Najeriya a Yau

News HA ↓ 958 episodes

Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.

Category

News

Podcast website

www.buzzsprout.com

Latest episode

Jun 23, 2026

Where to listen?

Podcasts in the app Replaio Radio Coming soon

Podcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts

Get it on Google Play Install for free Android 5M+ downloads · 4.8 rating iOS soon

Episodes

Abin Da Ya Haddasa Dambarwar Sarauta A Kano 27.05.2024

Send us Fan Mail A ‘yan shekarun da suka gabata tsohon gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya sanya hannu a kan wata doka da ta karkasa Masarautar Kano gida biyar, daga bisani kuma ya tsige sarkin Kano na 14 bisa zargin aikata ba daidai ba da rashin da’a. Yanzu kuma gashi shekaru hudu bayan hakan, gwamnan Kano na yanzu Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata dokar da ta soke wadancan matakan da...

Abu Na Gaba Da Zai Faru Da Sarakunan Kano Da Aka Tuɓe 24.05.2024

Send us Fan Mail Batun  cire sarakun da aka faro ta kamar wasa ga shi ta tabbata. Sarki Sanusi shi ne sarkin da ya sake dawowa bayan tube sarakuna biyar na jihar, lamarin da za a iya cewa wasu sun yi hasashen hakan tun da fari. Shin mene  ne mataki  na gaba da ya rage wa sarakunan? Ya alaka za ta kasance tsakanin wadanna gidajen sarautar. Shirin Najeriya a Yau ya tattauna kan wannan batu.

Shin Ganawar Atiku Da Obi Na Kaɗa Hantar APC? 23.05.2024

Send us Fan Mail Alkiblar siyasa da ke kaɗawa daga ɓangaren ‘yan adawa ta fara daukar hankalin jam’iya mai mulki. Yawaitar ganawar da aka hangi wasu jiga-jigan adawa na yi ta sa ana diga ayar tambaya me ke shirin faruwa, lamarin da jam’iyar APC ta ce 'yan Najeriya za su bude idanunsu kada su yarda da irin mutanen da tace suna kasuwar bukata. Toh shin wannan ganawa na rikita APC ne? Shirin Naj...

Tasirin Auna Hauhawar Farashi A Rayuwar Talaka 21.05.2024

Send us Fan Mail Wata kalma da ’yan Najeriya ke yawan ji ita ce ƙimar hauhawar farashi, wato ‘Inflation rate’ a turance.  Sai dai kuma ba kowa ne ya fahimci abin da Kalmar take nufi ba, balle ya san yadda ake auna hauhawar farashin. Shin ta yaya yan kasa za su gane tasirin hakan a rayuwarsu ta yau da kullum? Shirin Najeriya a Yau zai yi kokarin amsa muku wadaannan tambayoyi. Ku biyo mu

Yadda Za Ku Ceto Yaron Da Ya Kamu Da Jijjiga 20.05.2024

Send us Fan Mail Shin kun taba cin karo da yara masu jijjiga? wani yanayi ne da larurar kwakwalwa ko kasancewar guba a cikin jinni kan haifar wa manya, zazzabi mai tsanani kuma kan haifar wa yara. Yanayin kan sa yaro ya shiga yanayin sarkewar gabobin jiki da numfashi kamar dai mai farfadiya a wasu lokutan. Shirin Najeriya a Yau na dauke labarin wata matar da irin hakan ya faru ga 'yarta har m...

Yadda Za Ka Ɗauki Mataki Idan Aka Ɓata Maka Suna Saboda Cin Bashi 17.05.2024

Send us Fan Mail A wannan zamani da mutum zai iya samun bashi kaitsaye ta waya daga manhajoji daban-daban amma idan mutum ya kasa biya kamfanonin bada bashin kan aika sakonnin cin zarafi da barazana har ga ‘yan uwan wanda ya ci. Duk da gargadin da hukumomi mutane da dama na kukan ana ɓata musu suna, kuma an kasa kulle irin wadannan manhajoji kamar yadda aka ce. Shirin Najeriya a Yau ya tattauna ka...

Dalilin Da Ba Za A Biya Wasu Ma’aikata Albashinsu Ba 16.05.2024

Send us Fan Mail Gwamnatin tarayyar ta ce za a ɓullo da tsarin auna ƙwazon ma’aikata bisa mizani ta yadda dagewar ma’aikaci zai sa ya samu ƙarin girma ko albashin ma zai iya bambanta, wato dai iya kwazonka iya albashinka. Irin wannan yunkuri na gwamnatin tuni ma’aikata da ‘yan kwadago suka fara suka da tunanin wata manufa ce ta kauda hankali. Toh ko ta fannin shari’a hakan na da tasiri wajen hakki...

Abin Da Ya Sa Masu Gidajen Haya Suke Tsuga Kuɗi 14.05.2024

Send us Fan Mail A baya-bayan nan mazauna manyan biranen Najeriya na ta kokawa game da yadda masu gidajen haya ke neman mai da su saniyar tatsa  wajen tsuga kudin haya. Sai dai masu gidajen na cewa ana fama da tsadar rayuwa kuma kula da irin wadannan gidaje na cin kudi sosai. Shirin Najeriya a Yau ya yi nazari kan  yadda lamarin ke shafar rayuwar mutanen da  suke zaune a gidajen haya.

Gwamnatin Zamfara Ta Sa Zare Da Ta Tarayya Kan Yaƙi Da ’Yan Bindiga 13.05.2024

Send us Fan Mail Takaddama a tsakanin gwamantin Tarayya da ta jihar Zamfara a kan hanyar da ya kamata a bi don kawo karshen matsalar tsaro na neman yin kafar ungulu ga yunkurin kawar da barazanar ’yan bindiga. Gwamnatin Jihar ta Zamfara dai ta sa kafa ta shure duk wani yunkuri na sasantawa da ‘yan bindiga tana mai cewa ba da ita ba, sannan ta zargi gwamnatin Tarayya da hawa teburin shawarwari da ‘...

‘An Yafe Wa Masu PoS Biyan Harajin Yin Rijista Da CAC’ 10.05.2024

Send us Fan Mail Ga alama nan ba da dadewa ba yanayin sana’ar POS a kasar nan zai sauya.  Babban Bankin Najeriya (CBN) ya wajabta wa masu wannan sana’a yin rajista da Hukumar Rajistar Kamfanoni da Kungiyoyi (CAC) zuwa nan da 7 ga watan Yulin 2024. To amma ya batun harajin da suke korafi a kai? Ku biyo mu a Shirin Najeriya a Yau don jin matsayar CAC game da biyan kudin.

'Za Mu Ɗaure Duk Wanda Bai Yi Gwajin Jini Kafin Aure Ba' 09.05.2024

Send us Fan Mail Sabuwar dokar da gwamnatin jihar Kano ta sanyawa hannu kan yin gwajin lafiya kafin aure na shan yabo da suka. A cewar gwamnatin, yawaitar yaduwar cututuka a tsakanin ma’aurata bayan aure shi ne makasudin yin wannan doka. Amma me ya sa za a daure wanda ya taka dokar tsawon shekara 5 ko tarar 500,000? Idan aka samu wanda ya taka dokar miji za a daure ko mata ko madaurin auren? Shiri...

Abun Da Za A Fara Lura Kafin Shiga Tasi A Abuja 07.05.2024

Send us Fan Mail Yanayin da ake ciki na tsadar rayuwa ne ya sa kowa ya koma neman kudi da mota don daukar fasinjan a Abuja. Sai dai hukumomi sun ce an dauki matakin hana duk wani mutum da bai cika ka'idojin yin tasi ba. Shirin Najeriya a Yau ya duba dalilan da suka sa hukumomi ke shirin tabbatar da halascin yin kabu-kabun ga masu zaman kansu ba tare da sun yi fentin ba.

Ɓarkewar Cutar Ƙyanda: Sakaci Ko Annoba? 06.05.2024

Send us Fan Mail A karshen shekarar 2023 ne dai, hukumar Lafiya ta Duniya WHO da Cibiyar hana yaduwar cututtuka suka yi gargadi cewa cutar kyanda na ci gaba da zama barazana ga yara a Najeriya. Sai ga shi kwatsam an samu rahotanni game da barkewar cutar a wasu yankunan Naijeriya har ta kashe wasu mutane da dama. Shirin Najeriya a Yau ya mayar da hankali ne kan cutar ta kyanda, da yadda za ku kare...

Dalilan Da Ake Yi Wa Mutum Kutse A Soshiyal Midiya 03.05.2024

Send us Fan Mail Masu amfani da shafukan sada zumunta kan fada hannun masu dandantsa inda sukan yi kutse a shafin mutum har ya rasa iko da shi. Kwararru sun ce ana yi wa wasu hakan domin bata suna ko kuma neman kudi da damfara. Shirin Najeriya a Yau ya tattauna da kwararru a fannin samar da matakan tsaro a soshiyal midiya game da dabarun inganta tsaron shafukanku.

“Tabbas Muna Biyan Ma’aikatan Borno Albashin N7,000, Amma...” 02.05.2024

Send us Fan Mail Shafukan sada zumunta na ta girgiza bayan da wani labari ya bayyana game da yanayin walwalar ma’aikata da albashinsu a jihar Borno. Ma’aikata da dama sun yi ta yada hoton albashinsu na N7,000; wasu N8,000 ko N13,000 ko N15,000 ga ma’aikatan lafiya. Shirin Najeriya a Yau ya gano gaskiyar abin da ya sa gwamnatin jihar Borno ke biyan irin wannan albashi da wasu suka ce bai taka kara...

Yadda Wahalar Fetur Ke Jigata ’Yan Najeriya 30.04.2024

Send us Fan Mail Karancin man fetur na neman tsayar da al'amura cak ga al'umma a wasu sassan Najeriya. Da dama sun ce lamarin ya shafe su kaitsaye kuma sakamakon haka suna dandana kudarsu. Shin yaushe wannan lamari zai zo karshe, musamman idan yi la’akari da cewa tun a  Kamafanin Mai Na Kasa (NNPC) ya ce ya maganace matsalar? A shirin Najeriya a Yau mun tattauna da wadanda abin ya shafa...

Abin Da Ya Sa Gwamnonin Arewa Suka Je Amurka Taron Tsaro 29.04.2024

Send us Fan Mail Gwamnonin Arewacin Najeriya da ake fuskantar kalubalen tsaro na kokarin lalubo ko ta wace hanya a samu dabarar dakile matsalar. Tafiyar  gwamnoni 9 daga arewacin Najeriya zuwa Amurka a kwanan nan domin halartar taron tsaro ya nuna yadda suke kokarin daidaita lamarin har a matakin kasashen ketare. Saidai lamarin na zuwa ne a lokacin da wasu ke ganin an yi makamancinsa a Najeriya ba...

Dalilin Da Fasfo Ya Zama Wajibi Ga Ɗanƙasa Ko Ba Don Tafiya Ba 26.04.2024

Send us Fan Mail Shin ka taba tunanin damammakin da za ka iya rasawa saboda rashin mallakar fasfon dan kasa a Najeriya? Yawancin mutane basu maida hankali wajen mallakar fasfo domin a tunaninsu sai idan kana kokarin ketare kasa ya zama wajibi a gare ka, amma kuma akwai damammaki da za ka iya rasawa saboda rashin mallamar shi. To ku biyo mu cikin Shirin Najeriya a Yau domin jin irin amfanin da mall...

Da Gaske Haƙa Rijiyoyin Burtsatse Na Haifar Da Matsala A Anguwanni? 25.04.2024

Send us Fan Mail Ana cikin matsanancin karancin ruwa a yankuna daban-daban a Najeriya. Lamarin ya sa a 'yan shekarun mutane ke ta kokarin samar da rijiyoyin burtsatse wato 'Borehole' a turance. Sai dai a cewar masana yawanci yanzu rijiyyoyi na kafewa da kuma haifar da zaizayar kasa. Shirin Najeriya a Yau ya duba yadda ko haƙa bohol-bohol zai iya haifar da matsala ga muhalli da kuma...

Me Ya Sa Ake Ɓoye Wa Mata Wasu Abubuwa Idan Za Su Yi Aure? 24.04.2024

Send us Fan Mail Akwai abubuwan da ya kamata a rika bayyana wa mata idan za su yi aure amma kunya tana hanawa. Wasu sai sun je gidan aure suke tarar da abubuwan da ya kamata ace sun sani daga magabata, amma sai dai su tsinta a wajen kawayensu. Shirin Daga Laraba ya duba dalilan da ya sa ake kin bayyanawa mata wasu mahimman abubuwan da ya kamata su sani idan za su yi aure.

Yadda Tsananin Zafi Zai Iya Cutar Da Dalibai A Makarantu 23.04.2024

Send us Fan Mail Hukumomi sun bayyana jihohin da za a samu matsanancin zafi a Najeriya. Lamarin ya zo daidai lokacin da makarantu ke komawa hutu, inda ake fargabar yiwuwar yaduwar cututtuka a azuzuwa masu cunkuso. Shin ta wace hanya makarantu za su kauce wa yaduwar cututtuka masu alaka da matsanancin zafi? Shirin Najeriya a Yau na da karin bayani

Rawar Da NNPP Ke Takawa A Dambarwar Dakatar Da Ganduje 22.04.2024

Send us Fan Mail Dambarwa ta siyasa ci gaba da daukar hankali game da dakatar da shugaban jam’iyar APC na kasa Ana ta takaddama da zargin juna tsakanin jam’iyyun siyasa musamman na Kano da gwamnati mai ci a can. Toh amma wa ke wasa da hankalin wani ko rura wutar rikicin dakatar da Ganduje a jam’iyar APC, Shirin Najeriya a Yau na da karin bayani a kai.

Dalilin Da Kotuna Ke Yanke Hukunci Mabambanta Kan Shari’a Iri Ɗaya 19.04.2024

Send us Fan Mail Ba shakka dokokin kasa iri guda ne a duk inda ake a Najeriya. Sai dai ana yawan samun kotuna da yin mabambantan matsaya kan shari’a iri guda a lokuta daban-daban. Ko me ya jawo haka? Shirin Najeriya a Yau ya duba abin da ya sa kotuna ke yanke hukunci daba-daban kan shari’a iri guda.

Me Ya Sa ‘Yan Kasuwa Suka Ƙi Karya Farashi Duk Da Karyewar Dala? 18.04.2024

Send us Fan Mail Ana ta murnar dalar Amurka na karyewa watakila a samu saukin kayan masarufi. Sai dai a ganin wasu yadda ‘yan kasuwa suke azamar tsawwala kudi idan ta tashi ba su yi hakan ba a yayin da take saukowa. Shirin Najeriya a Yau ya duba dalilin da ya zama wajibi ‘yan Kasuwa su sauke farashin kayayyaki.

Wa Ke Da Ikon Dakatar Da Ganduje A Jam’iyar APC? 16.04.2024

Send us Fan Mail An shiga saƙe-saƙe game da mutanen da suka yi ikirarin dakatar da Ganduje daga jam’iyar APC tun daga matakin mazaba. Sai dai uwar jam’iyar ta yi watsi da hakan, inda kuma daga bisani suka zargi jami’iyar adawa. To amma ko da ace za a dauki irin wannan matakin, wa ke da hurumin dakatar da shugaban jamiyar APC na kasa a dokance? Shirin Najeriya a Yau na da karin bayani.

Listen to the Najeriya a Yau podcast in Replaio

Radio and podcasts in one app - free, with no sign-up. Install today and do not miss the launch

Get it on Google Play

Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.