Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Where to listen?
Podcasts in the app Replaio Radio Coming soonPodcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts
Episodes
Dalilin Rashin Fitar ’Yan Najeriya Zaben Shugaban Kasa 03.03.2023 14:56
Send us Fan Mail Shirin Najeriya a Yau na wannan karo ya maida hankali kan yadda miliyoyin ’yan Najeriya suka ki fita yin zaben da ya gabata. Ko me ye dalili? Ku biyo shirin namu na yau ku ji dalilai daki-daki.
Kalubalen Da Ke Gaban Zababben Shugaban Kasa Tinubu 02.03.2023 12:52
Send us Fan Mail Tun bayan bayyanar sakamakon zaben da Bola Tinubu ya lashe, masu sharhi suka fara hangowa sabon shugaban na Najeriya wadansu matsaloli da ke gabansa. Shin ta yaya ya kamata Tinubu ya tunkari matsalolin da suka dabaibaye tattalin arziki da ilimi, da tsaro? Saurari shirin Najeriya A Yau domin jin yadda masana suka kalli matsalolin da suka dabaibaye kasar.
Shin ’Yan Najeriya Sun Gamsu Da Yadda Sakamakon Zabe Ke Fitowa? 28.02.2023 15:55
Send us Fan Mail A yayin da sakamakon zaben 2023 ke fitowa daga wasu jihohin Najeriya, yaya ’yan kasar ke kallonsa? Wasu ’yan Najeriya na nuna gamsuwarsu, wasu kuma na bayyana korafinsu a fili. Ku biyo cikin shirin Najeriya A Yau don jin yadda abin yake.
Zaben Shugaban Kasa Ya Bar Baya Da Kura 27.02.2023 14:55
Send us Fan Mail Shirin Najeriya a Yau ya rairayo wasu abubuwan da suka bar baya da kura a zaben shugaban kasa da ’yan majalisun tarayya da aka yi ranar asabar a Najeriya. Mun duba rikicin mazabar shugaban ja’miyyar APC na Jihar Kano Abdullahi Abbas da dan takarar gwamnan jihar a Jam’iyyar adawa ta NNPP, Abba Gida-Gida, da kuma batun sayen kuri’u a Kalaba, Jihar Kuros Riba.
Yadda Bangar Siyasa Ka Iya Dagula Lissafi A Wannan Zabe 24.02.2023 14:59
Send us Fan Mail A daidai lokacin da jama’ar Najeriya ke shirin fita zaben shugaban kasa da ’yan majalisun tarayya a gobe Asabar, an samu rahotannin bangar siyasa a wadansu yankunan kasar. Shin wace irin illa bangar siyasa za ta yi ga zaben da ke tafe? Shirin Najeriya A YAU na wannan lokaci na tafe da bayanai masu gamsarwa domin sauraron ku
Yadda Sabon Shiga A Kada Kuri'a Ke Hangen Zabe 23.02.2023 12:37
Send us Fan Mail A dokar Najeriya sai mutum ya kai shekara 18 kafin ya kada kuri'a zabe. Ko yaya sabon shiga kada kuri'a ke kallon zaben da ke tafe? Saurari shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci domin sauraron yadda sabon shiga kada kuri'a ke kallon zaben.
Shin Kuri’un ’Yan Najeriya Za Su Yi Tasiri a Zaben 2023? 21.02.2023 15:43
Send us Fan Mail ’Yan Najeriya dai za su yi zabe ranar Asabar 25 ga watan Fabrairu mai zuwa, domin zaben shugabaninsu. Shin kuri’un ’yan Najeriya za su yi tasiri kuwa a yayin zaben? Mun tattauna da ’yan Najeriaya, da hukumar zabe, da kuma wani masani a kan al’amarin.
Shin don talakawa gwamnoni ke adawa da canjin kudi? 20.02.2023 14:31
Send us Fan Mail Tun bayan da Gwamnatin Najeriya ta canza kudaden kasar wadansu gwamnoni ke adawa da tsarin, saboda a cewarsu, tsarin zai shafi masu karamin karfin jihohinsu. Shin da gaske domin talakawa gwamnonin ke wannan fada? Shirin Najeriya A YAU ya ji ta bakin ’yan Najeriya kan yadda suke kallon fadan da gwamnonin suka ce suna yi domin su.
Yadda ’Yan Najeriya Ke Kallon Karin Wa'adin N200 17.02.2023 14:57
Send us Fan Mail Tun bayyanar batun sauya fasalin kudaden Najeriya ’yan kasar ke fama da karancin tsabar kudin kashewa. Shin ko yaya kuka ji da aka kara wa’adin karbar tsofaffin takardun Naira 200? Mun tattauna da masu ruwa da tsaki kan wannan batu, mun kuma ji ta bakin masana. A yi sauraro lafiya.
Yadda Wadanda Aka Soke Rumfar Zabensu Za Su Kada Kuri’a 16.02.2023 14:42
Send us Fan Mail ’Yan Najeriya na ci gaba da maida martani kan soke runfuman zabe 240 da Hukumar INEC ta yi. Mene ne makomar kuri’un mutanen da aka soke rumfunan zabensu? Shirin Najeriya A YAU ya tattauna da INEC kan dalilan sokewar ya kuma ji ta bakin wadanda abin ya shafa.
"Bankuna suna Kin Karbar Tsofaffin Kudi"- Dan Kasuwa 14.02.2023 15:12
Send us Fan Mail ’Yan Najeriya sun shiga wani hali bayan bankuna da wasu ’yan kasuwa sun dain karbar tsofaffin kudin da aka sauya. Me ya sa wasu mutanen da bankuna daina karbar kudin, alhali Kotun Koli ta dage lokacin haramta amfani da su? Shirin Najeriya A Yau ya dubi al’amarin tare da masana.
'Kisan Da Ake Yi Mana Ne Ya Koro Mu Daga Taraba' 13.02.2023 15:41
Send us Fan Mail Fulani makiyaya suna barin matsugunansu a jihar Taraba kan zargin cewa ana kashe su, kuma ana kwace masu dukiyoyinsu. A cewarsu, wasu ‘yan vigilante ke wannan aika-aikan. Shin su waye ke kashe makiyayan? Shirin Najeriya a yau ya tattauna da masu ruwa da tsaki a al’amarin.
Karancin Kudi Na Sa Farashin Kayan Masarufi Faduwa 10.02.2023 16:32
Send us Fan Mail Dole ta sa ’yan kasuwa sauko da farashin kayayyakin da suke sayarwa saboda karancin kudin da ke yawo a gari da kuma hannun mutane. Yaya ’yan kasuwan suke ji game da wannan al’amarin? Shirin Najeriya a yau ya tattauna da masu ruwa da tsaki da masana kan al’amarin.
Yadda ’Yan Takara Ke Kashe Kudi A Lokacin Zabe 09.02.2023 16:34
Send us Fan Mail A lokutan zabe ’yan takara da jam’iyyun siyasa a Najeriya kan kashe kudaden da ba a iya tantance yawansu. Amma sabuwar dokar zabe ta kayyade kudaden da za su kashe a lokacin yakin neman zabe. Shin suna bin dokar?
Yadda Harkar Kudi ta Intanet Ta Sa 'Yan Najeriya Tafka Asara 07.02.2023 15:04
Send us Fan Mail Rashin karfin intanet na wahalar da ’yan Najeriya wajen yin hada-hadar kudi ta intanet. Yawancin a Najeriya idan mutum zai tura kudi ta intanet yakan kasance cikin fargabar ko kudin ya ki tafiya, ko kuma kudin amma sun ki zuwa wurin wanda aka tura wa. Shin me ya sa ake yawan samun matsalar tura kudi ta intanet a Najeriya? Shin akwai karfin intanet na amfani domin yin harkar kudi a...
Manufofin ’Yan Takarar Gwamnan Kano A Zaben 2023. 06.02.2023 25:34
Send us Fan Mail Yan takarar gwamnan Jihar Kano sun bayyana kudurorinsu idan Allah ya ba su ikon darewa karagar mulkin jihar. Sun baje kolin manufofin ne a wajen wata muhawara da kamfanin Media Trust ya shirya a birnin Kano. Shin kun san manufofin nasu? Saurari shirin Najeriya A Yau domin sanin inda aka kwana.
Kwakwar da ’yan Najeriya Ke Ci Bayan Canjin Kudi 03.02.2023 15:21
Send us Fan Mail ’Yan Najeriya na ci gaba da dandana kudarsu sakamakon canjin fasalin Naira 1000, 500 da Naira 200 da Babban Bankin kasar (CBN) ya yi. Shin ko bankunan kasar sun fara bayar da sabbin kudaden a cikin banki? Shirin Podcast Najeriya A Yau na tafe bayani daga sassan Najeriya kan halin da ake ciki.
Wadanda Suke Yi Wa Tinubu Kafar Ugulu 02.02.2023 15:49
Send us Fan Mail Ba kasafai ake samun ‘yan jam’iyya daya suna yi wa junansu zagon kasa ba. Sai a wannan karon ga dan takarar jam’iyar APC yana korafin cewa ana yi wa takararsa kafar Ungulu. Shin wa ke yi Tinubu kafar Ungulu? Shirin Najeriya a yau ya tattauna da masu ruwa da tsaki da kuma masu sharhi.
Irin Tarbar Da Kanawa Suka Yi Wa Buhari 31.01.2023 16:03
Send us Fan Mail Kanawa a karon farko ba su yi wa shugaban kasa, Muhammadu Buhari kara ba a lokacin da ya ziyarci jihar domin kaddamar da wasu ayyuka. Ko mene ne dalilin su na rashin bai wa shugaban kasae kyakkyawar tarbar da suka saba bashi duk lokacin da ya ziyarci jihar a baya? Shirin Najeriya a yau ya dubi al’amarin.
Yadda ’yan Najeriya suka karbi karin wa’adin tsoffin kudade 30.01.2023 15:08
Send us Fan Mail Babban Bankin Najeriya CBN ya saurari korafe-korafen jama’a kan wa’adin daina amfani da tsoffin takardun Naira 1000, 500 da Naira 200 daga ranar 31 ga watan Janairu, inda a yanzu za a daina karbar kudaden daga ranar 10 ga watan Fabarairu. Shin ko ta wadanne bangarori wannan matakin na CBN zai shafi tattalin arziki? Shirin Najeriya A Yau ya ji ta bakin wadansu ’yan kasuwa, ya kum...
Yadda aka tsefe manufofin manyan ’yan takarar Shubancin Najeriya a zaben 2023 27.01.2023 15:13
Send us Fan Mail A jiya Alhamis, 26 ga watan Janairun 2023 aka gudanar da Taron Tattaunawar Daily Trust karo na 20 a Abuja, babban birnin Najeriya. Taron, mai taken: Bibiyar Manufofin ’Yan Takarar Shugaban Kasa a 2023 ya gudana ne a Dakin Taro na Cibiyar Sojin Saman Najeriya da ke Abuja, wato NAF Center . Shin kun san manufofin ’yan takarar shugabancin kasa da aka bibiya? Shirin Najeriya A Yau y...
Yadda INEC Za Ta Kare Ma’aikatanta Daga Barazanar Tsaro Lokacin Zabe 26.01.2023 14:50
Send us Fan Mail A yayin da ranar zabe ke ta karatowa, Me hukumar Zaben ke yi don tabbatar da samun isasshen tsaro ga ma’aikatan ta? Ma’aikatan a shirye suke don gudanar da ayukan zabe a watan gobe? Shirin Najeriya a yau ya tattauna da masu ruwa da tsaki da kuma masu sharhi kan batun.
Kalubalen da muke fuskanta a harkar sufuri - ’Yan Najeriya 24.01.2023 15:04
Send us Fan Mail ’Yan Najeriya da dama na kokawa da matsalolin da suke fuskanta a lokacin tafiye-tafiye saboda tsadar kudin mota da kuma rashin kyan hanyoyi. Shin mene ne mafitar wadannan matsalolin? Sai ku biyo mu cikin shirin Najeriya a yau domin sauraro.
Kwana 8 Kafin A Daina Karbar Tsoffin Kudade, Shin Sabbin Sun Zo Hannun Ku? 23.01.2023 15:00
Send us Fan Mail Nan da kwanaki 8 za a daina karbar tsoffin takardun Naira dari biyu, dari biyar da dubu daya. Shin wadan nan sabbin kudaden sun shiga lunguna da sakunan kasar nan? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ziyarci wadansu kasuwanni, domin sanin gaskiyar halin da ake ciki.
Cutar Da Ke Ajalin Yara A Kano 20.01.2023 14:59
Send us Fan Mail Wata bakuwar cuta mai halaka kanana yara ta hanyar toshe musu maƙogwaro da ake kira da Diptheria a Turance, ta bulla a Jihar Kano, inda kawo yanzu rahotanni suka bayyana mutuwar yara 25 a unguwanni biyu a cikin kamar Hukumar Ungogo da ke Jihar. Shin wace cuta ce wannan? Shirin Najeriya A yau ya bibiyi labarin cutar, ya kuma ji ta bakin masana kan abin da ya kamata a yi.
Similar podcasts
Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.