Najeriya a Yau

News HA ↓ 958 episodes

Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.

Category

News

Podcast website

www.buzzsprout.com

Latest episode

Jun 23, 2026

Where to listen?

Podcasts in the app Replaio Radio Coming soon

Podcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts

Get it on Google Play Install for free Android 5M+ downloads · 4.8 rating iOS soon

Episodes

Har Sumewa Yar'uwata Ta Yi Saboda Ba Mu Sami Zuwa Hajjin Bana Ba 22.07.2022

Send us Fan Mail Maniyata da dama da suka yi niyyar zuwa hajji, sun yi jiran gawon shanu. Saboda wasu daga cikin su sun biya kudin tafiya hajji tun cikin shekarar 2020, Amma hakar su ba ta cimma ruwa ba. Ko mene ne dalili? Shirin Najeriya a yau ya tattauna da wadanda abin ya shafa da kuma masu ruwa da tsaki a harkar jigilar maniyata

Abin Da Ya Sa Annobar Kwalara Ta Ki Ci Ta Ki Cinyewa A Kano 21.07.2022

Send us Fan Mail Ana iya cewa cutar kwalara ta yi kakagida a Jihar Kano da ma wasu sassan Najeriya inda a duk shekara ake samun barkewar cutar, take kuma lakume rayuka. Ko a kwana-kwanan nan, ma’aikatar lafiya ta jihar ta ce cutar ta kashe mutum biyar daga cikin 189 da suka kamu da ita a kananan hukumomi 20 na jihar a cikin wata shida . Shin me ya sa ake yawan samun wannan cuta? Wai shin ina jami’...

Katobara 3 Da Buhari Ya Yi A Jere 19.07.2022

Send us Fan Mail Shin me ya sa kalaman Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ke jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin ’yan Najeriya? A baya-bayan nan furucinsa ya bar baya da kura, bayan ya ce da ’yan Najeriya sun san halin da ’yan wasu kasashe ke ciki, da sun gode wa Allah. A baya ya ce zai bar kasar fiye da yadda ya karbi mulkinta, daga baya kuma ya ce ya kagara ya bar mulkin kasar. Shin yaya masana da ’yan Naje...

PDP Ta Yi Waje Da APC A Jihar Osun 18.07.2022

Send us Fan Mail Zaben Jihar Osun ya nuna alumu da yawa cewa babban zaben 2023 zai bambanta da sauran zabukan da suka gabata a Najeriya. APC ta sha kaye, inda ta ci kuri'u 375,027, jam'iyyar PDP ta yi nasara da cin kuri'u 403,371. Hakan ya sa masana na cewa, 'yan  najeriya sun fara gane siyasa yanzu.  Shirin Najeriya a yau ya tattauna da mazaunan Osun, game da yadda suka kalli...

Yadda Muka Rayu Kwana 100 A Hannun 'Yan Bindiga 15.07.2022

Send us Fan Mail Idan ba a manta ba, ranar Asabar din da ta gabata ne aka saki fasinjojin da aka kwashe a jirgin kasan Abuja-Kaduna. Mutane na ta cece-kuce a kan ko an biya kudi aka sake su, ko ba a biya ba. Abokan aikinmu a aikin jarida, sun tattauna da daya daga cikin fasinjojin. Inda za a ji zahirin abin da faru a cikin shirin Najeriya a yau.

Dalilan Da Suka Sa 'Yan Najeriya Ba Sa Tuhumar Shugabannin Su 14.07.2022

Send us Fan Mail A Kasashen da suka ci gaba, da zarar ba su gamsu da shugabancin da ake masu ba,  za su mike tsaye don tuhumar shugabannin na su. Amma ba safai 'yan Najeriya ke yin irin wannan hobbasan ba. Sun iya hadiye ko wacce irin gurbatacciyar gwamnati. A Najeriya shugabanni suna tafiyar da harkokin mulkin kasa  yadda suka ga dama, ba ruwan su da ko yan kasa na jin dadin abun da suke yi,...

Yadda 'Yan Siyasa Ke Raba Kan 'Yan Najeriya, Su Kuma Kansu A Hade 12.07.2022

Send us Fan Mail Najeriya kasa ce da Allah ya yi mata arziki, dimbin arziki sosai.  Wasu mashaharanta ma suna cewa, duk duniya ba wanda ya ke da arziki irin Najeriya.  Amma kuma ba talakawan da su ke wahala, kamar talawakawan Najeriya. Talakawan kasar na biye wa siyasa da yan siyasa, su yi ta cece-kuce, da fada, da gaba, a wani lokacin ma har da kisan junansu a kan siyasa, a yayin da su kuma yan s...

"Yadda Na Yi Kundumbalar Ceto Fasinjojin Jirgin Kasan Abuja-Kaduna' -Tukur Mamu 11.07.2022

Send us Fan Mail Wajen watanni uku ke nan tun da ‘yan ta’adda suka kwashe wasu fasinjoji daga jirgin kasan Abuja-Kaduna. Wasu a cikin su sai da aka biya diyya sannan suka sake su, wasu kuma haka nan suka sake su. You Toh amma har yanzu da yawan su suna can wurin ‘yan ta’addan, inda suke bukatar gwamnati ta sakar masu yan’uwansu kafin su sake sauran pasinjojin A cikin watan Yuni ne, wani bawan Alla...

Haduwar Ranakun Arfa Da Juma'a A Hajjin Bana 08.07.2022

Send us Fan Mail Hajjin bana ya zo da falalar haduwar tsayuwar Arfa da ranar Jumma'a.  Wadannan ranaku ne masu mahimmanci ga Musulmin duniya,  wadanda ake karfafa yin azumi da addu'o'i a cikinsu. Za a yi Babbar Sallah a Najeriya cikin tsadar raguna,  shin anya za a ci nama kuwa a wannan sallar? Mene ne kuma hukunce-hukuncen layya? Shirin Najeriya a yau ya tattauna da malamai,  kuma...

Harin Gidan Yarin Kuje: ’Yar Manuniya Ta Nuna 07.07.2022

Send us Fan Mail Hare-hare a gidajen yari a Najeriya sun karu a Najeriya, inda a baya-bayan na aka kai hari ranar Talata 5 ga watan Yuli a Gidan Yarin Kuje da ke Abuja. Rahotanni sun nuna cewa 'yan Boko Haram ne suka kai harin inda  suka taimakawa yan uwansu tserewa da gidan. Shirin Najeriya a Yau, ya ji ta bakin 'yan Najriya da masana.   

‘Yadda Aka Nemi Yin Lalata Da Ni A Wurin Aiki’ 05.07.2022

Send us Fan Mail Shin me ke sa a wasu wuraren aiki ake neman yin lalata da ma’aikata? Duk da cewa an fi neman mata domin yin lalata da su a wuraren aiki, bincike ya nuna yanzu lamarin ya kai ga har mazan ma ba a bari ba. Shirin Najeriya A Yau ya tattauna da wata wadda ta taba samun kanta a irin wannan yanayi, ta kuma ji ta bakin da masana da sauran masu sharhi a kan wannan matsala.

Ainihin Dalilin Da Man Fetur Ke Wahala A Najeriya 04.07.2022

Send us Fan Mail Kimanin wata tara ke nan da 'yan Najeriya ke dan-dana kudar su saboda tsada da wahalar man fetur. A Gwamnatance dai Naira 165 ne kudin litar man fetur, amma a halin da a ke ciki ana sayar da litar mai sama da Naira 200, a kasuwar bayan fage ma har Naira 500 litar man fetur din tana kaiwa. Shirin ya binciko dalilinda aka kasa magance matsalar wahalar man fetur a Najeriya. 

Ayyuka Na Musamman A Kwanaki 10 Farkon Watan Dhul-hijja 01.07.2022

Send us Fan Mail Watan Dhul-hijja ne wata na 12 a jerin watannin kidaya a addinin Musulunci. A cikin wannna wata ake aikin hajji, babbar sallah da layya. Akwai ayyuka na musamman da malamai suka bayyana a matsayin ayyukan da Allah ke so kuma suke sa Shi ya jikan bayinsa ya gafarta musu. Mun tattaro irin ayyukan da ya kamata Musulmi ya gudanar a cikin wadannan kwanaki masu daraja. 

Tasirin Kawancen NNPP Da ‘Labour Party’ A Zaben 2023 30.06.2022

Send us Fan Mail Yunkurin neman jam’iyyar da za ta hana jam’iyyar APC zarcewa a mulki da kuma hana PDP dawowa kan mulki a Najeriya ya sa hankalin manazarta siyasa kallon rade-radin kawance tsakanin Jam’iyyar NNPP da Labour Party a matsayin mafita ga masu irin wancan tunani. Amma shin da gaske ne akwai maganar kawancen? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya binciko irin tasirin da wannan kawanc...

Irin Shaidar Karatu Da Ake Bukatar Masu Neman Shugabanci Su Mallaka 28.06.2022

Send us Fan Mail Tun bayan bayyana cewa dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar APC bai mika takardun shaidar karatunsa ga  Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC ta yi .  Wani rikici mai kama da wanda ya nemi tadiye shugaba Muhammadu Buhari a zaben shekarar 2015 ya tasamma Bola Ahmed Tinubu. Shin wane tasiri takardun shaidar kammala karatu ke da shi ga mai neman shugabancin kasa?  Wane irin kwa...

Yadda Aka Shake Ni Aka Kwakule Min Idanu Da Wuka 27.06.2022

Send us Fan Mail A Karshen makon da ya gabata an samu labarin kwakule idanun wanin almajiri a Jihar Bauchi. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya tattauna da wannan almajiri da aka kwakule wa idanu, ya kuma bukatar iyayensa da malaminsu da kuma matsayar rundunar 'yan sandan jihar kan wannan mummunan alamari.  A yi sauraro lafiya. 

Kamun Ekweremadu A Idon ‘Yan Najeriya 24.06.2022

Send us Fan Mail Tun bayan bayyanar labarin kamun tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya Sanata Ike Ekweremadu da mai dakinsa Kan Safarar Sassan Jikin dan Adam 'yan Najeriya ke ta musayar ra'ayi.  Shirin Najeriya A Yau ya bi diddigin labarin, ya kuma tattauna da 'yan Najeriya mazauna kasar Birtaniya kan kamun da aka yi wa Ekweremadu.  A yi sauraro lafiya 

Yadda Sojoji Suka Bindige Kanina Sabida Fetur A Neja 23.06.2022

Send us Fan Mail Rahotanni sun bayyana daga jihar Neja kan kisan wani matashi dake aiki a wani gidan man fetur sakamakon rashin jituwar da ta shiga tsakaninsu a ranar Litinin din da ta gabata.  Shirin namu na wannan lokaci ya yi bincike kan ainihin abinda ya faru. 

Dalilin Da 'Yan Boko Haram Ke Yanka 'Yan Jari Bola A Maiduguri 21.06.2022

Send us Fan Mail A 'yan kwanakin nan rahotanni sun bayyana cewa 'yan boko haram sun yanka 'yan jari bola sama da 50 a kasa da kwana 30 a Jihar Borno. Irin wannan hari dai ba kasafai ake samun irinsa ba. Ko me ya janwo hakan? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya tattauna da masu ruwa da tsaki daga Jihar Borno kan yadda abin ya kasance, wadanda aka kashe da kuma dalilin makasan....

Yadda Aka Yi Cinikin Kuri’a A Zaben Ekiti 20.06.2022

Send us Fan Mail Rahotanni daga Jihar Ekiti inda aka gudanar da zaben gwamna a ranar Asabar sun bayyana zargin  sayen kuri’a. Mun tattauna da jama’a daga jihar ta Ekiti kan gaskiyar abin da ya faru, mun kuma tuntubi masana shari’a kan matsayin mai sayen kuri’a da mai sayarwa da kuma wanda aka saya domin sa. A yi sauraro lafiya.

Dalilin Ruguguwar Jama'a Zuwa Yankar Katin Zabe 17.06.2022

Send us Fan Mail A daidai lokacin da ya rage mako biyu hukumar zabe ta Najeriya (INEC) ta rufe yin rajistar masu niyyar kada kuri'a a babban zabe da za a gudanar nan da wata takwas masu zuwa, jama'a na ta rububin zuwa a yi musu rajista. Wani bidiyo da ke yawo a kafofin sada zumunta ya nuna yadda wani fasto yana hana duk wanda bai zo da katin zabe ba shiga cocin da yake jagoranta. Ko me y...

Inda Dalar Shinkafar Najeriya Ta Yi Aure Ta Tare 16.06.2022

Send us Fan Mail Kusan wata biyar kenan da shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da dalar shinkafa a babban filin tashin da saukar jiragen sama na Nmadi Azikwei a Abuja. Taron bikin kaddamar da wannan dala dai ya janyo hankalin jama'ar kasar musamman yadda labaran adadin  buhun shinkafa miliyan daya da dubu dari biyu da aka gina wanna dala da su.  Ance anyi wannan dalar ne da z...

Yadda Muke So A Tsayar Da ’Yan Takara A Zaben 2023 —CAN 14.06.2022

Send us Fan Mail Tun bayan kammala zaben dan takarar shugaban kasa na Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya aka fara tunanin wanda zai yi wa dan takarar jam'iyyar Bola Ahmed Tinubu mataimaki. Kungiyar kiristoci ta Najeriya (CAN) ta gargadi jam’iyyar da cewa kar su sake su bari a yi shugaba Musulmi mataimaki ma Musulmi. Wannan kira na CAN ya janyo martani daga wurin jama'ar kasar. Shiri...

Shekara 23 Da Mulkin Dimokuradiyya; Ina Aka Kwana? 13.06.2022

Send us Fan Mail Ranar 12 ga Yuni na 2022 mulkin dimokuradiyya ke cika shekara 23 da kafuwa a Najeriya ba tare da samun wani cikas ba. A wadannan shekaru idan an saka kasar a fai-fai, cigaba aka yi ko kuma baya, mene ne ake bukatar a gyara a tafiyar da  dimukuradiyya Najeriya. 'Yan Najeriya sun tofa albarkacin bakinsu kan yadda su ke kallon yanayin mulkin a Najeriya, sannan mun tuntubi masana...

Yadda Tsadar Taki Za Ta Hana Noma Bana 10.06.2022

Send us Fan Mail A yayin da damina ke kara kankama a Najeriya, hankalin manoma ya koma gona da yadda za su samu takin zamani. Sai dai kuma tsadar da takin ke yi a halin yanzu na neman tilasta wa da yawa daga cikinsu fasa noman. Mun tattauna da wani kamfani mai sarrafa takin zamani domin jin dalilin da taki ya yi tashin gwaron zabo, mun kuma tuntubi wani malamin gona domin sanin ko akwai wata dabar...

Listen to the Najeriya a Yau podcast in Replaio

Radio and podcasts in one app - free, with no sign-up. Install today and do not miss the launch

Get it on Google Play

Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.