Najeriya a Yau

News HA ↓ 958 episodes

Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.

Category

News

Podcast website

www.buzzsprout.com

Latest episode

Jun 23, 2026

Where to listen?

Podcasts in the app Replaio Radio Coming soon

Podcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts

Get it on Google Play Install for free Android 5M+ downloads · 4.8 rating iOS soon

Episodes

Mun Fi Son Shugaba Jajirtacce, Adali Mai Tsoron Allah- ’Yan Najeriya 19.01.2023

Send us Fan Mail 'Yan Najeriya sun ce suna bukatar shugaba na gari mai tsoron Allah, wanda zai fitar da su daga halin da suke ciki yanzu. A yayin da ya rage saura ’yan kwanaki a gudanar da babban zabe, wasu ’yan Najeriya sun bayyana irin shugaban da suke so su zaba. Ku biyo mu cikin shirin Najeriya a yau don jin ra’ayoyinsu. 

‘Muna Zaman Kunci Tun Da Mijina Ya Rasu A wajen Yi Wa Kasa Hidima’ 17.01.2023

Send us Fan Mail Matan sojoji ’yan mazan jiya da suka mutu a fagen daga, sun koka da rashin kulawar da ya kamata su samu. “Kudin jana’izar maigida na kawai muka samu” in ji daya daga cikin matan. Shin me shugabanni ke yi don tallafa wa iyalan sojojin da suka rasa ransu? Shirin Najeriya a yau ya tattauna da masu ruwa da tsaki?

Manufofin ’Yan Takarar Gwamna Ga Katsinawa A 2023 16.01.2023

Send us Fan Mail Yan takarar gwamnan Jihar Katsina sun bayyana kudurorinsu kan matsalar tsaro, tattalin arziki da kiwon lafiya.  Sun baje kolin manufofin nasu ne a  wani taron tattaunawa da kamfanin Media Trust ya shirya a jihar. Shin kun san manufofin nasu?  Saurari shirin Najeriya A Yau domin sanin inda aka kwana.  

“Daliban Yauri: ‘Tun baya sace ’yata kullum ina jinya asibiti’ 13.01.2023

Send us Fan Mail Shekara daya da wata takwas ke nan, da sace daliban makarantar sakandaren Birnin Yauri da ke Jihar Kebbi.  Shin ko a wane hali iyayen yaran da aka sace ke ciki zuwa yanzu? Mun tattauna da iyayen yaran, mun kuma ji ta bakin gamnatin Jihar, a yi sauraro lafiya. 

Abin Da Mata ‘Yan Takara Suke So A Zaben 2023 12.01.2023

Send us Fan Mail Kwana 43 kafin babban zaben Najeriya, mata ’yan takara a zaben na ta korafe-korafe. Shin me mene ne bukatunsu kuma me ya kamata a yi musu? Shirin Najeriya A Yau ya tattauna da su da kuma ’yan gwagwarmayar siyasa.

Ma’aikaatr Shari’a ta fadi gwajin da’a da tsare gaskiya -ICPC 10.01.2023

Send us Fan Mail Hukumar ICPC ta kimanta da’a da tsare gaskiyar ma’aikatun tarayya.  Hukumar na auna ma’aikatun ne don gano masu cin hanci da rashawa da almundahana da kudaden gwamanti. Shirin Najeriya a yau ya tattauna da masu ruwa da tsaki da kuma masana don fayyace mana yadda al’amarin yake.

Yadda Ake Safarar Makamai A Jihar Zamfara 09.01.2023

Send us Fan Mail Jihar Zamfara ta yi kaurin suna dangane da ta’addancin ’yan bindiga masu satar dabbobi, wanda daga bisani suka rikide zuwa satar mutane domin karbar kudin fansa.  Shin kun san yadda ake safarar makamai a Jihar Zamfara?  Shirin Najeriya A Yau ya bankado yadda aka maida kai makamai Zamfara sana’a.

Yadda Likitocin Bogi Ke Hallaka ’Yan Najeriya 06.01.2023

Send us Fan Mail Ya za ka yi, idan ka gano cewa likitan bogi ne ya yi maka tiyata? Ku san yadda masu shugunan sayar da maganin bature ke yin sojan gona a matsayin likitoci? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci na tafe bayanan wadansu da likitocin bogi suka jefa su cikin halin kaka-i-ka-yi, har da asarar rai.

Yadda Karin Albashi Zai Shafi Rayuwarku 30.12.2022

Send us Fan Mail Tun bayan kyankyasa batun karin albashi a shekara mai kamawa da Ministan Kwadago na Najeriya, Chris Nwabueze Ngige ya yi ake ta musayar ra’ayi kan yadda karin albashin zai shafi rayuwar ’yan kasar.  Shin kun san hakikanin yadda karin albashin zai shafi rayuwarku in ya tabbata? Shirin Najeriya A yau na tafe da karin haske.  A yi sauraro lafiya. 

Yadda Za A Tabbatar Da Zaman Lafiya A Harkokin Zabe 29.12.2022

Send us Fan Mail Daga yakin neman zabe, kada kuri’a zuwa bayyana wanda ya yi nasara, lokaci ne da akan samu hatsaniya. Shin ta wace hanya za a wanzar da zaman lafiya daga wannan lokaci na yakin neman zaben 2023 har zuwa lokacin da za a kammala zaben?  Shirin Najeriya A Yau ya tattauna da masu ruwa da tsaki a harkokin zaben.

Karin Kudi: Akwai Yiwuwar Daliban Jami’ar Maiduguri Su Daina Karatu 27.12.2022

Send us Fan Mail Batun karin kudin makarantar  Jami’ar Maiduguri na ci gaba da daukar hankalin masu alaka da makarantar.  Shin karin kudin makarantar na da alaka da rashin biyan bukatun malaman jami’o’i?  Saurari shirin Najeriya A Yau domin sanin ina aka dosa.

Abin Da Ya Kamata Ku Sani Kan Ranar Kyauta A Addinin Kirista 25.12.2022

Send us Fan Mail Kiristoci  sun kebe kowace ranar 26 ga  watan Disamba ta kowace shekara a matsayin Ranar Kyauta. Shin mene ne ka’idojin kyauta da kuma asalin wannan rana a addinin Kirista? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya tattauna da masana addinin Kirista domin kawo muku gamsassun bayanai.

Anya Kuwa Za A Iya Daina Mu’amala Da Tsabar Kudi A Najeriya? 23.12.2022

Send us Fan Mail Babban Bankin Najeriya (CBN) na ci gaba da bayyana aniyarsa ta takaita amfani da tsabar kudi a kasar. Amma anya Najeriya na da karfin kimiyyar komawa hada-hadar kudade ta intanet kuwa, kamar yadda CBN din ke hankoro? Shirin Najeriya A Yau ya zurfafa bincike kan wannan batu ya kuma tattauna da masu ruwa da tsaki domin warware zare da abawa.

Dalilin da ’yan Majalisa ke son CBN ya sassauta dokar cire kudi 22.12.2022

Send us Fan Mail Majalisar Dokokin Najeriya ta tsaya kai da fata cewa babban bankin kasar (CBN) ya dubi dokarsa ta kayyade cirar tsabar kudi.  Shin akwai siyasa a hakikancewar da mambobin majalisar suka yi kan sassauta dokar? Saurari shirin Najeriya A Yau domin samun bayanai masu gamsarwa. 

Abin Da Ke Jawo Asarar Rayuka A Kan Hanyoyin Najeriya 20.12.2022

Send us Fan Mail Shin dole ne sai mutane sun tafiya a lokutan bukukuwan Sallah, Kirsimati, da karshen shekara? Shin me ya sa jama’a ke tururuwar tafiye-tafiyen zuwa bukukuwa da kuma ganawa da ’yan uwa da abokan arziki, a irin wadannan lokutan da ake yawan samun haddura? Ku biyo mu cikin shirin Najeriya A yau don jin yadda abin yake . 

Asarar da Najeriya ta tafka Saboda Kasa Zuwa Gasar Cin Kofin Duniya a Qatar 19.12.2022

Send us Fan Mail Najeriya na daya daga cikin kasashen da aka cire da wurwuri a jerin kasashen da zasu taka leda a gasar cin kofin duniya da aka buga a Qatar.  Bayan cire 'yan kungiyar kwallon kafar Najeriya tun kan kaiwa ga matakin karshe da zai basu damar buga wasa a matakin duniya, shin kun san irin asarar da hakan ya janyo wa 'yan kungiyar kwallon kafar Najeriyar? Shirin Najeriya A Ya...

Shin Gwamnatin Kano Za Ta Rataye Abduljabbar? 16.12.2022

Send us Fan Mail Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana abin da take shirin yi kan hukuncin kisa ta hanyar rataya da Babbar kotun Musulunci ta yanke wa Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara kan yin batanci ga Manzon Allah (SAW). Shin kuna ganin za a aiwatar da hukuncin kotun? Saurari shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci domin sanin inda aka kwana.

Yadda Aka Fara Karbar Katin Zaben 2023 15.12.2022

Send us Fan Mail Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta fara rabon katunan zaben a cibiyoyinta da ke fadin Najeriya ranar Litinin 12 ga Disamban nan da muke ciki.   Shin yaya aikin rabon katunan zaben ke gudana?  Saurari bayanai daga bakin ’yan Najeriya da ke kokarin karbar katunan zabensu da kuma jami’an INEC.

IPOB Ko Gwamnati: Wa Ke Iko Da Kudancin Najeriya? 13.12.2022

Send us Fan Mail Yankin Kudu maso Gabashin Najeriya na fuskantar barazanar tsaro sakamakon hare-haren ’yan kungiyar IPOB da suka ki ci, suka ki cinyewa. Shin taskanin gwamnati da kungiyar ’yan ta'addan, wa ya fi iko da yankin? Shirin Najeriya A Yau, ya tattauna da masu ruwa da tsaki da kuma masana kan al’amarin.

’Yan Bindiga Sun Zafafa Hare-Hare Bayan Samuwar Mai A Bauchi 12.12.2022

Send us Fan Mail Tun bayan kaddamar da fara tonon man fetur da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi a yankin Alkaleri na Jihar Bauchi da wani yanki na Jihar Gombe, rahotanni na nuna cewa an samu karuwar hare-haren 'yan bindiga a wannan yanki.  Lura da yadda harkokin tsaron yankin ke kara tabarbarewa, ko akwai alaka tsakanin samuwar man fetur da rashin zaman lafiya?  Saurari shirin Najeriya A...

Shin Majalisa Na Da Ikon Dakatar Da Dokar CBN? 09.12.2022

Send us Fan Mail Majalisar Dokoki ta Kasa na neman taka wa Babban Bankin Najeriya (CBN) burki kan sabbin dokokinsa na takaita yawon kudi tsaba a hannun jama’a. Shin Majalisar na da ikon dakatar da dokokin CBN? Saurari shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci domin sanin inda aka dosa.

Yadda Dokar Rage Cire Kudi A POS Za Ta Shafi Zaben 2023 08.12.2022

Send us Fan Mail A yayin da ake tafiyar da harkokin siyasa, musamman yakin neman zabe a Najeriya da makudan kudade. Shin wane tasiri sabon tsarin Babban Bankin Najeriya (CBN) na kayyade yawan kudaden da za a cira a banki zai yi wa ’yan siyasa da kuma yakin neman zaben 2023? Ku biyo cikin shirin Najeriya A Yau don jin abin da masana suka ce.

Yadda Jirgin Kasan Abuja-Kaduna Ya Dawo Aiki 06.12.2022

Send us Fan Mail Jirgin kasan Abuja-Kaduna ya cigaba da aiki a jiya Litinin 5 ga watan Disamban nan da muke ciki, shirin Najeriya A Yau ya bibiyi yadda jirgin ya faro aiki.  Shin kun san abububbwan da suka faru a wannan rana da jirgin ya dawo aiki? 

Yadda 'Yan IPOB Ke Shirin Hana Zabe A Kudancin Najeriya 05.12.2022

Send us Fan Mail Rundunar  'yan sandan Najeriya ta ce  'yan haramtacciyar kungiyar aware ta IPOB ne ke bankawa ofisoshin Hukumar Zabe Ta Najeriya INEC wuta a Kudancin Najeriya.  Shin mene ne yasa ake ci gaba da kone ofisoshin INEC a Kudancin Najeriya, kuma wane irin tasiri hakan zai yi ga yankin a zaben 2023?  Shirin Najeriya A Yau ya bi diddigin wannan batu, ya kuma tattauna da hukumar...

Yadda Ake Sayen Zaman Lafiya A Arewa 02.12.2022

Send us Fan Mail Ta'addancin 'yan bindiga kullum sake salo yake a Arewacin Najeriya, musamman a Arewa ta Yamma.  Shin gwamnati ta sallama jama'ar wannan yankin ne? Saurari shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci domin jin yadda jama'ar wannan yanki ke hada miliyoyin Naira su baiwa 'yan bindiga domin su barsu su zauna lafiya 

Listen to the Najeriya a Yau podcast in Replaio

Radio and podcasts in one app - free, with no sign-up. Install today and do not miss the launch

Get it on Google Play

Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.