Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Where to listen?
Podcasts in the app Replaio Radio Coming soonPodcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts
Episodes
Yadda Rusau Ke Jefa Rayuwar 'Yan Najeriya Cikin Kunci 09.12.2021 15:13
Send us Fan Mail Duk lokacin da hukumomin tsara taswirar biranen Najeriya suka tashi jama'a daga inda suke gudanar da harkokin rayuwarsu don gudanar ayyukansu, lamarin na zuwar wa wadanda abun ya shafa da firgici da gigita. Wasu mazauna unguwannin da aka umarce su da su yi kaura wani lokacin sukan yi watsi da umarnin hukumar har sai ya kai wa'adin da za a yi amfani da katapila don rush...
Masu fasa gidajen yari sun fi mu karfin makamai-Ganduroba 07.12.2021 14:17
Send us Fan Mail Daga shekarar 2020 zuwa 2021 an kai manyan hare-hare 13 gidajen yari daban-daban a Najeriya, wanda suka yi sandiyyar guduwar fursunoni sama da 3,000. Me ke janyo yawaitar kai wa gidajen yari hari? Wadanne illoli wadanda suka gudo daga gidan yari za su yi wa al'umma? A yi sauraro lafiya.
Yawan Al'ummar Najeriya: Rahama Ga Kasa Ko Taron Yuyuyu? 06.12.2021 15:01
Send us Fan Mail A yayin da Shugabanni ke yawan alakanta talauci ko rashin ci gaban kasa da yawan haihuwar ’ya’ya, wasu na ganin yawan al'umma a kasa shi ginshiki ne kawo ci gaban kasa. Shirin Najeriya A Yau na kusnhe da tattaunawa ta musamman a kan alakar da ke tsakanin yawan al'umma da tattalin arzikin kasa. A yi sauraro lafiya.
Yadda Za A Taimaki Mata Manoma A Jihar Bauchi 03.12.2021 16:45
Send us Fan Mail Manoma mata a Jihar Bauchi sun bukaci a dabbaka Manufar Daidaita Manoma Maza Da Mata A Tallafin Gwamnatin Tarayya Na Kudade Da Kayan Aiki. Matan na ganin idan har suka samu tallafi za su iya samun nasara a harkokin noma fiye da takwarorinsu maza. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci na kunshe da bayanan bukatun nasu. A yi sauraro lafiya.
Bahaushiya Ta Kirkiri Shafin Koyar Da Lissafi Da Hausa 02.12.2021 15:09
Send us Fan Mail Lissafi na daya daga cikin darussan da ke baiwa dalibai tsoro a makaranta, duk da muhimmancinsa a fagen kimiyya da fasaha. Fatima mai shekara 24, 'yar asalin Jihar Jigawa ta bayyana mana dalilan ta na kirkiran shafin koyar da darasin lissafi a harshen hausa. Ayi sauraro.
Dalilan Kara Kudin Motar Haya Lokacin Bukukuwa A Najeriya 30.11.2021 14:59
Send us Fan Mail A duk lokacin da wani biki da zai shafi wasu rukunin al’umma ya taho a Najeriya, wahalarsa ba ta tsayawa a kan masu bikin kadai, hatta ’yan ba ruwanmu sai ta ritsa da su. A irin wadannan lokuta ’yan Najeriya kan dandana kudarsu wurin biyan motar haya. Amma me ya sa ake haka kuma wa ke da hannu a ciki?
Najeriya A Yau: Yadda bankuna ke 'tatsar' 'yan Najeriya 29.11.2021 15:17
Send us Fan Mail Yawan tatsar ’yan Najeriya da bankuna ke yi ta hanyar cire-ciren kudi daga asusun masu ajiya ya kai ’yan kasar bango, tun suna gunaguni, har sun fara fitowa kafafen sada zumunta suna bayyana bacin ransu. Me ya sa bankuna ke yawan zarar kudade ba tare da neman izini ba? Shin ’yan Najeriya na da damar bin kadun kudadensu a hukumance? Me doka ta ce a kan hakan? Ku saurari shirin Naje...
Tasirin kalaman kauna a rayuwar aure 26.11.2021 14:59
Send us Fan Mail Ana yawan zargin maza da cuzgunawa mata, sai dai a wadansu lokutan ana samun matan da laifin cuzgunawa mazajen nasu. Masana sun bayyana tasirin kalaman kauna wurin magance rikice-rikicen zamantakewar aure. Ayi sauraro lafiya.
Yadda "Ake Karo da Gawarwaki" a Jalingon Jihar Taraba 25.11.2021 12:24
Send us Fan Mail Rikice-rikicen kabilanci da na makiyaya da manoma ya dade yana addabar Jihar Taraba, sai kuma gashi ba a gama shawo kan wadancan tsoffin matsalolin ba, wani sabon salon rashin kwanciyar hankalin ya sake kunno kai, dan kuwa 'yan Jihar na zargin hukumomin tsaro da yin burus da batun rayukansu da dukiyoyinsu. Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau ya mayarda da hanakali ak...
Samun kudi da kashe kudi wanne ya fi wahala? 23.11.2021 12:03
Send us Fan Mail Da yawa mutane kanyi tunanin cewa samun kudi yafi kashe kudi wahala, abunda zai baka mamaki shine yadda wadansu ke shiga dimuwa idan sun samu kudade masu kauri a hanunsu lokaci guda. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci na kunshe da hanyoyin da Wadansu 'yan Najeriya ke sa ran zasu kashe kudaden da suka samu bagata tan.
Yadda uba ya yi wa 'yarshi fyade har ta yi ciki 22.11.2021 14:19
Send us Fan Mail kunnuwan 'yan Najeriya sun jima sunajin kalmar fyade, amma labarin mahaifi yayiwa 'yarshi fyade har ta samu ciki na iya zama sabon labari ga masu sauraro. A karshen satin da ya gabata Amnesty International sun ruwaito cewa a shekarar data gabata a kullum ana yiwa mata 374 fyade a Najeriya. shirin namu na yau na tafe da labarinh 1 daga cikin wadanda akayiwa fyaden, kuma...
Shin fitar da 'yan Najeriya Kasashen waje aiki zai taimaki kasar? 19.11.2021 15:07
Send us Fan Mail Wasu masana tattalin arziki a kasar nan sunyi hasashen cewa fitar da matasa masu sha'awar zuwa kasashe masu karfin tattalin arziki aiki a hukumance zai taimaki tattalin arzikin Najeriya, wasu kuma na ganin bazai taimaki kasar ba, hasalima rashin ci gaban kasar ya ta'allaka ne akan halin 'yan kasar. Wannene gaskiya?
Yadda Ake Taimakon Wanda Wuta Ta Kona 18.11.2021 14:48
Send us Fan Mail Lokacin kaka na zuwa da abubbuwa da yawa, ciki har da tashin wuta a wurare da dama. da yawa, idan gobara ta tashi, mutane kan rikice, maimakon a taimaki wanda wutar ta kona sai a wayi gari an kara jefa mara lafiyan cikin wahala. Muna tafe da bayanan me ke kawo gobara da kuma yadda ake taimakon wanda wuta ta kona.
Yadda cutar suga ta hana ni shiga aikin soja —Matashi 16.11.2021 14:59
Send us Fan Mail Mutane da yawa sun dauka sai tsofi ciwon suga ke kamawa, amma da muka bincika ba a nan gizo ke saka ba. wadansu gadar ta suke yi, wasu kuma tun kafin su kai shekara 30 suke kamuwa da ita. saurari cikakken shirin domin jin me ke jawo wannan cutar, alamunta sannan shin ana warkewa ko a'a?
A karon farko ta'addanci ya ci Janar din soja a Najeriya 15.11.2021 14:56
Send us Fan Mail Tunda aka fara yaki da ta’addanci a Najeriya a 2009 ba a taba rasa wani soja mai mukamin Janar ba a bakin daga. Sai ga shi a karon farko a 2021 ’yan ta’adda sun hallaka Birgediya-Janar Dzarma Zirkusu da dakarunsa. Ga bayanin yadda abun ya faru, musabbabin faruwar hakan da kuma abin da ya kamata a gyara. A yi sauraro lafiya.
Yadda 'Yan Najeriya 13 suka mutu wurin tonon zinare a Maradi. 12.11.2021 14:47
Send us Fan Mail An tabbatar da mutuwar mutane 13 a ramukan tonon zinare a kauyen Kwandago da ya ke Jihar Maradi a Jamhuriyar Nijar. Wani mai tonon zinaren da ya tsallake rijiya da baya, ya nuna akwai gangancin masu tonon zinaren. A yi sauraro lafiya.
Yadda Abubakar Shekau yayi kuruciyarshi 11.11.2021 14:40
Send us Fan Mail Shirin Najeriya A Yau ya binciko yadda Shekau yayi kuruciyarshi daga bakin mahaifiyarshi da dagacin garinsu. A karshen shirin munyi hira da masanin halayyar dan Adam domin sanin ko kuruciyar mutum nada tasiri akan yadda zai rayu. Ayi sauraro lafiya
Me ya sa ake ayyana zabe a matsayin inkonkulusib (inconclusive) 09.11.2021 15:22
Send us Fan Mail Me kalmar inkonklusib (inconclusive) a doka? Wace dokar zaben ce ta bada dama a ayyana zabe a matsayin inkonklusib (inconclusive)? Shirin Najeriya A Yau na kunshe da bayani mai gamsarwa daga bakin masani. Ayi sauraro lafiya.
Zaben Gwamna: Mutanen Anambra Sun Ba Da Mamaki 08.11.2021 25:53
Send us Fan Mail Tun kafin zuwan zaben gwamnan Anambra na 6 ga watan Nuwamba, an yi hasashen faruwar abubuwa da dama, galibi marasa dadi. Sai dai kuma mutanen Jihar sun bai wa marada kunya; abin jira a gani shi ne me zai biyo baya. Shirin Najeriya a Yau ya duba dalilan haka da kuma kalubalen da ke gaba, musamman ga sabon gwamna.
Yadda zabe ya gudana a Anambra 07.11.2021 29:23
Send us Fan Mail A jiya Asabar ne akayi zabe a tsakanin 'yan takaran gwamna goma sha tara (19) a jihar Anambra, shirin Najeriya A Yau na kunshe da bayanan abubbuwan da ya gudana a jihar baki daya. Ayi sauraro lafiya
Yadda ake ciki kan zaben Anambra 06.11.2021 25:53
Send us Fan Mail Yau take 6 ga wata, kuma yaune za a fafata tsakanin 'yan takaran zama gwamna 18 a jihar Anambra dake kudancin Najeriya. Shirin Najeriya A Yau na dauke da bayanan halin da ake ciki, sanna mun bibiyi me janyewar 'yan awaren IPOB daga matsayinsu na baza'ayi zabe ba ke nufi.
Yadda ake ciki kan zaben gobe a Anambra 05.11.2021 29:17
Send us Fan Mail INEC da IPOB sun sha ruwan rantsuwa a Anambra Shin za'ayi zabe a Anambra ranar Asabar? Yaya batun dokar kar kowa ya fito da IPOB ta kafa a Jihar? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci na dauke da amsoshin wadannan tambayoyin dama karin bayani akan zaben da za'ayi a ranar asabar mai zuwa
Yadda jami'ai ke 'agaza wa' masu fasa-kwauri 04.11.2021 14:44
Send us Fan Mail Ga alama kwalliya ba ta biyan kudin sabulu bayan da aka rufe iyakokin Najeriya da nufin hana fasa-kwauri. Hasali ma, jami'an da aka dora wa alhakin kula da iyakokin ake zargi da taimaka wa masu fasa-kwaurin, lamarin da ke haddasa nakasu ga tattalin arzikin Najeriya. Wannan shirin na Najeriya a Yau ya yi nazari a kan wannan batu.
Hauhawar farashin kayan masarufi (2) 02.11.2021 13:25
Send us Fan Mail A karo na biyu, shirin Najeriya A Yau ya kara duban matsanancin hauhawar farashin kayan masarufin da ya addabi Najeriya. Mun kai ziyara kasuwar Utako da ke Abuja domin jin halin da ake ciki. Ayi suraro lafiya.
Dalilan da ke jawo hauhawar farashin kayan matsarufi 01.11.2021 25:00
Send us Fan Mail Yaya za a yi a magance wannan matsala ta hauhawar farashi? Yaya za a yi a rage fifita dala a kan Nera? Kuma wadanne hanyoyi za a iya bi a farfado da darajar Nera?
Similar podcasts
Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.