Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Where to listen?
Podcasts in the app Replaio Radio Coming soonPodcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts
Episodes
Abin Da Ke Kawo Rashin Kyautata Wa Kwastoma a Najeriya 08.10.2024 28:18
Send us Fan Mail A makon farko na watan Oktoba a duk shekara ake bikin Makon Kwastomomi a fadin duniya. A lokuta da dama dai akan samu matsaloli da kalubale a tsakanin abokan ciniki. A kan hanyoyin warware waɗannan matsaloli shirin Najeriya a Yau na wannan lokacin zai tattauna.
Yadda Kudin Crypto Ya Sanya Matasa Yin Saki-Na-Dafe 07.10.2024 24:22
Send us Fan Mail Matasa da dama a Najeriya ne suka yi sake-reshe-kama-ganye saboda hangen Dala. Saboda tunanin zai samu kudi masu yawa ta hanyar kudin kirifto na Hamster, John Adams ya yi murabus daga aikinsa, daga karshe ya tashi ba tsuntsu ba tarko – ma’ana, babau aikin babu kudin. Shirin Najeriya A Yau zai tattauna ne a kan halin da wadannan matasa suka tsinci kan su ciki bayan mining din Hamst...
Me Zai Faru Idan Aka Dawo Da Tallafin Man Fetur? 04.10.2024 27:24
Send us Fan Mail Yayin da halin kuncin da ’yan Najeriya suke fama da shi yake karuwa, yawan masu kira da a dawo da tallafin man fetur ma sai karuwa yake yi. Sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba: shin me zai faru idan da za a dawo da tallafin? Wanne hali tattalin arzikin Najeriya zai shiga? Shirin Najeriya A Yau zai yi kokarin amsa wadannan da ma wasu tambayoyin masu alaka da su.
Abin Da Ya Sa Ake Yawan Samun Hadarin Kwalekwale A Neja 03.10.2024 23:29
Send us Fan Mail Jihar Neja na cikin jihohin da aka fi samun hadarin kifewar kwalekwale a Najeriya. Hadari na baya-bayan nan shi ne wanda ya auku a Karamar Hukumar Mokwa, inda wani kwalekwale mai dauke da mutum sama da 100,000 ya yi alkafura. Shirin Najeriya A Yau zai tattauna ne kan dalilan hadurran irin wannan da kuma mutanen da abin ya rutsa da su.
Me Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Sa Shaukin Ranar Samun ’Yancin Kai? 01.10.2024 26:42
Send us Fan Mail A duk lokacin da bikin tunawa da Ranar Samun ’Yancin Kai ya zagayo, bisa al’ada, akan ga ’yan Najeriya suna farin ciki. Sai dai a wannan karon alamu na nuna abin ya sauya; ba kamar yadda aka saba gani a shekarun da suka gabata ba, mutane da dam aba su ma san ana yi ba. Shirin Najeriya A Yau zai yi duba ne kan dalilan da suka sa ’yan Najeriya ba sa shauki kamar yadda aka saba gani...
Rawar Da Fassara Ke Takawa Wajen Habbaka Harshen Hausa 30.09.2024 30:18
Send us Fan Mail Yau ce Ranar Fassara ta Duniya wadda Majalisar Dinkin Duniya ta ware don jinjina ga ayyukan kwararrun da suke hada al'ummomi waje daya, da karfafa zaman lafiya da tsaro a duniya ta hanyar juya bayanai daga wani harshe zuwa wani. Albarkacin wannan rana, shirin Najeriya A Yau zai tattauna ne kan irin gudunmawar da fassara ke bayarwa wajen habbaka harshen Hausa.
Rashin Aikin Yi Da Hanyoyin Magance Su A Najeriya. 27.09.2024 25:31
Send us Fan Mail Rashin aikin yi na daya daga cikin manyan kalubalen da najeriya ke fuskanta a wannan lokaci, musamman la’akari da yanda ake cigaba da samun matasa dake da karfi a jika amma babu aikin yi. Hukumar kididdiga ta kasa ta fitar da bayanan dake baiyana cewa rashin aikin yi ya karu a najeriya da kaso 5.3 a farkon wannan shekarar, kazalika binciken ya baiyana cewa wadanda basu yi karatu m...
Shin Karin Kudin Ruwa Zai Farfado Da Tattalin Arzikin Najeriya? 26.09.2024 21:21
Send us Fan Mail A lokuta daban-daban, Babban Bankin Najeriya (CBN) kan ƙara kuɗin ruwa, ya kuma ce yana yin hakan ne da nufin daidaita tattalin arziki. Shin wanne irin tasiri wannan mataki yakan yi a kan tattalin arziƙin da ma rayuwar ’yan Najeriya? Shirin Najeriya a Yau zai yi nazari a kan wannan batu.
Hakikanin Dalilan Nasarar APC A Zaben Gwamnan Jihar Edo 24.09.2024 24:01
Send us Fan Mail Duk da kokawa da ’yan Najeriya suke ci gaba da yi game da wahalhalun da suke sha wadanda suka zargi manufofin Gwamnatin Tarayya ta APC da haddasa musu, wasu sun ce bas u yi mamaki ba da al’ummar Jihar Edo suka zabi jam’iyyar. Sai dai kuma abin tambaya shi ne: mene ne hakikanin dalilinsu na yin haka? Shirin Najeriya A Yau zai yi binciken kwakwaf a k kan ikirarain shugabannin APC ce...
Alkiblar Da Edo Za Ta Fuskanta Bayan Zaben Monday Okpebholo 23.09.2024 27:48
Send us Fan Mail A karshe dai Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ayyana Monday Okpebholo a matsayin zababben Gwamnan Jihar Edo. Ya yi nasarar lashe zaben da aka gudanar ranar Asabar ne dai bayan ya kayar da ’yan Takara 16. To ko me wannan nasara take nufi ga Jihar da al’ummarta? Wannan na cikin tambayoyin da shirin Najeriya a Yau zai amsa a wannan lokacin.
Turka-Turkar Da Ta Dabaibaye Zaben Jihar Edo 20.09.2024 24:25
Send us Fan Mail Masu fashin baki sun nuna fargabar yiwuwar samun hatsaniya yayin zaben gwamna da za a gudanar a Jahar Edo ranar Asabar. Sai dai kuma al’ummar jIhar sun ce ko ana ha-maza-ha-mata za su fito su kada kuri’a. Shirin Najeriya a Yau zai yi nazari ne a kan irin tanadin da masu ruwa da tsaki ke yi wa wannan zabe
Matakan Da Wasu Al’ummomi Suke Dauka Don Guje Wa Ambaliyar Ruwa 19.09.2024 21:43
Send us Fan Mail Wasu al’ummomi a Najeriya sun fara ɗaukar matakan kauce wa asarar da ambaliyar ruwa ka iya haifar musu idan aka buɗe Madatsar Ruwa ta Lagdo da ke Jamhuriyar Kamaru. A kwanan nan ne dai Hukumar da ke Kula da Albarkatun Ruwa ta Najeriya ta ce yankunan da ke gaɓar Kogin Binuwai a jihohi 11 na fuskantar barazanar ambaliyar. Shirin Najeriya a Yau zai yi nazari a kan wadannan matakai d...
‘Mun Yi Zaton Samun Sauki Da Zuwan Matatar Dangote’ 17.09.2024 22:55
Send us Fan Mail ‘Yan Najeriya sun yu ta sa ran zuwan matatar Dangote zai samar da saukin wahalhalun man fetur. Sai dai tun ba a je ko ina ba ana ta samun musayar kalamai tsakanin kamfanin NNPCL da Dangote kan batun. Shirin Najeriya a Yau zai tattauna kan yadda farshin man fetur ke ci gaba da karuwa duk da zuwan matatar Dangote
“Akwai Yiwuwar Kwata Ambaliyar Borno A Wasu Jihohin” 16.09.2024 14:11
Send us Fan Mail Rahotanni sun ce al’ummomin wasu yankuna a wasu jihohin Najeriya suna zaman ɗar-ɗar bayan da ruwa ya fara mamaye gonaki da gidajensu. Tun bayan mummunar ambaliyar ruwa a Maiduguri, hukumomi a Najeriya suke kara ankarar da al'ummomin wasu jihohin cewa akwai yiwuwar samun ambaliyar. Shirin Najeriya a Yau zai tattauna kan yadda za a dauki matakan kan-da-garki kan yiwuwar ambali...
Yadda Mazauna Maiduguri Za Su Kubuta Daga Illolin Ambaliya 13.09.2024 25:08
Send us Fan Mail Bayan mummunar ambaliyar ruwar da ta mamaye kusan kashi 70 cikin 100 na Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, masana na bayyana fargaba game da yiwuwar barkewar cututtuka da kuma ta'azzarar manyan larurori ga masu dauke da su. Shirin Najeriya a Yau zai tattauna a kan yadda al'ummar birnin na Maiduguri za su kare kansu kuma su tsira da lafiyarsu.
Shin Dole Ne Sai An Dauki Tsauraran Matakan Saita Najeriya? 12.09.2024 24:07
Send us Fan Mail Duk da kokawa da Yan Najeriya ke ci gaba da yi kan irin manufofin gwamnati da suka ce suna Kara jefa su cikin kangin rayuwa. Amma, a ko da yaushe Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu Yana kara nanata cewa, tilas ne a dauki tsauraran Matakai na saita tattalin arzikin kasar, idan har ana bukatar Jin dadi a nan gaba. Shirin Najeriya a Yau zai tattauna ne, kan ko tilas ne sai an dauki tsau...
Dabarun Magance Matsalolin Najeriya 10.09.2024 26:35
Send us Fan Mail Daga cikin manyan hakkokin da kundin tsarin mulkin Najeriya ya dorawa shugabanni, shine kirkirar dabarun samarwa Yan kasa saukin tsadar Rayuwa da tabbatar da kasancewar su cikin walwala. Sai dai, a baya-bayan nan, Yan Najeriya na ci gaba da nuna rashin gamsuwa irin dabarun da shugabanninin ke amfani dasu wajen magance matsalolin da kasar ke fuskanta. Shirin Najeriya a Yau ya tatta...
'Karin Farashin Mai Ya Fara Tilasta 'Yan Najeriya Ajiye Aiki' 09.09.2024 24:06
Send us Fan Mail Karin farashin man fetur da NNPCL ya yi a baya-bayan nan, na kara jefa 'yan Najeriya cikin kunci da rashin tabbas a rayuwar yau da Kullum. Tsadar kayayyaki musamman na abinci da sufuri, ya fara tilasatawa wasu Ma'aikata ajiye aiyyukan su Shirin Najeriya a Yau ya zai yi dubi kan illar yanayin ga wadanda abin ya shafa, da ma tattalin arzikin kasa.
Mece Ce Illar Zub-Da Kimar Najeriya A Kasashen Ketare? 06.09.2024 24:59
Send us Fan Mail Sau da dama, ana yawan batun yadda 'yan Najeriya ke bata wa kasar suna sakamakon ayyukan assha da suke aikata wa a kasashen ketare Wasu na alakanta wannan lamari da yadda ake ganin 'yan wasu kasar na yiwa 'yan Najeriyar gani-gani a kasashen nasu. Shirin Najeriya a Yau ya tattauna kan ne, kan wannan batu.
Hanyoyin Magance Kuncin ‘Yan Najeriya Cikin Gaggawa 05.09.2024 21:55
Send us Fan Mail Ana ci gaba da samun koke-koke game da yadda ‘yan kasa ke ji a jikinsu. Masana dai na ganin akwai matakan da in har gwamnati ta dauke su za a iya kawar da matsin tattalin arzikin da ta yi wa talaka dabaibayi. Shirin Najeriya a Yau zai tattauna kan matakan gaggawa da suka kamata gwamnati ta dauka domin kaiwa share hawayen ‘yan kasa.
Me Zai Faru Idan Aka Kara Kudin Mai A Najeriya? 03.09.2024 26:16
Send us Fan Mail A dai-dai lokacin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da kukan tsadar kayayyaki sakamakon irin manufofin gwamnati, musamman ma cire tallafin man Fetur, kwatsam sai ga wani rahoto ya fito daga kamfanin mai na kasa wato NNPCL dake nuni da yiyuwar karin farashin man fetur din. Shirin Najeriya a Yau, ya kalli yadda wannan batu zai yi tasiri ga rayuwar ’yan Najeriya.
Kuncin Rayuwar Da Ambaliya Ke Jefa Mutane 02.09.2024 26:48
Send us Fan Mail A duk lokacin da aka samu intila'in ambaliyar ruwa, rayuwar wadannan abin ya shafa kan shiga cikin halin ha'ula'i sakamakon tsananin matsin rayuwa da suke kasancewa a ciki. Irin wadannan mutane sukan rasa abin da zasu ci, da sauran muhimman abubuwan more rayuwa. Shirin Najeriya a Yau, ya kalli irin wannan yanayi da wadanda ambaliyar ruwan ta shafa ke kasancewa a cik...
Yadda Ambaliya Ke Raba Dubban ‘Yan Najeriya Da Muhallansu 29.08.2024 24:28
Send us Fan Mail Wata Babbar matsala da ambaliyar ruwa ke haifarwa a Najeriya ita ce, yadda dubban mutane ke rasa muhallansu a duk shekara. Alkalumman hukumar bayar da Agajin gaggawa ta NEMA sun nuna cewa kawo yanzu, ambaliyar ta raba kusan mutum dubu 208,655 da muhallansu a jihohi 28. Shirin Najeriya a Yau, ya tattauna kan irin matakan da suka kamata a dauka domin kaucewa matsalar da hakan ka iya...
Yadda Ya Kamata Alaka Ta Kasance Tsakanin 'Yan Sanda Da Al'umma 27.08.2024 27:14
Send us Fan Mail Babban alhakin da kundin tsarin mulkin Najeriya ya dora wa rundunar Yan Sanda shi ne kare rayuka da dukiyoyin yan kasa. Sai dai a lokuta da dama, akan samu fito-na-fito da 'yan kasa ke yi da 'yan sandan sakamakon zargin wuce gona da iri wajen gudanar da aiyyukan nasu. Shirin Najeriya a Yau ya tattauna kan yadda ya kamata alaka ta kasance tsakanin jami'an 'yan s...
Me Ya Sa 'Yan Siyasa Ke Naɗa Tarin Mataimaka A Gwamnati? 26.08.2024 14:55
Send us Fan Mail Gwamnatoci a matakai daban-daban na ta ikirarin rage kashe kudin gwamnatin ko tsuke bakin aljihu. Sai dai masu sharhi na gani wasu masu mukaman siyasa ke nada tarin mataimaka wadanda wasu ma ba lallai sun taba ido biyu da su ba. Shirin Najeriya a Yau zai yi sharhi ne kan rawar da masu taimaka wa ‘yan siyasa da yawa ke taka wa.
Similar podcasts
Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.