Najeriya a Yau

News HA ↓ 958 episodes

Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.

Category

News

Podcast website

www.buzzsprout.com

Latest episode

Jun 23, 2026

Where to listen?

Podcasts in the app Replaio Radio Coming soon

Podcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts

Get it on Google Play Install for free Android 5M+ downloads · 4.8 rating iOS soon

Episodes

Yadda Burodi Ya Hargitsa Rayuwar Wasu ’Yan Najeriya 18.10.2022

Send us Fan Mail A yayin da ake fama da tsadar rayuwa a fadin duniya,  yanzu haka a Najeriya burodi – wanda shi ne abin karin kumallo a kusan kowanne gida – ya zama sai dan wane da wane. Ko me ya sa haka? Shirin Najeriya a yau ya binciko mana yadda aka yi aka haihu a ragaya.

Yajin Aikin ASUU: Nasara Ko Asara? 17.10.2022

Send us Fan Mail Janye yajin aikin da Kungiyar Malaman Jami'o'in Najeriya (ASUU) ta yi a karshen makon da ya gabata na ci gaba da shan fassara daga wurin jama'ar Najeriya. Wasu na cewa yajin aikin ma ba shi da wani amfani, lura da cewa sun janye ba tare da an biya musu bukatarsu ko guda daya ba.  Shin da gaske ne yajin aikin ASUU bai tsinana komai ba?  Shirin Najeriya A Yau na wanna...

‘Mu ke da alhakin sayen audugar Al'adar ’ya’yanmu’ 14.10.2022

Send us Fan Mail Mata na bukatar tsaftace jikinsu duk lokacin da suke al’ada. Ko kun san akwai yara mata da ke fasa zuwa makaranta saboda rashin audugar al’ada? Saurari shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci domin jin taskun da ’ya’ya mata ke ciki sanadiyyar jinin al’ada.

Yadda Za Ku Yaki Alkawurran Bogi A Zaben 2023 13.10.2022

Send us Fan Mail ’Yan Najeriya sun jima suna kukan yadda ’yan siyasa ke zambatarsu da alkawuran ayyukan more rayuwa, amma daga bisani sai su karya wadannan alkawurra, su ki cikasu, su kuma sake dawowa su kara yaudarar jama’ar duk kakar zabe.  Shin me ya sa ’yan Najeriya ke fadawa tarkon irin wadannan ’yan siyasa a koyaushe? Saurari wannan kashi na shirin Najeriya A Yau domin jin hanyoyin da za a b...

"Ban So Ba Aka Yi Min Aure A Shekara 14 " 11.10.2022

Send us Fan Mail Yau take ranar ‘yaya mata ta duniya, kuma ko’ina ana tunawa da su ta bangarorin rayuwa dabam-dabam. ‘Ya mace, mutum ce kyakkyawa da ban sha’awa, shi ya sa wani lokaci a kan mata kirari da son kowa kin wanda ya rasa.  Shirin Najeriya a yau, saboda murnar zagayowar ranar ta tunawa da ‘yaya mata ta duniya, ya duba nasabar shi da ‘auren wuri’. 

Yadda kasafin Ban-kwanan Buhari Zai Shafi Rayuwarku 10.10.2022

Send us Fan Mail  Kasafin kudin shekarar 2023 da shugaba Buhari ya gabatar ne dai kasafi mafi yawa a tarihin Najeriya.   Wadanne bangarori wannan kasafi na karshe da Buahri ya yi zai shafi rayuwar jama'ar da su ka zabe shi harda mai-mai? Saurari dalilan da wannan kasafin ya fi duk wadanda aka yi a baya yawa, da kuma tanadin da aka yi wa 'yan kasar domin sharbar romon dimokuradiyya.  

Yadda Abinci Ke Cigaba Da Ajalin 'Yan Najeriya 07.10.2022

Send us Fan Mail  A kwanakin nan rahotannin mutuwar jama'a da dama a gida daya ko unguwa daya sakamakon cin wani abinci da aka sarrafa a tare sun karade kafafen yada labarai.  Shin wane abinci ne ke dauke da gubar da ke ajalin jama'a, kuma ya za ayi a ganeshi a kuma shawo kan matsalar?  Saurari shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci domin kare kai da masoya daga  fadawa hadarin gurbatacc...

Ko kayyade Kudaden Kamfen Zai Kawo Zabe Mai Tsafta a 2023 06.10.2022

Send us Fan Mail Hukumar INEC ta kara jaddada bukatarta ga  ’yan takara da jam’iyyu cewa su yi wa dokar da ta kayyade kudaden kamfen din zaben 2023 biyayya, a wani yunkuri na tabbatar da anyi zabe mai inganci.  Shin sanya iyakar kudin da za a kashe a yakin neman zabe zai yi tasiri wurin samun sahihin zabe?  Saurari bayanai da ga bakin INEC da masu ruwa da tsaki a harkokin zabe. 

Yadda Ruwan Kasashen Ketare Ke Janyo Ambaliya A Najeriya 04.10.2022

Send us Fan Mail Masu nazarin yanayi sun bayyana cewa an fi shekara 50 ba a samu ambaliya kamar ta bana ba a Najeriya. Ko me ya sauya aka samu yawaitar ruwan da ya zame iftila’i ga mutane da dama?  Saurari shirin domin jin abin da ya faru. 

Ƙarshen Boko Haram; Yadda Aka Yi Bikin Cikar Najeriya 62 A Borno 03.10.2022

Send us Fan Mail Shekara 12 da 'yan ta'adda suka yi suna cin karensu babu babbaka a Maiduguri Jihar Borno ta sanya tsawon wannan shekaru ba a bikin ranar 'yancin kai sai bana.  Ko a halin yanzu ana iya cewa an samu zaman lafiya a Maiduguri?  Saurari cikakken shirin domin jin hakikanin halin da Jihar Borno ke ciki. 

Shin Karin Kudin Ruwa Zai Hana Tsadar Kaya? 30.09.2022

Send us Fan Mail Karin kudin ruwa da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya yi zuwa 15% na ci gaba da janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin ’yan kasar, wadanda ke kukan tsadar kayan masarufi yya ya addabi akasarinsu. CBN dai ta ce ta dauki matakin ne domin shawo kan matsalar tsadar kayan masarufi da koma bayan tattalin arizki.  Shin da gaske karin zai hana kayan masarufi tashin gwauron zabo? Saurari shirin Najeri...

Ko Rikice-rikicen Cikin Manyan Jam’iyyu Zai Baiwa Masu Tasowa Nasara A Zaben 2023? 29.09.2022

Send us Fan Mail Hukumar INEC ta dage wa ’yan takarar takunkumin yakin neman zaben 2023 daga ranar Laraba 28 ga watan Satumbar da muke ciki. A yayin da aka ’yan takarar suka shiga fafutikar neman jama’a su zabe su, rikice-rikicen cikin gida sun dabaibaye manyan jam’iyyun siyasar Najeriya. Shi rikcin cikin gidan manyan jam’iyyun zai bai wa masu tasowa damar kai bantensu a zaben 2023?  Saurari shiri...

Yadda 'Yan Ciranin Katsina Ke Safarar Makamai Daga Legas 27.09.2022

Send us Fan Mail A lokacin da ake faman yaki da ta’addanci a Najeriya, an kama wadansu ’yan ci-rani dauke da buhunan albarusai da miyagun kwayoyi a wata tashar mota a Jihar Legasa karshen makon da ya gabata.  Wadanda ake zargin ’yan Arewa ne kuma suna hanyarsu ne kai makaman zuwa yankunansu; Shi me ya sa suka fada wannan muguwar sana’a? Saurari shirin Najeriya A Yau domin sanin yadda abin ya faru...

Yadda Manoma Suka Ragargaji ’Yan Bindiga A Taraba 26.09.2022

Send us Fan Mail Manoma daga garuruwa akalla 30 na kananan hukumomin Gassol da Bali Jihar Taraba sun kori ’yan bindiga daga yankunansu sun koma gonakinsu kai tsaye. Shin me ya bai wa manoman kwarin gwiwar daukar wannan mataki? Shirin Najeriya A Yau ya tattauna da masu ruwa da tsaki a wannan kokari, ya kuma ji ta bakin masanin tsaro kan abin da wannan ke nunawa a yaki da ta’addanci.

Halin Da ’Yan Gudun Hijirar Bama Ke Ciki Bayan Komawa Garinsu 23.09.2022

Send us Fan Mail A kokarin Gwamnatin Borno na wanzar da zaman lafiya a jihar, ta mayar da ’yan gudun hijira jihar garuruwansu bayan sun shafe shekaru a sansanonin gudun hijira, sakamakon rikicin Boko Haram. To ko a wane hali tsoffin ’yan gudun hijirar da aka mayar gidajensu ke ciki? Saurari cikakken shirin domin jin halin da wadannan bayin Allah da ta’addanci ya sauya wa rayuwa suke ciki bayan sun...

Ko Yakin Neman Zabe A Kafafen Sada Zumunta Zai Yi Tasiri A Zaben 2023? 22.09.2022

Send us Fan Mail Ranar Laraba 28 ga Satumba da muke ciki ’yan takarar zaben 2023 za su fara yawon tallata manufofinsu ga ’yan Najeriya, gabanin babban zaben kasar da za a gudanar a watan Fabrairu da Maris na 2023.  Lura da yadda kafafen sada zumunta suka yi tasiri a zabukan 2009 a Amurka, Rasha da sauran manyan kasashen duniya, kuna ganin yakin neman zabe a kafafen sada zumunta a Najeriya zai yi w...

Irin Asarar Da Cin Ganda Ke Janyo Wa Tattalin Arzikin Najeriya 19.09.2022

Send us Fan Mail Fatar dabbobi da ake gyarawa ana ci da aka fi sani da ganda ko kpomo na daga cikin arzikin da Allah Ya huwace wa Najeriya, domin kuwa bayan ci a matsayin nama ana amfani da fatu da kiraga wurin yin takalma da jaka da sauransu. Shin kun san irin asarar da masu cin ganda a matsayin nama ke janyo wa Najeriya kuwa? Saurari cikakken shirin domin sanin yadda za a sarrafa ganda domin sam...

Yanka 11 Na Gani A Jikin Ummita - Mai Wankan Gawa 19.09.2022

Send us Fan Mail A Yau mun bi diddigin yadda wani dan kasar Chana Mr Geng da ke soyayya da wata 'yar Najeriya  UmmuKhulsum (Ummita) ya caccaketa da wuka har sau 11, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarta. Ko mene ne ya yi zafi har Geng ya dauki wannan danyen hukunci akan masoyiyar ta sa?  Ku biyomu cikin shirin domin sauraron yadda abin ya kasance.  

Abubuwan Da Mutuwar Sarauniyar Ingila Za Ta Sauya 16.09.2022

Send us Fan Mail Ranar litinin 19 ga Satumbar wannan shekarar ake sa ran yin jana’iazar Sarauniyar Ingila,  Elizabeth II, wadda ta mulki kasashe 15 shekara 70 da ta yi a  kan karagar mulki.  Mutuwar Sarauniya Elizabeth II zai kawo sauye-sauye da dama a kasashen 15 da ke karkashin mulkinta, ciki har da sauyin takardun kudi a kasashen. Saurari cikakken shirin domin sanin irin sauye-sauyen da za su b...

Dalilin Da INEC Ta Soke Rajistar Mutum Miliyan 1.2 15.09.2022

Send us Fan Mail A ci gaba da shirye-shiryen zaben 2023, Hukumar Zabe Ta Kasa (INEC) ta bayyana soke rajistar zaben mutum 1,126,359 daga cikin mutum 2, 523,458 da suka yi rajista daga watan Yunin 2021, zuwa 14 ga Janairu na 2022. Me ya sa  hukumar ta soke su, ina makomar wadanda aka soke wa rajista, kuma ta wadanne bangarori matakin na INEC zai shafi zaben 2023 mai karatowa? Ku biyo mu cikin shiri...

’Yan Kudu Sun Mayar Da Mu Abin Kashewa A Yankinsu —’Yan Arewa 13.09.2022

Send us Fan Mail ’Yan Najeriya na yi wa kasarsu kirari da cewa ‘kasa daya, al’umma daya’. Amma ’yan Arewacin kasar mazauna yankin Kudu sun koka bisa yadda suka yi zargin an mayar da su abin kashewa da kuma tsangwama a yankin da suke zama. Shin ina ’yancin da tsarin mulkin Najeriya ya bai wa kowane dan kasar na zama a duk inda yake so a bisa doka, ba tare da an cutar da shi ko an nuna masa wariya b...

Dalilin Da Masu Shiga Tsakanin Hukumomi Da ’Yan Ta’adda Ke Samun Matsala 12.09.2022

Send us Fan Mail Kamun da hukumomin tsaron Najeriya suka yi wa Tukur Mamu, wani shahararren mai shiga tsakanin ’yan ta’adda da mutane a Najeriya ya sanya tunanin a zukatan jama’a a ciki da wajen kasar. Shin masu shiga tsakanin ’yan ta’adda da gwamnati ko jama’ar gari na da wata alaka da ta’addanci ne? Shin me ya sa suke ba sa wanyewa lafiya da gwamnati? A shirin namu na wannan lokaci, mun tattauna...

Ruwa Ya Tashi Cinye Jihar Jigawa 09.09.2022

Send us Fan Mail Rahotanni daga garuruwa da dama a Jihar Jiagawa na nuna cewa mamakon ruwan saman da ake samu a wannan daminar na barazana ga garuruwa da yawa.  Shin mene ne dalilin da duk shekara sai an samu ambaliyar ruwa a Jigawa?  Kusan ganaki dubu biyu ruwa ya wanke a Karamar Hukumar Babura. Shirin Najeriya A Yau ya tattauna da wadanda abin ya shafa domin jin halin da su ke ciki 

Yadda INEC Ke Son A Yi Yakin Neman Zaben 2023 08.09.2022

Send us Fan Mail Nan da mako uku za a kada gangar siyasa domin bai wa ’yan takarar zaben 2023 damar shiga lungu da sakon Najeriya domin zawarcin kuri’u.  Shin kun san cewa akwai yiwuwar ’yan siyasa da dama su yi asarar takararsu, wasu kuma su biya harajin kudade masu kauri idan suka taka dokokin INEC? To wadanne ka’idoji Hukumar INEC ta sanya domin tabbatar da aminci a lokacin yakin neman zabe?  S...

Mai Yiwuwa A Fuskanci Matsanancin Wahalar Mai Kwanan Nan A Arewacin Najeriya 06.09.2022

Send us Fan Mail Kungiyar dillalan man patir mai zaman kanta na Najeriya, IPMAN ta ce ba za su yi aiki ba, in dai gwamnati ba ta biya ta kudaden   da ta bin ba. Sun ce suna bin gwamnati kudi da suka Kai biliyan 50, idan  kuma ba   haka, toh lalle za su tafi yajin aiki... Shirin Najeriya a yau ya tattauna da masu ruwa da tsaki a wannan al'amari.

Listen to the Najeriya a Yau podcast in Replaio

Radio and podcasts in one app - free, with no sign-up. Install today and do not miss the launch

Get it on Google Play

Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.