Najeriya a Yau

News HA ↓ 958 episodes

Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.

Category

News

Podcast website

www.buzzsprout.com

Latest episode

Jun 23, 2026

Where to listen?

Podcasts in the app Replaio Radio Coming soon

Podcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts

Get it on Google Play Install for free Android 5M+ downloads · 4.8 rating iOS soon

Episodes

“Makomar Bangaren Ilimi A 2025 Tana Cikin Hadari” 03.01.2025

Send us Fan Mail Ga mai son yin nazari a kan makomar bangaren ilimi a Najeriya a 2025, tanade-tanaden Kasasfin Kudi na bana ka iya zama manuniya. A kasafin kudin Gwamnatin Tarayya na 2025 dai, an ware wa bangaren ilimi sama da naira tiriliyon uku. Wannan ne kuma karo na farko da bangaren ya samu irin wannan gata. Sai dai da alamu hakan bai yi wa malaman makaranta da masu ruwa da tsaki dadi ba. Shi...

Halin Da Matsalar Tsaro Ya Jefa Wasu Alummomin Arewa A Shekarar 2024 02.01.2025

Send us Fan Mail A cikin ‘yan shekarun nan, matsalar tsaro ta kasance babbar kalubale a Arewacin Najeriya. Musamman a jihohin Kaduna, Zamfara, Katsina da kuma jihar Sakkwato. Daga matsalar ‘yan fashi zuwa ta’addanci, yankin ya fuskanci barazanar tsaro daban daban. Duk da irin wadannan kalubale, mutanen wadannan yankuna sun nemo wasu hanyoyi daban-daban na jure irin wadannan matsaloli. Taimakon ‘ya...

Yadda Takkadama Ta Kanannande Siyasar Kananan Hukumomi A Shekarar 2024 31.12.2024

Send us Fan Mail Zabukan Kananan hukumomi na cikin al’amuran da suka dauki hankali a fagen siyasar Najeriya a shekarar 2024. Duk da an gudanar da zabukan cike gurbi a wasu daga cikin jihohin Najeriya, zabukan kananan hukumomi na cikin batutuwan da ’yan Najeriya suka fi zantawa a kai, mai yiwuwa saboda ganin da ake yi cewa wadannan zabukan sun fi shafar alumma kai tsaye. Shirin Najeriya A Yau na wa...

Yadda ’Yan Najeriya Suka Jure Wa Matsin 2024 30.12.2024

Send us Fan Mail Tun bayan rantsar da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu a watan Mayun bara ne dai ’yan Najeriya suke ta kokawa da matsin tattalin arziki sakamakon wasu tsare-tsare da manufofi da Gwamnatin Tarayya ta bijiro da su. Wadannan manufofi sun hada da janye tallafin man fetur da kyale kasuwa ta yi halinta a kan darajar Naira da janye tallafin wutar lantarki da sauran su. Shirin Najeriya a Ya...

Gaskiyar Lamari Game Da Harin Sojoji Kan Al’umma A Sakkwato 27.12.2024

Send us Fan Mail A baya bayan nan ana cigaba da samun hare hare da sojoji ke kaiwa kan fararen hula kamar yadda wasu suka bayyana. Ko A shekarar da ta gabata, rundunar sojin kasar nan ta kai wani hari garin Tudun biri dake karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna inda harin yayi sanadiyyar mutuwar gomman mutane. Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zaiyi duba ne kan harin da rundunar sojin kasar nan t...

Dalilan Da Suka Sa Ake Gudanar Da ‘’Boxing Day’’ A Ranar 26 Ga Disamba 26.12.2024

Send us Fan Mail Ranar 26 ga watan disambar duk shekara ne ake rabon kyaututtuka a cigaba da gudanar da bukuwan kirsimeti wanda ake ma wannan rana da boxing day. Alumma da dama da sunji boxing day abun dake fara zuwa musu a rai shine wasan dambe da ake yi a wasu kasashe da ake kira da boxing.  Shirin Najeriya A Yau zai yi duba ne kan wannan rana na Boxing Day don warware zare da abawa.

Abin Da Ya Sa ’Yan Sanda Suke Kama Mutanen Da Ba Su Ji Ba, Ba Su Gani Ba 24.12.2024

Send us Fan Mail Lokacin bukukuwa lokaci ne da ake samun karuwar zirga-zirga da hada-hadar jama’a. Wannan ne ya sa hukumomin da nauyin samar da tsaro ya rataya a wuyansu suke kara kaimi wajen ganin sun tabbatar da doka da oda. Sai dai  wasu ’yan Najeriya sukan yi zargin cewa ’yan sanda kan yi amfani da wannan dama don kamen mutane babu gaira babu dalili. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokacin zai...

Gaskiyar Lamari Game Da Harin Sojoji Kan Al’umma A Sakkwato 23.12.2024

Send us Fan Mail Lokacin da Victoria Faith, wata baiwar Allah mai shekara 27 da haihuwa, ta je coci a Gundumar Maitama da ke birnin Abuja, cike take da kyakkyawan fatan samo abincin da za ta yi bikin Kirsimeti da shi. Amma a maimakon haka da kyar ta tsira da ranta, ta yi “sa’a” da ta farka a gadon asibiti, bayan da aka tattake ta a turmutsutsun da ya yi sanadin mutuwar mutum 10. Shirin Najeriya a...

Yadda Direbobi Suke Zaman Kashe Wando A Tasha 20.12.2024

Send us Fan Mail A shekarun baya, idan mutum ya shiga tashoshin mota a biranen Najeriya a irin wannan lokaci, zai same su cike da jama’a da hayaniya. Sai dai a bana, a tashoshi da dama, wasu direbobin a kwance suke yayin da fasinjoji suke zaune tsawon sa’o’i suna jiran tsammanin motoci su cika. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan dalilan faruwar hakan a karshen wannan she...

Hadarin Da Ke Tattare Da Aiwatar Da Kasafin Kudi Biyu A Lokaci Guda 19.12.2024

Send us Fan Mail Yayin da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yake gabatar da Kudurin Kasafin Kudi na 2025, shi kuwa Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio dauke hankalin jama’a ya yi da sanar da tsawaita wa’adin Kasafi na bana zuwa tsakiyar badi. Sai dai masana sun yi gargadin cewa wannan lamari ka iya haifar da rikita-rikita a bangaren tattalin arziki da ma wasu bangarorin. Shirin Najeriya a Ya...

Yadda Tamowa Ke Yaduwa Kamar Wutar Daji a Katsina 17.12.2024

Send us Fan Mail Wani rahoto da Kungiyar Likitoci ta Médecins Sans Frontières (MSF) ta fitar ya nuna cewa Arewa maso Yamma ta fi kowacce shiyya yawan karuwar yara masu tamowa. A shiyyar kuma, inji rahoton, Katsina ta fi ko wacce jiha yawan masu fama da cutar. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi bincike ne don gano yadda lamarin yake.

Rayuwar Maza Masu Fama Da Matsalar Rashin Haihuwa 16.12.2024

Send us Fan Mail Rashin haihuwa matsala ce da ke wargaza gidajen aure da dama a wannan zamani. Da an samu shekara biyu zuwa uku bayan an daura aure ba tare da an samu karuwa ba za a fara yamadidi da matar a kan ba ta haihuwa. Sai dai Likitoci sun ce maza ma ka iya fama da wannan larura saboda wasu dalilai. Shirin Najeriya A Yau zai yi nazari ne a kan wadannan matsalolin da suke hana maza haihuwa.

Yadda Ya Kamata Alaka Ta Kasance Tsakanin 'Yan Sanda Da Al'umma 13.12.2024

Send us Fan Mail Babban alhakin da kundin tsarin mulkin Najeriya ya dora wa rundunar Yan Sanda shi ne kare rayuka da dukiyoyin yan kasa.    Sai dai a lokuta da dama, akan samu fito-na-fito da 'yan kasa ke yi da 'yan sandan sakamakon zargin wuce gona da iri wajen gudanar da aiyyukan nasu.    Shirin Najeriya a Yau ya tattauna kan yadda ya kamata alaka ta kasance tsakanin jami'an &apos...

Dalilan Da Suka Sa Farashin Albasa Yayi Tashin Gwauron Zabo 12.12.2024

Send us Fan Mail Albasa na taka muhimmiyar rawa wurin kara wa abinci armashi ko dai ta hanyar kara dandano da kamshin girki, kai a wasu lokutan ma alumma kanyi amfani da albasa saboda likitoci sun bayyana cewar yana kara lafiya ga jikin dan adam. Sai dai a kwanan nan, an wayi gari albasar tayi karanci a kasuwanni wanda hakan yasa aka samu karuwar farashin ta a kasuwanni da ma manyan dilolin ta. Sh...

Yadda Matsalar Cin Zarafin Mata Ta Zama Karfen Kafa A Najeriya 10.12.2024

Send us Fan Mail Cin zarafin mata a Najeriya matsala ce da ke ci gaba da ci wa masu ruwa da tsaki a Najeriya kwarya. Hanyoyin cin zarafin na mata dai suna da yawa; kama daga lakada musu duka zuwa yi musu fyade da wasu abubuwan da dama. Ko wanne irin hali mata suke shiga sakamakon cin zarafi a gidajen aurensu? Shirin Najeriya a Yau zai yi magana da matan da aka ci zarafinsu da ma mazan da suka ci z...

Kuncin Da Marasa Lafiya Suke Ciki Sakamakon Tsadar Magani 09.12.2024

Send us Fan Mail Farshin maganin asibiti yana ci gaba da tashin gwauron zabo a Najeriya, inda yake jefa marasa lafiya da ’yan uwa da abokan arziki cikin halin tsaka mai wuya. Da yawa daga cikin marasa lafiya dai sukan koma amfani da abin da ya fi musu sauki – ko dai sayen maganin a hannun masu tallansa a kafada, ko amfani da maganin gargajiya, ko kuma, a wasu lokutan, hakura da maganin. Shirin Naj...

Abin Da Ya Sa Ake Hana ’Yan Najeriya Fadin Albarkacin Bakinsu 06.12.2024

Send us Fan Mail Sashe na 4 na kundin tsarin mulkin kasa na dauke da tanadetanade musamman da suka shafi ‘yancin dan adam a dokar Najeriya. Cikin tanade-tanaden akwai ’yancin da doka ta bai wa kowane dan najeriya na rayuwa, da shiga taro, da fadin albarkacin baki. Shirin Najeriya A Yau zai yi duba a kan tanade-tanaden doka a kan ’yancin fadin albarkacin baki.

‘Karambanin’ Malamai Kan Ƙudurorin Harajin Tinubu 05.12.2024

Send us Fan Mail Kudurorin Dokar Haraji da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya aike wa Majalisar Dokoki ta Kasa suna ci gaba da tayar da kura a Najeriya. Muhawara a kan batun ta dauki sabon salo ne bayan da wasu malaman addinin Musulunci daga Arewacin Najeriya suka ki amincewa da wasu tanade-tanaden kudurorin dokar. Shin har da kaza ne a cin danko? Karambani ne ya sa malamai tsoma baki a muhawarar...

Dalilin Ƙulla Yarjejeniyar Gwamnatin Kaduna Da ’Yan Ta’adda 03.12.2024

Send us Fan Mail Yankin karamar hukumar Birnin Gwari dake jihar Kaduna na daya daga cikin alummomin da suka fi fuskantar matsalar tsaro musamman a arewacin Najeriya. A kwanan nan rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin jihar ta shiga yarjejeniya tsakanin yan bindigan da kuma gwamnatin jihar. Shirin Najeriya A Yau yayi Nazari ne kan wannan yarjejeniya da kuma abun da hakan ke nufi ga jihar da ma alumm...

Dalilan Yawaitar Gobara A Lokacin Hunturu 02.12.2024

Send us Fan Mail Lokacin hunturu lokaci ne da sau da yawa akan fuskanci barazanar tashin gobara a sassa da dama na Najeriya. A wasu lokutan kuma, abubuwan da mutane suke yi kan taka muhimmiyar rawa wajen tayar da gobara a gidaje, da kasuwanni da ma sauran wuraren zamantakewar jama’a. Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan dalilan da suka sa aka fi samun gobara a irin wannan...

Kalubalen Da Iyaye Ke Fuskanta Wajen Tarbiyyan 'Ya'yan Su 29.11.2024

Send us Fan Mail Duk wanda ya shekara arbain zuwa sama ya san irin tarbiyyan da ya samo daga wurin iyayen sa a da baya can, irin mu’amalan dake tsakanin sa da iyaye har ma da shakuwan dake tsakanin ‘ya’ya da iyaye. A yanzu kuwa abubuwa sun canza daga yadda aka san su, inda abubuwa suka rincabe sukayi wa iyaye yawa. Daya daga cikin manyan sauyin da aka samu sun hada da aikin gwamnati ko aikin wata...

Matakan Da Manoman Jihar Taraba Suka Dauka Kan 'Yan Ta'adda 28.11.2024

Send us Fan Mail Wata matsala da kasar nan ke cigaba da fuskanta itace matsalar karancin abinci sakamakon ‘yan ta’adda dake barnata amfanin noma, hana manoma yin noma, a wasu lokutan ma karbar kudaden haraji daga manoma a wasu yankunan kasar nan. Hakan yasa alummomin Karamar hukumar Gassol da Balli dake jihar Taraba daukar wasu matakai don samawa kan su mafita daga ayyukan irin wadannan yan ta’add...

Abin Da Ya Sa Mutanen Tudun Biri Suka Juya Baya Ga ₦33B 26.11.2024

Send us Fan Mail Al’ummar Tudun Biri sun ce su da ma ba su sa a ka bayan da aka ba da labarin cewa kotu ta yi fatali da wata kara da aka shigar a madadin su. Tun a bara dai, lokacin da wasu lauyoyi suka shigar da ƙara suna neman a bi wa wadanda wani harin rundunar sojin sama a kan kauyen ya hallaka hakkinsu, mazauna yankin da dama suka nesanta kansu da lamarin. Shirin Najeriya a Yau na wannan loka...

Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da CNG 25.11.2024

Send us Fan Mail Galibin ’yan Najeriya ba su san amfanin da sauya ababen hawansu daga masu amfani da man fetur zuwa masu amfani da iskar gas ta CNG ke da shi ba, musamman a wannan lokaci da ake fama da tsadar man fetur.    ’Yan Najeriya da dama dai suna amfani da man fetur ne saboda karancin wuraren sauya ababen hawan da sauran dalilai.    Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kan i...

Tasirin Rancen Naira Tiriliyan 138 A Rayuwar ’Yan Najeriya 22.11.2024

Send us Fan Mail Bayan  da Majalisar Dattawa ta sahale wa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu karbo wani sabon rance na sama da Naira tiriliyan daya, yawan bashin da ake bin Najeriya ya kai matakin da bai taba kaiwa ba a tarihi.  Da wannan amincewa dai yawan bashin da ake bin Najeriya ya kai Naira tiriliyan 138! Wannan shirin na Najeriya a Yau zai yi bincike ne a kan tasirin da wannan bashi yake da sh...

Listen to the Najeriya a Yau podcast in Replaio

Radio and podcasts in one app - free, with no sign-up. Install today and do not miss the launch

Get it on Google Play

Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.