Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Where to listen?
Podcasts in the app Replaio Radio Coming soonPodcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts
Episodes
Sirrin Da Bello Turji Ya Bayyana Mana A Maboyarsa 07.03.2022 17:47
Send us Fan Mail Shirin Najeriya A Yau ya yi tattaki zuwa maboyar Bello Turji, shugaban ’yan bindiga da ke ci wa harkar tsaro, musamman a Arewacin Najeriya tuwo a kwarya. A hirar tasu gaba-da-gaba, Turji da sauran ’yan bindigar sun bayyana wa wakilin namu wasu muhimman abubuwa game da ayyukansu da kuma matsalar da ta ki ci, ta ki cinyewa.
Dalilin Watsi Da Dokar Ba Mata 35% Na Mukaman Shugabanci 04.03.2022 16:01
Send us Fan Mail Mata a Najeriya na ci gaba da kumfar baki bayan majalisar dokokin kasar ta yi fatali da kudurin dokar wajabta ware musu kashi 35 cikin 100 na mukaman gwamnati da na jam’iyyun siyasa. Matan suna kuma bukatar majalisa ta kafa doka cewa duk mijin da suka aura dan wata kasa to ya zama dan Najeriya, albarkacinsu. Shirin Najeriya A Yau na dauke da dalilan da suka sa kudurorin dokar ba s...
Wahalar Man Fetur: Yadda Mutane Ke Yaba Wa Aya Zakinta 03.03.2022 13:07
Send us Fan Mail Karancin man fetur da ya biyo bayan shigowa da gurbataccen man fetur a Najeriya ya jefa al’ummar Abuja da sauran wurare a cikin halin ni-’yasu. Farsahin ababen hawa ya tashi, gami fa karancin ababen hawa na haya da ya tilasta wa fasinjoji yin doguwar tafiya a kasa, a yayin da gidajen mai da ’yan bumburutu ke cin karensu babu babbaka. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci na tafe...
Yadda ’Yan Najeriya Ke Rayuwa Cikin Kunci 01.03.2022 15:56
Send us Fan Mail Jama'a da dama a Najeriya na kokawa bisa yadda rayuwa ke kara kuntata lokaci bayan lokaci. Rana zafi inuwa kuna, har wasu ma kan ce jiya ta fi yau, suna kuma tsoron zuwan gobe. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci na tafe da bayanan halin da 'yan Najeriya ke ciki na tsadar rayuwa da matsanancin raunin tattalin arziki, mun kuma tuntubi masana kan hasashen abinda zai b...
Yadda Sabbin Dokokin Zaben Najeriya Za Su Shafi Harkokin Zaben Kasar 28.02.2022 15:10
Send us Fan Mail Bayan yi wa dokar zaben Najeriya garambawul, hankula sun fara karkata zuwa tunanin yadda wadannan sauye-sauye za su shafi harkokin zaben kasar. Shirin Najeriya A Yau ya yi bitar wadansu daga cikin wadannan dokoki domin gano irin sauyin da za su kawo wa harkokin zaben kasar, musamman babban zaben da ke tafe nan da kasa da watanni 12
Yadda Rikicin Rasha Da Ukraine Ya Dugunzuma ‘Yan Najeriya 25.02.2022 14:57
Send us Fan Mail Yakin da ya barke tsakanin Ukraine da Rasha zai shafi kasashen duniya da dama, musamman wadanda su ka dogara da samun kudin shiga ta hanyar fitar da danyen mai. a daya gefen kuma akwai yiwuwar a samu fantsamar kananan makamai cikin duniya sanadiyyar wannan yaki idan ya yi kamari. Shirin Najeriya A Yau na tafe da bayanan musabbabin rikicin da kuma hanyoyin da zai shafi sauran sassa...
Da Bazar Wa Za A Yi Rawa A Sabuwar Tafiyar TNM? 24.02.2022 16:03
Send us Fan Mail Yayin da zabukan 2023 ke kara karatowa, fagen siyasar Najeriya sai kara tumbatsa yake yi. Tuni ‘yan siyasa suka fara kai-kawo don fasalta bukatunsu da hanyoyin cimma buri. A wannan yanayi ne wasu gaggawa ‘yan siyasa, ciki har da tsohon Gwamnan Kano Rabi’u Musa Kwankwaso suka kudiri aniyar wata sabuwar tafiya. Sai dai wasu na ganin ba a fage horar wannan tafiya a ka lokaci ba, yayi...
Yadda Kwadayi Ke Jefa Masu Daukar Albashi Cikin Garari A Najeriya 22.02.2022 15:59
Send us Fan Mail Da dama daga cikin masu aikin albashi na kukan cewa albashinsu ba ya wadatarsu zuwa karshen wata. Wani lokacin ma kaji wadansu na cewa da bashi su ke karasa wata, wadansu ma masu shagunan unguwarsu na guduwa idan sun gansu musamman in wata ya yi nisa. Wai to daga ina matsalar take? Albashin ne ba ya isa, ko kuwa rashin tsari ne?
Yadda Daukar Doka A Hannu Ke Lakume Rayukan Mutane a Najeriya 21.02.2022 15:54
Send us Fan Mail Dabiar daukar doka a hannunsu ta yadda da an kama mai laifi kafin a yi bincike sai kawai a kaddamar da hukunci ta hanyar duka, sara ko sakawa mutum taya a wuya a zuba fetur a cinna wuta na kara karfi a tsakanin mutane a kwana kwanan nan. Rahotanni na yawan fitowa daga kudu maso yammaci da Arewa maso yammacin Najeriya kan hukuncin gurguzu ko kuma a ce daukar doka a hannu. Me yasa h...
Yadda 'Yan Daba Ke Juya Akalar Siyasar Najeriya 18.02.2022 15:29
Send us Fan Mail Bangar siyasa ta jima tana janyo hasarar dukiya, a wadansu lokutan ma in akayi rashin sa’a a rasa rai ma baki daya a Najeriya. Shirin Najeriya A Yau na wannna lokaci ya yi nazarin irin mumunan rawar da 'yan daba ke takawa wurin rikita harkokin zabe a kasarnan.
Wahalar Man Fetur; 'Yan Najeriya Na Yaba Wa Aya Zakinta 17.02.2022 14:52
Send us Fan Mail Tun farkon satin nan ake wahalar man fetur a babban birnin tarayyar Najeriya Abuja da kewa, sakamakon shigowa da gurbataccen man fetur din da a ka ce anyi a satin da ya gabata. Farsahin ababen hawa ya tashi, an kuma samu karancin ababen hawan da ya tilastawa da yawa fara tafiyar kafa. yayinda masu sayar da mai a galan da aka fi sani da 'yan bumburutu ke cin karensu babu babba...
Abin Da Abba Kyari Ya Fada Kafin A Kama Shi 15.02.2022 13:40
Send us Fan Mail Bayyanar suna da hotunan hafsan dan sandan nan da ya yi fice wajen yaki da masu garkuwa da mutane, DCP Abba Kyari, a matsayin wanda ke da hannu a safarar miyagun kwayoyi ya dauki hankalin ’yan Najeriya. ’Yan kasar sun rabu tsakanin masu gaskata bidiyon da masu ganin kirkirar sa aka yi saboda . Tun a kwanakin baya dai DCP Abba Kyari ya shiga tsaka mai wuya a zargin a badakalar damf...
Yadda Wayar Hannu Ta Zamo Jinin Jikin Mutane A Yau 14.02.2022 14:56
Send us Fan Mail Wayar salula na daya daga cikin manya-manyan abubuwan cigaban da aka samu a karni na 21 kuma ta samu tagomashi sosai ne bayan yaduwar kafofin sada zumunta. A kan haka ne mutane kan shafe tsawon lokaci suna gudanar da harkoki daban-daban ta wayoyinsu. Shin wadanne alfanu mutum zai samu daga yawan zama tare da wayar salula? Wadanne illoli kuma za a samu idan wayar ta zame wa mutum w...
Tasirin Harshen Koyarwa Kan Neman Ilimi 11.02.2022 15:02
Send us Fan Mail Mutane da dama na da tunanin idan aka koyar da karatu a harshensa na asali, zai samu saukin koyon abin da ake koya masa cikin dan lokaci. Shin me bincike ya nuna game da alakar harshen da aka koyar da mutum karatu da kuma fahimtarsa? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci na tafe da gamsasshen bayani akan wannan batu.
Yadda ’Yan Jarida Ke Rura Wutar Rikici A Najeriya 10.02.2022 15:44
Send us Fan Mail Mutane na yawan korafi kan yadda ’yan jarida ke canza musu maganarsu, wanda hakan ke rura wutar rikici ko tayar da ita. Shin wannan zargi gaskiya ne? Mene ne abun yi? Shirin Najeriya A Yau ya warware zare da abawa.
Rashin Shigar Da Matasa Harkokin Mulki, Laifin Waye? 08.02.2022 13:40
Send us Fan Mail Matasa ne kashin bayan kowace al'umma, domin su a ke fatan su gaji magabatansu, har a kan yi wa matasan wakar cewa, "yara manyan gobe". Sai dai a Najeriya har yanzu matasan basu fara gani a kasa ba, domin kuwa ba a tsarmawa da su a harkokin mulki. A ina matsalar take, kuma mene ne a ke yi ba dai dai ba?
Za a koma biyan kudin haya wata-wata a Abuja 07.02.2022 15:26
Send us Fan Mail Tsadar gidajen haya a Abuja ta sa yawancin mazauna birnin kan shafe shekara a koyaushe suna fadi-tashin tara abin da za su biya kudin haya. Duk da haka, wasu masu gidaje a birnin ba sa karbar kudin haya sai na shekara biyu zuwa sama. A kan haka ne Majalisar Dattawa ta fara aikin kafa dokar wajabta biyan kudin haya wata-wata a Abuja, maimakon shekara-shekara. ’Yan hayar Abuja sun b...
Kama Mana Maza Ya Sa Mu A Tsaka Mai Wuya —Matan ’Yan Canji 04.02.2022 14:37
Send us Fan Mail A ranar Alhamis ne matan ’yan canji daga Kasuwar Wapa da aka tsare suka ziyarci Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero domin neman ya sanya baki a bayyana musu halin da mazajen nasu suke ciki. Shirin Najeriya A Yau ya dauko cikakken rahoton halin da iyalan ’yan canjin suke ciki shekara guda tun bayan tsare su.
Ma'anar hijabi a idon duniya 03.02.2022 15:30
Send us Fan Mail A yayin da sanya hijabi ya kasance umarnin addinin Islama ga mata domin rufe tsiraici da kare mutuncinsu; dokokin kasashen duniya sun ba wa dan Adam damar yin addininsa ba tare da tsangwama ba. Sai dai kuma a lokuta da dama ana samun ce-ce-ku-ce game da sanya hijabi ko masu sanyawa. Shirinmu na yau ya mayar da hankali ne a kan hakikanin ma'anar hijabi.
Ka'idojin tuki da mutane suka dauka kwalliya ce 01.02.2022 15:29
Send us Fan Mail Shin kun san dalilin da ake yin zane-zanen da ke kan hanyoyin titi? Jama'a da dama, ciki har da wasu matuka sun dauka zane-zanen da ake yi wa tituna kwalliya ce; alhali kowanne daga cikin zane-zanen yana da ma'anarsa, kuma an yi shi ne da nufin kyautata tsarin tafiya a hanyoyin da zimmar kare rayuka da lafiyar matafiya da sauran masu amfani da hanya. Yau shirin Najeriya...
Fasa Janye Tallafin Man Fetur; Gwamnoni Sun Goyi Bayan Kungiyoyin Kwadago 31.01.2022 13:20
Send us Fan Mail Gwamnonin Najeriya na ganin ci gaba da biyarda tallafin man fetur din da Gwamnatin Tarayya ke yi ba abu ne mai iya dorewa ba, hakan tasa sukayi ta goyon bayan a cire wannan tallafi domin sanya wadannan makudan kudade a wasu bangarorin da 'yan Najeriya za su amfana da tallafin ka tsaye. Shirin namu na yau na tafe da bayanan sabuwar matsayar da gwamnonin Najeriya su ka dauka...
Laifin Wane Ne Rashin Daukar Masu Digiri Aiki A Najeriya? 28.01.2022 16:22
Send us Fan Mail Rashin samun aikin yi a tsakanin wadanda suka kammala karatu mai zurfi na ci gaba da janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin ’yan Najeriya, har wasunsu na yin da-na-sanin bata shekarunsu a yin karatun. Masana kuma na dora laifin rashin aikin yi a tsakanin matasa masu ilimin boko a kan rashin ingancin manhajar karatun kasar. Shin a ina gizo ke saka? Shirin Najeriya A Yau na tafe amsar wannan...
Zaben 2023: Wa zai kai Najeriya tudun mun-tsira 27.01.2022 12:58
Send us Fan Mail A yayin da zaben shekara ta 2023 ke kara karatowa, wane irin shugaba ne zai kai Najeriya tudun mun-tsira? Yawancin ’yan Najeriya dai sun kosa lokacin ya yi, su zabi shugaban da suke ganin zai share musu hawaye tare da magance matsalolin da suka yi wa kasar kullin goro. Shirin Najeriya A Yau, ya yi dubi kan irin shugabannin da Najeriya da ’yan kasar ke bukata domin fitar da jaki da...
Dalilan Gwamnatin Jihar Kano Na Dakatar Da Lasisin Makarantu Masu Zaman Kansu 25.01.2022 15:29
Send us Fan Mail Gwamnatin Kano ta dakatar da daukacin makarantun kudi na Jihar da nufin sake nazari a kan yadda ake gudanar da su, a cewarta. Matakin dai ya biyo bayan kururuwar da al’umma ta yi bayan gano gawar Hanifa Abubakar, wata daliba da ake zargin shugaban makarantar da take ya sace, ya kuma kashe ta. A shirin Najeriya a Yau za mu ji hikimar yin hakan da ma yadda hakan zai shafi ilimi a J...
Yadda Iyaye Da Malaman Makarantu Za Su Kare Lafiya Da Rayuwar ’Ya’ansu 24.01.2022 15:10
Send us Fan Mail Alaka ta yi tsami tsakanin iyaye da malaman makarantu tun bayan bayyanar labarin wani mai makarantar nan da ya sace, ya kuma kashe dalibarsa. Faruwar wannan lamari na barazana ga kyakkyawar alakar da ke tsakanin malamai da iyayen yara tun tale-tale. Mun tattaro hanyoyin da iyaye za su bi wurin tabbatar da tsaron ’ya’yayensu a hannun malaman makarantu.
Similar podcasts
Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.