Najeriya a Yau

News HA ↓ 958 episodes

Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.

Category

News

Podcast website

www.buzzsprout.com

Latest episode

Jun 23, 2026

Where to listen?

Podcasts in the app Replaio Radio Coming soon

Podcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts

Get it on Google Play Install for free Android 5M+ downloads · 4.8 rating iOS soon

Episodes

Dalilin Da Har Yanzu 'Yan Bindiga Suka Ki Sakin Dalibin Bethel Baptist 05.09.2022

Send us Fan Mail Shekara guda da wata daya ke nan da satar daliba 121 na makarantar Bethel Baptist da ke Kaduna. An sako yara 120 daga cikin su amma har yanzu akwai dalibi daya da ke hannun su.  Ko menene dalilin da har yanzu wannan dalibi ke hannun 'yan ta'addan? Shirin Najeriya A Yau na kunshe da karin bayani.  Shirin Najeriya A Yau ya tsananta bincike kan dalilan da har yanzu 'ya...

"Dole A Gwada Kwarewarsu Kafin A Ba Su Aiki" - Tilde 02.09.2022

Send us Fan Mail Domin sauke shirin domin sauraro a duk lokacin da kuke so, latsa nan  Wadansu da suka samu horon koyarwa  a matakin farko wanda UNICEF da Gwamnatin Jihar Bauchi suka hada gwuiwa akai sun koka kan kin daukar su aiki a makarantun mallakin gwamnatin Jihar kamar yadda aka musu alkawarin lokacin turasu karatu.  To ko ya akayi labari ya sha bam_bam akan daukar malaman? Shirin Najeriya A...

Yadda Nada ’Yan APC Kwamishinonin INEC Zai Shafi Zaben 2023 01.09.2022

Send us Fan Mail Bayyanar sunayen wadansu ’ya’yan Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya a matsayin kwamishinonin zaben kasar da ke tafe a 2023 ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin kungiyoyi masu zaman kansu a kasar. Shin wane irin tasiri nada ’yan APC a irin wannan matsayin zai yi ga zaben na 2023 da ke tafe? Wannan shi ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya mayar da hankali a kai. 

Sauya Shekar Shekarau: Wa Gari Zai Waya? 30.08.2022

Send us Fan Mail Kasa da wata uku da sauya shekar tsohon Gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau daga Jam’iyyar APC zuwa NNPP, ya sake yin tsallen batake zuwa jam’iyyar PDP. A jiya ne tsohon Gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau ya tabbatar da fita daga jam’iyyar NNPP ya kuma shige jam’iyyar PDP kai tsaye. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya tattauna da masu ruwa da tsaki akan wannan batu. 

Yadda Kabilanci Ke Neman Hana Banki Gina Kasuwar Taminus Ta Jos 29.08.2022

Send us Fan Mail Yunkurin wasu kungiyoyi na hana Bankin Jaiz sake gina Kasuwar Taminus da ke Jos a Jihar Filato ya bar baya da kura. Rahotanni sun bayyana cewa kasuwar da ake takaddamar sake ginawa ita ce ginanniyar kasuwa  mafi girma a Afirka ta Yamma. Shin me ya sa kungiyoyin ba sa so a  sake gina kasuwar? Shirinmu na yau ya binciko irin asarar da ake tafkawa a dalilin  rashin kasuwar da ma wasu...

Ranar Hausa Ta Duniya: Yadda Harshen Uwa Zai Taimaka Wurin Inganta Ilimi 26.08.2022

Send us Fan Mail Tun 26 ga watan Agustan shekarar 2015 aka fara bikin Ranar Hausa ta Duniya, wanda a bana ake bikin karo na takwas. Wadanne abubuwa ya kamata Hausawa da masu magana da harshen su sani a wannan zamani? Tun 26 ga watan Agustan shekarar 2015 aka fara bikin Ranar Hausa ta Duniya, wanda a bana ake bikin karo na takwas. Wadanne abubuwa ya kamata Hausawa da masu magana da harshen su sani...

Zaben 2023: Zai Yiwu A Aika Sakamako Ta Intanet? 25.08.2022

Send us Fan Mail Batun gwama aikawa da sakamakon zaben 2023 ta kafar intanet da kundin hannu, na ci gaba da daukar hankalin ’yan Najeriya da masu sha’awar siyasar kasar.  Wadanne matsaloli wannan yunkuri ke fuskanta?  Mun tattauna da jami'an INEC da kuma masanin fasahar zamani kan wannan batu.  A yi sauraro lafiya 

Kalubalen Da Ke Tattare Da Tubar Bello Turji 23.08.2022

Send us Fan Mail Rahotanni sun tabbatar cewa shahararren dan ta’adda, Bello Turji ya tuba, ya kuma rungumi zaman lafiya har ma ya fara kaddamar da hare-hare a kan ’yan ta’addar da ba sau daina kai wa jama’ar jihar hari ba.  Mene ne gaskiyar wannan batu, kuma wane kalubale tubar Turji ke tattare da su? Shirin Najeriya A Yau ya ji ta bakin masana kan wannan batu.

Gaskiyar Batun Kyautar Motocin Yakin Da Najeriya Ta Bai Wa Kasar Nijar 22.08.2022

Send us Fan Mail Kwanakin baya Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa ta baiwa Gwamnatin Nijar kyautar motocin yaki na sama da naira miliyan dubu. wanna kyauta ta janyo ce-ce-ku-ce da musayar ra'ayi a wannan lokaci. Shin ya dace a halin da Najeriya ke ciki na fama da matsanancin rashin tsaro ta yi kyautan motocin yaki?  Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya bi diddigin wannan labari, ya kuma...

Yadda Fasa Madubin Mota Ya Yi Sanadiyar Rasa Rayuka A Ajase Jihar Kwara 19.08.2022

Send us Fan Mail Mako guda bayan mutuwar mutane sama da 10, da jikkatar da dama a wata kasuwar dabbobi dake Ajase a Jihar Kwara sakamakon rikicin da ya barke tsakanin Fulani da 'yan kungiyar OPS sanadiyyar fasa madubin mota da wata saniya ta yi.  A kwai cikkaken bayanin halin da ake ciki zuwa yanzu a cikin wannan shirin. 

Kalubalen Da Ke Gaban Mata A Zaben 2023 18.08.2022

Send us Fan Mail Hukumar Zaben Najeriya (INEC) ta bayyana cewa matasa da mata ne kaso 75 cikin dari na wadanda suka cancanci kada kuri'a a zaben 2023.  Ko wannan na nuna cewa mata ne zasu  juya akalar zaben na 2023?  Shirin namu ya yi nazarin wannan bayani na INEC ya kuma ji ta bakin matan, domin sanin irin kalubalen dake gaban su a zabukan da za a gudanar a badi. 

Yadda Ake Ririta Jari A Kasuwanci 16.08.2022

Send us Fan Mail Jari domin fara sana'a da ririta jarin a harkar kasuwanci na daya daga abubuwan da ke ci wa jama'a da yawa tuwo a kwarya.  To amma mene ne ke janyo narkewar jari a harkar kasuwanci ? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya tattauna da masu ruwa da tsaki a harkar kasuwanci, domin baiwa masu bukatar fara kasuwanci shawara mafi dacewa.

Yadda Sojoji Suka Shiga Wurin 'Yan Ta'adda Suka Ragargajesu": Ganau 15.08.2022

Send us Fan Mail A karshen makon da ya gabata ne rundunar sojan Najeriya suka yi nasarar shiga wani kauye a karamar hukumar Chukun suka ragargaji wadansu gungun yan ta'adda.  Rahotanni sun tabbatar cewa kauyen da jami'an sojan suka kashe 'yan ta'dddar a ciki babu mutumin kirki ko daya, sakamakon kwace garin da 'yan ta'addan suka yi.  A shirin namu na yau mun tattauna...

Yadda Kwadayi Ya Kai ’Yan Najeriya Tashar Wulakanci A Aljeriya 12.08.2022

Send us Fan Mail Wadansu ’yan Najeriya da kwadayin albashi mai tsoka ya ja su ka yi tafiya zuwa kasar Aljeriya sun gamu da gamonsu, domin kuwa suna dandana kudarsu da yunwa da talauci. Wai dama irin wadannan tafiye-tafiyen da  jama’a ke yi a yanzu na da hadari ne? Shirin Najeriya A Yau ya ji ta bakinsu kan wannan tafiya da kuma halin da suka tsinci kansu tun daga kan hanya har zuwa kasar Aljeriya.

Yadda Sabuwar Dokar Zabe Za Ta Hana Magudi A 2023 11.08.2022

Send us Fan Mail Sauye-sauyen da aka yi wa dokar zaben Najeriya sun karfafa amfani da fasahar zamani domin toshe hanyoyin murdiyar zabe.  Shin tura sakamako kai tsaye daga rumfunan zabe zuwa intanet ta yadda kowa zai iya gani a fadin duniya zai kawar da magudi a zaben 2023?  Shirinmu na yau ya mayar da hankali ne kan tasirin sabbin  sauye-sauyen kan zaben da ke tafe a 2023. 

’Yan Najeriya Za Su Fara Yin Wayar Minti Biyu a N100 09.08.2022

Send us Fan Mail Gwamnatin Najeriya za ta kara kudin sayen data zuwa N2,500 a kan gigabyte daya. Sabon matakin biyan harajin zai ninka kudin kiran waya daga N20 zuwa Naira 40 a duk minti daya. Shin yaya ’yan Najeriya ke kallon wannan lamari?

Yadda ‘IPOB’ Ta Yi Wa ’Yan Nijar 7 Kisan Gilla A Imo 08.08.2022

Send us Fan Mail Wasu mahara da ake zargin ’yan ta’addan haramtacciyar kungiyar IPOB ne sun yi wa wasu ’yan kasar Jamhuriyyar Nijar bakwai kisan gilla a cikin gidansu a Jihar Imo da ke Kudancin Najeriya. Bincikenmu ya gano ba wannan ba ne karon farko da ake yi wa ’yan Nijar kisa cikin ruwan sanyi a yankin. Shin ta yaya hakan zai shafi alakar Nijar da Najeriya? Shirin Najeriya A Yau ya tattauna wan...

"Yadda Malamin Mu Ya Dagargazamin Kashin Wuya" Dalibar Makaranta 05.08.2022

Send us Fan Mail Ranar Laraba 21 ga watan Yulin 2022, Aminiya ta ruwaito labarin wata yarinya  yar makarantar sakandire a zariya da wani malami ya buga da gora a wuya. Shirin Najeriya  A Yau na wannan lokaci ya binciko wannan yarinya, ya tattauna da ita, kuma ji halin da ake ciki a yanzu. Domin sauraron matakin da iyayen wannan yarinya su ka dauka, da irin matakin da hukumomi suka dauka, ku saurar...

Shirin da matasan Najeriya ke yi wa zaben 2023 04.08.2022

Send us Fan Mail A yayin da zaben 2023 ke kara karatowa, hankalin duniya ya fara dawowa Najeriya. lura da irin adadin 'yan kasar da kuma zaman ta giwar Afirika.  Masu hikima na cewa matasa ne kashin bayan al’umma, shakka babu, ko wane irin tanadi matasan ke yi wa wannan zabe da zai baiwa sabbin shugabanni damar mulkarsu har na tsawon shekara hudu? Wannan shine batun da shirin namu na wannan l...

Abin Da Ya Sa Burodi Ba Zai Daina Tsada Ba Yanzu 02.08.2022

Send us Fan Mail Shin me ya sa burodin ke tsada ne? Burodi dai abu ne da ya zama babban abin karin kumallon yawancin iyalai, wanda kuma suke samu ba tare da jibin goshi ba sosai. Shin me ya sa yanzu burodin ke tashin gwauron zabo yake neman gagarar talaka? Shirin Najeriya A Yau ya tattauna da ’yan Najeriya, mai sayar da fulawa, masu gasa burodi da masanin tattalin arziki.

Yadda 'Yan Najeriya Ke Kallon Batun Tsige Buhari 01.08.2022

Send us Fan Mail  Tun ranar 28 ga Watan Yulin 2022 ne yan majalisar dattawan Najeriya na jamiyyun adawa suka fara batun tsige shugaba Muhammadu Buahri, kafin daga bisani takwarorinsu na majalisar wakilai su bi sahun su na ganin an tsige Buhari.  Batun tsige Buhari na daga cikin batutuwan da ke cin kasuwarsu a tsakanin jama'ar kasar. Shirin Najeriya A Yau ya binciko yadda batun ya samo asali,...

Hukuncin Dauri Kafin A Rataye Abdulmalik Bai Mana Ba —Dangin Hanifah 29.07.2022

Send us Fan Mail Iyayen karamar yarinyar nan Hanifa Abubakar, wadda malaminta ya sace sannan ya kashe ta a Kano, sun ce ba su gamsu da hukuncin daurin shekara biyar kafin a zartar mishi da hukuncin rataya ba. A ranar 28 ga watan Yulin shekarar 2022 kotu ta yanke wa Abdulmalik Tanko da abokinsa wurin kisan Hanifa hukuncin dauri a gidan gyaran hali da kuma kisa ta hanyar rataya bayan sun cinye wa’ad...

Matsalar Tsaro Zai Iya Kawo Wa Zaben 2023 Cikas 28.07.2022

Send us Fan Mail Shin za a yi zabe a wasu  kauyukan karkarar kuwa a zaben 2023?  Ta'addanci dai ya yi kakagida a jihohin Kaduna, Katsina, Neja da Zamfara. Ganin cewa  an sami karancin yin rajistar katin zabe a wadannan yankuna, wasu kungiyoyi masu zaman kansu ne ke taimakawa wasu yankunan karkara yin rajistar katin zaben. Shirin Najeriya a yau ya tattauna da hukumar zabe mai zaman kanta ta ka...

Rashin Tsaro Ya Jawo Tsugunu Tashi A Makarantar FGC Kwali, Abuja 26.07.2022

Send us Fan Mail Harin ’yan bindiga ya sa Ma’aikaatar Ilimi ta Tarayya rufe Makarantar Sakandaren Gwamnatin Tarayya ta Kawali a Abuja. ’Yan ta’adda sun kai hari ne a kauyen Sheda da ke makwabtaka da makarantar a kan babbar hanyar Abuja zuwa Lakwaja. Shirin Najeriya A Yau ya tattauna da tsofaffin daliban makarantar da masu ruwa da tsaki a al'amarin.

Muhammad Abacha Ya Ga Samu Ya Ga Rashi A Zaben PDP A Kano 25.07.2022

Send us Fan Mail Dambarwar siyasa ta sake barkewa tsakanin 'yan siyasa na Jam'iyyar PDP a jihar Kano. Wannan rikici ya sake bayyana a fili a karshen makon nan da ya gabata. Idan ba a manta ba daman zaman doya da manja ake yi a Babbar hammayar jam'iyar ta PDP, tsakanin bangaren Ambasada Aminu Wali da bangaren Shehu Wada Sagagi. Shirin Najeriya a yau ya tattauna da 'yan Najeriya...

Listen to the Najeriya a Yau podcast in Replaio

Radio and podcasts in one app - free, with no sign-up. Install today and do not miss the launch

Get it on Google Play

Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.