Najeriya a Yau

News HA ↓ 958 episodes

Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.

Category

News

Podcast website

www.buzzsprout.com

Latest episode

Jun 23, 2026

Where to listen?

Podcasts in the app Replaio Radio Coming soon

Podcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts

Get it on Google Play Install for free Android 5M+ downloads · 4.8 rating iOS soon

Episodes

Abin Da Zai Faru Da Zaben Adamawa A Abuja 17.04.2023

Send us Fan Mail Tun bayan kin amincewa da bayyana Sanata Aishatu Dahiru Binani a matsayin wacce ta lashe zaben gwamnan Adamawa da aka karasa a Ranar Asabar 15 ga Afrilu, da hukumar INEC ta yi, hankalin 'yan Najeriya ya koma kan ina aka dosa.  INEC ta gayyaci Kwamishinan zaben Adamawa Abuja, ko za a karasa bayyana sakamakon zaben a Abuja ne?  Shirin Najeriya A Yau ya yi hasashen yadda za a ka...

Kalubalen Da Ke Gaban Aishatu Binani A Zaben Asabar 14.04.2023

Send us Fan Mail Ranar Asabar 15 ga watan Afrilun shekarar nan ta 2023 ake sa ran  karasa zaben jihohin da aka bayyana a matsayin zaben da bai kammala ba a fadin Najeriya. Lura da yadda kallo ya koma Jihar Adamawa sakamakon samun mace 'yar takara dake neman doke gwamna mai ci, ko wadanne kalubale ne ke gaban Aishatu Binani?  Shirin Najeriya A Yau na tafe da karin bayani. A yi sauraro lafiya. 

Yadda Sabon Tsarin CBN Zai Raba Mutane Da Ayyukansu 13.04.2023

Send us Fan Mail Asusun Bada  Lamuni Na Duniya (IMF) ya bai wa Babban Bankin Najeriya CBN shawarar yin karin kudin ruwa ga masu ajjiya a bankunan kasar nan.  Mene ne wannan shawara ke nufi, kuma wane irin tasiri wannan shawara za ta yi ga tattalin arzikin 'yan Najeriya ga kuma gwamnatin kasar?  Shirin NAJERIYA A YAU ya yi bitar wannan shawara, ya kuma baiwa masana dama sun bayyana ababen da k...

Dalilin Da ’Yan Najeriya Ke Gudun Kayayyakin Da Aka Yi A Kasar 11.04.2023

Send us Fan Mail 'Yan Najeriya sun yi  suna wurin  sayen kayayyakin kasashen waje.  Mene ne ya sa 'yan Najeriya suka aminta da kasashen ketare fiye da kasar su?  Shirin NAJERIYA A YAU ya bi diddigin wannan batu, ya ji ta baki masu ruwa da tsaki domin samo mafita. 

Yadda Naira Ta Dawo Da Satar Mutane 10.04.2023

Send us Fan Mail An dan samu raguwar satar mutane a yankunan Arewacin Najeriya da ma sauran sassan kasar.  Ko mene ne dalilin da satar mutane domin karbar kudin fansa ke dawowa a 'yan kwanakin nan?  Shirin Najeriya A Yau na tafe da bayanai daga jihohi daban daban na Najeriya domin sanin halin da ake ciki 

Tsutsa Ta Sa Kudin Kwandon Tumatir Kaiwa N20,000 A Kano 07.04.2023

Send us Fan Mail Tumatir na gaba cikin sinadaran hada miyar dage-dage a Arewacin Najeriya.  Mene ne ya sa tumatir tsada a jihar Kano a daidai wannan lokaci? Shirin Najeriya A Yau ya tattauna da masu ruwa da tsaki a harkar tumatir domin gano dalilin da tumatir din ya zama zinare a Kano.

Ko Jam'iyyun Adawa Za Su Kwace Shugabancin Majalisa? 06.04.2023

Send us Fan Mail Lura da yadda jam'iyyun adawa suka samu kujeru masu yawan da ke neman basu rinjaye a zauren Majalisar Tarayyar Najeriya.  Ya ya zata kaya s sabuwar majalisar kasar?  Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya dubi irin tasirin da yawan 'yan majalisun da suka fito daga jam'iyyun adawa zai shafi tafiyar da harkokin majalisar.  

Yadda Kalaman Abba Gida-Gida Ke Yamutsa Hazo A Kano 04.04.2023

Send us Fan Mail Zababben gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP ya fara bai wa jama'ar jihar shawarwari kan wadansu al'amurra da ke ci wa yan jihar tuwo a kwarya.  Ya ya 'yan Jihar Kano ke kallon shawarwarin na Abba? Shirin Najeriya A yau na tafe karin bayani kan wainar da ake toyawa a jihar Kano.

Gayyatar 'Yan IPOB A Legas Kamar Gayyatar 'Yan Boko Haram Ne —Lauya 03.04.2023

Send us Fan Mail Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta tabbatar da cafke Fredrick Nwajagu, shugaban 'yan kabilar Igbo na rukunin gidajen Ajao a Jihar Legas, bayan ya yi barazanar gayyato 'yan haramtacciyar kungiyar ipob su karesu.  Shin mene ne matsayin dokar Najeriya kan wannan kalamai na Fredrick?  Saurari shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci domin jin abin da ya fada, da matsayin doka...

Yadda Na Yi Asarar Sama Da Miliyan Dari Sanadiyyar Murnar Cin Zabe —Baban Chinedu 31.03.2023

Send us Fan Mail Samun abin alheri na sa jama'a jin dadi har murnarsu ta bayyana. Kama daga daurin aure ko suna har ma da cin zabe, ko kammala karatu da sauransu.  Me yasa murna ke rikidewa ta koma tarzoma ko tashin hankali? Mene ne ke janyo yin asara ta dukiya da rayuka a wadansu lokuta yayin murna a Najeriya?  Shirin NAJERIYA A YAU na  wannan lokaci ya yi nazarin wannan batun lura da irin a...

Yadda Ake Shirin Kammala Zaben Gwamna A Adamawa 30.03.2023

Send us Fan Mail 'Yan siyasa a Jihar Adamawa sun kara tsunduma yakin neman zabe a karo na biyu sakamakon bayyana cewa za a gudanar da zaben cike gurbi Ranar 15 ga watan Afrilu in Allah ya kai mu. Ya ya 'yan siyasa Adamawa ke shirin shiga zaben cike gurbin da ke tafe? Shirin Najeriya A yau na wannan lokaci na tafe da karin bayani.

Matsin Tattalin Arziki Na Neman Hana Yin Burodi – Kungiya 28.03.2023

Send us Fan Mail Rahotanni sun tabbatar da cewa an rufe gidajen burodi sama da 200 a Jihar Yobe da ke Arewa maso Gabashin Najeriya. Shin mene ne dalilin da ya jawo rufe gidajen har 200 a wannan Jiha? Shirin Najeriya A Yau na tafe da karin bayani kan halin da ake ciki dangane da yin burodi a Najeriya.

Shin Umarnin CBN Na Dawo Da Tsoffin Kudi Ya Yi Tasiri? 27.03.2023

Send us Fan Mail Ranar Juma’a 24 ga Maris Babban bankin Najeriya CBN ya fara sakarwa bankunan kasar tsabar kudi, kuma ya umarcesu su yi aiki a ranakun Asabar da Lahadi.  Shin matakin da babban Bankin ya dauka ya yi tasiri? Ku biyo shirin namu na yau ku ji halin da ake ciki a Najeriya dangane da samun tsabar kudi a sassa daban daban na kasar. 

Ana Azumin Bana Cikin Mawuyacin Hali 24.03.2023

Send us Fan Mail Matakin CBN na sauya fasalin Naira 1000, Naira 500 da Naira 200 na cigaba da shafar rayuwar 'yan Najeriya kai tsaye.  Shin kun san yadda 'yan Najeriya suka fara azumin watan Ramadan a cikin wannan yanayi?  Saurari shirin Najeriya A YAU domin sauraron irin halin da 'yan Najeriya masu yin suka tsinci kansu a shigowar azumin Ramadan. 

Ta Ina Mamallaka Manhajojin Hada-hadar Kudi Ta Intatent Ke Samun Kudin Su? 23.03.2023

Send us Fan Mail Kasantuwar da dama cikin ’yan Najeriya masu hada-hadar kudi ta intanet sun fara gamsuwa da sabbin manhajojin hada-hadar kudi ta intanet. Shin ta ina masu wadannan manhajojin hada-hadar kudi ta intanet ke samun nasu kudin?  Lura da cewa wadannan manhajojin ba dukansu ke caji ba idan an tura ko an turo kudi, shirin Najeriya A Yau na tafe da karin bayani.    

Shin Kwankwaso Zai Kyale Abba Ya Yi Mulki A Kano? 21.03.2023

Send us Fan Mail Magoya bayan Jam’iyyar NNPP a Jihar Kano na ci gaba da murnar samun nasara a zaben gwamnan da ya gabata ranar Asabar 18 ga watan Maris. Yaya ake sa ran zaɓaɓɓen gwmana Abba Kabir Yusuf ya gudanar da mulki a Kano? Shirin Najeriya A Yau ya ji irin burin da Kanawa ke yi wa gwamnatin Abba, ya kuma ji yadda alakar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso za ta shafi mulkin.

Ko Tasirin Jam'iyyar NNPP Da Leba Zai Wanzu A Najeriya? 20.03.2023

Send us Fan Mail Jam'iyyar Leba da NNPP sun yi rawar a zo a gani a zaben 2023 a Najeriya, in an yi la'akari da yadda manyan jamiyyun kasar ke hana sauran jamiyyun rawar gaban hantsi a zabukan da suka gabata. Ko wannan tasiri da wadannan jamiyyu masu tasowa suka yi zai dore a zabuka masu zuwa? Shirin Najeriya A YAU na wannan lokaci ya dubi yiwuwar dorewar da abinda zai iya yi musu tarnaki...

Shin Sakamakon Zaben Shugaban Kasa Zai Shafi Na Gwamnoni? 17.03.2023

Send us Fan Mail Bisa al'adar zabe a Najeriya sakamakon zaben shugaban kasa yana tasiri a sakamakon zaben gwamnoni.  Amma a wannan karon anya sakamakon zaben shugaban kasa zai yi tasiri a zaben gwamnoni?  Shirin Najeriya A YAU na wannan lokaci ya dubi wannan lamari da idanun basira. 

Akwai Yiwuwar Sayen Kuri’a A Zaben Gwamnoni -Masana 16.03.2023

Send us Fan Mail Lura da yadda ’yan Najeriya suka wahala kan rashin tsabar kudi a kwanakin nan, shirin Najeriya A Yau ya yi nazarin abin da zai biyo bayan umarnin Kotun Koli na ci gaba da karbar tsoffin kudi da kuma ta yadda zai shafi zaben gwamnonin da ke tafe.  Shin kuna ganin dawo da amfani da tsoffin kudi zai ba da damar sayen kuri’a? 

Dalilan Yawan Tashin Gobara A Kasuwanni 14.03.2023

Send us Fan Mail Kasuwanni a sassan Najeriya na yawan samun gobara a baya-bayan nan, inda ake asarar dukiya ta biliyoyin Naira. Shin me ya kamata a yi domin magance wannan matsala? Shirin Najeriya A Yau ya duba wannan al’amari; ku biyo mu.

Ko Yaya Mulkin Tinubu Zai Kasance? 13.03.2023

Send us Fan Mail Ganin cewa jam'iyyun adawa sun samu kuri'u sama da miliyan 13 a zaben shugaban kasa da ya gudana ranar Asabar 25 ga watan Fabrairun 2023, shin yaya karfin adawa zai shafi tafiyar gwamnatin zababben shugaban kasar Najeriya, Bola Tinubu? Shirin Najeriya A Yau ya ji ta bakin wadansu da ba su zabi Tinubu ba a zaben da ya gabata ba, ya kuma ji ta bakin masana kan wannan maudu...

Yadda Dage Zabe Ya Dagula Lissafi 10.03.2023

Send us Fan Mail Dage zaben gwamnoni da 'yan majalisun jihohin da hukumar INEC ta yi daga ranar 11 ga watan maris zuwa ranar 18 ya shafi rayuwar mutane da dama, ciki harda masu shirin aure.  Ko mene ne ainihin dalilan da INEC ta dage zaben da mutane da yawa suke fatan a yi a gama su cigaba da harkokinsu? Saurari cikakken shirin domin jin yadda wannan mataki na INEC ya shafi rayuwar jama'...

Fadi-Tashin Gwamnoni Don Cin Zaben 2023 09.03.2023

Send us Fan Mail Gwamnonin da jam’iyyunsu ba su kai bantensu a jihoinsu ba a zaben shugaban kasa na fadi-tashin ganin ba a maimaita hakan ba a zaben gwamna da za a yi Ranar Asabar 11 ga Maris.  Anya wannan farga da gwamnonin suka yi bazata zama fargar jaji ba?  Shirin Najeriya A Yau ya dubi yadda gwamnonin da jam’iyyarsu ta fadi a jihohinsu a zaben shugaban kasa ke tunkarar zaben gwamna da ke tafe...

Muna So A Yi Zaben Gwamnoni Lafiya - ’Yan Najeriya 07.03.2023

Send us Fan Mail Zaben shugaban kasar Najeriya da ya gabata da kuma bayyana wanda ya yi nasara ya bar baya da kura. Wasu na ganin an yi magudi a zaben, don haka haka suke neman hakkinsu a gaban kuliya. To me ’yan Najeriya suke tsammanin gani a zaben gwamnoni da ke tafe?

Iyalan Wanda Sojojin Sama Suka Kashe A Funtua Na Neman Agaji 06.03.2023

Send us Fan Mail Iyalan wanda sojojin sama suka kashe a Funtua, Jihar Katsina na neman agajin kungiyoyin sa kai domin kwato musu hakkin jinin mahaifinsu da sojojin suka kashe a kwanakin baya.  Shin mene ne ke sa sojoji saurin farma fararen hula a kwanakin nan?  Shirin Najeriya A YAU ya bibiyi labarin kisan, ya kuma ji ta bakin mahukunta,  da kuma bukatar iyalan mamacin

Listen to the Najeriya a Yau podcast in Replaio

Radio and podcasts in one app - free, with no sign-up. Install today and do not miss the launch

Get it on Google Play

Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.