Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Where to listen?
Podcasts in the app Replaio Radio Coming soonPodcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts
Episodes
Yadda Zaben Shugabancin Majalisun Najeriya Zai Kasance 13.06.2023 13:52
Send us Fan Mail Yau Talata 13 ga Yuni, 2023 za a kaddamar da Majalisar Dokoki a Tarayyar Najeriya a karo na 10 a karkashin mulkin Dimokuradiyya. Yaya zaben shugabancin Majalisar Dokoki a Tarayyar Najeriya zai kasance? Saurari shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci, domin jin yadda za ta kaya.
Gwagwarmayar June 12 A Dimokuradiyyar Najeriya 12.06.2023 15:26
Send us Fan Mail Yau rana ce ta demukradiyya a fadin kasar Najeriya, wato goma sha biyu ga watan Yuni da kowa ya sani da June 12. An sha fama da gwagwarmaya kafin a kai ga yin zabubbukan ranar 12 ga watan Yunin shekarar 1993 da gwamnatin mulkin soja ta Ibrahim Badamasi Babangida ta soke. Shirin Najeriya a Yau ya tattauna da masanin harkokin siyasa da ya yi cikaken bayani tare da bayar da tarihin...
Yadda Ciniki Ya Yi Baya A Gidajen Mai Saboda Tsadar Man Fetur 09.06.2023 15:01
Send us Fan Mail 'Yan Najeriya, masu hannu da shuni da 'yan Rabbana ka wadata mu, na ci gaba da shan radadin tsadar mai sanadiyar cire tallafin mai da shugaba Tinubu ya yi daga hawa karagar mulkin kasar. Abin ya yi tsananin da har ma gidajen mai na kuka da karancin masu zuwa shan mai kuma yanzu haka a dole mutane sun fara canza salon mu'amalarsu da ababen hawa masu aiki da man fe...
Anya Kuwa Buhari Zai Iya Rayuwa A Daura? 08.06.2023 13:44
Send us Fan Mail Tun ranar 29 ga Mayun 2023 tsohon shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya koma garinsa na asali, Daura a Jihar Katsina. Lura da cewa shugaba Buhari da iyalansa sun kwashe shekara 8 a gidan gwamnatin tarayyar najeriya Villa, anya kuwa akwai kayan more rayuwa da zai iya rayuwa a Daura da su? Shirin Najeriya A Yau na tafe da karin bayani.
Shin Da Gaske Tinubu Ya Janye Tallafin Man Fetur? 30.05.2023 13:23
Send us Fan Mail Duba da cewa da yawa cikin 'yan Najeriya na ganin da tallafi man fetur su ke amfana kai tsaye. Me batun cire tallafin mai ke nufi, wane mataki kungiyar masu hada-hadar man fetur za su dauka, kuma ya ya 'yan Najeriya suka kalli wannan batu? Shirin Najeriya A Yau na tafe da karin bayani
Bukatun Al'ummomin Jihohin Arewa 4 Ga Sababbin Gwamnoninsu 29.05.2023 14:40
Send us Fan Mail Yau Litinin 29 ga watan Mayu, za a rantsar da sabon shugaban kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu tare da mataimakinsa Kashim Shettima, kuma a yau din ne suma sababbin gwamnonin jihohi ke yin rantsuwar kama aiki, a cikinsu akwai wadanda aka zaba a karon farko a matsayin Gwamnoni a Arewa kuma a karkashin tutar wata jam’iya ta daban da wadda ta yi mulki a jihohinsu. Ko wace fata al&ap...
Dole Gwamnatin Tinubu Ta Fara Neman Amincewar Duka 'Yan Najeriya - CNG 26.05.2023 14:58
Send us Fan Mail Akwai jan aiki a gaban gwamnatin Bola Ahmed Tinubu inji wani jigo a Gamayyar Kungiyoyin Mutanen Arewa, CNG, sannan ya bayar da shawarwari game da yadda sabuwar gwamnati za ta fitar da jaki daga duma. Kwamred Jamilu Aliyu Chiranci ya yi tsokaci game da rawar da yankin Arewa ya taka wajen kai Bola Ahmed Tinubu ga cin zabe, haka kuma ya yi gargadin cewa a rabon mukamai ya zama wajib...
Yanayin Tattalin Arzikin Da Buhari Zai Bar wa Tinubu. 25.05.2023 15:39
Send us Fan Mail Tattalin arzikin Najeriya da na ‘yan kasar na daga cikin bangarorin da gwamnatin Shugaba Buhari ta ce ta mayar barin gado ta mai da hankali wajen ingantawa; Ko tattalin arzin naku ya samu ingantuwa kuwa? Shirin Najeriya A Yau ya dubi irin yanayin tattalin arzikin da Gwamnatin Buhari za ta bar wa wadda za ta gaje ta.
Fatan ’Yan Najeriya Kan Harkar Tsaro A Gwamnatin Tinubu 23.05.2023 13:36
Send us Fan Mail Me ’yan Najeriya ke son ganin Gwamnatin Bola Tinubu mai jiran gado ta yi wajen magance matsalar tsaro da ta ke ci ki, ta ki cinyewa a kasar. A yayin da Shugaba Bola Tinubu mai jiran rantsuwa ke shirin kafa aiki daga ranar 29 ga Mayun da muke ciki, tabarbarewar sha’anin tsaro na daga cikin manyan matsalolin da Gwamnatin Shugaba Buhari mai barin gado za ta bar masa. Sin zai iya shar...
Ko Sabuwar Gwamnati Za Ta Iya Hada Kan ‘Yan Najeriya? 22.05.2023 14:53
Send us Fan Mail Nan da kwanaki 7 za a rantsar da sabuwar gwamnati a Najeriya wadda za ta karbi mulki a cikin wani yanayi na kalubalen da sai shugabanni masu kwarewa da sanin makamar aiki za su iya saita kasar da dinke baraka da kuma sake hada kan yan kasar su koma al’umma daya. Shirin Najeriya A Yau ya tattauna da masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa da mulki, ya kuma baiwa masana dama sun to...
Yadda Kishi Ya Sa Matar Aure Farka Cikin 'Yar Makwabta Da Wuka 19.05.2023 14:08
Send us Fan Mail In da ranka, ka sha kallo! Yanzu haka ‘yan sanda a Jihar Kano suna farautar wata matar kan zargin ta farka cikin wata karamar yarinya ’yar makwabtansu da wata zabgegiyar wuka, bayan da ta dauki yarinyar a hannun iyayenta, da sunan za ta raka ta unguwa. Ina dalilin wannan danyen aiki da matar ta yi wa wannan karamar yarinya? Wakilanmu a Kano sun bin diddigi sun samo cikakken baya...
Yadda Zaben Shugaban Majalisar Wakilai Zai Shafeku 18.05.2023 14:56
Send us Fan Mail Zaben shugabancin majalisar wakilai ta Najeriya da za a gudanar a tsakiyar watan Yunin da ke tafe daya ne daga cikin batutuwan da ke daukar hanakalin ‘yan Najeriya. Ta wadanne hanyoyi shugaban majalisar tarayya ke shafar 'yan Najeriya? Shirin namu na wannan lokaci ya dubi lamarin ta mahanagar masana.
Shin Noma Zai Yiwu Ba Tare Da Takin Zamani Ba? 16.05.2023 13:29
Send us Fan Mail Tsadar takin zamani daya ne daga cikin matsalolin da ke ci wa manoma tuwo a kwrya a Najeriya. Shin noma zai yiwu ba tare da takin zamani ba? Shirin Najeriya A Yau ya dubi ko zai iya yiwuwa a yi noma ba tare da amfani da takin zamani ba.
Yadda 'Yan Najeriya Za Su Ci Moriyar Bankin Musulunci 15.05.2023 12:09
Send us Fan Mail Bankin Raya Musulunci IsDB ya kirkiro wadansu hanyoyin habaka tattalin arziki ga 'yan Najeriya domin yakar talauci da bunkasa harkokin kasuwanci da noma a kasar. Shin ta wadanne hanyoyi za ku amfana da wadannan tsare-tsaren? Shirin Najeriya A Yau na tafe da karin bayani.
Nakan Yi Yaji Saboda Tsabar Shan Duka Daga Matata —Maigidanci 12.05.2023 14:45
Send us Fan Mail Shirin Najeriya A Yau ya tattauna da wani magidanci, wanda ya bayyana yadda matarsa ta sha yi masa dukan kawo wuka, har ta kai ga yana yin yaji ko ya kirkiri tafiya domin ya samu sauki. Akwai kuma labarin wanda shi kuma matarsa ba cin zalinsa take yi ba kawai, har shigowa unguwarsu ta hana shi. Mun kuma tattauna da ’yan kallo da masana shari'a kan abin da doka ta tanada kan i...
"Yadda NYSC Ta Canza Rayuwata" 11.05.2023 15:12
Send us Fan Mail Ranar 22 ga Mayun da muke ciki tsarin hidimar kasa ta NYSC zai cika shekaru 50 da kafuwa. Ko kwalliya tana biyan kudin sabulu? Shirin Najeriya A Yau na tafe da tattaunawa ta musamman tare da wadanda suka yi hidimar kasa a farko-farkon tsarin.
Abin Da Ya Kamata 'Yan Najeriya Su Koya Daga Rikicin Sudan 09.05.2023 14:41
Send us Fan Mail Yakin da aka dauki kwanaki ana tafkawa a kasar Sudan ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama, ya kuma janyo hasarar dukiya mai tarin yawa. Ko wane darasi Yakamata gwamnatin Najeriya da kuma 'yan Najeriya su koya? Shirin Najeriya A Yau na tafe da karin bayani kan rikicin Kasar Sudan, da kuma shawarwari kan darussan da ya kamata a kowa.
Yadda Kamfanin Jiragen Saman AA Rano Zai Shafi Tattalin Arzikin Najeriya 08.05.2023 13:35
Send us Fan Mail Mai gidajen man fetur na AA Rano ya kaddamar da tashin jiragen saman kamfaninsa na Rano Air Lahadin nan a Jihar Kano, bayan an kwashe shekaru uku ana shirye-shirye. Shin ta wadanne bangarori wannan kamfani zai shafi tattalin arzikin Najeriya? Shirin Najeriya A Yau na tafe da karin bayani.
Inda Aka Kwana A Jigilar Yan Najeriya Daga Sudan 28.04.2023 15:07
Send us Fan Mail Gwamnatin Najeriya ta fara jigilar yan Najeriya mazauna kasar Sudan bisa kulawar Hukumar Bada Agajin Gaggawa Ta Kasa, NEMA. Me ake ciki kuma ina aka kwana game da kwaso yan Najeriya zuwa gida daga Sudan? Shirin Najeriya A Yau na tafe da karin bayani.
Abin Da Ya Hana Mata Samun Nasara A Zaben 2023 27.04.2023 14:23
Send us Fan Mail Mata 1,553 ne suka yi takara a zabukan 25 ga watan Fabrairu da 18 ga watan Maris na 2023. Mene ne ya hana matan samun nasarar a zo a gani a zaben da ya gabata? Shirin Najeriya A yau na tafe karin bayani kan dalilan da suka hana matan kaiwa ga nasara.
Dalilin Jinkirin Kwaso ’Yan Najeriya Daga Sudan 25.04.2023 15:18
Send us Fan Mail Yau Talata 25 ga Watan Afrilun 2023 ake sa ran fara jigilar daliban Najeriya 5000 daga kasar Sudan. Mene ne ya janyo jinkirin zuwa debo ‘yan Najeriya daga kasar Sudan? Shirin Najeriya A Yau ya bi kwakkwafin batun, ku biyomu sannu a hankali a cikin shirin.
Sankarau Ta Kashe Mutum 118 A Najeriya, Abin Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Cutar 24.04.2023 14:36
Send us Fan Mail Cibiyar Yaki da Cututtuka ta Najeriya NCDC ta bayyana cewa kawo yanzu an samu mutane 235 da aka tabbatar sun kamu da cutar sankarau a Najeriya, sannan ana zargin mutum 1,479 sun kamu da cutar. Mene ne ka sani game da cutar sankarau? Shirin Najeriya A Yau na tafe da bayanai daga bakin masana kan wannan cuta, da hanyoyin guje mata.
Azumi Da Habibi Dadi Kamar Aljanna —Amarya 21.04.2023 14:29
Send us Fan Mail Daga cikin abin da ya fi daukar hankali a Najeriya a cikin watan Azumin Ramadan akwai yadda sabbin ma'aurata suka rika zumudi da nuna farin ciki a kafafen sadarwa na samun yin azumi da masoyansu wuri guda a karon farko. Shin ya ya wadannan sabbin ma'aurata suka yi azuminsu na farko tare da juna? Shirin Najeriya A Yau ya tattauna da wadansu sabbin aure, ya ji yadda azum...
Yadda Matasa Suka Taka Rawar Gani A Zaben 2023 20.04.2023 15:03
Send us Fan Mail Masu nazarin harkokin siyasa sun bayyana zaben 2023 a matsayin zaben da ya bai wa matasa dama fiye zabukan da suka gabata a kasar. Mene ne ya bai wa matasa da dama nasara a zaben na 2023? Shirin Najeriya A Yau na tafe da karin bayani akan wannan batu.
Abin Da Zai Faru Idan An cire Tallafin Man Fetur A Watan 6 18.04.2023 14:55
Send us Fan Mail Gwamnatin Najeriya za ta baiwa magidanta masu karamin karfi miliyan 10 Naira dubu biyar-biyar daga watan Yuni in an cire tallafi man fetur baki daya. Yaya rayuwa za ta kasance idan an cire tallafin? Shirin Najeriya A yau na tafe karin bayani kan wannan batu.
Similar podcasts
Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.