Najeriya a Yau

News HA ↓ 958 episodes

Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.

Category

News

Podcast website

www.buzzsprout.com

Latest episode

Jun 23, 2026

Where to listen?

Podcasts in the app Replaio Radio Coming soon

Podcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts

Get it on Google Play Install for free Android 5M+ downloads · 4.8 rating iOS soon

Episodes

Yadda Tsaro Da Tattalin Arziki Za Su Shafi Zaben 2023 21.01.2022

Send us Fan Mail Yanayin tsaro da tattalin arziki na taka muhimmiyar rawa a wurin gudanar da zabe wanda kuma babban jigone wajen tabbatar da dorewar tsarin Dimokuradiyya. Taron tattaunawa na shekara-shekara da kamfanin Media Trust mai buga jaridar Daily Trust na wannan karon ya mayar da hankali ne a kan rawar da yanayin tsaro da tattalin arzikin Najeriya za su taka wurin juya akalar zaben kasar na...

Shin Ya Dace Malaman Addini Su Shiga Siyasa? 20.01.2022

Send us Fan Mail Mutane da dama na kallon siyasa a matsayin wani fage da bai dace da malaman addini ba, wasu kuma na ganin ai siyasa wani bangare ne na shugabanci, don haka malamai suna da rawar da za su taka, saboda haka ya kamata su tsaya takara har ma su rike mukamai a gwamnati.  Mun tattaro ra’ayoyin jama’a ciki har da na malaman sannan muka mika su ga wani mai sharhi domin warare zare da abaw...

Shirin Da 'Yan Najeriya Suke Yi Wa Zaben 2023 18.01.2022

Send us Fan Mail Hukumar zabe ta kasa ta fara shirye-shirye don gudanar da zabukan shekarar 2023.  ’Yan takara kuwa har sun fara fitowa suna bayyana aniyarsu ta neman tsayawa takara.  Amma abin tambaya shi ne, shin ’yan Najeriya masu zaben a shirye suke kuwa? A yau shirin namu ya yi duba ne a kan shirye-shiryen da ’yan Najeriya ke yi wa zaben 2023.

Yadda Tinubu, Dattawan Arewa Suka Yamutsa Hazon Siyasar Najeriya 17.01.2022

Send us Fan Mail Bayyana aniyar takarar shugabancin kasar da Bola Ahmed Tinubu yayi a fadar shugaban kasar Nijeriya Muhammadu Buhari ta tada kura a fagen siyasar kasar.  Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya zaƙulo dalilanda Tinubu ya ƙaddamar da maganar takaransa a fadar shugaban ƙasar Najeriya da kuma matsayar Ƙungiyar Dattawan Arewa dangane da wanda suke son yayi takara.

Rufe Twitter: Yadda ’Yan Najeriya Suka Yi Asara, Gwamnati Ta Ci Riba 14.01.2022

Send us Fan Mail A kwana akalla 220 da gwamnatin Nejeriya ta rufe harkokin kafar sada zumunta ta Twitter, ‘yan kasar sun tafka asarar makudan kudade, a yayin da gwamantin kasar kuma ta ci gagarumar riba a sakamakon matakin da ta dauka. Masana sun yi bayanin irin makudan kudaden da Gwamnatin Tarayya za ta rika samu daga harajin da za ta rika karba daga hannun kamfanin Twitter a sakamakon amfanin da...

Yadda Likitoci Ke "Jawo Asarar Rayuka" 13.01.2022

Send us Fan Mail Lafiya uwar jiki in ji masu iya magana. Sai dai kuma a wasu lokuta masu neman lafiya kan fada cikin muwuyacin hali idan suka je asibiti don neman lafiya.  Hakan na faruwa ne saboda kurakurai ko sakaci na likitoci da ma’aikatan jinya wajen gudanar da ayukan su.  A yau Shirin na mu ya duba yadda a wasu lokuta ake samun kurakurai ne yayin yi wa marasa lafiya aiki a wasu asibitoci.  

Yadda Rage Kwanakin Zuwa Makaranta Zai Shafi Dalibai A Jihar Kaduna 11.01.2022

Send us Fan Mail Bayanin rage adadin kwanakin zuwa makaranta da Gwamnatin Jihar Kaduna ta fitar a wannan zango ya dauki hankalin malaman makarantu da masana harkar ilimi a Jihar.  Malaman Makaranta na ganin cewa tsarin da zai tilastawa makarantu hutun kwana 3 a sati  zai kara takure su wurin shirya jadawalin darussan da za su koyar. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci na kunshe da tattaunawa ta...

AFCON 2021: Tana Kasa Tana Dabo 10.01.2022

Send us Fan Mail Hankulan masoya kwallon kafa a Najeriya kamar na takwarorinsu a kasashen Afirka da ma wasu sassan duniya sun koma Kamaru, inda aka bude Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka 2021. Kasashen Afirka 24 ne za su fafata a gasar, kuma tuni kasar Kamaru mai karbar bakuncin gasar ta kara da Burkina Faso a wasan da aka tashi 2-1. Najeriya ma ta samu damar shiga gasar amma tana kasa tana dabo, sab...

Za’a Kashe Duk Wanda Ya Saci Mutum A Jos 07.01.2022

Send us Fan Mail A yunkurin ta na neman dakile ayyukan masu garkuwa da mutanen da ya fara yawaita  kwanan nan, gwamnatin Jihar Filato ta kara jaddada kudirinta na kashe duk wanda aka tabbatar ya saci wani domin karbar kudin fansa, Anya zai yiwu kuwa? Me doka ta ce dangane da kashe wanda bai yi kisa ba?  Mun tattauna da Gwamnatin Jihar domin sanin yadda za a gudanar da wannan hukunci. Kuma mun ji t...

Me Sabon Mashawarcin Shugaban Kasa Kan Tattalin Arziki Zai Tsinana Wa Talaka? 06.01.2022

Send us Fan Mail Kasa da wata 16 kafin karewar wa'adin mulkinsa, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada sabon mai ba shi shawara a kan al'amuran tattalin arziki. Wannan lamari dai ya jawo martani iri-iri daga 'yan Najeriya. Shirin Najeriya a Yau ya leka Fadar Shugaban Kasa don gano dalilin wannan mafi a wannan lokaci, sannan ya yi nazari a kan sauyin da hakan ka iya haifarwa.

Ba Rabo Da Gwani Ba: Abubuwan Da Ba ku Sani Ba Game Da Bashir Tofa 04.01.2022

Send us Fan Mail Alhaji Bashir Usman Tofa ya kwana daya da rasuwa bayan ya kwashe shekara 75 yana rayuwa a doron duniya.  Me za ku tuna game da shi?  Mun tattauna da makusanta marigayin kan yadda rayuwar marigayin.

Yadda Za A Bunkasa Fasahar Zamani Domin Samar Da Ayyukan Yi 03.01.2022

Send us Fan Mail Rashin aikin yi a tsakanin matasa a Najeriya na cikin matsalolin da suka yi wa kasar katutu, har ta kai duk gwamnatin da ta zo sai an koka da gazawarta wurin samar wa ‘yan kasa abin yi. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci na kunshe da bayanan yadda za a bunkasa fasahar zamani ta intanet domin samar wa ‘yan kasar aikin yi cikin sauki.

Yadda ’yan bindiga ke samun bayanan sirri 31.12.2021

Send us Fan Mail Rahotanni daga jihohin da ke fama da matsin lambar ’yan ta’adda sun tabbatar da cewa ’yan biindigan na samun bayanan sirri daga wurin mutanen yankunan. Yayinda wadannan bayanai da ’yan bindiga ke samu ke ci gaba da jefa yankunan cikin mawuyacin hali, yake kuma hana jami’an tsaro samun nasara. saboda duk lokacin da jami’an tsaron suka kitsa wani matakin sirri sai an samu wanda ya t...

Tattalin Arziki: Yadda 2021 Ta Zo Wa 'Yan Najeriya 30.12.2021

Send us Fan Mail A shekarar 2021, tattalin arzikin Najeriya ya gamo da abubuwa da dama, masu daɗi da marasa daɗi. Ina wadannan abubuwan suka kai 'yan Najeriya, a ina kuma suka baro su? A wannan shirin na Najeriya a Yau, mun yi bitar muhimmai daga cikin al'amuran da suka wakana a Najeriya ta fuskar tattalin arziki.

Sakacin Gwamnati Ne Silar Kai Hari A Makarantu A 2021 28.12.2021

Send us Fan Mail An kai wa makarantu akalla 10 hari a cikin shekarar 2021 inda aka sace yara sama da 700 a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.  Shin daga ina matsalar take; anya gwamnati ta shirya tunkarar 2022?   A yi sauraro lafiya.

Rashin Tsaftar Abinci Ke Haifar Da Cutar Typhoid 27.12.2021

Send us Fan Mail Rashin tsaftar muhalli da ruwan sha da abinci na taka muhimmiyar rawa wurin yada cutar typhoid, inji masana. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci na kunshe da bayanan yadda ake kamuwa da cutar da yadda za a kare kai daga kamuwa da ita.

Anya magoya baya za su bari Ganduje da Kwankwaso su daidaita? 24.12.2021

Send us Fan Mail Batun sulhu tsakanin tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da gwamna mai ci Abdullahi Ganduje na kara karfi. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci na dauke da bayanan magoya bayan bangaren Kwankwaso da Ganduje da kuma hasashen masana kan alfanun sulhun. A yi sauraro lafiya.

Shin kashe ’Yan Bindiga Zai Magance Matsalar Tsaro? 23.12.2021

Send us Fan Mail Masana da mahukunta sun sha bayar da shawarwari kan yadda za a magance matsalar tsaro ta hanyoyi daban-daban. Sai ga shi Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce shi dai gwmnatinsa ba za ta karbi tubar ’yan bindiga ba, kashe su za ta yi, domin a wurinta, dan bindigar da aka kashe kawai shi ne kawai ya tuba. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci na dauke da fashin bakin masana d...

Yadda ’Yan Ta’adda Suka Ruguza Ilimi A Arewacin Najeriya 21.12.2021

Send us Fan Mail Arewacin Najeriya ya yi kaurin suna wajen tabarbarewar ilimi da kuma yawan yara marasa zuwa makaranta. Ana cikin haka kuma, a  ’yan shekarun nan ayyukan ’yan ta’adda suka kara sako bangaren ilimi a gaba a yanki. Shin ina makomar ilimin yara masu tasowa a yankin? Abin da shirinmu ya tattauna ke nan a wannan karon. Da fatan za a yi sauraro lafiya.

Dalilan 'rashin yanke' wa masu laifi hukunci a Najeriya 20.12.2021

Send us Fan Mail ’Yan Najeriya da dama na mamakin yadda mutanen da suke gani a matsayin manyan masu laifi ke kubuta idan an kai su gaban kotu. Sau tari ana murnar an kama mai laifi, amma ana zuwa kotu sai yanke hukunci ya gagara a cikin lokaci; Wani lokaci kuma bayan dan lokaci da yanke mishi hukunci, sai a ga ya dawo cikin al’umma yana harkokinsa. Ina gizo ke saka, sannan me ya sa mutane debe kau...

Yadda ’yan Najeriya ke rayuwa a kan Naira 1000 17.12.2021

Send us Fan Mail Naira 1000 ita ce takardar kudi mafi girma a Najeriya da gwamnatin kasar ta fara fitarwa a shekarar 2005, wadda har yanzu ita ce takardar kudi mafi girma a kasar . Shin mece ce kimar N1,000 ga ’yan kasar a halin yanzu? Matasa da magidanta sun bayyana wa shirin Daga Laraba yadda rayuwarsu ta kasance a kan N1,000. A yi sauraro lafiya.

Yadda Karin Harajin 2022 Zai Shafi Rayuwar ’Yan Najeriya 16.12.2021

Send us Fan Mail ’Yan Najeriya na ta yi wa kalaman Ministar Kudin kasar fassara iri-iri bayan ta sanar da yiwuwar karin harajin da gwamnatin kasar ke karba daga hannunsu a shekar 2022 mai kamawa.  Shin kun kun san ta hanyoyin da wannan karin harajin zai shafi rayuwarku kai-tasaye kuwa? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya fayyace ma’anar kalaman ministar, sannan ya zakulo hanyoyin da karin ha...

Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Katobara A Kan Matsalar Tsaro 14.12.2021

Send us Fan Mail Fadar Shugaban Kasa ta yi raddi ga jaridar Daily Trust saboda jaridar ta bayyana rashin jin dadinta kan yadda Shugaba Buhari ke yin rikon sakainar kashi ga matsalar tsaro musamman a Arewacin Najeriya.  Masana sun dora martanin gwamnatin a gadon fida, sannan suka bayyana cewa akwai tsabar katobara a ciki bayanan na Fadar Shugaban Kasa. A yi sauraro lafiya

Me Dimokuradiyya Ta Tanada Wa Talaka Idan Tura Ta Kai Bango? 13.12.2021

Send us Fan Mail Tsarin Dimokuradiyya na gaskiya ya ba wa ’yan kasa ikon zabar wadanda suke so su mulke su da kuma bin bahasi kan inda aka kwana da inda aka dosa. ’Yan Najeriya sun furta albarkacin bakinsu a kan halin rashin tsaron da ya addabi kasar. A yi sauraro lafiya.

Matasan Arewa: Da Noma Gara Zaman Jiran Tsammani 10.12.2021

Send us Fan Mail Allah Ya yi wa matasan da ba su da ba aikin yi a Najeriya yawa sosai, duk kuwa da irin baiwar da Allah Ya yi wa kasar na filin noma da gulaben da za a iya amfani da su wurin noma rani da damana. Shirin Najeriya A Yau ya gano dalilan wadannan matasa da ke zaman jiran aikin ofis da kuma wadanda suke noman da yadda suka fara.

Listen to the Najeriya a Yau podcast in Replaio

Radio and podcasts in one app - free, with no sign-up. Install today and do not miss the launch

Get it on Google Play

Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.