Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Where to listen?
Podcasts in the app Replaio Radio Coming soonPodcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts
Episodes
Kalubalen ’Yan Takarar Shugabancin Najeriya A 2023 09.06.2022 14:40
Send us Fan Mail A ranar Laraba 8 ga watan Yuni, 2022 Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta kammala zaben fid-da gwanin da zai yi mata takara a babban zaben 2023. Kasantuwar akwai jam'iyyun hamayya da ke hankoron hankade jam'iyyar APC din daga karagar mulkin kasar, ko wadanne kalubale ’yan takarar kujerar shugaban kasa a Najeriya ke fuskanta? Ku biyo mu domin sauraron irin fata da m...
Hakikanin Abin Da Ya Faru A Owo, Jihar Ondo 07.06.2022 15:11
Send us Fan Mail A Ranar Lahadin da ta gabata, wasu 'yan bindiga suka kai farmaki kan wasu masu ibada, a wata cocin Katolika da ke kusa da gidan sarkin Owo wanda kuma garin gwamna Oluwarotimi Akeredolu ne na jihar Ondo. Sun kashe masu ibada da dama suka kuma jikata wasu. Shirin Najeriya a yau ya dubi yadda Al'amarin ya faru.
Yadda Matasa Za Su Mori Tsare-Tsaren Bayar Da Bashi 06.06.2022 14:57
Send us Fan Mail Matasa da dama na fama da rashin sanin hanyoyin samun bashi domin fara sana'a. A 'yan shekarun nan Gwamnatin Najeriya ta bayarda bashi ga manoma da masu kanana da manyan sana'a, sai dai da yawa matasan kasar na cewa basu san yadda ake neman wannan bashi ba, wasu kuma su ce in ma sun nema basa samu. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya binciko hanyoyin da mai...
Dalilan Da Matasan Najeriya Ke Raina Jari 03.06.2022 12:59
Send us Fan Mail A halin da ake ciki na rashin aikin yi a gwamnatin tarayya da na jihohi, matasan Najeriya na cigaba da kukan abin yi sakamakon rashin jari domin fara sana'a. Ko da yake wadansu na ganin ba jari matasan Najeriya ke bukata ba, lura da cewa jari domin fara sana'a baya kadan in anyi la'akari da bayanan da wadansu 'yan kasuwan ke yi. Shirin Najeriya A Yau na wanna...
Abin Da Ke Sa 'Yan Najeriya Karya Doka 02.06.2022 12:03
Send us Fan Mail Bin doka da oda na nuni ga sanin ya kamata a harkar rayuwa, amma a zahirin abinda ke faruwa a Najeriya shine jama'a da dama na ganin bin doka ya yi karanci a tsakanin mutane, ko mene ne dalili? Duk wanda ka taba zaice eh gaskiya ne yana karya doka amma mene ne ya hana a gyara? mun tattauna da 'yan Najeriya kan wannan sannan mun tuntubi wani masanin zamantakewa domin ne...
Yadda Tsawaita Lokacin Kamfen A Zaben 2023 Zai Shafi 'Yan Najeriya 31.05.2022 13:49
Send us Fan Mail Daga cikin sauye-sauyen da dokar zaben 2022 ta zo dasu akwai tsawaita lokacin yawon yakin neman zabe. Lura da yadda harkokin siyasa ke gudana a Najeriya, wane irin tasiri wannan sauyi zai kawo a fagen siyasar kasar, da kuma zaben 2023 idan Allah ya kaimu? Mun tattauna da wani masanin kimiyyar siyasa kan wannan batu. Ayi sauraro lafiya
Yadda Aka Yi Jina-Jina A Taron APC A Kano 30.05.2022 14:57
Send us Fan Mail Rahotanni sun bayyana yadda aka kashe mutum biyu aka kuma jikkata da dama a wurin zaben fid-da-gwani na APC a Kano. Ko yaya aka yi filin zabe ya koma fagen daga har da kisan kai? Mun tattauna da masu ruwa da tsaki a siyasar Kano, mun kuma tuntubi rundunar ’yan sandan jihar domin jin inda aka kwana.
Rayuwata Da Tsohon Ciki A Hannun Maharan Jirgin Kasa 27.05.2022 13:57
Send us Fan Mail Harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna na ranar 28 ga Maris ya rutsa da mata 18 ciki harda masu ciki. Wadansu matan sun haihu a cikin daji a hannun maharan, sannan sun sako wata mai cikin da ke sa ran haihuwa ko yau ko gobe. Mai cikin da ta kubuta tayi mana bayanin yadda ta rayu a hannun maharan, ta kuma bayyana mana bukatar maharan.
Gudummawar Da Kowa Zai Bayar Wa Wurin Kawar Da Ta'addanci 26.05.2022 15:00
Send us Fan Mail Zuwa yanzu ya fara zama zahiri a idanun duniya cewa Najeriya ta fada cikin taskun rashin tsaro da kullum yake mata barazanar cigaba da kasancewar ta kasa dunkulalliya mai shugabancin da ake yi wa biyayya. Tuni dai kasar ta ayyana kungiyoyin yan bindiga guda biyar a matsayin 'yan ta'adda. Hudu daga cikinsu a Arewacin kasar daya a Kudancin ta. To ko ta wadanne hanyoyi &a...
"Hukuma Ce Kadai Za ta Iya Hana Bara": Malamin Addini 24.05.2022 16:33
Send us Fan Mail Bara daya ce daga cikin batutuwan da ke ci wa yawancin jama’a tuwo a kwarya, musamman wanda kananan yaran da ake turowa birni karatun allo suke yi. Shin yaya matsayin bara da mabarata a addinin Musulunci? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya binciko wadanda aka yarda su yi bara da wadanda bai dace su yi ba.
Yadda Dokar Zabe Ta Tantance Daliget 23.05.2022 15:06
Send us Fan Mail kawo yanzu dai kasuwar daliget ne ke ci a kasuwar siyasar Najeriya, saboda karatowar zabukan fidda gwani a jamiyyun siyasar kasar. To sai dai kuma hankali ya koma kan gyaran da sabuwar dokar zabe ta yi kan wane ne daliget a zaben fidda wakilan da zasu wakilci jam'iyyun siyasa a zaben badi. Muna tafe da karin bayani kan dokar da ta tan-tan ce wane ne daliget da kuma fashin ba...
Podcast Din Aminiya A Idon Abokan Hulda 20.05.2022 13:29
Send us Fan Mail A ci gaba da murnar cika shekara daya da fara podcast din Aminiya, mun tuntubi abokan huldanrmu na ciki da wajen Najeriya domin jin yadda ta kasance a tsakaninmu da su kawo yanzu. S un bayyana ra’ayinsu dangane da shirye-shiryenmu da kuma abin da suke fata mu inganta.
Shekara 1 Da Fara Rediyon Aminiya Ta Intanet 19.05.2022 15:00
Send us Fan Mail Yau rediyon Aminiya ta intanet ke cika shekara guda da fara yada shirye-shiyensa. Daga ranar 19 ga watan Mayun 2021 da muka faro zuwa yau, mun wallafa shirin Najeriya A Yau sau 171 da kuma shirin Daga Laraba guda 53. Shirin namu na yau ya yi waiwaye ne kan yadda muka faro da kuma ra’ayoyin wadansu masu sauraro kan shirye-shiryen mu.
Wuraren Da Rashin Tsaro Zai Hana Noma Bana 17.05.2022 15:07
Send us Fan Mail Manoman da 'yan bindiga suka kora daga gidajensu na fama da zullumin yadda rayuwarsu zata kasance sakamakon rashin iya wata sana'a bayan noma; wanda a yanzu kuma babu halin yi. Wace barazana ke fuskantar Najeriya a sakamakon rashin samun wadataccen noma da za a yi?
Matsayin Daukar Doka A Hannu A Mahangar Shari’a 16.05.2022 14:48
Send us Fan Mail Mene ne kundin tsarin mulkin Najeriya ya ce kan wanda aka fusata shi ya dauki doka a hannunsa? Tun bayan abin da ya faru na zargin batanci ga Annabi Muhammad (SAW) a Sakkwato da daukar matakin da matasan Musulmi suka yi na halaka wacce ta yi batancin nan take, jama’a ke ta musayar ra’ayi kan matsayin shari’a kan wannan batu. Wakilinmu a Jihar Sakkwato ya fada mana halin da jihar k...
Yadda Dokar Zabe Ta Kawar Da ’Yan Fadar Buhari 13.05.2022 15:09
Send us Fan Mail Shin akwai lokacin da zababbun shugabanni a Najeriya za su sauka daga kujerunsu idan suna son tsayawa takarar zabe? Kawo yanzu dai, dokar zaben da Shugaba Muhammadu Buhari ya sanya wa hannu a watan Fabrairu ta wajabta mishi sauke ’yan fadarsa masu niyyar shiga zabe. Shin wane tasiri wannan sauyi da sabuwar dokar zai yi ga dimokuradiyyar kasar? Wadannan da ma wasu batutuwan da suka...
Hatsarin Da ASUU Ke Neman Jafa Najeriya A Ciki 12.05.2022 13:13
Send us Fan Mail Tunda daliban Jami'oi mallakar Gwamnatin Tarayya da na jihohi suka dawo gida sakamakon yajin aikin ASUU, masu nazari suka shiga bibiyar kalubalen da zaman wadan nan dalibai zai janyowa Najeriya. Shin wane hali yajin aikin ASUU ya jefa daliban kuma wane tasiri hakan zai yi a kan kasar?
Yadda Sauyin Yanayi Zai Shafi Daminar Bana 10.05.2022 15:02
Send us Fan Mail Alamu sun fara nuna yadda sauyin yanayi zai shafi daminar bana, bayan hasashen hukumomin Najeriya suka yi kan ruwan sama da kuma katsewarsa a farkon daminar. Ana ciki haka sai ga wata guguwa mai karfin gaske da ta shafi jihohin Adamawa da Katsina a makon jiya. Mun tattauna da Hukumar lura da yanayi ta Najeriya da kuma masanin kimiyyar noma domin jin yadda za a tunkari wadannan k...
APC A Idon 'Yan Najeriya Bayan Tara Fiye Da N20bn 09.05.2022 15:00
Send us Fan Mail Tun bayan bayyana kudin fom din takarar jam’iyyar APC ’yan Najeriya suke zura ido domin ganin wadanda za su saya. Rahotanni sun bayyana cewa kudaden da jam’iyyar ta tara kawo yanzu, sun sa yawancin ’yan Najeriya sun saki baki saboda mamaki, lura da yadda APC din take yawan ambatar yaki da cin hanci. ’Yan Najeriya da masu sharhi sun bayyana wa shirin Najeriya A Yau irin kallon da...
Bankwana Da Ramadan, Maraba Da Shawwa 29.04.2022 14:47
Send us Fan Mail A lokacin da watan Ramadan ya taho karewa, ta wace hanya za a kammala ibadun da suka rage domin neman yardar Allah? Wane ne ya kamata ya fitar da Zakkar Kono da ake bayarwa a karshen azumin Ramadan, yaya ake fitarwa kuma me ake yi? Malamai sun yi wa shirin Najeriya A Yau gamsasshen bayanai kan wannan batu da kuma sauran ibadun da ake so Musulmi ya gabatar a watan Karamar Sallah. A...
Za A Kai Harin Bom Wuraren Ibada_DSS 28.04.2022 15:58
Send us Fan Mail Kwana 30 da harin Jirgin Kasan Kaduna zuwa Abuja da ya yi sanadiyyar satar mutane da dama, Hukumar DSS ta yi hasashen sabbin hare-hare a wuraren ibada da na shakatawa. wane shiri gwamanti da limamai da fastoci ke yi da samun wannan labari daga hukumar DSS?
Yadda Bara Ta Shigo Karatun Allo 26.04.2022 15:09
Send us Fan Mail Batun yawon bara da almajirai ke yi a birane da ƙauyuka domin neman abinci da sutura ya ɗauki hankalin mutane a Najeriya. Wai shin bara wani yanki ne na karatun Allo ko kuma saɗaɗowa al'adar ta yi har aka wayi gari ba a iya raba karatun Allo da yawon bara? Yaushe aka fara yawon bara a tsarin karatun Allo? Shin kuskure ne ko kuma daidai ne? Shirin Najeriya A Yau na wannan lok...
Dalilanda Jiragen Sojan Najeriya Ke Yawan Yin Hatsari 25.04.2022 18:02
Send us Fan Mail Daga shekarar 2015 zuwa 2022 jiragen Sojan Najeriya 11 sunyi hatsari, wanda sanadiyyar wannan hatsari anyi asarar rayuka da dukiya mai yawan gaske. ko mene ne ke sa jiragen sojan Najeriya yawan faduwa, in ya fado wace irin asara ake tafkawa, shin an kamo hanyar gyara kuwa? Akwai amsoshin wadannan da ma wadansu tambayoyin a shirin namu na yau.
Yadda Za A Ribaci Kwanaki Goma Na Karshen Ramadan 22.04.2022 15:08
Send us Fan Mail Musulmin duniya baki daya na hankoron dacewa da falalar kwanaki goman karshe na watan azumin Ramadan. Sanin cewa a cikin wadannan kwanaki goma na karshen Ramadan ake riskan daren “Lailatul Kadari”, kirdadon wannan dare na sa Musulmin dagewa da ayyukan ibada. Wadanne ibadu aka fi son a yawaita a wadannan kwanaki masu alfarma?
Yadda Tsadar Takardar Takara Za Ta Shafi Zaben 2023 21.04.2022 13:05
Send us Fan Mail Kudin takardun takarar babban zaben 2023 ya ninku akalla sau biyu a kan na zaben 2019. Daga Jam’iyyar APC mai mulki zuwa babbar jam'iyyar adawa ta PDP har da sabuwar jam'iyyar NNPP, abin samma-kal. Mene ne dalili Ko me ya sa hakan faruwa? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci na tafe da karin bayani
Similar podcasts
Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.