Najeriya a Yau

News HA ↓ 958 episodes

Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.

Category

News

Podcast website

www.buzzsprout.com

Latest episode

Jun 23, 2026

Where to listen?

Podcasts in the app Replaio Radio Coming soon

Podcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts

Get it on Google Play Install for free Android 5M+ downloads · 4.8 rating iOS soon

Episodes

Yadda Aminu Kano Ya Fara Daukar Mace Mataimakiyar Dan Takarar Shugaban Kasa 19.04.2022

Send us Fan Mail Bayan shekara 38 da barin duniya, ’yan Najeriya na ci gaba da tunawa da Malam Aminu Kano a bangarori da dama. Jama’a da dama na kallon Malam Aminu Kano a matsayin wanda ya sauya akalar siyasar Najeriya ta hanyar zama mutum na farko da ya zabi zabi mace a matsayin ’yar takararsa ta mataimakin shugaban kasa. Shin kawo yanzu, burin Malam din na ganin an dama da kowa da kowa a fagen s...

Abin Da Ya Sa Aka Yafe Wa Dariye Da Jolly Nyame 18.04.2022

Send us Fan Mail Yafe wa tsohon Gwamnan Taraba Jolly Nyame da na Filato Joshua Dariye ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin ’yan Najeriya. Abin da da dama ke kallo shi ne irin kudaden da wadannan bayin Allah suka salwantar a lokacin da suke kan karagar mulki. Mene ne abin da doka ta ce danagne da yafe wa wanda ya zalunci al’umma da dama?  

Karshen Tashe A Kasar Hausa 15.04.2022

Send us Fan Mail Goman tsakiya na watan Ramadan lokaci ne da ake fatan gani a kasar Hausa, saboda ayyukan ibada da ake yawaitawa da kuma wasan tashe da ake nishadantar da jama’a a unguwanni da sauran wurare. Mene ne tarihin tashe da amfaninsa kuma ya aka yi ya rasa martabarsa da kimarsa a kasar Hausa?

Yadda ’Yan Bindiga Ke Sheke Ayarsu A Filato Da Taraba 14.04.2022

Send us Fan Mail ’Yan bindiga sun samu gangarar wadansu yankunan jihohin Taraba da Filato ta yadda duk lokacin da su ka ga dama suke zuwa su kaddamar da hari kan mutanen kauyuka daban-daban daga lokaci zuwa lokaci. Me ya kamata a yi kuma su wa ya kamata su taimaki wadannan mutane?

2023: Yadda Tinubu Ya Karbi Batun Takarar Osibanjo 12.04.2022

Send us Fan Mail Hankalin ’yan Najeriya ya koma kan yadda Uban Jam’iyyar APC na Kasa, Bola Ahmed Tinubu, da ke neman takarar shugaban kasa ya ji da fitowar Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osibanjo, takarar kujerar. Da wace fuska Tinubun ya karbi aniyar ta Osibanjo, wanda ake kallo a matsayin  yaron gidansa? Shin wuyan Osinbajo ya kai yanka? Wadanne kalubale takarar tasa take tattare da su?...

Yadda Ruwan Sha Ke Neman Gagaran Talakan Kano, Katsina da Jos 11.04.2022

Send us Fan Mail Jama'ar Kano, Katsina da Jos na fama da rashin ruwan sha da na ayyukan yau da kullum a cikin gida. Hakan ya jefa da yawa cikin mawiyacin hali.  A cikin shirin za ku ji yadda mutane ke barin gidajensu cikin dare domin neman ruwansha da na ayyuka.  Shirin Najeriya A Yau ya bankado inda gizo ke saka

Hukuncin Wanke Bakin Mai Azumi Da Rana 07.04.2022

Send us Fan Mail Jama'a da dama na tambayar halacci ko haramcin wanke baki da ashuwaki ko buroshi da man wankin baki da rana a wurin azumi. Wadansu  na ganin bai halatta mai azumi ya wanke bakinsa da rana ba, wadansu kuma na ganin ya halatta. Shirin Najeriya A Yau ya binciko matsayar manzon Allah (S.A.W) akan wanke baki da rana a wurin mai azumi.

Ko Watsi Da Tsarin Karba_Karba Zai Kai PDP Tudun Muntsira? 07.04.2022

Send us Fan Mail Bayanai sun karade Najeriya kan mai yiwuwa babbar jam'iyyar adawa ta kasar PDP ta yi watsi da tsarin karɓa_karɓa a wani yunkuri na ƙwace mulki daga hannun jam'iyya APC mai mulki a zaɓen baɗi.  Anya wannan yunƙuri zai kaita ga nasara kuwa? Saurari amsar wannan tambaya da ma waɗansu masu alaƙa. 

Yadda Dabino ya Zame Wa Mazauna Kudancin Najeriya Zuma 05.04.2022

Send us Fan Mail An so mai azumi ya fara bude bakinsa da dabino. Duba da cewa azumin watan Ramadan bai wajabta akan akasarin ‘yan kudancin Najeriya ba, amma duk da haka akwai Al’Ummar Musulmi a cikin su, to ko ta yaya su ke samun dabino domin dabbaka wannan sunnar? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci na tafe da bayanan yadda Musulmin wannan yanki ke samun dabino domin buda-baki.

‘Illolin kaurace wa zabe sun fi na kada kuri’a yawa’ 04.04.2022

Send us Fan Mail Bayan ya dade yana jan hankalin hukumomi game da bukatar daukar mataki a kan rashin tsaron da ya gallabi ’an Najeriya, wani limami ya yi kashedin cewa mutane ba za su fito zabe ba a 2023 idan ba a amsa wasu tambayoyi ba. Da jin haka, kwamitin masallacin da Sheikh Nuru Khalid yake jan sallar Juma’a ya ce malamin ya wuce gona da iri, yana tunzura mutane kada su fito zabe.  Shirin Na...

Yadda Sakacin Hukumomin Tsaron Najeriya Ya Hallaka Jama'a Da Dama 01.04.2022

Send us Fan Mail Binciken da kafar sadarwa ta Daily Trust ta gudanar ya gano cewa hukumomin tsaron Najeriya na da sanin cewa za'a kaiwa jirgin kasan Abuja zuwa kaduna hari ranar litinin din da ta gabata amma basu dauki matakan dakile harin da ya yi sandiyyar mutuwar 'yan Najeriya da dama ba. Daga ina matsalar take? saurari asirin da wannan bincike ya tona.

Ainihin Abinda Ke Hana Super Eagle Cin Nasara 31.03.2022

Send us Fan Mail Rashin nasarar da kungiyar kwallon kafa ta Najeriya "Super Eagle" ta yi a wasan da ta buga da takwararta ta kasar Ghana ya janyo musayar ra'ayi a Najeriya. Daga Ina matsalar ta samo asali? Menene ba'ayi dai-dai? Wa ke da bukatar ya yi gyara, kuma me ya kamata a gyara?

Yadda Maye Ya Cinye Aljan A Babban Taron APC 29.03.2022

Send us Fan Mail Magoya bayan Sanata Abdullahi Adamu da Sanata Umaru Tanko Al-makura na yi musu lakabi da maye da kuma aljan ko aljani, Abdullahi Adamu shi ne maye, Al-makura kuma aljani. Kafin APC ta gudanar da babban taronta na kasa, ‘yan siyasa musamman a Jihar Nasarawa sun yi ta cewa aljan zai cinye maye ko kuma maye zai cinye aljan. To wai ya ya aka yi maye ya cinye aljan?

Manyan Dalilan da Suka Sa aka zabi Abdullahi Adamu Shugaban APC 28.03.2022

Send us Fan Mail Zaben tsohon gwamnan Jihar Nasarawa, Sanata Abdullahi Abdullahi Adamu a matsayin shugaban jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ya bar tambayoyi da yawa a cikin zukatan jama'a. Ganin cewa Abdullahi Adamu na daya daga cikin wadanda su ka kafa jam'iyyar PDP, ya yi gwamna sau biyu a karkashin inuwar  PDP, ya taba zama sakataren kwamitin amintattu a PDP. Wadanne dalilai ne...

’Yan sandan da gaskiyarsu ta girgiza jama'a 25.03.2022

Send us Fan Mail Jinjinar da Shugaban ’Yan Sandan Najeriya ya yi wa wasu jami'ansa uku saboda kyawawan halaye da suka nuna ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin jama'a. Wadansu na ganin ai aikinsu suka yi, mene ne abin burgewa? Wadansu kuma na ganin sun yi abin a yaba, lura da yadda ’yan sanda a Najeriya ke rayuwa kan dan albashin da bai taka kara ya karya ba. Shin me ya sa ake mamaki idan dan...

Majalisa Ta Sakawa Dokar Da Za Ta Hana 'Yan Siyasa Sauya Sheka Hannu 24.03.2022

Send us Fan Mail Majalisa ta sakawa dokar da za ta hana ’yan siyasa sauya sheka bayan darewa kujerun mulki a Najeriya. Menene ke hana ’yan siyasa zama a jam'iyya daya tunda ance jam'iyya akidace, kuma ta wadanne hanyoyi wannan doka za ta taimaki siyasar kasar?

Yadda Kabilanci Ke Barazana Ga Hadin Kan Najeriya 22.03.2022

Send us Fan Mail Kabilanci na samun wurin zama a Najeriya sakamakon wadansu ƙaidoji da aka gindaya wurin karɓar bayanan jama'a a asibitoci da wuraren ayyuka. Tambayar garin asali da addini na ɗaya daga cikin ƙaidojin da ake zargin suna rura wutar ƙabilanci a tsakanin 'yan Najeriya.   Yaushe aka fara wannan ɗabi'a, akwai yiwuwar za'a daina kuwa? 

Yadda Ake Sayen Aikin Gwamnati A Najeriya 21.03.2022

Send us Fan Mail Batun samun aiki a ma’aikatu da hukumomin gwamnati bisa cancanta a matakin jihohi da gwamnatin tarayya ya tasan ma zama tarihi a Najeriya. A wadansu ma’aikatun kudi ake yanke wa kowane irin matsayi da matakin aiki, mai so ya biya, a ba shi. Shin wane tasiri hakan zai yi ga ci gaban kasar da ake kallo a matsayin uwa a Afirka?

Dalilan Da Mutane Ke Kashe Kansu Saboda Soyayya 18.03.2022

Send us Fan Mail Mummunan al'adar nan ta kashe kai saboda soyayya na kara karbuwa a tsakanin matasa a Arewacin Najeriya. Ko me ke janyo hakan? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya tattauna da masana lafiyar kwakwalwar dan Adam domin gano dalilan masu yin wannan aik-aika na kashe kai domin katsewar soyayya.

Abin Da Dokar Dan Takara Mai Zaman Kansa Ta Kunsa 17.03.2022

Send us Fan Mail Akwai yiwuwar korafe-korafe su ragu a fagen siyasar Najeriya idan dokar dan takara mai zaman kansa ta samu karbuwa a kasar. Majalisar Dokokin kasar ta amince mai bukatar tsayawa takarar da bashida jamiyya, ko kuma ba ya son alaka da wata jam’iyya ya tsaya da sunansa, jama’a su zabe shi da halinshi. Wadanne sauye-sauye wannan doka za ta kawo a siyasar Najeriya?

Gaskiyar Inda Mai Mala Buni Yake A Yanzu 15.03.2022

Send us Fan Mail Tun bayan daukar dimin da jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta yi,  jama’a ke cigiyar inda shugaban rikon jam’iyyar, Mai Mala Buni, ya shige. Shirin Najeriya A Yau ya zakulo inda shugaban rikon jam’iyyar yake a yanzu da kuma bayanan masana kan inda rikicin zai kai jam’iyyar idan ba a gaggauta daukar mataki ba.

’Yan Najeriya Miliyan 19 Za Su Rasa Abinci —Rohoto 14.03.2022

Send us Fan Mail Wani bincike da cibiyar Cadre Harmonisé (CH) da ke bincike kan samuwar abinci a kasashen Yammacin Afirka da yankin Sahel ta gudanar tare da gwmantin Najeriya ya gano mutum miliyan 19.4 a kasar za su yi fama da yunwa a cikin ’yan watanni masu zuwa. Rahoton ya nuna daga yanzu zuwa watan Agustan 2022, za a samu karin mutum miliyan biyar da ke fama da yunwa a jihohi 21 —kimanin mutum...

Majalisar Dattawan Najeriya Ta Kafe, Duk Mai Rike Da Mukamin Siyasa Sai Ya Taba Kasa In Yanason Takara 11.03.2022

Send us Fan Mail Majlisar Dattawa ta juya wa Shugaba Buhari inda ta kafe a kan dokar da ta haramta wa masu rike da mukaman siyasa tsayawa takara ko zaben tsayar da ’yan takara har sai sun yi murabus. Sashen da Buharin yake so majalisar ta soke na kunshe ne a sabuwar dokar zaben da Buharin ya sanya wa hannu a kwana-kwanan nan. Shin wane sauyi wannan sashe zai kawo musamman ga zaben 2023?

Yadda Rashin Wutar Lantarki Ya Jefa ’Yan Najeriya Cikin Kunci 10.03.2022

Send us Fan Mail A yayin da kusan kowane bangare na rayuka ke kara dogaro da amfani da wutar lantarki, samuwar watar sai kara wuya take a Najeriya, inda a halin yanzu bukatar wutar ke karuwa saboda matsanancin zafi da tsadar man fetur. Shirin Najeriya  A Yau na dauke da yadda ’yan kasar ke rayuwa a cikin duhu, rashin tabbacin samun wutar da kuma musabbabin matsalatar, wadda ta sa cibiyoyin kiwon l...

Ranar Mata: Yadda Magidanta Suke Koda Matansu 08.03.2022

Send us Fan Mail   Ranar 8 ga watan Maris ta kowace shekara ce Majalisar Dinkin Duniya ta ware ranar a matsayin Ranar Mata ta Duniya. Fiye da shekara 100 ke nan ake gudanar da bikin ranar  ta musamman da aka ware wa mata a fadin duniya, domin yaba musu da kuma nuna muhimmancinsu ga al’umma a matsayinsu na uwaye, abokan rayuwa, ’yan uwa da kuma ’ya’ya. Hakan ya sa wasu magidanta suka jinjina wa muh...

Listen to the Najeriya a Yau podcast in Replaio

Radio and podcasts in one app - free, with no sign-up. Install today and do not miss the launch

Get it on Google Play

Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.