Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Where to listen?
Podcasts in the app Replaio Radio Coming soonPodcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts
Episodes
Matsayin Kuri’ar ’Yan Gudun Hijira A Zaben 2023 01.12.2022 15:01
Send us Fan Mail A yayin da ya rage kwana 85 a yi zaben 2023, ta yaya miliyoyin ’yan Najeriya da ke gudun hijira za su kada kuri’a? Shin INEC ta shirya bai wa ’yan Najeriya da ke sansanonin gudun hijira damar amfani da ’yancinsu na kada kuri’ar zaben mutanen da za su shugabance su? Shirin Najeriya A Yau na kunshe da karin bayani.
Ainihin Dalilin Ci Gaban Wahalar Mai —Masani 29.11.2022 14:43
Send us Fan Mail Rige-rige da dogayen layikan ababen hawa sun ki karewa a gidajen mai sakamakon wahalar samun mai da ta ki ci, ta ki cinyewa a Najeriya. A baya, rahotanni sun nuna danganta matsalar da gurbataccen man da aka shigo da shi da kuma rashin hanya saboda ambaliyar ruwa, da dai sauransu. Shin me ya sa wahalar man ta ki karewa duk kuwa da cewa an shawo kan wadancan mastalolin da aka dora w...
Dalilin Kara Dage Dawowar Jirgin Kasan Abuja-Kaduna 28.11.2022 14:45
Send us Fan Mail Rahotannin cigaba da jigilar mutane a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna sun karade kafafen labarai, sai dai kuma kafin safiyar yau Litinin 28 ga watan Nuwamba da aka ayyana cewa jiragen kasan za su cigaba, sai ga sanarwar dakatarwa . Shin mene ne ya sa aka dakatar da wannan aiki? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci na tafe da karin bayani.
Abin Da Ya Kamata Ku Sani Kan Sabbin Kudaden Najeriya 25.11.2022 15:01
Send us Fan Mail Bayyanar launin sabbin takardun kudaden Najeriya da shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar a fara amfani da su ranar 15 ga watan Disamba mai zuwa ya bar baya da kura, inda da dama cikin 'yan kasar ke cewa ba haka suka zata ba. Shin ko sauyin launin da aka yi wa kudaden abin a zo a gani ne? Saurari shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci domin sanin abinda sabbin kudaden suka k...
Rikicin PDP: Shin Atiku Zai Kai Bantensa A 2023? 24.11.2022 14:49
Send us Fan Mail Shin rikicin cikin gida da yakici, yaki cinyewa a Jam’iyar PDP zai bari dan takararta na shugaban kasa, Atiku Abubakar ya kai bantensa a zaben 2023? Ci gaba da bijire wa shugabancin jam’iyyar da wasu gwamnoninta biyar ke yi a halin yanzu ya sa a fargabar takarar tsohon mataimakin shugaban kasan na neman shiga halin rashin tabbas. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya bi diddi...
Yadda ’Yan Bauchi Da Gombe Ke Kallon Hakar Mai A Yankinsu. 22.11.2022 16:06
Send us Fan Mail A Najeriaya, idan aka ce akwai mai a wani yanki, ana ganin; shi ke nan kakarsu ta yanke saka ke nan. Shin haka abin yake kuwa? Masu iya magana kan ce, “ba giringirin ba tai mai”. Shirin Najeriya a yau ya tattauna da masu sharhi, da masu ruwa da tsaki da kuma ‘yan yankin Bauchi da Gombe game da hako mai a yankunan su.
Pi Ta Fashe A Yankin Birnin Tarayya 21.11.2022 14:55
Send us Fan Mail Pi wani samfurin kudin intanet ne da har yanzu ake jiran fashewarsa a fadin duniya. Sai dai kuma an fara amfani da shi wajen yin kasuwanci a Gwagwalada da ke Yankin Birnin Tarayya. Ko dai Pi ta fashe ne? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya yi tattaki zuwa garin Gwagwalada domin kawo muku yadda ake kasuwanci da Pi.
Yadda Dan Chana Ya Ce Ya Kashewa Ummita Miliyan N120 18.11.2022 14:47
Send us Fan Mail A ci gaba da sauraron karar kisan gillar da ake zargin wani dan kasar Chana da yi wa wata bakanuwa (Ummita), wanda ake zargin ya bayyana yadda ya kashe wa marigayiyar miliyoyin Naira. Ko kun san a ikirarin dan Chana harda bayyana cewa ya na baiwa marigayiya Ummita alawus din Naira dubu dari duk mako? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci na dauke da cikakken bayanin abin da ya...
Yadda Tinubu Ke Shirin Bin Sawun Buhari 17.11.2022 14:59
Send us Fan Mail Bola Ahmed Tinubu ya yaba kamun ludayin gwamnatin Shugaba Kasa Muhammadu Buhari kan yaki da ta’addanci a lokacin kaddamar da yakin neman zabensa. Shin idan Tinubu ya bi sawun Buhari a yaki da ta’addanci, za a kawo karshen matsalar tsaro? Saurari Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci domin sanin wainar da ake toyawa a tawagar Bola Ahmed Tinubu
Saukar Farashin Hatsi ba zai Dore Ba —Masani 15.11.2022 15:31
Send us Fan Mail So da dama a Najeriya, idan farashin hatsi ko sauran kayan masarufi ya tashi sama ko ya sauka, aka alakanta shi farashin canjin Dala. Shin komai ne ake saya da Dala, kuma komai ne canjin Dala ke shafa a Najeriya? Mun tattauna da manoma, ’yan kasuwa da masana kan wannan batu.
Irin Asarar Da Aka Yi A Gobarar Kasuwar Badume 14.11.2022 15:02
Send us Fan Mail A yayin da ake bin diddigin gobara mafi muni da ta tashi a Kasuwar Kayan Gwari ta Badume da ke Karamar Hukumar Bichi a Jihar Kano, Aminiya ta gano abubbuwa da dama kan wannan lamari da kuma kasuwar.
Yadda Magidanci Ya Babbaka Agololinsa 11.11.2022 12:40
Send us Fan Mail Wani magidanci dan shekara 64 ya babbake ’ya’yan matarsa guda biyar a Jihar Ondo kudu maso Yammacin Najeriya. Mene ne ya yi zafi har wannan magidanci ya yanke wannan danyen hukunci? Saurari shirin Najeriya A Yau domin samun karin bayani.
Me Ke Sa Tinubu Baya-baya Da Shiga Jama’a? 10.11.2022 15:07
Send us Fan Mail Rashin halartar taruka da dan takarar shugaban kasa a APC Bola Tinubu ke yi ya sa ’yan Najeriya yi masa fassara iri-iri. Shin me ya sa Tinubu ke kaurace wa tarukan da ake ganin zuwansa na da muhimmanci, kuma zai ba shi damar tallata kansa? Saurari Najeriya A Yau na wannan loikaci domin jin inda gizo ke saka.
Yadda Hauhawar Farashin Kayan Masarufi Ke Neman Hana Mu Kasuwanci 08.11.2022 14:17
Send us Fan Mail Yanzu ba sabon abu ba ne yadda kayan masarufi ke ta tashin gwauron zabo a Najeriya. ‘Yan kasuwa da masu sayayya na ta kokawa game da tsadar kaya a kasuwannin Najeriya. Shirin Najeriya A Yau ya shiga kasuwa ne ya tattauna da ‘yan kasuwa don jin yadda abin yake.
Yadda Soludo Ke Gyaran Tarbiyya A Anambra. 07.11.2022 14:59
Send us Fan Mail Tun bayan darewa karagar mulkin Jihar Anambra, Farfesa Charles Chukuma Soludo ya yi wa 'yan jihar bazata, domin kuwa ya mayar da hankalinsa a bangaren gyaran tarbiyya da kyautata mu'amala. Shin ko kunsan bangarori da ababen da Soludo ya tabo a jihar ta sa tun bayan zamowarsa gwamna? Shirin Najeriya A Yau ya kalli ababen da Soludo ya tabo da idanun basira, bayan dorasu...
Dalilin Da EFCC Ke Kama 'Yan Canji 04.11.2022 14:56
Send us Fan Mail Hukumar EFCC ta kai samame wurin masu canjin kudaden ketare a Abuja da Kano. Shin ko mene ne dalilin EFCC na wannan kame a daidai wannan lokaci? Saurari shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci domin sanin abin da ke faruwa.
Anya APC ta Shirya Cin Kano A Zaben 2023? 03.11.2022 12:09
Send us Fan Mail Jam’iyyar APC ta jima tana fama da rikici tsakanin ’ya’yanta a Jihar Kano. Lura da matsayi da tasirin Kano a siyasar Najeriya, anya APC ta shirya kawo jihar a zaben 2023 kuwa? Shirin Najeriya A Yau ya tattauna da ’yan jam’iyyar a jihar, da masana kimiyyar siyasa domin game da tasirin rikice-rikicen ga makomar jam’iyyar a zaben 2023.
Dalilan Da Darajar Naira Ke Kara Faduwa 01.11.2022 14:51
Send us Fan Mail A ’yan kwanakin nan darajar Naira ta kara faduwa inda ake sayen Dala daya a kan kusan Naira dubu daya. Shin me ya sa darajar Naira sai kara faduwa take yi? Saurari shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci domin sanin dalilan.
Barazanar Hari A Abuja: Abinda Gwamnati Ke Boyewa. 30.10.2022 14:55
Send us Fan Mail Tun bayan fitowar rahoton yiwuwar samuwar hare-haren ta'addanci a Abuja da gwamnatocin Amurka da Birtaniya suka yi aka shiga zaman dar-dar a cikin birnin. Shin mene ne gaskiyar abinda ke faruwa a Abuja? Saurari cikakken shirin Najeriya A Yau domin jin wurin da gizo ke saka.
Yadda Yiwa Wadansu Takardun Naira Garambawul Zai Shafe Ku 28.10.2022 15:16
Send us Fan Mail Rahoton yi wa wadansu takardun Nairar Najeriya garambawul ya zo wa 'yan kasar da mamaki, lura da babu wanda ke tunanin za a samu sauyin a daidai wannan lokaci. Ko ta wadanne bangarori wannan hukunci zai shafi 'yan Najeriya? Saurari cikakken shirin domin jin gamsassun bayanai kan wannan batu.
Shin Da Gaske Peter Obi Ya Jingine Yakin Neman Zabensa? 27.10.2022 14:26
Send us Fan Mail Jam’iyyar Leba ta sanar cewa dan takararta na shugabancin Najeriya, Peter Obi ya jingine yawon neman zabensa. Shin da gaske ne, kuma mene ne dalili? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya binciko muhimman batutuwa dangane da yanayin kamfe din ’yan takara a zaben 2023.
Dalilin da ’Yan Najeriya Ke Wasarere Da Gargadin Hukumar DSS. 25.10.2022 15:02
Send us Fan Mail Hukumar Tsaro Ta Farin Kaya DSS na gaba-gaba cikin hukumomin tsaron Najeriya masu alhakin bayyana duk wata barazanar tsaro a kasar ya rataya a wuyarsu. Ko me ya sa ’yan Najeriya ke kin daukar gargadin wannan hukuma da muhimmanci? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya tattauna da masu ruwa da tsaki kan wannan batu domin samun bayanai masu gamsarwa.
Kudurin Dokar Hukunta ’Yam Madigo Da Luwadi A Kasar Nijar 24.10.2022 15:27
Send us Fan Mail Kudirin yin dokar da za ta haramta auren jinsi, ko mu’amala tsakanin jinsi guda na daya daga cikin batutuwan da suka dauki hankalin jama’ar Najeriya da Nijar. Shin mene ne dalilin yunkurin yin wannan doka a Nijar a dai-dai wannan lokaci? Saurari yadda aka haramta auren jinsi a Najeriya da kuma yadda Nijar suka yunkuro wurin yakar wannan dabi’a.
Yadda Sakaci Ya Sa Likita 1 Duba Lafiyar Mutum 45,000 A Arewacin Najeriya 21.10.2022 15:17
Send us Fan Mail Ana ganin karancin kulawar da Gwamnatin Najeriya ke yi da albashin likitocin ta, na ci gaba da sa su ficewa daga kasar, dalilin da ke kara je fa rayuwar ’yan kasar a cikin hatsari. Ko kunsan likitoci guda nawa muke da su a Najeriya baki daya? Saurari shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci domin sanin inda gizo ke saka.
Me Ya Sa Atiku ya ce ’yan Arewa su zabi dan uwansu? 20.10.2022 14:39
Send us Fan Mail Wasu manyan ’yan takarar shugaban kasa a zaben Najeriya na 2023 sun furta wasu kalamai masu kama da bangaranci a yakin neman zabensu da suka bar baya da kura. Shin wane tasiri irin wadannan kalaman za su yi a zaben 2023 ga ’yan takarar da ke neman saye zukatan masu zabe?. Saurari shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci domin jin yadda za ta kaya.
Similar podcasts
Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.