Najeriya a Yau

News HA ↓ 958 episodes

Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.

Category

News

Podcast website

www.buzzsprout.com

Latest episode

Jun 23, 2026

Where to listen?

Podcasts in the app Replaio Radio Coming soon

Podcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts

Get it on Google Play Install for free Android 5M+ downloads · 4.8 rating iOS soon

Episodes

Abin Da Za A Iya Yi Da Kudin Rigar Maman Diezani 29.10.2021

Send us Fan Mail Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta kudiri aniyar yin gwanjon wasu kadarorin da ta kwace daga tsohuwar ministar man fetur din kasar a zamanin mulkin Shugaba  Goodluck Jonathan, Diezani Allison-Madueke, wadda ake zargi da azurta kanta fiye da kima da kudaden kasa ba ta hanyar halal ba. Ayi sauraro lafiya

Tsarin Makarantun Tsangaya Jiya Da Yau 28.10.2021

Send us Fan Mail Bukatar bai wa yaran da ke karatu a tsangaya ilimin zamani na cikin daililan da suka sa wasu hukumomi daukar matakan yin garambawul ga tsarin tsangaya. Ayi Sauraro lafiya

Me Ayyana 'Yan Bindiga A Matsayin 'Yan Ta'adda Zai Haifar 26.10.2021

Send us Fan Mail Maganar neman a ayyana ’yan bindiga a matsayin ’yan ta’adda na ci gaba da shan muhawara a Najeriya.  Shin ayyana su a matsayin ’yan ta’adda zai taimaki jami’an tsaron Najeriyar ne ko kuma kara ta’azzara ayyukan bata-garin zai yi?  

Kalubalenku 'Yan Jarida 25.10.2021

Send us Fan Mail An bukaci cibiyoyin watsa labaran Najeriya dasu zama masu kishin kasa da kwarewa wajen gudanar da ayyukan su don inganta hadin kai da cigaban kasa.   shin dagaske ne 'yan jarida a Najeriya basuda kishin kasa?  wannan shine batun da shirin Njaeriya A yau zai maida hankali. 

Harin Jirgin Kasa: Najeriya za ta rikayin asarar N25m kullum 22.10.2021

Send us Fan Mail Najeriya za ta rika yin asarar cinikin sama da Naira miliyan 25 a kowace rana, sakamakon dakatar da zirga-zirgar jiragen kasan da Hukumar Sufurin Jiragen Kasa ta yi, bayan an kai wa jirginta harin nakiya.

’Yar Tinke Ko Deliget: Wane Tsarin Zabe Ne Ya Fi Dacewa A Najeriya? 21.10.2021

Send us Fan Mail A yayin da matsaloli da zargin magudi ke ci gaba da mamaye zabukan fitar da ’yan takara da na shugabannin jam’ iyya da sauran zabuka a Najeriya, wane tsarin zabe ne ya fi dacewa? Shirin Najeriya a Yau na wannan karon ya yi dubi ne a kan amfani da daliget su yi zabe da kuma a bari kowa ya shiga a dama da shi. A yi sauraro lafiya.

Yadda Aka Kashe Mutum 65 A Goronyo 19.10.2021

Send us Fan Mail Kisan mutum 65 din da ’yan bindiga suka yi a Babbar Kasuwar Goronyo na Jihar Sakkwato na ci gaba da tada hankalin al’umma, lura da cewa an dan samu saukin wadannan hare-haren a jihohin Zamfara da Katsina.  Shirin namu na yau yayi duba ne a kan mene ne ba a yi daidai ba yasa hakan ya faru.  

Rikicin Majalisar Malaman Kano Ya Bar Baya Da Kura 18.10.2021

Send us Fan Mail Yunkurin sauke Malam Ibrahim khalil daga kujerarsa ta shugabancin Majalisar Malamai ta Jihar Kano ya janyo cece-kuce a jihar Kano da ma Arewacin Najeriya baki daya. Jama’a da dama sun zargi gwamantin jihar da  hannu wurin tsige malamin.

Taskun da 'Yan Gudun Hijira Ke Ciki A Najeriya 15.10.2021

Send us Fan Mail ‘yan gudun hijira na cikin tasku a sansanonin gudun Hijira a Najeriya. Rashin abinci, rashin makaranta da tsananin talaucin da suke ciki na cigaba da barazana ga wanzuwarsu a matsayin cikakkun mutane masu ‘yanci. Ayi sauraro lafiya.

Shin Tura Sakamakon Zabe Ta Intanet Zai Kawo Karshen Magudin Zabe? 14.10.2021

Send us Fan Mail Hukumar zaben Najeriya (INEC), ta samu amincewar Majalisar Dattawa wajen bayyana sakamakon zabe ta intanet. Shin hakan na nufin an yi maganin magudi da murdiyar zabe a kasar ke nan? Abin da shirinmu na yau ya mayar da hankali a kai ke nan. A yi sauraro lafiya.

Yadda Shugabannin Najeriya Ke Boye Kudaden Haram 12.10.2021

Send us Fan Mail Binciken da ya fallasa yadda 'yan siyasa da shugabanni da attajiran Najeriya da wasu kasashe suka azurta kawunansu da kudaden haram na ci gaba da shan fashin baki a fadin duniya.  Shirin Najeriya A Yau zai dubi wannan batu daga tushe domin bai wa mai sauraro damar fahimtar halin da ake ciki game da binciken na  'Takardun Pandora', wanda 'yan jarida masu bincike...

Yadda Kasafin Kudin 2022 Zai Shafi Rayuwarku 11.10.2021

Send us Fan Mail Kasafin kudin sheakara mai zuwa shine kasafin kudin da ya fi kowanne yawa a tarihin Najeriya. Shirin Najeriya A Yau yayi nazari akan bangaororin da shirin zai shafi rayuwar 'yan kasar kai tsaye.  Ayi sauraro lafiya. 

Shin Za A Hana Yara Mallakar Waya A Najeriya? 08.10.2021

Send us Fan Mail Yunkurin hukumar NCC na hana kananan yara amfani da waya ya bar baya da kura.  'Yan Najeriya na ci gaba da fadin albarkacin bakinsu. Hukumar ta yi martani akan wannan batu. Ayi sauraro lafiya.

'Yadda IPOB Da ’Yan Siyasa Ke Wasan ‘Buya’ A Anambra 07.10.2021

Send us Fan Mail Nan da kasa da kwana 30 za a gudanar da zaben gwamna a Jihar Anambra, amma rahotanni na nuna cewa babu dan siyasar da ya kafe fosta kuma babu mai yakin neman zabe.  Hakan dai na faruwa ne sakamakon ayyukan haramtacciyar kungiyar IPOB mai fafutukar kafa kasar Biafra. Za mu duba abin da ke faruwa da kuma abin da hakan ke nufi ga Jhar da ma kasa baki daya.

‘Yan Ta’adda Sun Kafa Sabbin Dokoki A Wadnsu Yankuna A Jihar Neja 05.10.2021

Send us Fan Mail Wadansu da ake zargin ‘yan kungiyar boko haramun ne sun kafawa al’ummar kauyukan Awulo da Kuregbe na karamar hukumar shiroron sabbin dokokin zamantakewa.  Yan bindigar dai sun ce dole ne a aurar da duk wadda takai shekaru 12 da haihuwa. Sun kuma haramta kaiwa ‘yan sanda da kotu kara. 

Shin Najeriya Kasa Ce Mai Cikakken ’Yanci? 04.10.2021

Send us Fan Mail Bayan shekara 61 da samun ’yancin Najeriya, wasu ’yan kasar na bayyana shakku game da zaman kasar tasu mai cikakken ’yanci. A gefe guda kuma al’ummomin duniya sai taya kasar murna suke ta yi game zagayowar ranar samun ’yancin kan nata daga turawan mulkin mallaka. Shirin Najeriya ya gayyato masana kuma sun yi bayani dalla-dalla game irin ’yancin na Najeriya, wadda ta yi bikin zagay...

Shekara 61 Da Mulkin Kai: Gaba Najeriya Take Yi Ko Baya? 01.10.2021

Send us Fan Mail Shekara 61 ke nan tun bayan da Najeriya ta samu 'yanci daga hannun 'yan mulkin mallaka. Shin a wadannan shekaru gaba kasar take yi ko baya? Shirin Najeriya a Yau zai tattauna da wadanda suka shaida karbar mulkin, da ma sauran 'yan Najeriya da suka biyo baya, don zube komai a faifai a auna a tantance, sannan a amsa wannan tambayar.

Tsarabar Zamfara: 'Da Shiga Jihar Za Ka Ga Damuwa Miraran' 30.09.2021

Send us Fan Mail Yau kusan makwanni hudu ke nan al’ummar Jihar Zamfara na rayuwa ba wata hanyar sadarwa ta waya da sauran sassan duniya.  Abokinmu a Kaduna, Muhammad Ibrahim Yaba, ya ziyarci jihar domin gane wa idonshi halin da ake ciki a yanzu. Bayan dawowarsa ya shigo dakinmu na hada shirye-shirye don raba mana tsarabar abin da ya gano.

Matakin Haramta Fina-Finai Ya Bar Baya Da Kura 28.09.2021

Send us Fan Mail Hukumar Tace Fina-Finai da Dab’i Ta Jihar Kano ta haramta shiryawa da nuna fina-finan da ake nuna garkuwa da mutane da kuma yadda ake amfani da muggan makamai.    Hukumar ta ce fina-finan da aka hana din ka iya karantar da masu kallo yadda za su yi barna a maimakon gyara.    A shirin Najeriay a Yau za mu duba abin da dokar ta tanada da martanin masu ruwa da tsaki.

Abin Da Shugaba Buhari Ya Fada Wa Majalisar Dinkin Duniya 27.09.2021

Send us Fan Mail Shugaban Najeriya Muhammmadu Buhari ya yi jawabi a taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 76, wanda a cikinsa ya bukaci a yafe wa Najeriya bashin da ake bin ta. Ya kuma kalubalanci Majalisar da ta yi wa tsarin Kwamitinta na Tsaro garambawul.  A wannan shirin za mu duba muhimman abubuwan da Shugaba Buhari, da yadda za su amfani talakan Najeriya.

Takaddama Kan Yi Wa Malaman Jihar Kano Gwajin Kwakwalwa 24.09.2021

Send us Fan Mail A kokarinta na tsaftace wa'azi a jihar Kano, gwamnati na yunkurin yin dokar gwada lafiyar kwakwalwar malamai.  Wannan yunkuri na shan raddi daga malaman da almajirai da dama, har ma wasu na bayar da shawarar a fara daga shuwagabanni masu rike da mukaman siyasa zuwa kan masu unguwanni kafin a zo kan malamai. 

Illar Da COVID-19 Ta Yi Wa Harkokin Kasuwanci A Najeriya 23.09.2021

Send us Fan Mail COVID-19 ta rusa wa mutane da dama shirinsu na cimma wani mataki a rayuwa a Najeriya.    Hatta gwamnatin kasar ta ji a jikinta da bullar wannan cuta.     Shirin zai yi duba a kan yadda cutar COVID-19 ta raba nutane da dama da ayyukansu a Najeriya.

Abin Da Ya Sa Mutane Ke Gudun Riga-Kafin COVID-19 21.09.2021

Send us Fan Mail An shafe watanni tun bayan kawo allurar rigakafin cutar COVID-19 Najeriya, inda gwamnati ke ta kokarin ganin an yi wa mutane. Duk da tsawon lokacin da hukumomi suka dauka suna wayar da kan jama’a game da muhimmacin yin wannan allurar, har yanzu wasu ’yan Najeriya sun turje. Ko mene ne dalili?

Matakin Da Gwamnati Ke Shirin Dauka Kan Hayakin Janareta 20.09.2021

Send us Fan Mail Gwamnatin Tarayya ta jaddada matsayinta a kan hana shigo da kananan injinan janara domin kare lafiyar al'umma. 'Yan Najeriya da dama dai sun dogara ne kacokan a kan wadannan injina don samun wutar lantarkin da suke bukata don gudanar da harkokinsu.  Ko yaya wadanda abin ya shafa ke ji da wannan mataki?

Katse Layukan Waya: Zamfarawa, Katsinawa Na Kaura Daga Gida 17.09.2021

Send us Fan Mail Kusan mako biyu ke nan tun bayan da gwamnati ta bayar da umarnin katse layukan sadarwa a Jihar Zamfara; kusan mako guda bayan Katsina ta bi sahu. Ko wanne hali mutanen jihohin ke ciki, musamman ta fuskar mu'amalar kasuwanci, ko zumunci? Shirin Najeriya a Yau ya tambayi wasu 'yan asalin yankin yadda suke mu'amala da 'yan uwa da abokan arziki.

Listen to the Najeriya a Yau podcast in Replaio

Radio and podcasts in one app - free, with no sign-up. Install today and do not miss the launch

Get it on Google Play

Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.