Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Where to listen?
Podcasts in the app Replaio Radio Coming soonPodcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts
Episodes
Idan Najeriya Ta Karbo Sabon Bashin Naira Tiriliyan 2 16.09.2021 13:44
Send us Fan Mail 'Yan Najeriya da dama na caccakar Gwamnatin Tarayya bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya aike da takarda ga Majalisar Dattawa yana neman sahalewarta ya ciyo wani sabon rance. Masu sharhi kuma na cewa ba a taba samun gwamnatin da ta ciyo bashi kamar gwamnatin nan ba. Shin mece ce hikimar karbo rancen, kuma wanne tasiri zai yi a kan rayuwar 'yan Najeriya?
Me Ake Yi Da Kudaden Harajin Da Ake Karba? 14.09.2021 14:05
Send us Fan Mail 'Yan Najeriya kan biya nau'i daban-daban na haraji kama daga harajin cinikayya zuwa ga harajin kudin shiga. 'Yan kasuwa ma kan biya kudaden haraji iri-iri, direbobi ma haka, musamman a matakin karamar hukuma. Shi me ake yi da wadannan kudade? Me ya sa mutane ba sa son biya?
Gaskiyar magana a kan maganin sanyin mara 13.09.2021 14:42
Send us Fan Mail Shaye-shayen magun gunan sanyin mara akan tituna da cushe cushen da mata kanyi na haifar da matsaloli masu girman gaske a cikin jikin dan Adam. likitoci sun bayyana irin rawar da wannan halayyar ke takawa wurin kara jefa mutane cikin tasu
'Abin Da Ya Sa Na Fasa Kashe Kaina Bayan Na Kulle Daki' 10.09.2021 14:59
Send us Fan Mail Idan aka tambayi mutane da dama - musamman matasa - ko sun taba tunanin kashe kansu, za su ce sam! Amma matasa da dama sun shiga wani yanayi wanda ya sa suka ji mutuwa ta fiye musu rayuwa. Ko me ke saka matasa sake-saken da ba shi ke nan ba? Yaya za a yi a ceto masu irin wannan mugun tunani?
NIMET Ta Yi Hasashen Sake Samun Ambaliyar Ruwa 09.09.2021 14:57
Send us Fan Mail Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NIMET) ta yi hasashen za a sake samun ruwan sama kama da bakin kwarya wanda ka iya haifar da asarar rayuka da rugujewar gidaje a jihohi 17. Toshe magudanan ruwa da shara na cikin abubuwan da ke jawo ambaliya, da ma haddasa cutar kwalara. Ku biyo mu sannu a hankali domin jin yadda wannan lamari ke shafar rayuwar al'umma.
Abin Da Ya Sa Matasa Ba Sa Rajista Don Yin Zabe 07.09.2021 14:14
Send us Fan Mail Yanzu dai saura kwana 529 a gudanar da manyan zabubbuka a Najeriya. Sai dai har yanzu matasa, wadanda su ne suka fi yawa a kasar suka kuma fi kowa babatu a kan bukatar sauyi, suna raba daya biyu wurin yankar katin zaben. Ko meye dalilansu?
Yadda Kwaya Ke Kashe Aure Da Ma'aurata 06.09.2021 14:29
Send us Fan Mail A wannan zamanin akan alakanta wasu abubuwa da ke faruwa a tsakanin ma'aurata da ta'ammali da miyagun kwayoyi. Wannan ne ya sa Shugaban Hukumar Yaki da Ta'ammali da Miyagun Kwayoyi (NDLEA), Janar Buba Marwa Mai Ritaya, ya yi kira da a rika gwajin kwayoyi kafin a yi aure. Ko wanne tasiri hakan zai yi wajen magance matsalolin aure ko hana auren rushewa?
Abin Da Ya Sa Sai Yanzu Buhari Ya Fara Sauya Ministoci 03.09.2021 14:12
Send us Fan Mail Domin sauke shirin latsa nan A karo na farko tun da ya dare karagar mulkin Najeriya, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi waje da wasu ministoci. Ko me ya sa? Me wannan mataki da ya dauke ke nufi? Kuma me zai biyo baya? Wadannan ne tambayoyin da shirin zai amsa.
Matsalar Tsaro: Wasu Gwamnoni Sun Ga Uwar Bari 02.09.2021 14:59
Send us Fan Mail Gwamnatocin jihohin Kaduna da Katsina da Neja da Zamfara sun kuduri aniyar daukar matakin bai-daya don kawo karshen matsalar tsaron da ta addabi al'ummarsu. Matakan da jihohin, wadanda suka fi fama da hare-haren 'yan bindiga, suka dauka sun hada da rufe wasu kasuwanni da hanyoyi. Shin me ya hana su daukar wannan mataki tun tuni?
CBN ya Fito Da Kudi Ta Internet 31.08.2021 15:05
Send us Fan Mail Babban Bankin Najeriya ya ayyana ranar daya ga watan Oktoban a matsayin ranar fara amfani da tsarin kudin intanet na E-Naira. Ko yaya wannan tsari yake, kuma yaya za a yi hada-hada da shi? Batun da za mu duba ke nan a cikin Shirin Ayi Sauraro Lafiya
Yadda Labaran Kanzon Kurege Ke Haifar Da Illoli Ga Al'umma 30.08.2021 14:29
Send us Fan Mail A lokuta da dama, akan dora alhakin faruwar wasu abubuwa marasa dadi a kan yada labaran kanzon kurege, musamman a kafofin sada zumunta. A baya-bayan nan ma hukumomi a Najeriya sun yi gargadin cewa wasu na yada irin wadannan labarai da nufin tayar da zaune tsaye ko rura wutar rikici. Su wane ne suke kirkirar labaran kanzon kurege, mece ce manufarsu, kuma wacce illa suke haddasawa?
Abin Da Ya Sa Tashe-Tashen Hankula Suka Ki Karewa A Najeriya 27.08.2021 23:23
Send us Fan Mail Tashe-tashen hankula sun zama tamkar jamfa a Jos a Najeriya - ana kokarin shawo kan wannan, sai wani ya barke a wani wuri. A Karamar Hukumar Jos ta Arewa ta jihar Filato ana cikin kokarin kwantar da kurar da ta taso sakamakon kisan wasu matafiya, sai ga wasu sun kai hari a kan wata al'umma inda suka kashe mutane suka kona gidaje. Shin babu hanyar kawo karshen wadannan rikice...
Yadda Daruruwan Likitoci Ke Tururuwar Barin Najeriya 26.08.2021 11:08
Send us Fan Mail A wannan makon, an ba da rahoton yadda daruruwan likitoci suka rubuta jarrabarwa don neman guraben aiki a kasashen ketare. A ranar Talata kadai an ce likitoci fiye da 500 sun yi jarrabawar da Ma’aikatar Lafiya ta Saudiya ta shirya a Abuja. Me hakan ke nufin, kuma wanne tasiri zai yi a kan bangaren kiwon lafiya a Najeriya?
Matsayin Shawarar Shugabannin Siyasa: 'Yan Najeriya Su Kare Kansu 24.08.2021 19:39
Send us Fan Mail Shugabannin siyasa a sassa da dama na Najeriya na ta kiran al’ummominsu da su tashi su kare kansu daga harin yan bindiga. Wadannan kiraye-kiraye na tayar da hankulan al’umma, domin kuwa mutane da dama na ci gaba da tambayar wai shin wadannan 'yan bindigar sun gagari hukumomin tsaro ne, ko yaya lamarin yake?
Abin da Ya Faru A Afghanistan Zai Yiwu A Najeriya? 23.08.2021 20:24
Send us Fan Mail Tun bayan da mayakan Taliban suka karbe mulki a Afghanaistan ake ta tafka muhawara a kafofin sada zumunta. A nan Najeriya, daya daga cikin batutuwan da ake tattaunawa a kai shi ne ko zai yiwu a wayi gari Boko Haram ta karbe iko? Wannan ne batun da shirin Najeriya a Yau ya tattauna a kai.
Abin Da Ya Sa Hukumomi Suka Kasa Shawo Kan Kwalara 20.08.2021 16:15
Send us Fan Mail Yayin da cutar amai da gudawa ke ci gaba da lakume rayuka cikin ruwan sanyi a jihohi sama da 22 a Najeriya, ga alama shawo kanta na nema ya gagari wasu daga cikinsu. A wannan shirin na Najeriya a Yau, za mu duba halin da ake ciki a wasu daga cikin jihohin da dalilan da suka hana kawo karshen matsalar zuwa yanzu.
Yadda Dokar Hana Fita Ta Jefa Mutanen Jos Cikin Kunci 19.08.2021 18:51
Send us Fan Mail Gwamna Simon Lalong na Jihar Filato ya sassauta dokar hana fita ta sa;o;i 24 da ya dora a kan Karamar Hukumar Jos ta Arewa tun ranar Lahadi. Daukar matakin sassauta dokar, wadda yanzu za ta fara daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe, ya biyo bayan wata ganawar bita da gwamnan ya yi da shugabannin hukumomin tsaro a jihar. Kafin sassauta dokar, shirin Najeriya a yau ya yi nazari a ka...
Yadda Sabuwar Dokar Man Fetur Za Ta Shafi Rayuwarku 17.08.2021 22:07
Send us Fan Mail Shugaba Muhammadu Buhari ya sanya wa Kudurin Dokar Harkar Man Fetur hannu bayan an kwashe shekara da shekaru ana kwan-gaba-kwan-baya.. Ana sa ran wannan Doka dai za ta sauya yadda ake gudanar da harkar man fetur a Najeriya. A Najeriya a Yau mun yi nazari a kan abin da Dokar ta kunsa da kuma yadda za ta shafi rayuwar 'yan Najeriya kai-tsaye.
Abin da Ya Biyo Bayan Kisan Wasu Matafiya A Jos 16.08.2021 17:30
Send us Fan Mail Bayan kisan gillar da aka yi wa wasu matafiya a Jos, babban birnin Jihar Filato, Gwamna Simon Lalong ya kafa dokar hana fita dare da rana a Karamar Hukumar Jos ta Arewa. Muna dauke da bayanai daga bakin makusantan wadanda aka karkashe da sauran masu ruwa da tsaki. A yi sauraro lafiya.
Ambaliya Ta Tafi Da Hanyar Jirgin Kasa Daga Legas Zuwa Kano 13.08.2021 15:39
Send us Fan Mail Ruwan sama ya lalata hanyar jirgin kasa a kudu maso yammacin Najeriya, lamarin da ya tilasta jinkirta farfado da zirga-zirgar jirgin kasa daga Legas zuwa Kano. A da dai da yammacin ranar Juma'a aka shirya dawowar zirga-zirgar. Shirin Najeriya a Yau ya duba wannan lamari da ma muhimamncin dawo da sufurin jiragen kasar ga al'ummar Najeriya.
Bankin Duniya Na Bin Ko Wanne Dan Najeriya N24,000 12.08.2021 11:13
Send us Fan Mail Bankin Duniya ya ce Najeriya ce ta biyar a jerin kasashen da bashi ya yiwa katutu. Sai dai kuma gwamnati da ma wasu masana sun ce in dai an zuba kudin a abubuwan da za su amfani al'umma, ba matsala.
Za A Dauki Tsauraran Matakai A Kan Direbobin Manyan Motoci 10.08.2021 16:43
Send us Fan Mail A ’yan kwanakin nan an samu karuwa a rahotannin hadurran mota a kan hanyoyin Najeriya. Wasu daga cikin hadurran kuma direbobin tanka ake zargi da haddasa su. Mai yiwuwa wannan ne ya sa Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa ta kuduri aniyar daukar tsauraran matakai a kan su. Shirin Najeriya a Yau ya yi nazari a kan matakan da ma zarge-zargen da ake yi cewa direbobin na tukin gangance.
Ana Laluben Hanyar Sa Yara Miliyan 10 A Makaranta A Najeriya 09.08.2021 15:21
Send us Fan Mail Wata gidauniyar kasa-da-kasa mai cibiya a kasar Birtaniya ta ce za ta hada gwiwa da gwamnatin Najeriya don shawo kan manyan matsalolin da ke hana yara miliyan 10.19 zuwa makaranta a kasar. Bayanai sun tabbatar da cewa a kasashen nahiyar Afirka Kudu da Sahara, Najeriya ta fi yawan yaran da ba sa zuwa makaranta. A shirin Najeriya a Yau mun yi nazari a kan wannan matsala da yadda...
Abin Da Ke Saka 'Yan Najeriya Shakku Game Da COVID-19 06.08.2021 14:22
Send us Fan Mail Alkaluman da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta fitar ranar Alhamis sun nuna cewa a ranar 4 ga watan Agusta kadai mutane fiye da 700 aka tabbatar sun kamu da COVID-10. Sai dai 'yan Najeriya masu yawa ba su yarda da cewa akwai cutar ba, ballantana su dauki matakan kare kansu da sauran jama'a.
Yadda Jam'iyyar PDP Ta Fada Tsaka Mai Wuya 05.08.2021 14:52
Send us Fan Mail Ranar Alhamis 5 ga watan Agusta Kwamitin Amintattu na PDP zai yi wani taro a Abuja don bitar guguwar da ke neman kai babbar jam'iyyar adawar ta Najeriya kasa. Taron dai ya biyo bayan ajiye aiki ne da wasu shugabannin jam'iyyar na kasa su bakwai suka yi a farkon mako. Shirin Najeriya a Yau ya duba a kan wannan lamari don gano yadda aka yi aka haihu a ragaya.
Similar podcasts
Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.