Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Where to listen?
Podcasts in the app Replaio Radio Coming soonPodcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts
Episodes
Yadda Cutar Amai Da Gudawa Ta Yi AjalinMutum 25 A Sakkwato 21.11.2024 22:46
Send us Fan Mail A ’yan kwanakin nan an samu rahotannin bullar cutar amai da gudawa a wasu sassan Jihar Sakkwato, inda aka ba da rahoton mutuwar mutum 25. Kafafen yada labarai da dama dai sun fitar da rahotanni kan wannan al'amari da ya tayar da hankulan alumma a ciki da wajen Jihar. Sai dai kuma hukumomi sun ce wannan adadin na wadanda cutar ta yi ajalinsu daga watan Janairu ne zuwa yanzu. S...
Me Ya Sa Ake Daukar Masu Kwarewar Aiki A Bar Masu Digiri? 19.11.2024 14:55
Send us Fan Mail Jama’a da dama na burin da zarar sun mallaki takardar digiri, za su samu domin sun kammala jami’a. Saidai a yanzu da alama masu daukar aiki suna yawan tallata neman ma’aikata, amma kuma a cikin sharudda za a ce dole sai mai kwarewa a da sanin makamar aiki a fannin. Shirin Najeriya a Yau ya duba abin da ya sa masu daukar aiki suka fi sha’awar masu kwarewa fiye da masu kwalin...
Kalubalen DaZai Yi Wa Zababben Gwamnan Jihar Ondo Dabaibayi 18.11.2024 22:50
Send us Fan Mail Tun bayan da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ayyana Lucky Aiyedatiwa a matsayin wanda ya lashe Zaben Gwamna da aka gudanar a Jihar Ondo ranar 16 ga watan Nuwamba, hankula suka karkata zuwa ga kalubalen da ke gabansa. Kama daga rikicin cikin gida a jam’iyyarsa ta APC zuwa ga barazanar jam’iyyun adqawa da muradun al’ummar da ya yiwa alkawura, anya Aiyedatiwa bai sha ta fi cikinsa ba...
Shirin Da Masu Ruwa Da Tsaki Suka Yi Kan Zaben Ondo. 15.11.2024 30:39
Send us Fan Mail A ranar Asabar 16 ga wannan watan ne za’a gudanar da zaben gwamna a jihar Ondo, sai dai kamar sauran zabukan da aka saba gudanarwa a Najeriya, tuni masu ruwa da tsaki suka bayyana kammala shirye shiryen tunkarar wannan zabe. To amma ba’a nan gizo ke sakar ba, domin kuwa a mafi yawan lokuta al’umma a kasar nan na korafin cewar duk da shirye shiryen da masu ruwa da tsaki suke bayyan...
Yadda Za A Kauce Wa Gadon Ciwon Suga 14.11.2024 27:18
Send us Fan Mail Wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa akalla ’yan Najeriya miliyan biyar ne suke cikin hadarin kamuwa da ciwon suga nan da shekarar 2030. Yaduwar lalurar a tsakanin wadanda iyayensu suke fama da ita tana cikin hanyoyin da suke taimakawa wajen karuwar ta. Albarkacin Ranar Ciwon Suga ta Duniya, shirin Najeriya A Yau zai tattauna a kan hanyoyin da wadanda suke fuskantar barazanar...
Hanyoyin Hana Lalata Turakun Rarraba Wutar Lantarki. 12.11.2024 18:39
Send us Fan Mail Barnata kayan gwamnati ba sabon abu ba ne a Najeriya; sai dai a wannan karon barnar ba gwamnati kadai ta shafa ba har ma da alummar gari. A kwanakin baya ne wasu yankuna na Arewacin Najeriya suka fuskanci rashin wutar lantarki na tsawon kusan kwanaki goma. A cewar hukumomin da abin ya shafa dai hakan ya faru ne saboda ’yan ta’adda sun kai wa turakun wutar lantarki hari. Shirin Naj...
Dalilan Durkushewar Kananan Sana’o’i Da Hanyoyin Magance Su 11.11.2024 26:03
Send us Fan Mail Kanana da matsakaitan masana’antu, kamar yadda masana tattalin arziki suka bayyana suna taka muhimmiyar rawa wajen karuwar arziki a kowace kasa. Galibi irin wadannan masana’antu matasa suke kafa su don samun abun sakawa a bakin salati. Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan dalilan durkushewar kanana da matsakaitan sana’oi a Najeriya.
Me Zai Faru Bayan Cikar Wa’adin Da Lakurawa Suka Bai Wa Sakkwatawa? 08.11.2024 29:58
Send us Fan Mail A yau Juma’a wa’adin da wata sabuwar kungiya mai suna Mujahidin – wadda aka fi sani da Lukarawa - ta bai wa al’ummar wasu yankunan Jihar Sakkwato ya zo karshe. Kungiyar dai ta bai wa al’ummar yankunan zuwa yau Juma’a su girbe amfanin gonarsu, amma a cewar wani mazaunin daya cikin yankunan ya ce ai ba su bari wa’din ya cika na suka dauki mataki. Shirin Najeriya A Yau na wannan lok...
Me Nasarar Shugaban Amurka Donald Trump Yake Nufi Ga Najeriya? 07.11.2024 29:06
Send us Fan Mail Tun bayan dawowar Najeriya mulkin demokaradiyya a shekarar 1999 ne dai ake gudanar da zaben shuwagabanni a duk lokacin da aka ce wa’adin shugaba ya kawo karshe. Toh sai dai tun dawowar mulkin demokradiyyar ne ake samun korafe korafe kan yadda ake gudanar da zabuka da ma irin rawar da shugabancin wanda da ya lashe zabe a Amurka ke tasiri kan Najeriya. Shirin Najeriya A Yau na wanna...
Shin Addu’oi Kadai Najeriya Take Bukata Don Ficewa Daga Matsaloli? 05.11.2024 28:27
Send us Fan Mail Galibin ’yan Najeriya dai sun yarda cewa Allah ne mai bayarwa, Shi ne kuma mai hanawa. Mai yiwuwa hakan ne kan sa a rika yin kira, musamman ga mabiya addianai mafiya rinjaye na Musulunci da Kiristanci, da su yi addu’oi don samun waraka daga matsalolin da aka fama da su. Sai dai kuma wasu ’yan kasa suna ganin fadar haka alama ce da take nuna cewa siukuwa ta kare saura zamiya. Shir...
Abin Da Ya Kamata A Yi Da Kananan Yara Masu Zanga-Zanga 04.11.2024 27:38
Send us Fan Mail Gurfanar da yaran nan da aka kama watanni uku da suka gabata yayin zanga-zangar ‘#EndBadGovernance’ na ci gaba da yamutsa hazo a Najeriya. Mutane da dama dai, musamman a Arewa, suna ta tofin Allah-tsine a kan kamen yaran, wadanda wasu suke cewa kanana ne, shekarunsu ba su kai a kama su ba ballantana a kai su gaban kotu. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai tattauna ne kan ta...
Yadda Dawo Da Wutar Lantarki Zai Sauya Wasu Sassan Arewa 01.11.2024 26:41
Send us Fan Mail A wasu sassan Arewa, mutane sun cika da farin ciki da annashuwa bayan da wutar lantarki ta dawo a yankunansu. Yankin na Arewa dai ya tsinci kansa cikin rashin wutar lantarki na kusan kwanaki goma bayan da babban layin dakon wutar lantarkin ya durkushe. Shirin Najeriya A Yau zai duba tasirin dawowar lantrakin a yankin na Arewa.
“Matsin Tattalin Arziki Ya Sa Ba Na Iya Aikina Yadda Ya Kamata” 31.10.2024 28:44
Send us Fan Mail Alamu sun nuna cewa sakamakon kuncin rayuwa da ake fama da shi a Najeriya, ingnacin aikin da ma’aikata suke yi yana raguwa. Aiki yana ingnatuwa ne dai da samun wasu abubuwa da suka hada da kyakkyawan yanayin wurin aiki da isasshen hutu da kwanciyar hankali da kuma biyan bukatar ma’aikaci a dukkan lokaci. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai tattauna ne kan yadda matsin tatta...
Dalilan Da Ake Cin Zarafin ‘Yan Najeriya 29.10.2024 21:01
Send us Fan Mail Cin zarafi da daidaikun alumma ke fuskanta a Najeriya yayin da suke gudanar da ayyukan su na yau da kullum ba sabon abu bane, musamman la’akari da cewa mutanen biyu a mafi akasarin lokaci basu san abun da doka ta tanada game da cin zarafi ba. A wasu lokuta ma, cin zarafin nan na fito wa ne daga wadanda suke rike da madafun iko, inda zaka ga suna bayyana cewar ‘’zan keta maka haddi...
Ko Wadanne Dalilai Ne Ke Sanya Wasu ‘Yan Najeriya Ajiye Ababen Hawan Su? 28.10.2024 24:45
Send us Fan Mail Tsadar man fetur a Najeriya ya tilastawa da yawa daga cikin ‘yan kasa ajiye ababen hawan su inda suka koma bin na haya don zuwa wuraren aiki, Ziyara da sauran zirga-zirgar su ta yau da kullum. A baya manyan biranen Najeriya su kan cika su batse da ababen hawa da kan yi zirga-zirga da kai kawo, wanda wasu suke ganin wadata da fin karfin bukatun yau da kullum ne ke sanya hakan. Shir...
Kuncin Da Arewa Ta Shiga Sakamakon Rashin Wutan Lantarki 25.10.2024 22:55
Send us Fan Mail Fiye da mako guda ke nan wasu sassan arewacin Najeriya suna fama da rashin wutar lantarki. Hakan ya haddasa gagarumar matsala a rayuwar mutane da dama. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai duba irin halin matsi da mazauna yankin suka shiga sakamakon daukewar wutar lantarkin.
Ko Garambawul Din Da Tinubu Ya Yi Zai Kawo Wa ’Yan Najeriya Sauki? 24.10.2024 26:41
Send us Fan Mail A karon farko tun bayan rantsar da shi, Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi sauye-sauye ga Majalisar Ministocinsa. ’Yan Najeriya dai sun dade suna jiran wannan garambawul din na Shugaban Kasa; said ai abin tambaya shi ne: mene ne zai biyo bayan wannan garambawul din? A kan wannan batu shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari.
Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da CNG 22.10.2024 23:52
Send us Fan Mail Galibin ’yan Najeriya ba su san amfanin da sauya ababen hawansu daga masu amfani da man fetur zuwa masu amfani da iskar gas ta CNG ke da shi ba, musamman a wannan lokaci da ake fama da tsadar man fetur. ’Yan Najeriya da dama dai suna amfani da man fetur ne saboda karancin wuraren sauya ababen hawan da sauran dalilai. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kan irin ab...
Sai Da Kudi Mai Yawa Za Ku Iya Cin Abinci Mai Gina Jiki? 21.10.2024 26:16
Send us Fan Mail Galibin ’yan Najeriya sun koma cin abin da suka samu ba tare da sun yi la’akari da abin da zai gina musu jiki ba, musamman a wannan lokaci da suke fama da matsin tattalin arziki. Sai dai masana sun ce ba sai mutum ya kashe kudi mai yawa ba zai iya cin abincin da zai gina mishi jiki ba. Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi duba a kan irin abincin da mutane za su iya ci da ku...
Fashewar Tankar Mai: Asarar Da Al’ummar Majiya Suka Tafka 18.10.2024 23:07
Send us Fan Mail Galibin waɗanda suka rasa rayukansu sakamakon fashewar tankar man da ta yi ajalin sama da mutum 150 a garin Majiya na Jihar Jigawa matasa ne. Ɗaya daga cikinsu, Hassan Hamza, matashi ne da ya yi karatu a fannin Harhaɗa Magunguna, karatun da ake matuƙar buƙatar masu yinsa a tsakanin al’umma. A shirin Najeriya a Yau na lokacin za mu yi nazari ne a kan girman asarar da al'ummar...
Faduwar Tanka A Jigawa: “Mun Kasa Cin Abinci Tun Da Abin Ya Faru”. 17.10.2024 20:30
Send us Fan Mail Al’ummar Majiya a Jihar Jigawa na ci gaba da jimamin mutuwar mutum sama da dari sakamakon hadarin tankar mai. Saboda tashin hankalin da suke ciki, wasu daga cikin mazauna garin sun ma ce sun kasa cin abinci. Shirin Najeriya a Yau zai tattauna da wasu daga cikin ’yan uwan wadanda abin ya shafa game da yadda suka ji da faruwar wannan lamari.
Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Sa Ganin Tasirin Cire VAT Kan Kayan Abinci 15.10.2024 26:52
Send us Fan Mail Daya daga cikin nau’ukan harajin da gwamnatoci suke karba shi ne harajin VAT wanda akan dora a kan kayayyaki ko hidimomi. Tasirin wannan haraji a kan farashin kayayyaki ya sa gwanatin Najeriya dauke harajin a kan wasu kayan abinci. Amma bayan watanni da daukar wannan mataki, ’yan Najeriya ba su ga tasirin yin hakan ba. Shirin Najeriya A Yau zai bincika dalilan da suka sa hakan.
Shin Cire Tallafin Mai Ne Ya Jefa ’Yan Najeriya Cikin Kunci? 14.10.2024 26:35
Send us Fan Mail Galibin Najeriya suna rataya alhakin kuncin rayuwar da suke fama da shi kacokan a kan janye tallafin man fetur. Sai dai wasu masan suna ganin idan ma janye tallafin yana taka rawa, to akwai wasu matakan da suke bayar da gudunmawa mai tsoka. Ko wadanne matakai ne wadannan? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci za iyi kokarin warware zare da abawa.
Me Ya Sa ’Yan Najeriya Suka Fara Yanke Kauna Da Samun Sa’ida? 11.10.2024 23:38
Send us Fan Mail Muhawara ta barke a Najeriya bayan sanar da aka sanar da karin farashin man fetur a gidan gidajen mai na NNPC a kan wane ne zai kare muradun ’yan kasa, ya hana a yi musu hawan kawara? ’Yan kasa da dama dai na ganin wannan kari a matsayin wani karin mataki na takura wa rayuwarsu, wadda tuni dama take cikin wani yanayi na tsaka-mai-wuya.
Alakar Lafiyar Kwakwalwa Da Sakamako Mai Kyau A Wurin Aiki 10.10.2024 30:08
Send us Fan Mail Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana ranar 10 ga watan Oktoba a duk shekara a matsayin Ranar Lafiyar Kwakwalwa ta Duniya. Taken bikin a bana dai shi ne “Kulawa Da Lafiyar Kwakwalwa A Wurin Aiki”. Don haka ne shirin Najeriya A Yau za iyi nazari a kan alakar da ke tsakanin lafiyar kwakwalwar da ingantuwar aiki.
Similar podcasts
Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.