Najeriya a Yau

News HA ↓ 958 episodes

Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.

Category

News

Podcast website

www.buzzsprout.com

Latest episode

Jun 23, 2026

Where to listen?

Podcasts in the app Replaio Radio Coming soon

Podcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts

Get it on Google Play Install for free Android 5M+ downloads · 4.8 rating iOS soon

Episodes

Gaskiyar Magana Kan Bullar Kungiyar Luwadi Da Madigo A Kano 09.07.2024

Send us Fan Mail Labarin bullar wata kungiyar da ake zargin tana rajin yada akidar auren jinsi a Kano na ci gaba da yamusta hazo. Tuni hukumomi suka bayyana matakin da za su dauka a kan wadannan zarge-zarge duk da yake sun amince cewa sun taba ganawa da kungiyar. Shirin Najeriya a Yau zai bincika yadda aka yi ana zaton wuta a makera, ta tashi a masaka.

Dalilin Dawowar Layukan Mai A Najeriya 08.07.2024

Send us Fan Mail Jihohi da dama a wannan lokaci sun fada cikin yanayin dogayen layukan mai da kuma karancinsa. Wasu gidajen mai sun kasance a kulle yayin da masu siyarwar kuma farashin sai wanda ya gani, baya ga ‘yan bumburutu da ke cin kasuwarsu a bayan fage. Shirin Najeriya a Yau domin jin dalilin wahalar mai a Najeriya

Abin Da Ya Sa Ake Ƙara Wa ‘Yan Band A Kuɗin Wutar Lantarki 05.07.2024

Send us Fan Mail Zuwa yanzu masu shan wutar lantarki da ke tsarin Band A sun samu sanarwar kara kudin wutar lantarki Sai dai wasu na ganin ba a iya biyan bukatun da wannan kari ba zai samu muhalli ba  Shirin Najeriya a Yau zai tattauna ne kan Dalilin da ya sa ake kara wa masu tsarin Band A kudin lantarki a kai a ka i.

Abin Da Dokar Ta-Baci Kan Man Fetur Ke Nufi 04.07.2024

Send us Fan Mail Ana ta musayar ra’ayin bayan da Kamfanin man fetur na kasa NNPCL ya ayyana dokar ta-ɓaci kan harkokin haƙowa da kuma fitar da ɗanyen mai daga ƙasar. Mutane na neman amsar shin me hakan ke nufi, da muhawarar ko hakan abu mai yiwuwa ne? Shirin Najeriya a Yau nzai tattauna kan abin da dokar ta baci kan man fetur ke nufi.

Hanyoyin Magance Kuncin Da ‘Yan Najeriya Suke Ciki 02.07.2024

Send us Fan Mail Ana ci gaba da samun koke-koke game da yadda ‘yan kasa ke ji a jikinsu. Masana dai na ganin akwai matakan da in har gwamnati ta dauke su za a iya  kawar da matsin tattalin arzikin da ta yi wa talaka dabaibayi. Shirin Najeriya a Yau zai tattauna kan matakan gaggawa da suka kamata gwamnati ta dauka domin kaiwa share hawayen ‘yan kasa.

Abin Da Ke Sa Mutum Ya Fara Tunanin Kashe Kansa 01.07.2024

Send us Fan Mail A ‘yan kwanakin nan ana samun rahotannin yadda mutane suke kashe kansu. Wasu dai suna alakanta hakan ne da tsananin damuwa ko matsin rayuwa. Shirin Najeriya a Yau zai yi duba na tsanaki don tantance yadda lamarin yake.

Dalilin Da ’Yan Najeriya Ba Su Tsaftace Muhalli 28.06.2024

Send us Fan Mail Masu fafutukar kare muhalli suna cewa yadda ’yan Najeriya suke shakulatin bangaro da tsaftar muhalli abin damuwa ne. Yayin da ake bikin Ranar Kula Da Tsaftar Muhalli Ta Kasa a yau, shirin Najeriya a Yau zai tattauna a kan halin da Najeriya ke ciki da abin da hukumomi suke yi game da tsaftar muhalli.

Kimar Sarakunan Gargajiya A Idon Al’ummar Arewa 27.06.2024

Send us Fan Mail A baya-bayan nan ana samun muhawara, wani lokaci ma zazzafa, a kan kimar masarautun gargajiya. Shin yaya al’umma ke kallon sarakunan gargajiya a halin yanzu? Shirin Najeriya a Yau zai tattauna a kan kimar masu rike da masautun gargajiya a wannan zamani.

'Taron Tsaro Zai Samar Da Zaman Lafiya a Arewa Maso Yamma' 25.06.2024

Send us Fan Mail Gwamnonin Arewa maso yamma suna wani babban a taron tsaro da nufin lalubo hanyar kawar da matsalar tsaro a yankin. Hukumar Raya Kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya ce ta shirya taron da hadin gwiwar Kungiyar Gwamnonin Arewa maso Yamma domin hada kan gwamnatocin yankin. Shin ta wace hanya gwamnonin za su iya cimma wannan buri? Ku biyo mu a cikin shirin Shirin Najeriya a Yau

Alamomin Da Suke Nuna Alhaji Ya Yi Hajji Karɓaɓɓe 24.06.2024

Send us Fan Mail Yayin da aka kammala aikin Hajjin bana ana sa ran duk wanda ya je kasa mai tsarki ya yi Hajji karbabbe. Amma ko akwai wasu alamomin da suke nuna cewa Hajjin mutum ya karbu?  Shirin Najeriya a Yau na dauke da karin bayani.

Yadda Za Ku Fahimci Shari’ar Masarautun Kano Dalla-Dalla 21.06.2024

Send us Fan Mail Masu bibiyar tirka-tirkar masarautun Kano na ci gaba da shiga ruɗani bayan hukuncin Babbar Kotun Tarayya. Ko wane bangare na murnar shi ne yake da nasara, lamarin da ya sa mutane tambayar shin wane ne Sarki? Don fahimtar inda wannan hukuncin ya dosa, ku biyo mu cikin shirin Najeriya a Yau.

Shin Ko Kalaman Kwankwaso Sun Kaɗa Hantar APC Ne? 20.06.2024

Send us Fan Mail Wasu kalaman da jagoran Kwankwasiyya Rabi’u Musa Kwankwaso ya furta yana zargin Gwamnatin Tarayya suna ci gaba da tayar da kura. Fadar shugaban kasa da jam’iyyar APC a matakin kasa da jihar Kano sun yi kakkausan suka da kiran a yi maza-maza a kama shi. Shin me ya girgiza Jam’iyyar ta APC game da wadannan kalamai?  Shirin Najeriya a Yau zai tattauna kan wannan turka-turka.

Abubuwan Da Ya Kamata A Yi Don Kawo Karshen Tsadar Abinci 18.06.2024

Send us Fan Mail A kullum farashin kayan abinci kara tashi yake yi a Najeriya. Masu sharhi kuma suna ta kokarin bayar da shawarwari a kan hanyoyin fita daga wannan yanayi. Shirin Najeriya a Yau zai tattauna kan wadannan hanyoyi da tasirin da za su iya yi.

Hadarin Da Ke Tattare Da Cin Naman Layya Fiye Da Kima 17.06.2024

Send us Fan Mail Wuce gona da iri wajen cin nama ka iya rikita cikin mutum ya yi ta zarya a banɗaki Shirin Najeriya a Yau zai tattauna da masana kan abin da ya kamata ku yi domin kauce wa gurbacewar ciki saboda cin nama

Shin Mutum Zai Iya Cinye Naman Layyarsa Shi Kadai? 14.06.2024

Send us Fan Mail A lokacin Bikin Babbar Sallah da mutane kan yi layya, ana sa ran wanda bai yi ba ma ya samu ya ci nama. Amma wasu masu karamin karfi kan bayyana yadda makwabtansu da suka yi layya sukan shige da namansu gida su yi tuwo-na-mai-na. Shirin Najeriya a Yau zai duba halalcin yin hakan a Musulunce.

'Kananan Hukumomi Na Daf Da Zama Mabarata' 13.06.2024

Send us Fan Mail Gwamnatocin Kananan Hukumomi sun koka cewa za a dora musu nauyi idan har aka amince da N62,000 a matsayin mafi karancin albashi. Sai dai ma’aikatansu na ganin ba su dalilin fadin hakan, ganin yadda suka samu ninkin kudaden shiga bayan cire tallafin man fetur. Ku biyo mu cikin Shirin Najeriya a Yau domin jin yadda za a warware wannan takaddama.

Yadda Gurɓacewar Iska Ke Shafar Rayuwar ‘Yan Najeriya 11.06.2024

Send us Fan Mail Gurbacewar iska na ci gaba da jan hankalin masu ruwa da tsaki a duniya. Hukumomi sun ce ‘yan Najeriya na amfani da wasu abubuwa da ke bayar da gudummuwa wajen gurbacewar iskar da muke shaka da barazana ga lafiyar dan adam. Shin ya girmar matsalar take a Najeriya? Shirin Najeriya a Yau ya tattauna kan wannan batu.

Abin Da Ya Sa Tamowa Ke Nema Ta Gagari Kundila A Arewa 10.06.2024

Send us Fan Mail Kiraye-kiraye na karuwa game da matakin da ya kamata a dauka don dakile matsalar karancin abinci mai gina jiki wato tamowa a jikin kanan yara Kungiyar likitoci ta 'Doctors Without Borders' ta ce an samu ƙaruwar yara masu fama da tamowa a jihohi 11 da ke arewacin Najeriya. Shirin Najeriya a Yau zai duba matakan da za ya kamata a dauka don kare kai daga kamuwa da tamowa.

Me Manoma Suka Shirya Wa Daminar Bana? 07.06.2024

Send us Fan Mail A yayin da damina ta fara kankama a wasu sassan Najeriya, fatan manoma shi ne samun yabanya mai kyau. Akwai matakan da masana ke ganin ya kamata manoma su dauka duk a lokacin da ruwa ya fara sauka domin kauce wa lalacewar amfanin gona. Shirin Najeriya a Yau ya tattauna kan matakan da suka kamata manoma za su dauka a wannan yanayi.

Mafi Karancin Albashi: Shin Me Ma’aikata Suke Fatan Samu? 06.06.2024

Send us Fan Mail Yayin da muhawara ta yi zafi a kan mafi ƙarancin albashi, inda kungiyoyin kwadago ke bukatar a biya Naira 494,000, wasu kamfanoni da gwamnati kuma suke ganin a yi karin da hankali zai dauka, me ma’aikata da kansu suke ganin ya fi dacewa?  Shirin Najeriya a Yau zai duba wannan domin an ce mai daki shi ya san inda yake yi mishi yoyo.

Yadda Yajin Aiki Ke Durkusar Da Sana’o’i 04.06.2024

Send us Fan Mail A duk lokacin da ’yan kwadago suka tsunduma yajin aiki ana cewa suna kassara tattalin arziki. Shirin Najeriya a Yau zai tattauna a kan yadda yajin aiki yake shafar rayuwar al’umma.

Dalilin Ƙarancin Tumatur Da Sauran Kayan Miya 03.06.2024

Send us Fan Mail Farashin kayan miya, musamman tumatur, ya yi tashin gwauron zabo a kasuwanni. Lamarin dai ya sa wasu komawa sayen busasshen tumatur domin yin girki. To shin me ya sa ake samun karanci da tsadar tumatur da sauran kayan miya? Shirin Najeriya a Yau ya ziyarci wasu kasuwanni don jin dalili.

Yadda Aka Shekara 25 Ana Yi Wa Ɓangaren Shari’a Hawan Ƙawara 31.05.2024

Send us Fan Mail Bangaren shari’a yana cikin ginshikai uku na mulkin dimokradiyya. A cikin shekara 25 da aka yi ana mulkin dimokradiyya ba tare da katsewa ba wannan bangare ya fuskanci kalubale da dama. Shirin Najeriya a Yau ya yi duba a kan wannan lamari.

Yadda Dawo Da Tsohon Taken Ƙasa Zai Mayar Da Najeriya Baya 30.05.2024

Send us Fan Mail Dawo da tsohon taken Najeriya da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi na shan yabo da suka. Mutane da dama dai na cewa a yanzu talakan Najeriya ba abin da yake bukata ba ke nan. Shirin Najeriya a Yau zai duba alfanun dawo da taken da muhimmancinsa a mizanin bukatun ’yan Najeriya. 

Matakan Kauce Wa Yaɗuwar Cututtuka Da Damina 28.05.2024

Send us Fan Mail A yankuna da dama an fara samun ruwan sama, duk da cewa damina ba ta yi karfi ba a wasu wuraren. Bayanai sun nuna cewa a irin wannan lokaci Kwalara ko amai da gudawa da Maleriya da Thypoid da dai sauransu na cikin cututtukan da ke saurin yaduwa. Shirin Najeriya a Yau zai tattauna a kan wasu daga cikin waɗannan cututtuka da matakan kauce musu.

Listen to the Najeriya a Yau podcast in Replaio

Radio and podcasts in one app - free, with no sign-up. Install today and do not miss the launch

Get it on Google Play

Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.