yadda "Sojoji Suka Kashe Farar Hula" A Karo Na Biyu A Wata Guda 13.01.2025

Send us Fan Mail Bayanai na kara bayyana game da wani hari da Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta kai a kan wasu kauyuka biyu na Karamar Hukumar Maradun ta Jihar Zamfara, wanda ya yi sanadin mutuwar farar hula akalla 15. Wadanda suka shaida faruwar lamarin dai sun ce sojojin sun kai hari da jirgi mai saukar ungulu ne a kauyukan biyu wadanda ’yan bindiga suka kaiwa hari . Wannan na zuwa ne mak...

Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Sa Samun Wadataccen Abinci 09.01.2025

Send us Fan Mail A wannan zamani, ’yan Najeriya da dama ba sa samun wadataccen abinci a yini. Magidanta da dama, musamman, sun tsallake sun bar iyalansu sun shiga bariki don neman na sanyawa a bakin salati. Mene ne dalilin hakan, kuma yaya za a yi a kauce wa fadawa cikin irin wannan yanayi? Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan halin da galibin ’yan Najeriya suka tsinci kansu...

Amfanin Komawa Makaranta A Ranar Da Aka Bude Bayan Hutu 07.01.2025

Send us Fan Mail Malamai na dauri sun karantar da cewa idan mutum ya bar karatu na kwana daya, karatun zai bar shi tsawon mako guda; idan ya bar karatu mako guda, karatun zai bar shi wata guda. Sai dai a yau, a duk lokacin da aka ce an koma makaranta bayan hutu, a kan samu rashin komawar dalibai a ranar da aka koma – a wasu lokutan ma, har da malamai. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi...

Yadda Ma’aikata Za Su Daina Jira Kafin Shigowar Albashin Watan Janairu 06.01.2025

Send us Fan Mail A duk lokacin da aka ce an biya albashi, yanayi kan sauya ga masu karba har da masu sana’oi a kasuwanni da kananan shaguna a unguwanni. Sai dai watan Janairun ko wace shekara kan zo da kalubale kasancewar an biya masu aikin albashi da wuri a cikin watan Disamba, sun kuma karar da shi a kan bukukuwan da watan kanzo dasu.   Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a k...

Listen to the Najeriya a Yau podcast in Replaio

Radio and podcasts in one app - free, with no sign-up. Install today and do not miss the launch

Get it on Google Play

Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.