Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Where to listen?
Podcasts in the app Replaio Radio Coming soonPodcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts
Episodes
Gudummuwar ‘Yan Najeriya Wajen Cin Hanci Da Rashawa 23.08.2024 26:58
Send us Fan Mail Masana na ganin kaso mafi tsoka na ‘yan Najeriya suna bada gudummuwa wajen cin hanci da rashawa. Ta fuskar addinai ma akwai yadda ake kallon matsayin cin hanci. Shirin Najeriya a Yau zai maida hankali kan irin kallon da al’umma ke yi wa cin hanci da kuma yadda suke bada gudummuwa a kai.
Shin Har Yanzu Akwai Masu Matsakaicin Karfi A Najeriya? 22.08.2024 23:57
Send us Fan Mail Wane mizani kuke amfani da shi wajen auna masu matsakaicin karfi ko wadata ko kuma masu karamin karfi a Najeriya? Shirin Najeriya a Yau zai tattauna kan matsayin da za a iya dora yadda al'umma ke rayuwa.
Yadda Bacewar Kananan Takardun Naira Ke Shafar Kasuwanci 20.08.2024 21:54
Send us Fan Mail A 'yan kwanakin nan da wuya a ci karo da kanana takardun Naira. Wasu na ta'allaka hakan da rashin abubuwan da za a iya siya a wannan kudade. Shirin Najeriya a Yau ya yi nazari kan bacewar kanana takardun Nairar da yadda haka ke shafar kasuwanci.
Mece Ce Cutar Kyandar Biri Kuma Me Ke Jawo Ta? 19.08.2024 15:40
Send us Fan Mail An samu ɓarkewar cutar ƙyandar biri a ƙasashen Afrika, wadda majalisar Ɗinkin Duniya ke ganin cutar za ta iya tsallake Nahiyar. Hukumar yaki da cutuka ta Najeriya ta ce ta samu akalla mutane 39 da suka harbu da cutar daga farkon shekarar nan zuwa yanzu, inda WHO ta ayyana dokar ta baci kan wannan cuta. Shirin Najeriya a Yau zai tattauna kan abubuwan da suka kamata ku sani game da...
Me Doka Ta Ce Idan Mutum Bai Iya Rera Taken Najeriya Ba? 16.08.2024 24:06
Send us Fan Mail Bayan cece-ku-cen da aka yi ta yi game da wani kuduri da majalisa ta so gabatar wa domin hukunta wadanda suka kasa rera taken Najeriya, an jingine batun. Shin wane hurumi taken Najeriya ke da shi a cikin dokar kasa? Abin da shirin Najeriya a Yau zai tattauna a kai kenan.
Shin Matasa Sun Shirya Karbar Ragamar Shugabanci A Najeriya? 15.08.2024 21:12
Send us Fan Mail Matasa na ta hankoron a ba su dama domin su jagoranci shugabanci da dora shugabanni na gari. Sai dai wasu na ta diga ayar tambaya ko matasan za su iya tabuka abin kirki ba tare da sun bayar da kunya ba. Shirin Najeriya a Yau ya tattauna kan yiwuwar matasan na iya yin abin da ya dace.
Dabarun Fara Kananan Sana’o’i A Najeriya 13.08.2024 24:03
Send us Fan Mail Wata babbar matsala da ke yawan kashe sana’o’i musamman kanana da matsakaita ita ce ta rashin sanin makamar sana’ar kafin shigarta. Shin me ya kamata masu sana’o’in su sani domin tsaya wa daram a kowane hali? Shirin Najeriya a Yau zai tattauna kan abubuwan da ya kamata masu sana’o’in hannu su rike da kyau domin dorewar sana'arsu duk da irin matsin tattalin arzikin da ake ciki...
Wane Sauyi Zanga-Zangar Tsadar Rayuwa Ta Kawo? 12.08.2024 14:44
Send us Fan Mail Kwana 10 masu zanga-zanga tsadar rayuwa suka ware a fadin Najeriya. Sai dai a wasu wuraren ba ta wuce tsawon kwanaki biyu zuwa uku ba Shirin Najeriya a Yau zai yi fashin baki kan abin da zanga-zangar ta haifar a Najeriya.
Abin Da Ya Kamata Ku Sani Kafin Siyan Hannu Jari A Banki 09.08.2024 24:19
Send us Fan Mail A ‘yan kwanakin nan bankuna da kansu suke bukatar mutanr su zo don zuba hannun jari ko da kudi kalilan ne. Masana hada-hadar kudi na ganin zuba jari a fannin na da tasiri kuma ana iya a girbar abin da aka shuka idan an dace Shirin Najeriya a Yau ya tattauna game da wasu mahimman abubuwa da suka kamata ku sani idan kuka yi kudurin siyan hannun jari a bankuna.
Tasirin Fitattun ‘Yan Soshiyal Midiya Wajen Sauya Ra’ayin Al’umma 08.08.2024 21:15
Send us Fan Mail A duk lokacin da wani maudu’i ke tashe a soshiyal midiya a kan samu wasu fitattaun mutane a shafukan da ke tsokaci a kai Irin wadannan mutane su ake kira influencers a turance, kuma suna tsokaci kan batutuwan da mutane tattauna wa. Shirin Najeriya a Yau zai tattauna kan yadda fitattun masu amfani da shafukan sada zumunta ke tasiri ga rayuwar al’umma.
Yadda Zanga-Zanga Ke Durkusar Da Sana’o’i Da Tattalin Arziki 06.08.2024 23:32
Send us Fan Mail Wasu jihohi an sanya dokar hana fita yayin da ake ci gaba da zanga-zanga a Najeriya. Masu sana’o’i na ci gaba da korafin yadda hakan ke durkusar da sana’o’insu. Shirin Najeriya a Yau zai yi nazari akan tasirin zanga-zanga ga sana’o’i da tattalin arziki.
'Abin Da Ya Sa 'Yan Najeriya Ba Su Gamsu Da Jawabin Tinubu Ba' 05.08.2024 23:14
Send us Fan Mail Ana ci gaba da bayyana mabanbantan ra’ayoyi tun bayan jawabin shugaba Tinubu kan tsadar rayuwa. Wasu na ganin kamar bai tabo inda yake musu kaikayi ba, musamman game da batun nan na tallafin man fetur. Shirin Najeriya a Yau zai yi sharhi kan abin da ya sa ‘yan kasar ba su gamsu da jawaban shugaban ba.
Kuskuren Da Gwamnati Ta Yi Har Aka Fara Zanga-Zanga 02.08.2024 23:12
Send us Fan Mail Yadda zanga-zangar tsadar rayuwa ke gudana a Najeriya na cigaba da daukan hankali al'umma. Ana ganin wasu lamuran ba su tafi daidai ba saboda matakan da aka yi ta dauka ba su yi tasiri ba. Shirin Najeriya a Yau ya yi sharhi ne kan abin da gwamnati ta yi sakaci da shi har mutane suka kai ga yi ma ta zanga-zanga.
A Ina Shinkafar Gwmanatin Tarayya Ta 40,000 Ta Maƙale? 01.08.2024 15:36
Send us Fan Mail Mutane na ta tambaya inda shinkafar nan da gwamnatin tarayya ta ce a siyar ga yan kasa kan Naira 40,000 take. Shin ya ake ciki game da shinkafar yayin da wasu gwamnonin jihohi ke cewa har yanzu ba a basu wannan shinkafar mai tallafin ba. Shirin Najeriya a Yau ya tattauna kan wannan batu.
Yadda Sabon Mafi Karancin Albashi Zai Iya Daidaita Al’amura 30.07.2024 18:18
Send us Fan Mail Shugabann Kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan sabon mafi karancin albashi na Naira 70,000. Yayin da ma’aikata ke ganin za su fara shagali, a gefe guda wasu masu kamfanonin da ‘yan kasuwa na ganin kamar an dora musu nauyin da ya fi karfinsu. Shirin Najeriya a Yau ya tattauna kan sauyin da za a iya samu saboda sabon albashin.
Dalilin Takaddama Kan Rushe Hukumomin Raya Biranen Kaduna 26.07.2024 21:46
Send us Fan Mail Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta soke dokar da ta kirkiri hukumomin raya wasu biranen jihar uku. Wannan mataki dai ya haifar da zazzafar muhawarar a kan nasabarsa da nuna yatsa da ake yi a tsakanin gwamnati mai ci da wadda ta gada. Shirin Najeriya a Yau zai binciki dalilin daukar wannan mataki da yadda zai shafi ci gaban kananan hukumomin da abin ya shafa.
Shin Zanga-Zanga Na Tasiri A Najeriya? 25.07.2024 22:27
Send us Fan Mail A lokuta da dama idan ran ‘yan kasa ya baci su kan dauki matakin nuna fushinsu ga gwamnati ta hanyar zanga-zanga. Ana yawan kokwantn shin zanga-zangar da ake gudanarwa a Najeriya suna haifar da ɗa mai ido? Ta wace hanya zanga-zanga ta zama silar samar da maslaha? Ku biyo mu cikin Shirin Najeriya a yau.
Abin Da Masu Zuba Jari Suke Gudu Daga Najeriya 23.07.2024 22:15
Send us Fan Mail Masana na nuna fargaba game da rashin tabbas a harkar zuba jari a Najeriya. Tun a watannin da suka gabata ake ta samun ficewar manyan kamfanoni daga kasar, lamarin da ake alakantawa da wasu tsare-tsaren tattalin arziki. Shirin Najeriya a yau zai tattauna kan yadda hakan zai ci gaba da tasiri a kan tattalin arzikin Najeriya.
Alaƙar Da Ke Tsakanin Masu Haƙar Ma’adanai Da ‘Yan Bindiga 22.07.2024 25:45
Send us Fan Mail Jihohin Zamfara da Neja a Arewacin Najeriya na cikin jihohin da ke fuskantar kalubalen tsaro duk da tarin ma’adanai da suke da su. Sai dai duk da zafin hare-haren da ake samu a wadannan jihohi aikin hakar ma’adanai na ci gaba kamar yadda aka saba. Shin wace alaka ke tsakanin masu hakar ma’adanai da ‘yan bindiga? Wani binciken da Daily Trust ta gudanar ya gano haka, kamar yadda za...
‘Yadda APC Ke Kokarin Rufe Bakin Masu Sukar Gwamnati’ 19.07.2024 26:22
Send us Fan Mail Ana musayar yawu kan ’yancin ’yan kasa na fadin albarkacin bakinsu game da manufofin gwamnati mai ci. ’Yan adawa na zargin jam’iyar APC mai mulki da kokarin rufe bakin masu yi mata gyara a inda ta yi kuskure. Shirin Najeriya a yau zai tattauna ne a kan abin da ya sa hakan yake faruwa.
Me Ya Sa Gwamnoni Ke Rige-Rigen Yin Zaben Kananan Hukumomi? 18.07.2024 22:07
Send us Fan Mail Gwamnoni da dama a Najeriya sun bayyana aniyarsu ta gudanar da zabukan kananan hukumomi kafin karshen wannan shekarar. Zuwa yanzu jihohi 13 aka lissafa za su gudanar da zabubbukan, lamarin da wasu ke alakantawa da hukuncin Kotun Koli da ya bai wa kananan hukumomin ’yancin cin gashin kai. Shirin Najeriya a yau zai yi bincike ne don gano gaskiyar wannan lamari.
Abin Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Azumin Tasu’a Da Ashura 16.07.2024 14:59
Send us Fan Mail A yau ne ake kammala azumin Tasu'a da Ashura, wato na kwanakin Tara da Goma cikin watan farko na kalandar Musulunci da Musulmai ke yi. Azumi ne da ake yi cikin watan Muharram, wanda malamai ke cewa yana daya daga cikin watanni hudu mafiya Alfarma a shekarar Musulunci. Shirin Najeriya a Yau ya duba yadda ake azumin Tasu'a da Ashura da muhimmancin shi ga rayuwar Musulmai.
Yadda Matasa Za Su Gina Rayuwarsu Da Ta Al’umma 15.07.2024 19:13
Send us Fan Mail Yau ce Ranar Matasa Masu Sana’a ta Duniya. A wannan shekarar Majalisar Dinkin Duniya, wadda ta ayyana wannan rana, tana son a yi amfani da basirar matasa wajen samar da zaman lafiya da ci gaba. Shirin Najeriya a Yau zai duba yadda wanann buri zai cika.
Wane Sauyi 'Yancin Cin Gashin Kai Zai Kawo A Kananan Hukumomi? 12.07.2024 27:34
Send us Fan Mail Hukuncin kotun koli kan ikon kananan hukumomi ya jefa su cikin farin ciki a fadin Najeriya. Sai dai yanzu abin da ake son ganin ya faru shi ne yaushe wannan tsari zai yi tasiri kuma me ya rage ga kananan hukumomi. Shirin Najeriya a Yau ya yi fashin bakin kan abin da hukuncin ya kunsa da mataki na gaba ga kanana hukumomi.
Rayuwar Sheikh Dahiru Bauchi Cikin Ƙarni Guda 11.07.2024 21:29
Send us Fan Mail A wannan makon babban malamin Addinin Musulunci Sheikh Dahiru Usman ya samu ni’imar cika shekara 100 a duniya. Malamai da mabiya da al’umma sun jinjina yadda ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidima ga Addini. Shirin Najeriya a Yau zai yi nazari a kan gudummuwar da Shehin Malamin ya bayar a cikin shekara fiye da 70 da ya yi yana karantar da Al-Kur’ani.
Similar podcasts
Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.